Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
yanzun. Ba zata fara aro jarumtar da tasan bata da ita ba in dai akan Haris da Aise ne, saboda bayan kaddarar auren Haris, Allaah Ya kara jarabata da soyayyarshi, so takeyi masa da dukkan zuciyarta, irin soyayyar nan da zuciya zata dinga yiwa wanda take so uzuri batare da gajiyawa ba, amman akan Aise dai har zuciyar ma ta nuna mata ba zata iya dauka ba.
"Waike baya fada miki ba zai aureta ba? Me yasa ba zaki cire tunanin nan daga zuciyarki ba?"
Khairi ta fadi a hankali, Maryama ta share hawayen da sai lokacin suka zubo mata
"Na kasane Adda Khairi, yana sonta, ko musu baiyi mun akan yana sonta ba har yanzun...a rashinta ne fa aka bashini ya karba saboda babu yanda zaiyi...ni din da ba auren soyayya mukayi ba ki kalli yanda yake zaune dani, kuma da kuke 'yan uwana kalli yanda yakeyi muku...idan kuma yau akace wadda yake so ce ya auro fa? Kingane abinda nakw tsoro Adda? Kingane fargabata yanzun?"
Shiru Khairi tayi cikin rasa abin fadi
"Ganja ya iya kula da abinda yake so Adda, yanzun nake gane ko da na kamashi da wata, na hakura ne saboda ina da tabbacin ba soyayya ce ta hadasu ba, inajin mutuwa zanyi idan ya auro Aise, in ban mutu ba kam zai wahala ban hakura na bar mata shi ba tunda daman kaddara ce tayi musu katsalandan"
A tausashe Khairi tace
"Duk ma hakan ba zai faru ba In Shaa Allaah, ki cigaba da addu'a, kuma kiyi kokarin cire tunanin daga ranki, kinsan dai ba'a son masu ciki da yawan tunani"
Da
"Hmmm"
Maryama ta amsa, amman har ranar juma'ar nan inta kalli Haris ta hangoshi da Aise sai taji komai ya fice mata a rai, shima sai taji haushinshi ya turnuketa kamar ta shakareshi ta huta. Haka suka kwanta, amman tun cikin daren takejin bayanta ya riqe, tana tashi zaune Haris na bude idanuwa shima ya kuma kunna kwan dakin haske ya gauraye ko ina
"Ya akayi? Bayan ne?"
Ya tambaya tunda a satin ma gabaki daya ciwon bayan ya dameta, ta wuce Edd dinta na farko da kwana takwas, kai ta daga masa, a asibiti likitarta ta nuna masa yanda zai dinga taimakawa yana yi mata tausar bayan in yana mata ciwo. Haka suka kwana, basu koma bacci ba sai bayan da sukayi sallar asuba. Ta riga Haris tashi, lokacin karfe tara da wani abu, ta lallaba tayi wanka, ta saka wata doguwar rigar material dinkin bubu, kitsone, zanen hausa a kanta guda shida, yau kwana uku ma dayi mata shi, wata budurwa ce, kabila, amman musulma a saloon din da take zuwa, yarinyar ta iya kitso sosai, shisa ta karbi lambarta, sai take zuwa gida tanayi mata, kusan wuni sukayi ana abu daya, dan sai anayi ana tsayawa saboda ciwon bayan daya dami Maryama
"Gaskiya a hakura da kitson nan"
Haris ya fada daya dawo ya sameta tana zagayen daki, lokacin guda biyu akayi
"Haka zan shiga dakin nakuda da kai babu kitso? Salon azaba ta isheni inta cisgar kan in rasa na parking ko? Kazo kace zaka karo aure tunda ni bani da gashi"
Dariya yayi sosai ganin yanda take maganar da dukkan gaskiyarta, dakyar aka gama kitson data kira na shiga labour room. Kitchen ta shiga, yunwa takeji sosai, kwai kawai ta soya ta hada shayi ta dauko biredi, tana cikin karyawa Haris ya fito, shima yayi wankan, da gajeran wando baki a jikinshi sai singlet baka, sanin su kadaine a gidan. Da kanshi yaje ya hado shayi ya dawo falon ya zauna yana sha, tama daina wahalar da kanta wajen yi masa magana kan abinci, takaicinta daya, yanda a cikin yaran Rauda ce take gudun abinci kamarshi, gata nan sai kace tsinke, lokacin data yayeta haka suka sha fama, ta dinga bushewa saboda sai an matseta ake dura mata kunun alkama, shima ganin yanda take sharara amai yasa Maryama ta hakura ta kyaleta, duk wani multi-vitamin ta karbo mata a asibiti, amman tana nan tsigai-tsigai sai kace bulala. Sai dogon hanci irin na Haris din, amman ita bata kai su Awwab baki ba.
Har dariya take yiwa kanta idan ta tuna wai itace take auren bakin namiji kamar Haris, ta kuma goya bakaken yaranshi, balle kuma inta tuno yanda take tunanin babu namiji me kyan Ishaq a zamanin kuruciyarta saboda farinshi, shima yayi aure suna zaune a Lagos da matarshi saboda acan yake aiki, ta ganshi wajen sau biyar, suka gaisa tanata mamakin abinda ma taso a tare dashi, musamman yanda ya narka wata irin kiba harda tumbi, ganin da tayi masa na farko bayan aurenta ne ranar data fara ganin kyan Haris, ta dinga kallonshi bayan ta dawo gida, shafaffen cikinshi tana addu'ar Allaah Yasa kar yayi tumbi irin na Ishaq, ashe bama bakin namiji bane bataso, mai tumbi ne.
A yau kuwa in tumbinshi zai kai tulelen cikin da yake gabanta, in har ba zai auro mata Aise ta gansu tare ba, ba zata damu ba, data gama karyawa ne take ce masa
"Kana ganin Fa'iza ko? Haka fa tace tunda sassafe zata zo"
Yayi dariya
"Ai banyi magana bane, amman yaushe Fa'iza ta gama baccin safe balle ta tashi ta shirya ta fito?"
Gashi cikinta harya fara fitowa, da yake bata same shi da wuri ba, saida ta fara nuna damuwarta ma tukunna, cikinne yasa Haris siya mata mota, a cewarshi ba zai yiwu ta dinga yawon zuwa makaranta a napep ba
"Amman baka ganin mijinta zaiga kamar ana nuna masa iyakarshi akan Fa'iza? Tunda a tsaye yake, bafa zai yiwu daka ga bata da wani abu kace zakayi mata ba..."
Sai ya kalleta da wani yanayi yana fadin
"Dan na bata mota? Ba wata babba bace bafa, nasan zakiyi magana shisa na siya mata karama, sai in sai ma Auwal din wadda ta fita"
Dariya tayi tana girgiza masa kai, tunda a lokacin Auwal bashi da mota, hadari yayi da tashin, baiji ciwo ba, amman sai gwangwan din motar akayi, bai mayar ba har yanzun, da mashin yake hawa
"Ba ca nayi ka sai masa mota bafa"
Ya sauke numfashi
"To me kike cewa? Koshi zai kaita unguwa dai ai babu yanda za'ayi ta hau mashin da ciki ko? Balle kinsan ni bana son napep din nan da suke figa gudu kamar mutum zai fado..."
Kyaleshi tayi, in dai akan yaranshi ne da kashe musu kudi, Haris ba zai daina ba, ya daina shawara da ita, sai dai inta ga wani abin ta kwace kawai, to Fa'iza ma da yake mata rikon 'ya haka yakeyi, dakyar ta samu ya daina jibgar kayan abinci yana zuwa yana kai musu kamar Fa'iza tace masa Auwal na barinta da yunwa, yaron tsaye yake, wani abinma in yayi mata kamar yafi karfin samunshi, yanayi ne saboda Haris na sakashi jin kamar ya gaza akan iyalinshi, tausayi yake bata, tunda Allaah Ya hadashi da surukin zamani.
"Nima fita zanyi, amman zan jira Fa'iza tazo, bana son inyi nisa in barki ke kadai"
Yayi maganar a hankali, dan saida ta daga kai ta kalleshi
"Ina zakaje?"
Ta tsinci kanta da tambaya, ya danyi jim, karya na cikin abinda yakeyi masa wahala matuka, zai gujewa fadin gaskiya ta hanyar yin shiru in ba tambayarshi akayi kai tsaye ba
"I'm meeting someone..."
Ya fadi, akwai wani abu da bai zauna mata ba, taso ta kara tambayarshi sai taji mararta ta daure, ta kuwa riko hannunshi tana kiran sunan Allaah
"Menene? Bayan ne?"
Ya tambaya a rude yana saukowa, kai take girgiza masa jin ciwon ya taso mata gabaki daya, dumin da taji a jikinta kuma ya tabbatar mata da faya ce ta fashe mata
"Maryamm...muje asibiti, bari in dauko mukullin mota"
Haris yake fada a rude jinshi zaune cikin lema shima, kuma haihuwa uku ba wasa ba, ya riga yasan ruwan nakuda ne, kai take girgizawa tana kara rike shi
"Nishi nakeji Ganjaa...haihuwa zanyi"
Ya zaro idanuwa kamar zasu fado
"Nishi kikeji? Nishin ne haihuwar?"
Yake tambaya muryarshi da jikinshi gabaki daya yana rawa tare dana Maryaman
"Dan Allaah karkiyi nishin to, ki rufamun asiri ki rike nishin sai munje asibiti..."
Wani irin yunkuri tayi tana cigaba da kiran sunan Allaah, haihuwar ta taho mata gabaki daya
"Kan ya fara tahowa, leka...lekamun kagani"
Cikin wani irin tashin hankali da bai taba sanin akwaishi ba yace
"In leka me? Inga me? Wanne kan? Maryamm, Maryamm kar kiyi mun haka"
Ya karasa maganar yana kokarin mikewa amman saita sake damtse hannunshi kamar zata karya masa yatsu, inma wasu basu karye ba a karar da yaji sunyi, sallamar Fa'iza ta cika falon
"Fa'iza zo kiga abinda Maryamm zatayi mun, so takeyi ta haihu anan, ki kama mun ita mu tafi asibiti"
Da gudunta Fa'iza ta karasa falon, ita Mass communication take karanta, yanzun take shekararta ta biyu, bata taba ganin haihuwa ba tunda ba'a tabayi a gabanta ba, amman yanda Maryama ta damketa, rikone tayi mata daya tabbatar mata da in ba wanda yake cikin ciwon nakuda ba, babu wanda zai iya rikeka haka, saita tuno kauyensu, ta tuno mahaifiyarta, lokacin da kishiyarta take nakuda, kafin a koresu daga dakin, taji tace mata
"Ramatu rike mun hannuna"
Babarta ta matsa tana fadin
"A'a wallahi, rabani da rike mai nakuda ki karyani, rike karfen gadonki Abule"
Tabbas karfen ne ya kamaci masu nakuda su rike ba mutum ba, karfen ma mai kwari, a wannan asabar din, a cikin dakinta, a tsakanin Fa'iza da Haris, da taimakon Ubangiji Maryama ta haifo danta da kukanshi ya karade dakin, Fa'iza ce ta dauko mata jakar data hada kayan haihuwarta a ciki ta yanke cibin da kanta, sannan Fa'izar ta nadeshi cikin showel tana kallon Haris da fuskarshi tayi wani irin fayau
"Bani da lafiya Fa'iza..."
Kuma yayi kama da marar lafiyar
"Meya sameka?"
Maryama da takejin kamar an sauke mata nauyin duniya daga kanta ta tambaya
"Bansani ba, kamar mahaifata ce ta koma"
Daga Fa'iza har Maryama dariya sukeyi, yanda yayi maganar da dukkan gaskiyarshi, har suka tattara sukaje asibiti dan a tabbatar da lafiyarsu data jaririn, bayan Fa'iza ta gyara falon, ta nade kafet din da tasan zai wahala ya fita, basu daina yiwa Haris dariya ba, shi dai kallo daya zakayi masa kasan a firgice yake, ko da yake bin Maryama dakin nakuda, bai taba ganin tashin hankali irin na yau ba, koya hankalinshi a kwance yake tunda likitoci sun zagayeta, amman a gida, sai kawai ta haihu a gida? Ya kasa daina tunanin inda an samu wata matsalar da ya zaiyi? Da gaske kamar bashi da lafiya haka yakeji, dan bakar jallabiya ya saka a jikinshi da zasu fito asibitin, aka dubasu aka tabbatar musu da komai lafiya, sai bayan sun dawo gidane sannan aka fara kiran mutane ana sanar dasu haihuwar da tayiwa kowa bazata.
Lokacin ne kuma Haris ya samu kanshi ya dauki wayarshi da take a silent, missed call din Aise ya gani har guda goma sha daya, sai yaji cikinshi ya hautsina, shayin daya sha yana taso masa, babu shiri ya nufi bandaki yana yin aman har ruwan daya sha a ranar, su Fa'iza nayi masa dariya, yasan ya rude ne, bashi da mahaifa, amman da gaske yakeyi bashi da lafiya, wani abu nayi masa ciwo, daya daga hannayenshi ma sai yaga suna rawa, wani yanayi yakeji da bature yake kira uneasiness, ga zuciyarshi nata bugawa batare da wani dalili ba, sai ya cire kayanshi ya watsama jikinshi ruwa, ya fito ya samu kaya ya saka, amman yanayin nan bai barshi ba, ya dauki wayar tashi da mukullin mota ya fito, yanajin hayaniyar mutane daga babban falon gidan, yasan 'yan uwan Maryama ne da suka zo, ya gaisa dasu Adda Maimunatu, kilan wasune suka kara zuwa shiga hayaniyar ta karu.
Akwai wata kofar fita tanan bangaren nashi da yake mantawa da itama saboda ba amfani yakeyi da ita ba, yau ta nan ya fita, ya saka mukullin motar ya bude kenan zai shiga saiya tuna ya bar wallet dinshi, babu kudi a jikinshi sannan katikan bakinshi duka suna ciki, ya danja tsaki yana juyawa ya koma, daya dauka saiya manta ya taka yana bi ta babban falon, haka ya dinga bude hakora suna kara gaisawa da mutane saboda yanayin da yake jinshi, lokacin wayarshi ta hau kara dan ya cireta daga silent, ya nemi idon Maryama a cikin dakin, sai tayi masa murmushin daya kasa mayar mata, ya taka yana juyawa zuwa hanyar fita, kiran harya yanke, yana kaiwa bakin kofa aka sake kira, Aise ce dai, saiya daga muryarshi na rawa kamar wanda akayiwa dole yace
"Hello..."
48
Aise Modu
Aisha Muhammad shine cikakken sunanta, haka kuma mahaifinta ya saka mata a makaranta lokacin daya kaita, ta dade inta kalli sunan a takarda sai taga kamar ba nata ba, lokacin da tayi girma sosai ma sai takejin inama ta canza, tafison Aise, tana kuma jin dadin yanda yanda ake kiran mahaifin nata, musamman idan sukaje Maiduguri, yanda 'yan uwanshi suke furta sunan da harshensu daya fara karyewa da yaren Kanuri, akwai wani yanayi da suke fadin sunan dashi da a bakunansu ne kawai takeji.
Kamar kowanne dan adam, ta taso da burika masu yawa, tasani tana daga cikin mutane masu sa'a, saboda bakowa bane yake samun cikar kaso mai yawa na daga wadannan burikan, ita Aise tun tana da shekaru bakwai a duniya tasan cewa tana so ta zama likita, tana girmane komai na kara fito mata tar, tana kuma fahimtar abinda zuciyarta take so, kafin a hankali ta tsaya kan abu daya, saboda haihuwa da duk wani abu daya danganceta suna burgeta, duk lokacin da wata mai ciki zata shiga ofishinta sai abin yayi mata kamar sabo, kalmar ciki abu dayane, kuma hanyar samunshi ma da nature yazo dashi iri daya ce kafin zamani ya samar da wasu hanyoyin, amman kowanne ciki ya bambanta ne a tsakanin mata, kowa da yanayin laulayinta, wahalhalunta da makamantansu.
Tana rike duk wani jariri da zata taimaka wajen karbar haihuwarshi ne da sabon shafi a zuciyarta, shisa mutane sukeyi mamaki idan tace batason yara
"Inaso in taimaki duk wanda yake son yara da duk abinda zan iya har sai na mika musu yaransu sun rike a hannunsu, hakan baya nufin ni inaso a taimakamun in rike nawa..."
Amsar data bawa Mu'adh kenan lokacin daya tambayeta, saiya girgiza kai kawai. Shisa rashin yaranta baya wani damunta, bata da emotional attachment sosai dasu. Burinta na biyu bayan wannan shine irin mijin da zata aura, tana da tsare-tsare masu yawa a cikin kanta, da tarin hasashe na yanda zai kasance, ba zata tuna ko ya wannan tsarin nata yake ba bayan ta hadu da Haris, idan ma baiyi kama da abinda take hasashe ba, zuciyarta ta karbeshi, tayi masa karbar da ko wani namiji ne ya gifta ta gabanta sai Haris ya gifta a cikin zuciyarta.
Ko a mugun mafarki bata hango wai zatayi rayuwa da wani namiji ba shi ba, Haris kuma zai rayu da wata mace ba ita ba, haka wannan burin nata ya zama gari ya barbade yabi iska, to abinda yabi iska zai dawo ne? Haka tayi zato, ko bayan da ta rabu da tsohon mijinta. Sai da ta sake saka Haris a idanuwanta sannan, sai kuma data ganshi a gabanta, ta sake jinta a jikinshi. Haris, Haris dinta, taya ma zatayi tunanin hakura dashi bayan ta sake samun wannan damar? Sai dai abinda batayi zato ba shine zata dinga bin Haris yana zame mata, Haris fa da in bata daga wayarshi ba yake baro makarantarshi zuwa tasu batare da tunanin tazara ba, akwai ranar da yace mata
"Kina lafiya, abinda nazo gani kenan"
Kuma bai jira tace komai ba ya juya ya tafi abinshi, Haris yasan darajar abinda yake so kuma baya wasa dashi, ashe a baya karyar soyayya tayi tunda ta hakura dashi, yanzun ne ma taji ta fara sonshi, saboda a shirye take da tayi komai dan ta mallake shi, in tace komai, to tana nufin komai. A irin yanda take ganin taurin kan Haris kan sake basu wata dama, raunin shi akan mata kawai zatayi amfani dashi yazo hannunta, har mamaki takeyi, yanda itace take bin namiji haka, kuma wai har take shirin yin komai dan ta sameshi, a baya tana daga cikin mutanen da suke kallon mata masu irin abinda takeyi da ballagazai, ko a Italy in taga mace na bibiyar namiji yana yankwanata sai taja tsaki tana fadin
"Shashasha"
Sai gata cikin shashancin da take ganin tafi karfin ta aikata shi, a Abuja, akwai cousin dinta, 'yar kanwar Mamanta ce, tazo gidansu ta kwana, suna kwance suna duba abu a wayar Kariman, sai taga wani post a daya daga cikin blogs din da take bi na wata yarinya data ba saurayi kanta kuma yazo ya gujeta
"Wasu matan fa wawaye ne, me take tsammani zai faru to? Ya zakayi ma kana musulmi, da hankalinka kaje ka aikata wannan shirmen..."
Sai Karima ta kalleta, kallo na sosai
"Idan kikaga abu irin wannan, to kiyi addu'ar shiriya kawai, ki kuma nemawa kanki kariyar Allaah daga aikata abu makamancin shi, dan bakiyi ba, baya nufin kinfi karfin kiyine, Allaah Ne kawai ya kareki bai jarabeki ba...babu kyau"
Sai taja tsaki kawai, shisa ta tsani shiga dangin Mamanta, abu kadan zakayi su fara yi maka wa'azi, suna so su jingina maka kafurci, ita da hankalinta wanne namiji zata biyewa, ko data taso a kasar waje tasan darajar kanta, sai gata yau da booking hotel da hannunta saboda tana so ta samu kan Haris, saboda a halin yanzun bata da wani buri daya wuce ta ganta a matsayin matar Haris. Motarta ta dauka daga hotel din da suka sauka da abokan aikinta, ta riga ta gane hanyar da zata mayar da ita hotel din da taje ta kama jiya, sunyi da Haris zasu hadu wajen karfe daya na rana ne, shisa ta dinga jera masa kira tun wajen sha biyu kafin ma ta fita, sai dai bai daga ba, kawai ta shiga mota ta fice, tana ganin kiran Mamanta lokacin da take hanya, saita danne wayar tana kashe kiran, ta tura mata gajeran sako cewar tana busy zata kirata.
Batason duk wani abu da zaisa taji ta fasa kudurin da yake ranta, traffic ya tsayar da ita tare da wasu jerin motocin a gabanta da bayanta, yau hutun karshen mako, amman batasan ya akayi titin yake a cike haka da kwallin ranar da akeyi ba, turare ta janyo ta kara fesawa, data ajiye sai tayi atishawa, ta sakeyin wata, ta jera atishawa wajen biyar a lokaci daya, hakan yasa ta sauke gilasan motar, wasu