Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
can dinma sau biyu Haris ya barta, na biyun ma Mummyn ce batajin dadi, tayi zazzabi. Da cefanensu ya kare tayi masa magana
"Kabani kudin sai inje kasuwa in siyo"
Kallonta yayi kaman bata da hankali
"Kece zakije kasuwa yin cefane? Salon wani ya tunkudeki ki fadi ki karye ko?"
Mamaki ya kamata
"To me yasa ka saimun mota idan ba zan dinga zuwa wajeje da ita ba"
Batare daya kalleta ba, dan yana aiki a laptop dinshi ne lokacin yace mata
"Ki dinga kallo kina jin dadi, randa kike bukatar motar kiyi amfani da ita"
Ta rasa gane kanshi da kuma matsalar da yake da ita akan fitarta, da kanshi yace ya yarda da tukinta, rannan da yace mata
"Zo muje yawo, kina shan ice cream?"
Ita ya bari ta tukasu, yana nuna mata inda zatabi, amman ta fita ita kadai shine matsalarshi
"Ya zanyi da cefanen to"
Har lokacin hankalinshi na kan aikin da yakeyi yace mata
"Zamuje tare, akwai aikin da zanje gobe, ko kawai kiyi list din abubuwan da kike bukata zan taho dashi"
Saboda takaici ranar fice masa tayi daga dakin. Haka Khairi tace mata
"Allaah Yasa ba irin mazan nan bane masu kullen tsiya Maryama"
Itama kuma ta dinga jujjuyawa maganar a ranta, gashi in zasuyi waya sau goma da Khairi zatace mata tayi masa maganar komawa makaranta. Suna hira, ko tace tana masa hira sosai, tunda yakan zauna a falo inya ganta a zaune, wata rana ma da kanshi zaice ta bashi labarin film din da take kallo, ko in yasa hankali yana kallon ya dinga mata tambayoyi. Zancen makarantar ne saita rasa ta inda zatayi masa shi, kuma haka ta dinga bude baki tana mayarwa ta rufe har akayi kusan wata uku da aurensu, kafin wani yammaci sun fita sun dawo, shima gajiya tayi da zama ita kadai ta roke shi su fita ya sai mata ice cream, kuma baiyi musu ba yace mata to.
"Inaso in koma makaranta, inyi WAEC dina"
Yayi shiru kamar baiji taba, kafin a hankali yace
"Me zakiyi da ita? WAEC din?"
Ta dan gyara zamanta
"Zan koma makaranta mana, idan nayi sai inyi jamb, sai in cigaba da karatuna, inaso in karanta Midwifery"
Taga sanda wani abu ya gilma ta cikin idanuwanshi, kafin ya kalleta da idanuwan nan nashi tar yace mata
"Aure akayi miki Maryamm, muyi zaman auren kawai"
Itama tayi shiru, tanajin yanda idanuwanta suka tara hawaye, tana son karatunta, inta tuna yanda Abba yake alfahari da cewa zata karanta Midwifery tanajin dadi, tana so taga ranar da zata gama karatun nan ta mika masa shaidar gamawa
"Me yasa? Me yasa ba zanyi karatun ba"
A hankali yace
"Haka kawai"
Tunda bashi da wani dalili, ko fita yayi akwai wani abu da yakejin ya natsu a kirjinshi da sanin cewa tana can gida, a zaune, ko a kwance, koma dai a yayane tana gidanshi, tunda yake a rayuwarshi aurenta ne abu na farko da aka bashi batare daya nema ba, itace aka miko masa batare da yace yana so ba, kuma akanta yaji yana so ya mallaki abu da dukkan wata ma'ana ta kalmar, a hankali, da duk ranar da zatayi wani abu, maganarta, surutun nan nata da bata gajiya dayi masa, inta hada masa shayi, in tayi masa tayin wani abu da baisan dashi ba, inta kalle shi tace
"Ganja..."
Cikin murya da yanayin da ita kadai take fada yaji dariya ta kamashi, idan ya siyo mata wani abu yaga idanuwanta sun haska da farin ciki, ko tayi tsallen nan kamar yar karamar yarinya, yanzun da ta fara sabawa dashi, ta saki jiki da yanda yake riketa a duk wata dama da zai samu, takan riko hannunshi, ko in zatayi masa magana, ko tana masa magiya ya dandana wani abu da tayi, kuma ko da zai rantse to ba zaiyi kaffara ba, da taimakon matan waje ne kawai yake danne abinda yakan taso masa akanta, amman duk sanda zai kalli Maryamm
He wants to own her!
Haka yakeji, batare da wani dalili ba, yana son ya mallaketa shi kadai, ta zamana a karkashin ikonshi shi kadai, kuma watakila da sanda ta bude bakinta tace masa tana son cigaba da karatu ta zabi wani abu ba Midwifery ba, watakila daya mayar da ita makaranta
"Duk courses din dake karkashin health line, me yasa midwifery"
Ya tambayi Aise
"Saboda ina so in taimaki matan da zan iya a tsayin rayuwata, ina so ina wajen ingansu da yaransu rike a hannu, saboda banajin zan rike nawa"
Yayi murmushi
"Me yasa? Bakyason yara ne"
Ta kalle shi
"Ina sonsu, amman banajin ina musu son da nake fatan ni in same su"
A lokacin baima dauki maganarta da wani muhimmanci ba, kawai gani yakeyi wahalar da kanta zatayi a yanda take da kwakwalwa, ai gara ta tafi inda albashinsu yake da tsoka. Ko danshi duk wani hange da shirye-shiryenshi na yanda manyan kudi zasu dinga shigo masa ne shisa yake yiwa kowa irin wannan fatan? Ko kadan baiji wata matsala akan karatu ko aikin Aise ba. Amman Maryama bayaso yaji tace masa zata fita, to idan yana da matsala da fitarta unguwa wanda bama kullum bane, zai juri fitarta makaranta? Ita kadai? Babu shi?
Sannan ma yanda inya kalleta baya ganin abu ko daya da yayi masa kama da Aise yana sama masa natsuwa, ko kayanshi na waje in sukayi yanayi da ita hakura yake dasu, duk yarinyar da zatayi masa yanayi da Aise ko ta yatsun hannuwanta ne baya iya tabata, wani abu ne yakeji yana taso masa, waji abu da yake tokare masa wuya ya hana masa numfashi. Maryama ta zauna a gida, yana da kudin da zai kula da dukkan bukatunta, yanzun haka ba zaune yake ba, aikin daukar hoto yake samu har ma saiya zabi wanda yake so yayi da wanda bayaso, kudi na shigo masa, dan da Alhaji Mustafa ya tura masa da kudi watanshi na farko da auren Maryama ya kirashi yayi masa godiya sannan ya dora da
"Baba ka daina turamun kudi, ina samun ayyuka da yawa, ka daina turamun kudi, kasan account daya nake amfani dashi, suna hargitsewa bana gane lissafin abinda nake samu da kuma adadin bukatuna, inaso in fara yin dukkansu da kudin da suke shigo mun, ina so in fara gane kan samu na"
Kuma tun daga ranar bai sake tura masa da kudi ba, in ya koma makaranta ma, ba zama zaiyi ba ya tsaya iya karatun, aikin duk daya samu zaiyi kayanshi, zai kula da Maryama, idan akwai wani ma da take so ta kula dashi zaiyi mata wannan.
Ta zauna,
A karkashin shi,
Ya mallaketa shine kawai abinda yake so.
Data fadawa Khairi sai tace ta gayawa Abbansu, tasan zai yiwa Haris din magana, tunda a tunanin Khairi idan ma baiyiwa Haris magana ba, zasuyi maganar da Alhaji Mustafa, shikuma zaisa Haris ya barta ta koma makaranta, duk matan gidansu suna makaranta, sai Abban yayi yarjejeniyar za'a barsu su koma makaranta ko da ba zasuyi aiki ba. Wannan kwarin gwiwar shi Maryama ta samu tayi masa magana dashi, yayi shiru har tayi tunanin kiran ya yanke sannan yace mata
"Haris dinne yace kuyi zaman aurenku?"
Ta daga kai saboda bataso ta bude baki kuka ya kwace mata
"To Mairama kiyi hakuri kinji, kiyi wa mijinki biyayya, inda rabo sai kiga ya barki kin koma makarantar"
Aikuwa hawayen ne ya zubo mata
"Ba zanyi karatun bani Abba? Ba zakayi masa magana ba"
Ta karashe kuka na kwace mata
"Kiyi hakuri..."
Kuka tayima Abban ba dan kadan ba, ya dinga lallashinta da tausasan kalamai yana tuna mata ladan da yake cikin biyayyar aure da kuma biyayyar maganar miji
"Ke da zaki samu lahira in kika hakura, wa yake batun wata duniya Mairama?"
Tayi shiru tana ajiyar zuciya
"Ko bakyaso ki dinga karbar haihuwar matan aljanna?"
Maganar ta bata dariya, bai bari ta kashe wayar ba saida ya tabbatar ta warware, ta saki ranta, kuma ta hakuran da gaske, ko da Khairi ma tace ta kwantar da kai tayi dinga masa biyayya tayi dabara kilan ya barta sai ta amsa da
"In Shaa Allaah"
Amman a kasan ranta tanajin ta hakura da karatun, in ba Haris din bane yazo da kanshi yayi mata maganar, yanda Abbanta yace ta hakura, to ta hakura din. Kawai dai yanzun in ta kai masa shayi dakinshi tana tsayawa ta dinga kallon shi yana aiki da laptop
"Wanne irin aikine kakeyi?"
Ta taba tambayarshi
"Hotunan dana daukane nake gyarawa"
Cikin rashin fahimta tace
"Wanne irin gyara? Ba da an dauka ba shikenan"
Ya girgiza mata kai, yana mata bayani yanda yake tunanin zata fahimta
"Naga wajen laptop dinka hudu..."
Yace mata
"Daya ta lalace, sai an gyara"
Kai ta jinjina masa
"Da na iya ai da ka barmun daya sai in dinga tayaka"
Ya kalleta
"Da kin ragemun aiki kuwa, irin wannan hotunan, ba irin wanda nake so in dinga dauka bane ba, kawai aikine, kuma ina son kudin shisa, banajin dadin editing dinsu kwata-kwata"
Da sauri tace
"Ka koyamun, zan iya Allaah, ko akwai wahala zan iya in ka koyamun"
Da taga yana kallonta sai tace masa
"Da gaske fa, ka gwada kagani"
Ta karasa maganar tana yi masa murmushin nan da dukkan hakoranta suke bayyana, murmushin da ko baya cikin nishadi sai ya sakashi murmusawa shima. Sai ya matsa mata yana fadin
"Zauna to"
Ta kuwa zauna a gefenshi cike da tarin doki, dan batayi zaton zai yarda ya koya mata ba
A wannan ranar,
A wannan daren, suka bude wani sabon shafi daya kara shakuwa a tsakaninsu
Da yake bata gajiya da bashi mamaki, sai take fahimtar komai, harda wani littafi data dauka a dakinshi take yin rubutu a ciki na abubuwan da yake koya mata, wanda take tunanin zata manta. Ta maida hankali sosai, har yana ce mata
"Kinga in kika kware sosai saiki zama editor dina, mu zauna in tsara miki albashi"
Tayi masa murmushin nan
"Dan Allaah, irin wanda ake ba ma'aikata? Nima idan zan siyi wani abu sai in dinga cewa ina jiran salary ne, kagane irin yanda masu aiki sukeyi"
Ya girgiza kai kawai yana dariya. Tana jin dadin abinda yake koya mata din, yana rage mata kadaici, ta samu karin abinyi bayan kallo. Laptop daya yake bar mata in zai fita, sai taita gwada duk wani abu daya nuna mata, inda take da tambaya wata rana rubutawa takeyi dan karma ta manta, Haris baya gajiya da amsa mata wadannan tarin tambayoyin da basa karewa duk rana.
A cikin watanni shiddan nan,
A cikin abubuwan da suka faru, sunyi fada sau biyu,
Kuma in aka tambayi Maryama zatace duka fadan biyu itace da gaskiya, sannan kuma zata kara da fadin itace ta ja fadan...
27
Fada na farko...
Kasuwa ya shiga, da list din da tayi masa a hannu, kusan komai ya gama siya, sai dai ta rubuta masa da dankalin hausa, da yaje gurin siyarwar sai suka nuna masa kala biyu, ja da fari
"Ai Alhaji jan nan yafi dadi, ya dai danfi farin tsada ne kawai"
Mai siyarwar yace masa, ya sake duba list din, bata ce ga kalar wanda take so ba, baya kuma son surutun Maryama, da zai siyi kala biyun, gaba ta saka shi ta dinga masa fada waccen siyayyar
"Kai ba komai kake ci ba, ni kadaice fa a gidan, saika kwaso doya mai yawa haka? Yaushe zai kare?"
To yanzun sai take rubuta masa adadin yawan da zai siyo mata komai, kuma kwano daya tace na dankalin, ya laluba a aljihunshi ya zaro wayarshi, lokacin ne ya tuna cewa a tsayin watannin da sukayi aure, bashi da lambar wayarta, kuma ya kamata ace yana da lambarta, da yanzun zai kirata ya tambayeta ne kawai, sai ya bar siyan dankalin, ya siyi albasa a wajen mutumin yace masa zai sake dawowa kawai, har sauran abinda bai karasa bama ya barshi ya nufi gida, bayan ya gama shiga da kayayyakin ne ya mikawa Maryama da take tsaye tana jera masa sannu wayarshi
"Ki sakamun lambarki"
Da ta saka lambar sai ta mika masa, tana kallonshi yana dannawa alamar saving yakeyi, kafin ta jiyo karar wayarta a falo
"Kaine ka kira?"
Ya daga mata kai kawai, ta wuce zuwa falon ta dauki wayar, data tashi da murmushi a fuskarta tayi saving din lambarshi da Ganja.
"Wanne irin dankalin hausa? Sun nuna mun guda biyu, ja da fari, bansan wanne kike so ba shisa ban siya ba nace sai nazo"
Taji maganar shi a bayanta, hakan yasa ta juya ta kalle shi
"Ja? Dankalin hausan?"
Dan bata taba gani ba, batama tabajin akwai shi ba sai yau
"Kuma dankalin hausa kace musu kuwa?"
Ya kankance idanuwanshi akanta, wani abu data kula yakeyi idan yana so yace mata
"Da gaske? Tambayata kikeyi?"
Batare da yayi magana ba
"To aini ban tabajin jan dankalin hausa bane ba...in dauko hijabina muje tare in ganshi? Kaji? Dan Allaah"
Ya girgiza mata kai
"Dan Allaah fa, kaji...dan Allaah, kwana nawa banje ko ina ba, kuma rannan kace zan rakaka saika fasa"
Ta karasa kamar zatayi kuka
"Ni na fasa ko kece baki shirya ba zaki batamun lokaci?"
Da yake so takeyi ta bishi sai ta kara marairaicewa
"Ai yanzun na shirya, hijabi fa kawai zansa, dan Allaah"
Yaja numfashi, shi baima yi niyyar komawa kasuwar a lokacin ba, amman saiya daga mata kai yana kallon yanda ta ruga da gudu zuwa daki, wayarta ma anan kan kujera ta ajiyeta bayan ta fito, hijabin kalar pink ne mai laushi, yayi masa kyau, ya haska fuskarta da take fayau sai vaseline din data shafa a labbanta, ga alamar murmushi nan a fuskar, shine yasa yaga tayi masa kyau, abubuwa irin wannan, kananun abubuwa a tare da ita. Da sukaje kasuwar kuwa sai tace a saka mata jan dankalin rabin kwano, farin ma rabi, tana ta addu'a a ranta Allaah Yasa kar taji jan wani iri tayiwa Haris asarar kudinshi. Shiya rike musu ledojin, tunda taga salak tace tana so, suka siya da yawa, Mummy ta bata dakakken kuli, tunda ta bata shi tazo gida ta juye take hango kwado, kamar ta kirata tace mata ina zata samu zogale saita fasa kuma.
Haris ba wani barinta yakeyi tana fita ba, ba zuwa takeyi gidan ta gaishe da ita ba, sai kawai ta dinga dora mata dawainiya? Sun kusa wajen motarsu ne, daga tsallake ta hango mai saida gawasa da ita a saman kai
"Gawasa, kaga gawasa..."
Ta fadi tana nunawa Haris
"Ka saimun dan Allaah"
Ya kalli inda take nunawa, ya kalleta
"Mai gawasa!"
Baisan lokacin da ya kama hannunta yana janyowa ba, ganin wasu maza sun waigo
"Meye haka?"
Ya tambaya ranshi a bace, yana kuma kallon wannan mazan hadi da watsa musu harara
"Kawai saiki yage baki akan hanya wasu suna kallonki"
Ya fadi itama yana watsa mata nata kason hararar, ga mai gawasar kuwa yanata waige-waigen neman wanda ya kirashi, kayan ya fara sakawa a mota
"Ki shiga mota gani nan zuwa"
Sai kuwa tayi yanda yace, da kanshi ya tsallaka ya siya mata gawasar da ko a ido batayi masa kyau ba, tayi wani kaushi kaushi, danma ita zata fere abinta, tunanin da yazo masa kenan, yana karawa da tambayar ko meye ma gawasar? Ko me zatayi da ita oho, yanda Maryama bata wuni zawo a irin abubuwan da yake gani tana gabzawa cikinta yana bashi mamaki. Da ya dawo leda bakace ya mika mata
"Ya isa ko a karo"
Ta ganta da yawa, gashi ya saka mata manya
"A'a, kai ai da yawa ma sosai, nagode. Allaah Ya kara budi"
Bai amsa mata ba, kamshin gawasar ya dinga dukanta, ta kasa hakuri ta dauki robar ruwan data gani a motar, ta dibi guda biyu ta wanke ta gilas ta dan kara sama da gilas din, ta gutsira, ga zaqi
"Kaji zaqin wannan kuwa? Allaah Yasa sauran ma haka suke, ungo..."
Tayi maganar tana mika masa
"Banaci, haka zakici da bawon? Ba zaki fere ba?"
Ya tambaya da mamaki a muryarshi
"Gawasar zan fere?"
Ya dan daga mata kafadunshi, sai kawai ta girgiza kanta, abubuwan da Haris bai sani ba suna da yawa, ta gaji da lissafawa, ta dai kara da gawasar. Parking yayi zai siyi fruit, da yake ya samu wajen mutum hudu, shisa ya tsaya a gefe, Maryama da take cin gawasarta a tsanake tana kallon dayan gefen, ta ga wani Balarabe cikin doguwar rigarshi fara qal, gashi nan nashi daya aske yayi low cut baqiqirin, ya kwanta luf, da Maltina a hannunshi yana tsaye a gefen titin, daga cikin motar tana ganin yanda yake wani dorawa-dorawa saboda haske, kamar an ciroshi daga tv an ajiye shi a wajen, ga hancin nan dogo. Kuma da Haris ya shigo motar, taji shigowarshi saita juyo take ce masa
"Kalli wancen balaraben, su dai farare sunji dadinsu da kyau...ji hancin shifa"
Hannun Haris ya murda mukullin mota a lokacin, amman karar tashin motar bai karasa kunnuwanshi ba bayan maganar da Maryama tayi, tsikar jikinshi yaji ta tashi, wani abu yana tsirga masa, daya kalleta sai yaga ta sake juyawa, inda take kallo shima ya kalla, gayen ne a tsaye, waya ma yakeyi yana murmushi, a idanuwan Haris wasu irin manyan hakora yaga yana dasu na gaba da sukafi na zomo girma, kamar ma nashi a yanda Haris ya gani suna gab da taba habarshi, tunda yake bai taba ganin mummuna irin wannan gayen da yake tsaye ba
"Anya akwai munana a cikin farare kuwa?"
Maryama ta sake fadi batare data juyo ba, Haris yaji zuciyarshi na bugawa da sauri-sauri kamar zata fito daga kirjinshi, kamar inta fito zatayi hannaye da kafafuwa ta samu wannan gayen da jibga, sai gangar jikinshi ta jibgi Maryama da take cikin motar, sai kawai ya figi motar dan saida Maryama tayi baya, inya tsaya a wajen, a yanda yakeji zai tsaya a wajen ne ya jibgi dan mutane. Kallonshi takeyi da irin gudun da yakeyi da motar, wani abu da ba dabi'arshi ba
"Gudu kakeyi fa, kana gudu..."
Baiyi mata magana ba, baiko kalleta ba duk yanda ta dinga masa magana a tsorace dan saida ya kusa bugawa wani mai mota kafin Allaah Ya kaisu gida lafiya, ko gama kashe motar baiyi ba ta fito daga ciki tana maida numfashi, ledar gawasarta a hannu, ya bude bayan motar ya kwashi sauran kayan yayi cikin gida ta rufa masa baya, ta samu ya ajiye mata komai anan cikin falo
"Lafiyarka kuwa? Niyya kayi ka kashemu kome?"
Yanda ya juyo yasa ta matsa baya kadan, dan ta tsorata
"Bansani ba, ashe idan kika fita wasu kartin banza kike karewa kallo har kina ganin tsayin hancinsu?"
Kuma batasan me yasa ta zabi wannan yanayin tayi dariya ba
"Dariya na baki? Dariya zakiyi Maryamm? Kin saka kato a gaba kina kallo shine abin yake baki dariya? Saboda baki da hankali?"
Ta girgiza masa kai
"Nifa babu wanda nake kallo wallahi, to ina ruwana dasu, shima dan naga farine"
Yayi mata wani irin kallo da ba