Advertisements
Chapter 14 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   14 / 51

39K to 42K   out of 151K words

mabanbanta turarukansu ya cika wajen ba, sai taji an saketa, Ahmad ya karaso ya kama hannunta yana janta a hankali, duk mutanen da sukazo ana tsaye ana kallonsu.

Babu irin surutun da ba'ayi ba lokacin da Alhaji Sa'id yace, iya yaran nashi ne maza da mata zasu raka Maryam dakinta, duk wanda yake son zuwa yaga gida yabi masu kai jere, kuma suma ba zasu kwana ba, ya toshe kunnuwanshi, yaran ne sukayi masa wannan rokon da kansu, duk da yace motocin da suke gidan sun isa, sai da aka aiko da motocin da duk wanda ya gani ya shaida sana'ar Alhaji Mustafa, shima mota daya ce ta 'yan uwanshi da zasu dauki amarya, suma gefe suka koma ganin Yayyenta maza tsaye bakin motar da suka ajiye, dan direban ma da ya kawo motar AbdulKarim ne ya karbi mukullinta yace masa yaje abinshi basa bukatar wani direba.

Su suka saka Maryam a mota suka zaunar da ita, Ahmad da kanshi ya koma yanda ya kama hannunta ya ratsa cikin mutane yaje gefen Adda Maimunatu ya kamo hannun Khairi da fuskarta harta kumbure saboda kukan da tasha, ya jata ya sakata a motar da Maryam take zaune, ya mayar da murfin ya rufe, shi kuma ya zagaya ya shiga gaban ya zauna dan shine zai tukasu, shi da Khalifa da tun kafin ma a hau titi ya juya ya cewa su Khairi

"Muna shiga daji zansa Ahmad ya tsayar da motar nan inci ubanku idan kuka cikamun kunne da wannan koke-koken kamar wanda akayiwa mutuwa, musamman ke Khairi tun safe naji ana fama dake...Zahra tace mun ko abinci bakici ba duk yau, to idan auren ne a ranki in muka dawo sai in yiwa Abba magana kema ayi miki yanda aka yiwa Maryam din"

Sanin halinshi yasa su hadiye kukan nasu babu shiri

"Karbi nan"

Ya cewa Khairi yana mika mata wata leda da tajita da sanyi

"Kema ki bude wannan uban lullubin ki shaki iska, ku kuma cinye komai ku mikomun ledar..."

Saida Khairi ta bude taga yoghurt ne masu sanyi roba biyu, sai tsire da gurasa, gefe Zahra ta jashi tace masa yasan yanda zaiyi yasa daga Khairin har Maryam din su sa wani abu a cikinsu dan basu ci komai ba.

"Ya banji kun bude bane? Ahmad ko zaka samu waje ka dan tsaya in koma baya?"

Da sauri Maryam tace masa

"Ci zamuyi Yayaa"

Yafi kowa wasa da dariya a gidan, shine zaka samu yasa hannu a cikin kwanon abincinsu yana ci tare, kuma shine irin Yayyen nan da kowa yake tunkara da maganar a bashi kudi, ko a siya masa wani abu, amman kuma sunfi tsoronshi akan kowa, saboda a karkashin wannan wasa da dariyar, Khalifa na da zafi idan sukayi masa kuskure, sannan ba kamar sauran da zasuyi hargagi da zagi ba, ko su kai duka inka kauce ko ka ruga shikenan, Khalifa zai rikeka, zai saka bulala ya zane maka jikinka, inya fita saiya dawo maka da wani abu daka tambaye shi, kuma baka isa kace zakayi masa fushi saboda ya dakeka ba, saiya kara maka, yasa ka zauna a wajen ka gama kuka kuyi labari.

Ita Maryam dinma ta manta rabon da taci abinci irin wannan, batama san tana jin yunwa ba saida tsire da gurasar suka fara sauka a cikinta, sai gashi jikinta har rawa yakeyi, ta kuma shanye tata yoghurt din tas, tukunna ta karbi tissue din daya basu ta goge hannunta, data gyara zamanta ta jingina jikinta da motar sosai ta rufe idanuwanta, tsakanin sanyin AC din, kamshin turaren daya cika motar mai kwantar da hankali, da kuma karatun Qur'ani cikin muryar Qaari Abdullahi Abba Zaria, sai koshin da tayi ya tattaro mata gajiya da rashin wadataccen baccin da bata samu ba na tsayin kwanaki.

Zuciyarta ta nemi salama da kanta ta hanyar barin bacci ya dauketa...

15

Har yanzun Haris bashi da wasu abokai sama da 2Pac, Barde da kuma Lalaye, sauran kawai a hadune ayi sharholiya a wuce wajen. Barde a halin yanzun yana kasar Ingila, 2Pac kuma yana India, a cikinsu Lalaye ne da mahaifinshi ya fitar dashi kasar waje sai yaki karatun gabaki daya, haka ya tattaro ya dawo, da yake dan kasuwa ne babba, saima ya tattara Lalayen ya mayar dashi Kano, ya hadashi da kula da wani babban shagonshi a kasuwar singa, inda suke bada sarin kayan masarufi, ya hadashi da wasu amintattun yaranshi. Ga mamakin kowa sai kasuwancin ya karbi Lalaye, yanda akayi tunanin zai kadar da katafaren shagon yayi shaye-shayen shi da bin mata, sai ya basu mamaki, wani abu daya sanyaya ran mahaifinshi yasa yace ya mallaka masa shagon, shima ya tsaya da kafafuwanshi.

Sai dai babu abinda Lalaye ya fasa, tunda gida gareshi a cikin garin Kanon inda yake cin karenshi babu babbaka, kuma shine mutum na farko da Haris ya fadawa an daura masa aure, ya kuwa sheke da dariya yana fadin

"Wasa kake amman ko?"

Da yake waya sukeyi sai shima Haris din yayi gajeriyar dariya

"In ban manta ba na baka wata kusan takwas Lalaye, ni kuma wanne tsautsayi ne zai sani wasa da kai in jawa kaina raini"

Ashar din da Lalayen ya maka masa sai da yasa shi yin dariya mai sauti

"Da gaske an daura aurena yau kwana goma, ina tunanin kaman a Kano zamu zauna ma, ban dai gama yanke hukunci ba"

Gabaki daya lamarin ne yake ta bawa Lalaye dariya

"Ashe Ganja zaka rigamu shiga daga ciki...nan fa da wata tara sai dai muji eya ne"

Haris yaja tsaki, baisan ya Maryam take ba, amman haka kawai tunanin ma hada shimfida da ita sai yaji yasa kanshi ya hautsina

"Kana da matsala..."

Ya iya fadi kawai, kuma lokacin daya tabbatar da Kanon zai zauna, aka gama komai aka tsayar da ranar da za'a kai Maryam, Lalayen ya kira

"Dole fa a fitar dakai kunya"

Cewar Lalaye, Haris baija zancen ba, ya dai hada abinda yake tunanin zai bukata tun sauran kwana biyu yayi tafiyarshi garin Kanon, kuma daya isa gidan, maigadin da aka samar musu nata jera masa barka da zuwa har saida yaji babu dadi saboda babban mutum ne, amman kamar zai durkusa masa, tunda ya fito daga motar ya karasa matattakalar da zata hadashi da falon wani kamshi mai sanyin gaske ya daki hancinshi, Maminshi na son turaren wuta, har saida yayi zaton babu wanda yake amfani dashi kamar ita, dan ya taba jin Anisa nace mata

"Mami inda zamuje asibiti ace huhunmu ya samu matsala wallahi ba zan musa ba, na tabbatar hayakin turaren wutarki ne da muke shaka tun muna jarirai"

Shi dai yana son irin kamshin turarukan, shisa ya fada mata ake saka masa har a daki, wannan din yayi masa dadi, wani irin kamshine da zakaji kanaso ka samawa kanka hutu a cikinshi, daya bude gidan kuma sai yaji ashe baiji komai ba, saida ya sauke numfashi. Abinda Haris baisani ba, shine wannan aikin Adda Zahra ne, ko kudi ta baka sai kaji suna kamshin turarukanta, 'yan gidansu na yawan yi mata mitar duk garin Kano, saita tsallaka har Bauchi ta siyi turarukan wuta, sai dai tayi dariya abinta

"Nifa turare indai ba Meens incense ba akai kasuwa (08036387204)"

Tunda itama kawarta da suke makaranta lokacin itace 'yar Bauchi, ita ta bata shi a gudummuwar biki, sai gashi ta zama babbar customer, suma suna mata mitar, duk zuwan da zasuyi gidan sai sun roqeta ta dibar musu, ko suce in za'a kawo mata suna so a hado dasu. Shisa ta siyawa Maryam itama, kuma kafin subar gidan bayan sunyi jere saida ta saka a kusurwoyin kowanne daki na gidan, harda bayi a kasko-kasko, sannan suka rufe gidan, har window duk suka datse dan so takeyi ya kama ko ina, yanda in anzo kawota kafin ma su maimaita kowa zaisan ya shigo gidan amarya.

Jeren da akayiwa falon ba mai hayaniya bane ba, komai ya dace da mazaunin da aka ajiye shi, daya daga cikin bedrooms din ya bude, da yake 3 bedroom flat ne, ya ajiye jakarshi, sai yaji kamar bai kamata ya kwana a gidan ba, ya dauki abinda zai bukata a wata karamar jakar, ya fice yana mayar da kofar ya rufe. Hotel ya samu ya biya kwana uku, saboda Aise ne ya kasa kashe wayarshi a kwanakin biyun, yanda Hajiya Rumana take jera masa kira kan kira saida ya daga wayar dan dole

"Ni zan dinga kira kana kin dagawa Haris? Ashe akwai ranar da zaka zabi wata mace akan uwarka"

Ya dafe goshinshi

"Nifa babu macen dana zaba akanki Mami, kece kika kasa fahimtata"

Saita kara tunzura kuwa

"Taya zan fahimceka bayan ka biyewa ubanka zaku kasheni da raina...auren da nake hango rabashi kafin yayi nisa ashe kai zaka kwaremun baya"

Cikin gajiya da maganar raba wannan auren da takeyi masa ita da Aise yace

"Nifa ba zan rabu da ita ba, bansan sau nawa zan fada muku ba, ba zan rabu da ita ba"

Ta kuwa kwaso salati muryarta na rawa, yasan kuka zata saka masa

"Ko dai asirin da ake yawan magana akai bana yarda dashi ne tsautsayi ya fado kaina yau? Ko sun shanyemun kai Haris"

Dariyar takaici ta nemi kwace masa

"Kaina na ciwo Mami, dan Allaah ki huta, nima kibarni in huta akan maganar auren nan, an riga an daura, kema da bake aka kakabawa auren ba kinajin kin kasa samun abinda kike so, nikuma fa? Dan Allaah kibarni akan maganar nan..."

Ya karasa a gajiye, kafin kuma tace wani abu ya kashe wayar gabaki daya, daman da safiyar sukayi tashin hankali da Aise

"Sonta kakeyi?"

Ta tambaya, gabaki daya ya gaji, ya gaji da komai

"Ko kalarta ban sani ba Aise, sau nawa zan maimaita miki?"

Taja numfashi

"To akan me ba zaka saketa ba, karka kace mun saboda Baba"

Ya kuwa fada din yana dorawa da

"A cikin taro Uncle Modu ya kunyata mun Babana, ya hanani aurenki, so kike nima in bashi kunya, ni da yakejin ya isa yayi iko dani? Saboda ke?"

Cikin wani irin kuka da yakejin sautinshi har kasan zuciyarshi tace

"Ban isa ba ko? Ni ban isa ka rabu da ita saboda ni ba"

A gajiye yace

"Baki isa ba, ke baki isa in watsawa Babana kasa a ido saboda ke ba, na gaya miki bana sonta, banma san ya take ba, dame kike so inji? Rashinki da tunanin ranar da zan sameki? Idan kika sake cemun in zaba ko ke ko ita zan baki mamaki wallahi"

Itama cikin hargowar tace

"Ka zaba, wallahi sai dai ka zaba, koni ko ita, ba zan cigaba da sonka kana rayuwa da wata a matsayin matarka ba, ba zan aureka a mace ta biyu ba, ba zan iya ba"

Ya numfasa, yaji kamar iskar tayi masa kadan, wani abu ya qulle a cikin kirjinshi yana kare matse masa iskar da yake shaka

"Ke zaki kashe wayar koni? Bansan ya zan miki sallama ba"

Baisan dakikun daya dauka yanajin sautin kukanta ba, kafin ta iya cewa

"Me kake nufi?"

Wani abu na ratsa gabobin jikinshi yace

"Na zabeta..."

Sai ta kashe wayar, tana hadawa da wani haske da yakeji kuwa, duhu ya maye masa gurbinshi. Haka ya wuni banda hayaki babu abinda yake shiga cikinshi. Shisa duk abinda Lalaye yace masa sai yace

"Duk yanda kaga ya kamata"

Haka ya samu wasu abokanshi daya hadu dasu anan Kano din, da yake kuma kudi ba matsala bane, sai dai Lalaye yaja shi sukaje wani shago, a cewarshi ango babu manyan kaya ai bai amsa sunanshi ango ba, wasu tsadaddun shaddoji ne suka siya harda huluna da takalma, ya dinga kallon kayan, shi tunda yake tsakaninshi da manyan kaya sai sallah in zasuje idi, suna dawowa inya cire aka wanko sai yazo daukar wasu kayan yake ganinsu, sababbin kayan da yake dasu manya da bai taba sakawa ba kuwa kilan in suna da expiring date daya dauko zasuyi gari ne a hannunshi saboda ajiya. Yaji dariya na neman kamashi da yake tunanin zai saka babbar riga. Washegari kuwa da yake yana tunanin zuwan nasu, kuma Alhaji Mustafa ya bashi lambar wani Ahmad yace Yayan Maryam dinne, zai kirashi.

Yana ganin kiranshi yace masa sun kusan karasawa suka shirya shi dasu Lalaye cikin manyan kayansu, sai baza kamshi sukeyi, inka kallesu zakayi tunanin sunfi shekarunsu, kwarjinin nan na farar shadda da manyan kaya da suke suturta halayya sunyi musu wannan adalcin. Shi kanshi sai yakejin shi daban, ko dan da gaske daban din yakeji ne oho, kamar wanda yake yawo a cikin mafarki, saida Lalaye yasa sukayi tsaye-tsaye, yanata mamakin kayayyakin da aketa lodawa a bayan motocinsu, tun daga kan lemuka harda abinci

"Me za'ayi da duk wannan abincin Lalaye?"

Ya kalle shi kaman baiga dalilin da zaisa yayi masa tambayar nan ba

"Na tarbar baki mana, ko haka za'a jewa mutane sun taho tun daga Kaduna, kaifa Ganja baka da kai wani lokaci, shisa Barde yace in tsaya inga komai ya tafi dai-dai karka ja mana abin kunya"

Haris yayi shiru, yanajin su sunata masa tsiya kala-kala da Lalaye ya kira ya fada musu, shi 2Pac ma haka yace daya sani da wuri, daya zo, amman zasu ware lokaci dan dole ne suyi qara'i, shagalin da ba'ayi musu bane zasu zo su huce takaici. Lokacin da suka isa kuwa saida Haris yayi mamakin ganin zaratan mazan da suke tsaitsaye a jikin motoci sunata hirarrakinsu, haka suka karasa aka dinga gaisawa kamar ansan juna, tunda matan sun shiga ciki da Maryam tun isarsu, da suka fada musu akwai abinci, sai daya a cikinsu yayi waya aka fito aka dauka, kuma Lalaye ne yace su fita su suci nasu abincin a waje.

Sai dai wanda suka kai da yawa, da AbdulKarim ya fadawa Zahra saiya hana tace su shiga falon suci anan, a gyara mata komai tunda juyawa zasuyi a ranar ba zasu kwana ba, haka akayi harsu Haris din, shi dai su Lalaye da wasu a cikin Yayyen Maryam din nata tsokanarshi da cewar karya ji kunya ya saki jiki ya kwashi abinci, amman sai yake yake yi musu, Maltina kawai yasha, AbdulKarim ne yace

"Nifa na kasa natsuwa da yanda kaqi cin abincin nan, duk wani warning da nake shirin doka maka kan Kanwata ai sai kasa jikina yayi sanyi..."

Yayi dan murmushi kawai, amman duk da haka, yaji su, yaji duk wasu maganganu da suke fada masa a wasa da dariya, zai iya cewa gargadinsu ko karamin yaro ne shi yaji shi, dauka ce dai wani abu na daban, kuma tare suka fita suka tsaya a harabar gidan ana dan taba hira. Su Zahra kuma suka gyara komai, ta kirasu tace a kwashe sauran abincin a bayar dashi tunda ko sun barshi nan tasan lalacewa zaiyi, su Haris din baci zasuyi ba, su juyawa zasuyi kar dare yayi musu a hanya, sallar la'asar kawai suka tsaya sukayi. Tashin hankalin yana cikin dakin da suka ajiye Maryam, ita kanta sama-sama take jinta, da yake baccin da tasha a mota data tashi sai taji nauyin da kanta yayi ya rage.

Komai ya washe mata, shisa kuka tayi ba dan kadan ba, wani irin kuka da saida su Adda Maimunatu suka tayata lokacin da suka iso, aka riketa akace tayi addu'a, sannan ta shiga gidan da kafar dama bayan tayi sallama, nan bakin kofa ta durkusa tanajin kamar kirjinta zai rabe biyu, zuciyarta sai bugawa takeyi

"Kirjina Adda, ciwo, komai ciwo yakeyi..."

Suka kamata suna shiga daki da ita, akan gadon ta kwanta ta dunkule jikinta tana sakin wani kuka da yake fitowa tun daga zuciyarta, da akace ta hada kayanta da take so a tafi dasu jiya, sai Khairi ce tayi mata, ita dai sanda ta mike kananun abubuwa ta dauka, harda brush dinta, suka dinga mata dariya

"Me zakiyi da tsohon Brush ke da kike da sababbi"

Inji Asiya, Adda Maimuna ta shigar mata

"Ku ina ruwanku? Brush dinku ne? Dauki kayanki Maryam ki rabu dasu kinji"

Daman batayi niyyar musu magana ba, ta fito da turarukan nan da take ta boyo, wanda Ishaq ya bata, ta hada hardasu tanajin zuciyarta kamar an dora mata dutse. Ko yanzun dinma tunanin wannan turarukan takeyi, tunanin shikenan, rayuwarta ta tsaya anan, ita da Ishaq har sun kare tun kafin ma su faru? Tunanin me yasa duk a gidansu sai ita kaddara zata zaba haka? Yanzun da suka kawota gidan nan suna nufin tafiya zasuyi su barta a cikinshi? Babu wanda ya bata hakuri, batasan waye ya dagota ya cire mata laffayar jikinta ba saboda kukan da takeyi, haka batasan waya riketa a jikinshi cikinsu ba tayi kukanta har saida taji ya isheta, da kanta ta mike tana tambayar bayi cikin disashiyar murya.

Data shiga tayi nufin wanke fuskarta ne kawai, amman sai taji jikinta nayi mata kaikayi kamar tayi kwanaki batayi wanka ba, sai gata tana cire kayanta, akwai komai daga kan soso zuwa sabulu harda shower gel a cikin bayin an jera a mazauninsu, da a hayyacinta take watakila da tsarin bandakin yayi mata kyau, ita mai son abubuwa masu kyau. Da ta fara wankan kuma sai taji kamar akwai abinda take so ta wanke, kamar tana so ta wanke wani kaso na rayuwarta, bata dai san wanne ba, kafin auren ko auren, ko kuma yanzun, ta dai wanke wani kaso yabi ruwan nan ya shiga rariya. Ko zafin da jikinta yakeyi bataji ma, saida aka kwankwasa kofar bayin tukunna ta hakura, ta dauraye jikinta, ta mayar da kayanta, sai tayi alwala.

Batason musu ne, shisa ta dan tsakuri abincin da aka shigo musu dashi, da yake haduwa sukayi a waje daya sukaci tare, kuma batayi musu ba da suka zaro mata wata doguwar rigar atamfa suka bata ta saka, tayi sallah, Adda Zahra ta kara gyara mata fuskarta, harda wani jambaki aka shafa mata, jambakin da batasan ina ya goge ba, ko a jikin Khairi ne da ta kankame lokacin da sukeyi mata sallama, duk wata nasiha da hudubar Addan ma bata wani fahimta ba, babu abinda takeji sai tafiyar da zasuyi su barta. Tun suna tayata alhini ita da Khairi akan irin kukan da sukeyi, har saida Adda Zahra ta watsa musu zagi, baisa sun daina ba, balle ma su saki juna

"Wallahi zan kira Khalifa yazo yaci ubanku tunda bata mana lokaci zakuyi..."

Ita Maryam dince ta fara janye jikinta daga na Khairi, bata daina kukan da takeyi ba, Asiya da take ta sauke ajiyar zuciya ta ja hannun Khairi suka fice, aka bar Maryam da Adda Zahra, ta kamata ta mayar da ita kan gadon ta zaunar da ita

"Ki kwantar da hankalinki dan Allaah, kinji duk abinda na fada

14 / 51