Advertisements
Chapter 6 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   6 / 51

15K to 18K   out of 151K words

a ranta. Wai itace zatayi aure? Su duk bikin da akayi a gidansu babu wanda akayi party, harna matan, amman ana shirya Kamu, wannan Abba baya hanawa tunda taron mata ne, ko 'yan uwansu maza basa zuwa wajen. Kuma yana kayatar da ita, sai dai haka kawai taji inda ace za'ayi partyn ma tanaso, ko irin wannan kamun da sukazo, akwai maza da mata a wajen, sannan ita Munira din tasha shigarsu ta gargajiya ta Kanuri, a karo na farko tayiwa Maryam kyau, ga angon daya riko hannunta shima ya hadu, bakine kamarta, dogo sosai, dan duk da takalman da Munira tasa kanta bai karasa kafadarshi ba.

Itama ace haka zasu shigo wajen taro da nata angon, kuma wai saiga tunaninta ya hasko mata Ishaq, zuciyarta tayi wata irin bugawa, musamman data hangeshi da farar shadda kal, ya zaiyi a cikin fararen kaya? Tama taba ganinshi da fararen kaya kuwa? Zata so ta ganshi da fararen kaya, ta tabbata zaiyi kyau.

"Yau sai Munira tayi mun kama da Haris"

Wata da suke zaune a teburi daya ta fada, dan Maryam ta zauna inda Adda Aliya take ne

"Kai haba dai? Aisu suna kama da Baba ne kamar mu, shikuma Haris kamarshi daya da Mami..."

Cewar Adda Aliya, maganganunsu na kutsawa cikin tunanin Maryam, sai ta sake kallon Munira, ta kuma kalli Adda Aliya da take jajur kamar ka taba jini ya fito, dariya ta kusan kwace mata, taya ma za'ayi ace suna kama da juna? Ko kuma ita Munira na kama da Baba, ko dai ba Baban Tudun Wada take nufi ba? Kawai dai tace daga Munirar har sauran 'yan uwan nata, dashi Haris din na kama da Mamin shine abinda zaifi kama hankali.

"Wai baizo ba Haris din?"

Adda Aliya ta girgiza kai

"Ba zai samu damar zuwa ba, yana Italy"

Tunda Mami bata gajiya da fadawa duk wanda zai saurara cewa Haris baya kasar tun da ya tafi, har sun gaji, musamman da aka fara taron nan, zakaji tana

"Dan kiramun lambar Haris, ta Italy din"

Abinma dariya zai baka, in kaga yanda takeyi sai kayi zaton akwai bakon ketare Najeriya a cikinsu, musamman ita Hajiya Rumanan da karatunta ma kacokan a kasar waje tayi, ko dan Haris din ya zamana mutum na farko daya bar kasar da sunan karatu shisa abin yakeyi mata dadi oho. Maryam dai baki ta tabe, in ba dole ba ko maganarsu batason ji, tasan matar ba wani sonsu takeyi ba, koma tace ba son kowa takeyi ba, itama kuma batare da wani dalili ba tun asali batayi mata ba, daga ita har bakaken 'ya'yanta.

6

HARIS

"Hello Babaa"

Kalmomi biyu ne kacal, amman a wajen Haris suna da nauyin kalmomi dubu da doriya, har so yakeyi inya furta wani ya juyo ya kalle shi, shikuma ya fadada murmushin da baya barin fuskarshi, kamar yace

"Babana ne, Babana ne ya kirani, da Babana nake magana"

Shi baisan adadin son da yakeyiwa Alhaji Mustafa yana da yawa har haka ba sai yanzun, bambancin awa dayane tsakanin lokacin kasar Italy da kuma nan Najeriya, sunfi waya da daddare, a lokacin bayan isha'i a wajen Alhaji Mustafa, a wajen Haris kuma karfe tara ne da wasu 'yan mintina

"Ya makarantar? Ba dai ka bukatar komai ko?"

Haka zasu kusan awa suna waya Haris na bashi labaran darussan da akayi musu a ranar batare daya tabbatar ya fahimci duka abinda yake fada din ba, shekaru biyu ake neman hadawa yanzun, amman harshen shi ya riga ya fara sauyawa ta yanda ko waya yakeyi da 'yan gidansu saiya dinga tsintar kanshi da jefo kalmomi da yawa da yaren kasar, tunda ko turanci ba sosai yake shiga tsakaninshi da Logan bama, shima yaren yakeyi masa kamar kowa na kasar. Idan gidan Alhaji Modu yaje can dinma bata sauya zani, mafi akasarin zuwanshi saboda Aise ne.

Tun randa ya fara ganinta batayi masa kama da 'yar shekara sha uku ba, yanayin jikinta, maganganunta da wayonta duka, yanzun kuma a shekaru goma sha biyar, Aise tasan me take so tayi da rayuwarta, tana da wani irin wayau da baisan ko halittarta bane ko kuma yana da alaka da tashin da tayi a kasar waje. Soyayyar daya sani ba wata mai yawa bace ba, shisa ya tabbatar da abinda yakeji akan Aise soyayya ce, irin soyayyar nan da bata bukatar a zurfafa tunani a cikinta, ko wata mace ta burgeshi saiya tsinci kanshi da hasaso Aise yana hadata da wannan, yana kuma tsince bambancin da yake tsakaninsu. Yanda suke kiran Binta da Mamma shima haka yake cewa, Alhaji Modu ne kawai yake kira Uncle saboda ya riga ya saba haka yake ce masa.

Sun hadu da Kham, haduwa marar adadi, shima bashi da wata matsala. Da yake ma ba hayaniya yake da ita ba, ba miskili bane ko wani abu, kalmomin shine ba masu yawa ba, zaku iya wuni tare da Kham yana danna waya baice maka komai ba. Shisa ranar da ya fita wani dan lambu da Mamma take dashi a bayan gidan, yana busar hayakinshi, ko da Kham ya same shi a wajen baiji dar ba, shima kallo daya yayi masa ya dauke kai yana cigaba da wayar da yakeyi, harkar duk da bata shafi Kham ba baya shigarta. Da yake Mamma na aiki, itama tana wuni bata gidan, in yazo sai dai ta barsu su kadai shi da Aise inta dawo makaranta, yasha ganinsu Haris na zaune akan kujera, Aise tana kwance tayi pillow da cinyarshi, ko kuma tana zaune amman ta nade jikinta ta kwantar a nashi, sai anyi sa'a ma yake musu magana in ba wani a cikinsu ya gaishe dashi ba.

Har a zuciyar Haris babu wani abu banda tarin soyayyar Aise da burikan da yake dasu a kanta, in zai rike hannunta sau hamsin wani tunani bai taba gifta masa ba, kawai tana cikin matan da yakejin yana son karewa daga wani abu da bai kamata ba, ciki kuwa harda shi kanshi da gurbataccen tunanin da zai iyayi, sonta yake, so na gaske. Amman ranar da Mu'adh din daya manta sunanshi ya diro kasar Italy, bama a jikinshi yaga Aise ba, a tsaye suke, da tufa a hannun Aise din da take ci, sai yake kokarin karba, ya kwace ita kuma ta riko masa hannu, wani irin kallo ya watsa mata daya sata sakin hannun Haris babu shiri, kafin ya fara mata fada cikin harshen larabci, ta wuce da sauri idanuwanta cike taf da hawaye

"Haris?"

Cewar Mu'adh yanayi masa wani kallo mai cike da fassara kala-kala, sai Haris din ya harde hannayenshi a kirji shima yana zuba masa nasa idanuwan batare daya amsa tambayar da yaji a muryar Mu'adh din ba

"Karka sake riketa, ina nufin karka sake tabata, ina fada maka ne saboda ita ba zata sake ba, kai ya kamata ace ka zama mai hankalin..."

Da yaren Italian yayi masa maganar, yana kuma wucewa batare daya jira amsar Haris din ba. A wannan ranar Mu'adh ya shiga cikin jerin mutanen da Haris baya so, kamar yanda ya shiga jerin na Mu'adh din. A shekaru biyun nan da baizo gida ba, babu wani labari na Haris da baiji ba a bakin Aise, a yanayin yanda take bashi labaran ne kuma ya karanci cewar Haris ya wuce matsayin dan uwa a wajen Aise, Haris yana burgeta, shikuma hakan bai kwanta masa ba, yanzun daya dora idonshi akan Haris dinma sai ya kara fita daga ranshi. Daya gama shiryawa yayi wanka ya sake kaya, yaso ya dan fita ne ya nemi abinda zaici, amman bayason barin Aise ita kadai a gidan, kar Haris daya fita ya sake dawowa.

Ita yaje ya samu tayi masa order din abinda zataci, yasan wacece kanwarshi, wata nasiha ko lallami baya aiki a kanta, shisa ya fito mata sak, yaja mata kunne sosai akan zasu raba hanya, zai bata da ita idan ya kara ganin ko da dan yatsanta ne ya kai jikin Haris, harda hawayenta ta dinga bashi hakuri, dan sunfi shakuwa dashi akan Kham. Da Mamma ta dawo ma da fara'arta shi Mu'adh ranshi a bace yake

"Mamma Aise takai shekarun da komu 'yan uwanta idan ba lalurar data zama dole ba, bai kamata ace ana barinta a gida daga ita saimu ba balle wani wanda ba Muharraminta ba..."

Tayi murmushi, a kasar Italy ta haifi duka yaranta, sunyi kokari wajen saka su a Islamiyyar da suka samu, sai Mu'adh yafi kowa maida hankali akan addini, tun tasowarshi yake da son addini matuka, haka yake yawan fada musu cewa shi burinshi ya zama daga cikin manyan Malaman da za'a bada labarinsu wata rana na cewar sunyiwa addini hidima, haka zai dinga saka su a gaba da wa'azi in yaga sunyi wani abu daya sabawa addini, ita kanta Mamma din, kudi da wayewa yayi tasiri a kanta kamar dai mijinta, Mu'adh ne yayi tsaye wajen ganin tana suturta jikinta yanda ya kamata, hakama ya hanata karin farce, da yake macece mai son yaranta kuma mai saukin fahimta da karbar kuskure idan an gyara mata

"Za'a kiyaye Ustaz Mu'adh, kaga shi Haris dinma bawai yana zaune anan din bane ko yaushe, yana makaranta abinshi, sai yayi watanni baizo ba, in yazo dinma baya wuce kwana biyu"

Ya dan saki fuska

"Ko yini yakeyi bana sonshi su kadai a gida, dan Allaah Mamma"

Ta sake fadada murmushinta

"Ai nace za'a kiyaye, zo nan, kanata mita ko gaisawa ba muyi ba"

Shima murmushin yayi ya karasa yana rungumarta hadi da sumbatar goshinta da kunci tukunna ya zauna a gefenta.

*

Washegari da yamma Haris yayi musu sallama ya dauki jakarshi, wani coffee shop suka samu shi da Aise da sun riga sunyi magana zasu hadu a wajen saboda Mu'adh, ta kasa hakuri saida ta rungume shi kafin suka zauna

"Nasan dukanmu muna da tarin abubuwan da suke gabanmu, ban taba furta miki ba, amman banajin ina bukatar ince miki ina sonki Aise, ba so bane da nake so mu fara shi batare da ya kaimu ko ina ba, ina miki son da duk wani plan da nake dashi saina hango ki a ciki...amman bamu da lokacin wannan soyayyar a yanzun, duk mun sani..."

Ta daga masa kai, zatayi karya idan tace bata taba son wani, ko wani ya burgeta ba, aiko a ajinsu ma tayi samari wajen hudu suna batawa, hakama wanda suka wuceta aji, duka ma babu musulmi ko daya a ciki, sai dai wannan soyayyar shiririta ce akan abinda takeji kan Haris, idan taga biki, idan ana maganar biki, ita dashi take hangowa tare anayin nasu, kamar yanda yace tana cikin plans dinshi itama yana cikin nata, tana ji a jikinta soyayyarsu bata bukatar gaggawa, a hankali za subi komai, yanzun ne zata gama high school dinta tunda tana finals nema, kuma fannin data zaba na lafiya fanni ne da tasan yana bukatar duka natsuwarta, ba zata samu lokacin rabashi da wata soyayya ba

"Ina so insan cewa Mu'adh baya cikin abinda zai bani matsala dake Aise, ina so in san wannan"

Idanuwanta ta saka cikin nashi

"A yanzun, ko a gaba, ko da Mu'adh baya sonka in dai ni ina sonka baka da matsala"

Haris ya sauke numfashin da baima san yana rike dashi ba, wannan maganganun da tayi zasu rikeshi, sunma isheshi a yanzun.

Ta ina ita dashi zasu hango suna bukatar Mu'adh din?

Sunfi awa daya suna ta hirarsu da bata taba karewa, tukunna yayi suka fito kowa ya kama hanyarshi tunda daman makaranta zai koma, ita kuma zatayi gidane. A halin yanzun dai, a wajen Haris bayajin yana da wata matsala ko guda daya, zasuyi waya da Alhaji Mustafa kullum, zasu hira, haka ma Hajiya Rumana. A cikin hirarrakin nasu nema Alhaji Mustafa yake yawan nuna masa yanda yake son ace yana magana da sauran 'yan uwanshi kamar yanda yakeyi dasu Munira. Yaji wani yanayi ya saukar masa, shifa in suna da wayoyi ma to bashi da lambarsu

"Bani da lambar kowa a cikinsu Baba"

Suna gama wayar ya aika masa da lambar Aliya, sai dai yaji nauyin ya kirata, ya tura mata da sakon text yana gaya mata shine tayi saving lambarshi, kamar kuma a lokacin wayar na hannunta ta maida masa da reply harda godiyar nemanta da yayi, saida murmushi ya kwace masa. Daman haka mutum yakeji a lokacin da baya hangowa kanshi kowacce irin matsala? To daga matan har wiwin shi babu wanda yakeyi masa wahalar samu in bukatarsu ta taso, gashi abinda ranshi yake so shine yake karanta, duk sanda zaiji camera a hannunshi nishadin da yake shiga ba dan karami bane ba. Sannan a gefe guda, nan da wasu 'yan shekaru in yaso ya natsu waje daya, da mace daya, ya samu nashi iyalin juyawa kawai zaiyi ya mikawa Aise hannun shi.

Ko kadan baiyi hasashen akwai yiwuwar idan ya mika hannun wata daban ta saka nata a ciki ba...

Yanda Haris yake a kasar Italy yana hango filin rayuwarshi sambal batare da komai da zai iya cin karo da mafarkanshi ba, haka Maryam take nan gida Najeriya, garin Kaduna da nata mafarkan da take tattaunawa da 'yar uwa kuma mutum daya tilo da zata bugi kirji ta kira da kawarta, wato Khairi

"Nifa idan zan samu gurbin karatu a BUK zanfi son hakan, kinga sai inyi BSc dina a Midwifery ba saina wahala ba..."

Khairi ta jinjina mata kai

"Nifa irin wahalar da naga su Adda sunci wajen neman BUK yasa gwiwata tayi sanyi, sannan banason in tsaya jiran wata university bansan ko ina da kaddarar auren wuri ba, kaje karatu ya hade maka da hidimar gida ko mijin ma ya hanaka karatun, yar diplomar nan ta gagareka hadawa"

Sai kawai Maryam ta kwashe da dariya

"Meye abin dariya yanzun?"

Cewar Khairi

"To ai wani zancen naji kinayi, wai miji ya hanaka karatu..."

Muryar Khairi da damuwa tace

"Wallahi anayi fa, kinsan Mansura ta ajinmu ai? To yayarta da tayi aure haka mijin yace ba zata kara zuwa makarantar ba, gashi tana level 2"

Da madaukakin mamaki Maryam take kallon Khairi

"Wai da gaske? To ita kuma sai ta daina zuwan? Saboda bata da hankali...lallai ma, tafdin, ya latsa yaji da laushine shisa..."

Khairi ta kalleta kawai

"In yace ba zataje ba sai tayi yaya? Ai dole ta hakura, mijinta ne fa"

"Mijinta ubanta ne? Ko shine yake biya mata kudin makarantar da zaice ya hanata karatun? Ai na gaya miki, raini ne kawai ba wani abu ba, Astagfirullah waye ya isa yayi mun wannan latsin..."

Tunda duk matan gidan nasu da sukayi aure batare da sun karasa karatunsu ba, har yanzun Alhaji Sa'id ne yake daukar duk wata dawainiya tasu data shafi makarantar, ko da kuwa mazajen sun nemi zasuyi baya yarda, kowa a gidan ya sani, shisa ita Maryam tayi tunanin duk wata mace da take cigaba da karatunta bayan aure kawai iyayenta ne suke daukar dawainiyar karatun nata.

"Ke dai kiyi shiru da bakinki, kuma karki tsaya jiran wata university...duk inda kika samu kawai ki karba kiyi karatun shine mafi muhimmanci"

Maryam ta tabe baki

"Aiko dai ban samu university ba kinsan ba zan fada ko ina ba saboda inaso inyi karatu ko in fara kafin inyi wani aure..."

Asiya data shigo kitchen din ta samesu ta katse maganar ta hanyar kaiwa Maryam din mangari,fere dankali Hajja ta sakasu, suna zaune dirshan a kitchen din

"Firar dankalin kenan, wato ku 'yan tsigi-tsigi daku har kunsan wani zancen aure"

Maryam ta makawa Asiya harara kamar idanuwanta zasu fado

"Kinga Adda banason irin abin nan, na gaya miki, Abba ma yace ki daina mun, yanzun idan nace zan rama sai kuma kice nayi miki rashin kunya"

Wani mangarin Asiyar ta sake kai mata tana kaucewa hadi dayin maganganu kasa-kasa

"Zagina kike ko? Sai naci kaniyarki ai, marar kunya, ke kuma Khairi harda ke kuke hirar aure ko? Saina fadawa Hajja"

A tsorace Khairi tace

"Wallahi ba wani abu marar kyau mukace ba Adda, muna hirar makaranta ne nake ce mata gara duk inda muka samu mu tafi..."

Nan Khairi ta kwashe maganganun da sukeyi din ta fada mata

"To ku ko auren ne yazo meye zai dameku? Waye kuka taba ganin a gidan nan anyi masa aure bai cigaba da karatunshi ba? Ai kunsan Abba ba zaiyi muku haka ba, ke Maryam ma ai baki da wata matsala tunda na gidane"

Su duka suka daga ido suna kallon Asiya saboda yanayin yanda ta karasa maganar da wata dariya

"Bangane bani da matsala ba? Meye na gida?"

Dariyar dai Asiya ta karayi

"Ba Yaya Ishaq bane ba? Ai kinsan babu yanda za'ayi ya hanaki karatu"

Zuciyar Maryam ta buga, ta kara bugawa, ta tsaya cak da firar dankalin dan a yanda jikinta ya amsa da maganar Asiya tsaf zata iya fere yatsa a maimakon dankalin

"Shi Yaya Ishaq dinne yace ni zai aura?"

Ta tsinci kanta da tambaya cikin wata karamar murya

"Kunji dashi dai, inya gama zagaye-zagayen saiya fada miki da bakinshi, ai inajin kowa ma yasan zaryar da yakeyi tsakanin Zaria da Kaduna taki ce a gidan nan, wani zuwa yakeyi da?"

Asiya ta karasa tana daukar saka hannu cikin robar da suke zuba dankalin hausar ta tsami guda biyu manya ta fice daga kitchen din, Khairi data kasa daina murmushi tace

"To kinga saiki fara girmamani kina yimun biyayya yanzun tunda zamu zama surukai"

Duk da maganar ta saukarwa da Maryam din wani irin sanyi, har saida ta kasa boye murmushinta, sai tace

"Ko ba surukai ba? Kema yarda zakiyi da maganar Adda? Yaushe Yayan yace zai aureni? Kuma ko da mun zama surukai ai kece zaki dinga ce mun Anty ma tunda zan zama matar yayanki"

Khairi ta dibi ruwan dankalin da hannu tana watsawa Maryam da take dariya, haka kawai farin ciki ya gama mamayeta, tasan da gaske ne yanzun Ishaq na yawan zuwa gidansu, ko da kwana daya ne kuwa, kuma haka zaizo falo yayita janta da magana, tun tanajin nauyinshi saboda abinda takeji in yana mata maganar har yanzun ta fara sabawa dashi, amman aiko da alama bai taba nuna mata wata soyayya ba? Ko dai itace batasan soyayyar ba? In dai irin wadda akeyi a littafi ce bata ga alamarta a tare da Ishaq ba, haka ta film ma, yafi kulata akan Khairi tabbas, amman ai a cikin littafi haka saurayi zai dinga shakaro siyayya iri-iri yana kawowa budurwar da yake so ko da bai furta mata ba.

Shikuwa me ya taba siyo mata? Sai wata zuciyar ta saka mata ai shidin dan makaranta ne, yanzun nema zai shiga aji uku, meye zai siyo ya kawo mata tunda bashi da aiki, har Hajja ma ta ga idan yazo tana

6 / 51