Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
ta jira, dan haka nan ta gayawa Mummy ta sameta, tana ganinta taji hawaye na neman sake balle mata, ta daure
"Sannu Maryama, ya jikin nashi? Kawunku ne ya kirani dan shi baya gari ma"
A hankali tace
"Da sauki..."
Mummy ta jinjina kai cike da jimamin yanda taga Maryaman
"Akwai shago dana gani anan waje, ki zauna bari inga ko silipas ne in za'a samu in siyo kisa a kafarki"
Cikin emergency din ta koma ta zauna, sai taga daga Nurse din har Mummy duk sun dade, Nurse din ta riga dawowa, saida ta fara bata sauran kudadenta da taga sun rage da yawa, tukunna ta shige ciki, sai Mummy din itama, ta dawo da silipas harma da ruwan roba guda biyu
"Duk babu karamar lamba, har tsallakawa nayi ban samu ba, sai na siyo wannan din kawai"
Ta karba ta saka, babbar lamba ce, siraran kafafunta sunyi wani iri a ciki, ruwanma ta kwance ta kurba, sai taji ashe tana tare da kishi, dan haka tasha sosai, sauran kudin hannunta ta mikawa Mummy, ta karba ta saka a jakar hannunta batare da tace komai ba, kuma da Maryama ta jingina da jikinta sai ta kara gyara zamanta yanda zataji dadin jinginar, maganganun likita da gajeran mutumin nan ne suke ta dawo mata, kamar tana so ta kara fassara su yanda zata fi fahimta, ai taji ya kira abinda ya fado daga aljihun Haris da "Weed". Kalmar ce dai take ta zagayawa da ita daga wannan sashin zuwa wancan a cikin kanta kamar mai tsoron fassarar da zata tarar.
Bugun da zuciyarta ta tsagaita dashi ya dawo sabo, taya za'ayi ace Wiwi ce, sha yakeyi kenan? Kaurin da taji yana fitowa daga dakinshi na wiwin ne? Dan wiwi aka aura mata? Abba ya sani? Baban Tudun Wada ya sani? Ko shisa aka aura mata shi saboda yana shaye-shaye? Tunda ai tasan ko duniya yake kwankwada za'a hadu tare da Alhaji Sa'id a rufa masa asiri, Abbanta zai iya sadaukarwa da Baban Tudun wada komai daya mallaka in ya bukaci hakan. Amman idan basu sani ba kuma fa? Sai taji tsoro ya shigeta, taji idan basu sani ba tana so ta kare ma Haris wannan sirrin, ta tayashi boyonshi kar wanda yaji ballantana ya dingayi masa kallon dan shaye-shaye. Itama hadashi a jimla daya da kalmar hautsina wani abu yakeyi a cikinta.
Ba zatace ga adadin lokacin da suka dauka a wajen ba, Mummy ta tambayeta ko tana jin yunwa yafi sau babu adadi, tasan dai tun tana zaune harta gaji da zaman ta mike, ta sake dawowa ta zauna, ta kara mikewa tsaye, haka Mummy ma. Sai kuma can wayarta tayi kara, data duba sai taga Alhaji Sa'id ne, ta dauka tana amsa sallamar da yayi mata cikin karamar murya
"Eh muna asibitin"
Ta jinjina kai kamar Abban na gabanta, sannan ta sauke wayar daga kunnenta, kuma ba'a kara mintina ashirin ba ya sake kira, lokacin data fita ta tsaya bakin kofar emergency din nan, ta hango shi, saita manta da wani aure, ta manta da tarin jama'ar da suke kaiwa da kawowa a harabar asibitin ta ruga da gudu, irin gudun da takeyi lokacin tana kasa da shekaru biyar idan taji shigowarshi, ta kuma fada jikinshi kamar yanda bai kunyatata ba ya riketa, sai dai ta dauka zata fashe da kukane, zatayi yanda ta saba duk sanda take da wata damuwa inta ganshi, amman banda yaji babu abinda idanuwanta sukeyi, babu ko digon hawaye
"Inata murna ina gayawa kowa Mairama ta girma yanzun, ashe da mun taho tare da sunyi mana dariya"
Murmushi ya kwace mata, data dago daga jikinshi sai suka hada ido da Baban Tudun Wada, taji wata kunya ta lullubeta, da sauri taja dankwalinta daya sauka daga saman kanta ta rufe, cikin karamar murya ta gaishe dashi, ya amsa yana mata murmushi, yana gida lokacin da Alhaji Sa'id ya kira shi yake fada masa Haris bashi da lafiya, yaso yayi kawaici jin Alhaji Sa'id din yace masa ya shirya zaije Kanon, sai kuma ya kara masa da
"Bansan ko zaka samu sarari ba sai mu tafi tare"
Haka kuma Hajiya Rumana tayi tsalle tace sai an taho da ita, yasan ko yayi hargagi, koya tafi ya barta saita biyo bayanshi, shisa ma yace ta shirya kawai, sai direbanshi ya biya dasu gidan Alhaji Sa'id din suka taho tare, dan Maryama bata kula da ita bama sai lokacin, dan tana bayan Alhaji Mustafa ne
"Ina wuni"
Ta fadi da wani yanayi a muryarta, saida ta watsa mata wani kallo sannan ta amsa kamar mai ciwon makoshi, ba karamin kokari Maryama tayi ba na ganin bata tabe bakinta ba, shisa tayi saurin juyawa suna rufa mata baya, tana kallon Abbansu da Baban suka nufi wajen receptionist din, ita kuma ta koma wajen Mummy data taso ganinsu, ta gaishe da Hajiya Rumana, amman da yake babu idon Alhaji Mustafa, sai tayi watsi da ita bayan ta jefa mata wani kallo a wulakance, da Maryama ta kalli Mummyn sai tayi mata murmushi, duk da fuskarta ta nuna bataji dadin abinda Hajiya Rumana tayi mata ba, ita matar burgeta tayi yanda ta shigo cikin kasaita, masu kudi suna burgeta, sunayi mata kyau, amman kuma bata son wulakanci, inda duk taga za'a wulakantata tana kiyayewa sosai ta kuma kama kanta.
Shisa ta cewa Maryama
"Bari in karo ruwa"
Ita kuma lokacin hankalinta gabaki daya ma yana kan su Abba, dan taga likitan nan na dazun ya fito, kuma sunbi wani lungu tare, zuciyarta ta buga kamar tana son fitowa daga kirjinta ta bisu ko zata ga abinda zasu fada
"Uban me kika bashi? Wato kin aure shi kuna so ku kashe mun shi ke da ubanki ko?"
Hajiya Rumana tayi maganar data ratsa cikin tunanin Maryama kamar ta saka lasifika, zuciyarta tafasa kawai takeyi tunda suka kamo hanyar Kano, Alhaji Sa'id ya zauna a gidan gaba, ita da Alhaji Mustafa suna baya, ji takeyi kaman ta shaqo shi kowa ya huta, kamar kuma motar ta bugi wani abu, shi din ya fita ta gilas. Babu kalar tunanin da batayi ba, tunda akayi auren nan ta rasa gane kan Haris, ya botsare mata kamar bashi ba, kamar wanda aka juyawa kwakwalwa, yanzun kuma anzo ance bashi da lafiya har an kwantar dashi asibiti, Haris dinta? Yaron tun tasowarshi sai yayi shekara baiyi ko zazzabin rana daya ba, hakori ma Haris sai dai kanshi yayi zafi, haka ta dinga ganinsu a bakinshi. Ai ta riga tasan wannan auren bana Allaah bane, auren jari ne Alhaji Sa'id yayi da 'yarshi.
Maryama taji ta tar, taji abinda ta fada, ita tuntuni bata son matar, batayi mata ba kamar yanda tasan Abbanta ma da yayi sanadiyar haduwa kaddararsu waje daya ba abakin komai yake a wajenta ba, balle kuma su karan kada miya
"Magana nakeyi miki kika tsareni da ido kamar wata sa'arki, fitsararriya marar tarbiya"
Wani abu yazo wuyan Maryama yayi tsaye, kalaman Hajja suka dawo mata, lokacin da suke kallon wata tashar Hausa sunata rakadin surutu akan rashin tarbiya da kuma rashin kunya irinta 'yan fim, tunda ance maza ne suke cika danqam a wajen, harda 'yan kallo, amman haka zasu kwanta basuji komai ba, suyi rawa su markade can su juya can, sai Adda Maimunatu tace
"Iyayensu ne basuyi musu tarbiya ba"
Dai-dai shigowar Hajja
"Ki roki gafarar Allaah, su kuma ki roka musu shiriya, a duniya babu wata uwa da take so taga danta ya lalace, komin sakacin da zatayi da tarbiyarshi kuwa, fatanta ace yafi kowanne yaro tarbiya, yafi kowanne yaro nagarta, duk yaron da kuka ga yana wani abu, kar bakinku ya sake daukar alhakin iyayenshi, bakusan iya baccin da suka rasa akan wannan abin da yake aikatawa ba"
Kuma a ranar ta kara gane dalilin da yasa ko dambe ta kwasa a makaranta take fargabar ace Hajja taji, ko intayi wani abu data hanata, saboda ba bacin rai kadai take gani a fuskar Hajjan ba, harda fargaba mai yawan gaske, shisa da taji tana so ta kuntatawa Hajiya Rumana, musamman da babu idon kowa a wajen tayi wani guntun murmushi tace
"Kiyi hakuri Hajja, babu abinda na bashi wallahi, wiwi ce yasha tayi masa yawa..."
Kuma akan idanuwan Maryaman Hajiya Rumana tayi wani tangadi kamar tana shirin faduwa, ta kara gyara tsayuwarta, amman girman jikinta yaki taimaka mata wajen boye irin kaduwar da tayi, maganar ta daketa, dukan da ya sanyaya ran Maryaman yana sa abinda ya taso yayi mata tsaye a wuya ya sauka
"Shine fa muka kawo shi asibiti, amman naga likitan mane yaja su Abba, kilan bayani zaiyi musu tunda ya tambayeni me ya faru na gaya masa, baki ga yanda muka shigo asibitin nan ba Hajja, kinsan Allaah ba zaki..."
Cikin wata murya da izzarta ta sauka Hajiya Rumana ta katse Maryama
"Zaki rufe mun baki ko saina kwadeki a wajen nan? Bayanin ubanki zaiyi musu? Ke waye ya aikeki gaya masa? Waye yace miki abinda ya saka shi rashin lafiya kenan?"
Ita tunda akayi wannan case din na makaranta ta cire abin daga ranta, Haris bai daina ba? Bai daina sha ba? Allaah Ne shaida ba karamin alfahari take ciki ba ganin yanda alakarsu ta gyaru shi da Alhaji Mustafa, yanda duk hira saiya sako zancen Haris din, saiya dinga bata labari akan Haris kamar ita bata magana dashi, auren nan nema da yake tana fushi har yanzun ta janye jikinta, shima kuma ya shareta, tasan yaji dadin yanda Haris bai watsa masa kasa a ido ba, yanzun idan yaji cewa yana shan wiwi me zai faru? Hanjinta sai kadawa yakeyi, tabi hanyar da taga sunyi tana barin Maryama data samu waje ta zauna
"Haka kawai saiki zageni banyi miki komai ba, mata sai bakar fuska da bakar zuciya"
Ta fadi a ranta, a gefe daya tana fatan Allaah Yasa kar a fadawa su Abban wani abu. Sai dai fatanta bai karbu ba sam, dan babu wani abu da likitan nan bai warware musu ba, ya nuna musu hoton da akayiwa Haris din
"Inaso ku sani ne tunda kune iyayenshi, yaronku na bukatar taimako dan ya rabu da abinda yake sha...inaso inyi muku bayani yanda hankulanku ba zasu tashi ba, huhunshi na gab da samun matsala in har bai tsagaita da shan abin nan ba, musamman irin yanda yayi din nan babu komai a cikinshi, yanzun haka jininshi muke kokarin ganin ya sauka daga hawan da yayi, sannan bugun zuciyarshi ma yayi stabilizing..."
Alhaji Sa'id shine mai tarin tambayoyi, saboda Alhaji Mustafa kamar an liqe masa baki, kanshi ma a kasa yake ya kasa dagowa dan baisan ta inda zai fara hada ido da Alhaji Sa'id ba, idan yayi zaton ya nemi alfarmar a hada auren Maryama da Haris ne saboda wannan dalilin fa? Bayan shi babu abinda yake gani a tare da Haris din sai natsuwa da hankalin da yayi, Haris din da waya goma zasuyi, to takwas daga ciki sai sun tattauna akan kasuwanci da kuma plans dinshi, sai yayi masa wasu kalamai da suke nuna irin zurfin da tunanin shi yayi, irin yanda hankali ya fara zauna masa, ashe a gefe wiwinshi yake sha har yanzun, bai daina ba, ba bari yayi ba. Ko ma shine dalilin da yasa Alhaji Modu ya hanashi auren Aise?
Sanda suka fito daga ofishin likitan kuwa sai da Alhaji Sa'id ya tabashi tukunna, kafafuwanshi ma hardewa sukayi ya kusan yanke jiki ya fadi badan Alhaji Sa'id ya rike shi ba
"Haba Mustafa? Wanne irin abune wannan?"
Saiya jingina bayanshi da bangon wajen, cikin rauni ya kalli Alhaji Sa'id
"Wallahi Sa'idu bansan ya cigaba ba, kasan lokacin da akayi case din ai...wallahi na dauka ya bari, na dauka ya daina shisa harna nema masa auren nan, wallahi...."
Kallon da Alhaji Sa'id yayi masa yasa shi kasa karasa maganar
"Ashe Haris din nakane kai kadai Mustafa, ashe akwai abinda yake bukatar rantsuwa a tsakaninmu? Ashe Maryaman dana mika ma Haris babu taradaddi sanin cewa taka ce itama kai ba haka bane a wajenka?"
Kai yake girgizawa ya kasa magana
"To me yasa kake mun wadannan maganganun kamar wanda yayi mun wani laifi? Ba zaka barni inji da abinda yake damun yarona ba saika batamun rai?"
Kamar a lokacin kuruciyarsu, idan Alhaji Mustafan yayi halin shi na zuciya an kasa tankwara shi, yaki jin maganar kowa sai an kirawo Alhaji Sa'id sai yace
"Kayi hakuri to Sa'idu"
Alhaji Sa'id din ya girgiza kai, har ranshi ciwon Haris din yafi damunshi fiye da shaye-shayen da akace yayi, wannan ai yana daga cikin kaddararshi, yana kuma yi masa addu'a, zai kara da wannan ne yanzun, in suka hadu su duka sai Allaah Ya yaye masa, tare suka koma reception din, tunda ance da Haris din yayi stabilizing zasu canza masa daki ne su cigaba da monitoring dinshi na kwana biyu, kafin daga nan asan mataki na gaba, sunje suka karasa duk wani cike-cike da ake bukata, Hajiya Rumana na mayar da kafarta inda Alhaji Mustafa ya cire tashi, tunda taje ta rasa ina suke dole ta dawo, baiyi mata magana ba
"Amman dai ba zama zamuyi mu kwana ba ai, tunda ga matarshi, kuma akwai 'yan uwa anan din"
Alhaji Mustafa ya fada
"Ni dai zan zauna saiya warware gaskiya"
Cewar Hajiya Rumana, ya juya yayi mata wani kallo batare da yace komai ba, Alhaji Sa'id yasan Mummy zata zauna da Maryama idan kwana ya kama, sannan zatayi tsaye akan duk wani abu ma, matar har tafi Murtala zumunci, shi kanshi yanda take kira tana gaishe dashi, haka yaranta Murtala baya kira. Amman yana so yayi magana da Maryama, ya zauna da ita kona mintina ne
"Babu laifi, mu dai jira zuwa yamman mugani, in aka canza masa daki sai mu tafi...bari inyi magana da Maryama"
Dan yaga kamar Hajiya Rumana ma tana bukatar kebewa da mijinta, har lokacin Mummy bata dawo cikin wajen ba, dan can kasan wata bishiya ta samu ta saka takalmanta tayi zamanta a wajen. Alhaji Sa'id ya samu ya zauna kusa da Maryaman da take ta wasa da wayar hannunta
"Mairaman Abbanta, midwife din gidana, da kin gama karatun ma ai da yanzun kece zaki duba Haris din kiyi masa allura"
Tayi murmushi mai sauti tana hango zatayiwa Haris allura, to zaima yarda? Shi din da take ganin rashin yadda da abubuwa da dama game da ita, zai yarda tasan abinda takeyi ya mika mata jikinshi?
"Kai Abba...ni da zan dinga karbar haihuwa, ai ba za'a kawoni irin wajen nan ba"
Shima dariyar yayi, ya dan sauke numfashi
"Ya kuke Mairama? Ba lafiya lau din da kike cemun a waya ba, ya kuke?"
Ya karasa maganar a hankali, cike da fatan ta fahimci abinda yake nufi, saida ta kalle shi tukunna tace
"Lafiya lau Abba, wallahi lafiya lau, yana mun kirki sosai, tunda ya dawo ne bayajin dadi, amman muna lafiya"
Ya sauke wani numfashin da baisan yana rike da iskar shi ba
"Kinsan me yake damunshi?"
Ta daga kai a hankali
"Likita yayi mana bayani, nasan zai karayi miki kema, yanda zaki taimaka masa ya kula da lafiyarshi, nasan zaki iya ko?"
Ta sake daga kai
"Yawwa 'yan matana, nasan ba zaki bani kunya ba daman, Allaah Yayi miki albarka"
Dadi ya ratsata, daman tasan Abban nata mutum ne mai yawan uzuri, mai yawan fahimta, ko da an fada masa hankalinshi ba zai tashi ba, watakila daman ya sani
"Amman Abba ai babu kyau shaye-shaye"
Ya jinjina mata kai
"Shisa nake so ki fara yi masa addu'a idan kinyi sallah, Allaah zai yaye masa, zai bari, sai kin dage sosai, kin tayashi kula da kanshi"
Ta danyi shiru
"Amman Adda Zahra tace shine zai kula dani, tunda shine babba"
Alhaji Sa'id yayi shiru, sai can yace
"Kin tuna sanda nayi hawan jini? Aka bani magunguna?"
Ta daga kai da sauri, tunda lokacin faduwa yayi, sukaita kuka kuwa, akace jininshi ne ya hau, amman gajiya ce, ba wani abu bane da zasu daga hankalinsu, ita dai nata bai kwanta ba
"Ke na nada mai bani magungunana idan lokacin sha yayi, ke kika kula dani harna shanye dan kar in dinga mantawa"
Kai ta sake dagawa, dan wannan abin da yayi mata a lokacin ya sama mata da natsuwa ne
"To kwatankwacin wannan kulawar ake nufi, shine babba, amman a wajen kula da lafiyarshi kece babbar"
Ta gane sosai, ta fahimta, zata kuma yi duk wani kokari da zata iya. Su Abban ne suka fita suka siyo musu abinci, da abubuwan da ma yake tunanin zasu bukata, harda maigadinsu da bai tafi ba ya samu waje ne ya zauna, sai Alhaji Mustafa yace direbanshi yaja motar Haris din, ya kaisu gida harda Maryama da Mummy dan Maryaman ta dauko abubuwan da suke bukata tunda zata kwana a asibiti. Haka akayi, wajen karfe biyar da rabi aka sakewa Haris daki, dan sunce bacci yakeyi, alluran da akayi basu sake shi ba, sunata dai canza masa karin ruwa, ba karamin rikici Alhaji Mustafa sukayi da Hajiya Rumana ba, saida ya rantse ba zata kwana ba tukunna ta hakura, tanata share hawaye, musamman irin ramar da taga Haris din yayi kamar wanda yayi wata yana ciwo.
A ranta tayi niyyar washegari ma saita dawo, ko Alhaji Mustafa bai barta ta kwana ba, haka zataita zarya tsakanin Kaduna da Kano duk rana sai taga ya warke ras, bayan tafiyarsu ne Mummy ta cewa Maryama ta zauna wajen Haris din itama zataje gida tayi musu abincin dare saita dawo. Kafin ta tafine da likita ya sake shigowa ake fada musu mutum dayane kawai zai kwana wajen Haris din, Mummy taso anyi wannan maganar kafin tafiyar su Alhaji Sa'id, dan suyi musu magana su barta ta kwana itama
"Akwai Nurses da zasu kula dashi ko da babu kowa ma, mu munfi son hakan..."
Dole taje ta dawo ma da Maryama da abinci, wajen karfe takwas da rabi ta tashi da niyyar tafiya tana tanajin kamar karta tafi saboda tausayin da Maryaman ta bata
"Zaki iya kwana babu wata matsala kuma Maryama? Tun da sassafe zanzo In Shaa Allaah...ko da Abbanki zai kira kice masa muna tare kar hankalinsu ya tashi..."
Dan murmushi Maryama tayi
"Babu wata matsala Mummy, ai kinga sunce qila ma sai goben zai farka saboda alluran da sukeyi masa, da nayi sallar isha'i nima kwanciya zanyi..."
Haka sukayi sallama, ta koma cikin dakin, tayi sallar isha'i data idar saita ja kujera saitin gadon da Haris din yake kwance ta zauna tana kare masa kallo
"Ya rame, ya rame sosai"
Haka Hajiya Rumana ta dinga maimaitawa, kuma yanzun data nutsu taga wannan ramar a fuskarshi, bata dai kai yanda ita din ta dinga fada ba. Tabi hannunshi