Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
ya kasance mai tsananin hakuri karya dinga koro musu ita saboda rigima da taurin kanta. Shi ji yakeyi kamar ace ya hadata da wata na'ura ko na rana dayane a hasko masa diramar da yake hasashen zasu kwasa da wannan mijin.
Ishaq bayajin yayiwa AbdulKarim sallama, dan iska yaji yana nema, jikinshi ya dauki dumi, daga wajen shagon aski ya nufa ya zauna yana ce masa ya aske masa kan, da ya tambayeshi kowanne iri zaiyi masa sai kawai yace
"Ka rabani da sumar nan kawai...banajin iska ne, ka aske komai"
Amman saiya kasa aske komai din, ya dai rage masa, yayi mai askin da ake kira da low-cut, amman kuma baiji ya samu iskar da yake nema ba, ya dai bashi kudin ya fice, tafiya yakeyi har saida kafafuwanshi sukayi masa alamar idan ya kara taku daya tabbas zasu kunyatashi tukunna ya tsaya, ya samu mai mashin ya hau zuwa tasha, ya kuma shiga motar Kaduna, shine fasinja na farko a cikin motar shisa ma ya dade a motar, da ya karasa Kaduna yana fatan ya samu labari akasin wanda yaji a bakin AbdulKarim sai suka tabbatar masa da gaske an daurawa Maryam aure, da gaske an gina katanga a tsakaninsu. Kwanciya kawai ya samu waje yayi yanajin zazzabi ya rufe shi.
Ashe haka yake sonta da yawa bai sani ba? Yaso ya tashi ya juya inda ya fito ya kasa, aiko babu komai ya kamata yayi mata sallama, ya rasa wa zaisa ya kira masa itane sanda ya taso
"Kanwata"
Ya kira muryarshi na karyewa, saboda yau da take tsaye a gabanshi sai yake ganin wannan katangar da ta rabasu, bakinshi har daci yakeyi
"Ina wuni"
Ta tsinci kanta da furtawa, yaji murmushi mai sauti ya kwace masa
"Wanne wunin? Wunin da nayi a hargitse? Nayi kwauron baki ko Maryam? Ban furta da wuri ba, ko dama can akwai shi? Nine ban sani ba"
Ta rasa abinda zatace masa, tayi tsaye kanta a kasa, dan abubuwan da takeji basu da yawa, kanta yayi nauyi, duka jikinta yayi nauyi, kamar ruhinta ne a gajiye, saiya kwanta yana neman jan gangar jikinta su hadu su kwanta tare
"Daman zan ganki ne, zanyi miki fatan alkhairi"
Cikin karamar murya tace masa
"Nagode..."
Yaja wani numfashi da Maryam takejin ya samu waje ya zauna mata, haka kawai ta kasa kallonshi, duk da tanajin nashi idanuwanta a kanta
"Maryamm..."
Tsautsayi yasa ta daga kai, idanuwanta suka sauka cikin nashi, kuma tunda take jin labarai akan karaya, ta kuma ganta lokacin da Anas yayi hatsari ya karye a kafa, bata taba tunanin zata ganta a cikin idanuwan wani dan adam ba, tunda ai ko zuciyar da ake ikirarin tana karyewa kowa ya yarda bata da kashi, sai idanuwa? Murmushin da yayi mata ma a karye yake
"Allaah Yasa ki samu ninkin abinda nake tunanin zaki samu a tare dani"
Bai jira amsarta ba ya juya, sai Maryam take tunanin to ko dai idanuwanta ne sukeyi mata wasa? Tafiyarshi ma a karyen take ganinta, ko kuma kalmomi ne sukayi mata karanci shisa ta rasa guda daya da zata samu ta jinginata da abinda take gani a tare da Ishaq din?
Ko kuma itace wani abu ya karye a tare da ita?
Anan tsaye Khairi tazo ta sameta tana kama hannunta
"Dan Allaah Adda kina ganin karaya a jikina?"
Da mamaki Khairi ta kalleta
"Karaya?"
Maryam ta daga mata kai
"Ko a idanuwa na, basu karye ba? Ko jikina?"
Muryar Khairi na rawa tace
"Dan Allaah ki bari Maryam, dan Allaah ki daina..."
Ta karashe maganar idanuwanta cike da hawaye, yanda Maryam din ta koma kamar wata 'yar tsana sai yanda akayi da ita yana nukurkusar Khairin daman, ji takeyi kamar taje ta samu Alhaji Sa'id tace masa a warware auren da Maryam a mayar kanta, tunda ita babu wanda take so, batama tabayin wani saurayi ba, tana ganin abin ya taba Maryam ne saboda Ishaq, inda ba Ishaq zatayi mamaki ne an daura mata aure lokaci daya, da yanzun ma kila suna ta dariyar abin, ta ishi kowa da cewa anyi mata irin auren da, irin auren da tunda aka basu labarin shi saida ta shafe watanni tana damun Khairi da zancenshi, wata tambayar ma idan tayi mata sai dai ta girgiza kai tace
"Kina da matsala"
Ita kuma tayi dariya
"Allaah abinne yake bani mamaki, ko su Abba ma irin auren da sukayi kenan oho"
Nan nema tace
"Allaah Yasa Hajja taji ki"
Ta kama bakinta tana dariya. Ko ruwan sama bai taba firgita Maryam haka ba, bata taba ganinta a gigice irin na kwanakin nan ba. Haka tajata suka koma ciki, kuma daga ita har Maryam din abincin da basu ciba kenan a wannan daren. Haka suka kwanta kowa da abinda yake sakawa a zuciyarshi.
*
Daga Alhaji Sa'id har Hajjan hidima suke haikan, zaka rantse daga kan Maryam sun gama aure, tunda Alhaji Mustafa ya fada masa ranar da Haris zai dawo yake maganar kayan dakin Maryam, kar suje ayi maganar tarewarta, sai gashi a karo na farko Hajjan ta ajiye kawaici a gefe ana shiga kasuwa da ita, kowa ya kallesu a cikin yaran yasan shi yana bada kudine da fatan su wanke masa abinda yakejin yayiwa Maryam, ita kuma Hajjan tayi tsaye ne tana so ta dauki duk wata kala da tasan Maryam naso dama wani abu da zata tuna ta nuna sha'awarshi a daya daga cikin bukukuwan 'yan uwanta, ko babu soyayyar mijinta a ranta, to tanaso inta fito dakinta taci karo da wani abu da zai sanyaya mata zuciya, kafin fatansu da addu'arsu ta karbu.
Kullum Khairi saita matse hawaye in taga sun shirya zasu tafi Islamiyya banda Maryam, ita ta gama jarabawarta ta aji shidda tana jiran result ne da kuma lokacin da zatayi jamb, saboda haka tana zuwa wata makarantar koyon computer anan kasan unguwarsu, babu nisa da kafa take zuwa, sai dai tunda akayi zancen auren nan bataje ba ko sau daya, Islamiyyar ma dan tasan Hajja ba zata barta ba shisa take shiryawa suna tafiya da Asiya, kwanakin ma zuwa suke suna wuce musu babu wani sabon abu a ciki.
Sabon abin ya faru ne ranar da suka tsinkayi muryar Adda Zahra na fadin
"Kano kuma? Kano za'a kaita? To wai akan me?"
Khairi taji kamar wani abu ya rushe a cikin kirjinta, ai ko da ba'a kama sunan ita din ba tasan Maryam ce, Kano kuma? Akan me za'a dauke mata 'yar uwa a kaita har wata Kano? Shi Haris dinne ma yace Kano zai zauna kome? Yau dai taji wani abu da bataji ba tunda aka fada musu maganar auren nan, taji tana so tayi ido biyu da Haris din nan, ta kalle shi ta tambaye shi
Dame yake takama?
14
Tun tasowarshi abu daya ya sani, yasha jin bashi da kowa banda Hajiya Rumana, ita dinma yasan saboda shi dolenta ne, son da takeyi masa ba zabi bane a wajenta tunda ita ta haifeshi, bashi da kowa da ya taba sonshi ko ya damu dashi haka kawai batare da wani dalili ba sai abokan da yake haduwa dasu a makaranta, a cikin abokan nan ma su Barde sune mutanen farko da yasan sun soshi haka kawai, yana son su Munira da Anisa, amman ba wata shakuwa bace a tsakaninshi dasu, ya taso yaga suna da juna ita da Anisa, kusan komai tare sukeyi kamar 'yan biyu, fadan da akeyi tsakanin sako da sako ma su suna jimawa bai gifta musu ba, tunda Anisan wata irin makauniyar kauna take yiwa Munira kamar bata da kowa sai ita, shisa take kaffa-kaffa da bacin ranta.
Yaran Umma Fadime basa shigowa bangarensu, makaranta daya suke, amman ba tare ake kaisu ba, su yawanci ma Hajiya Rumana tafi kaisu da kanta, taje ta daukosu kuma. In dai yana cikin gidansu, zagaye yake da mutane, amman kullum cikin kadaici yake, shisa da Munira ta kirashi zatayi masa wasu maganganu yaja mata tsaki ya kashe wayarshi, ba zai tuna rana daya daya taba mata shisshigi a rayuwarta ba, to inama ta sakashi a ciki? Sai yanzun zatace masa
"Haris kaine zaka biyewa Baba ku kashe mana Mami ko? Me yasa ba zaka saurareta ba?"
Ta kyaleshi yaji da abinda yake damunshi, kowa ma ya kyaleshi, harda ita Mamin
"Nifa tunda can bani da ra'ayin zama a Kaduna Mami, bamu taba maganar bane ba, a Kano zan zauna na riga na fadawa Baba, har an samu gidan da yayi mun kuma na biya kudin"
Akwai kudadenshi da yake tarawa, na aikace-aikacen daya dingayi a Italy, bai taba kashe ko naira goma a ciki ba tunda masu bashi kudin kashewar suna da yawa, harma baisan abinda zaiyi dasu ba wani lokacin, daman niyyarshi in suka kai wani adadi ya fara gina kasuwancinshi dasu, kowanne yaro na gidan Alhaji Mustafa yana da gidan daya siya da sunan shi, wasu anan Kaduna, wasu a Abuja, kamar yanda kullum cikin ware wani kaso na dukiyarshi yake yana adanawa da sunayensu, shisa yaso Haris din yayi hakuri ya zauna anan Kaduna, amman yaki, da yake bayason matsa masa akan komai kuma tunda ya karbi auren nan saiya kyaleshi.
Ta wata fuskar ma sai yake ganin kamar zaman Kanon sai yafi musu alkhairi akan Kaduna, saboda Hajiya Rumana, shirun da tayi yana da tabbacin bana alkhairi bane ba, kuma dan ta dinga wanke kafa tana musu zarya a gida ta matsawa 'yar mutane batare da izininshi ba, ba komai bane a wajenta. Ya dai yiwa Alhaji Sa'id maganar Kano zasu zauna da kuma lokacin da suka yanke zata tare din shi da Haris, haka yace
"Allaah Ya kaimu lokacin Yasa alkhairinsu na tare da zaman Kanon"
Yaji dadi, ko da Haris bai gani ba a yanzun, yana da yakinin wata rana saiya gode masa da zabin nan, ita kanta Hajiya Rumanan sai lokaci ya nuna mata cewar ba zata taba samu surukai nagartattu kamar Alhaji Sa'id da matarshi ba, saita rissina tayi dana sanin kiyayyar da take nunawa auren, tunda ba karamin tashin hankali tayi masa ba akan maganar zaman Haris a Kano, saboda kin gaskiya ma haka tace shine ya kitsawa Haris maganar
"Ai wallahi baku isa ku rabani da dana ba, baku isa ba tunda babu wanda yayi mun dakon cikinshi"
Saima ta bashi dariyar daya kasa boyewa saida ta fito, ta kuwa kara haukacewa tana wani irin kuka da bai taba ganin tayi ba a tsayin zamansu, amman ya gaji, yayi lallashin duniya taki, shisa ya fice ma yana barinta a dakin. Abinda yake kara yi mata zafi shine kaf 'yan uwanta babu wanda ya goya mata baya, tasan tunda Alhaji Jibril yaga farin auren ba zai taba bari wani yaga bakin shi ba, ga bakin cikin lefen da taji ance an kaiwa Maryam din, tunda danginshi dan neman fitina da suka dawo daga wajen kai lefen sai suka biya tanan gidan wai zasuyi mata Allaah Yasa alkhairi, ta kasa danne zuciyarta
"Idan ma gulma ce ta kawoku dan kuyimun dariya sai dai ta kare a kanku wallahi, dane babu wanda ya isa ya rabani dashi, kuma wannan auren da yardar Allaah babu inda zaije"
Da yake darajar Alhaji Mustafa kawai takeci a wajen kaf danginshi, dukansu haushinta sukeji na yanda bata kaunar ganin sun rabeshi suka kuwa biye mata, dakyar wata Gwaggonshi ta tsawatar musu, suka fice suka koma bangaren Umma Fadime. Tunda Hajiya Rumana take bata taba sanin cewa akwai wani abu da zai daga mata hankali fiye da lokacin da Alhaji Mustafa ya kara aure, kuma matar ta fara haifa masa yara kafin ita ba sai yanzun. Dan nata namiji tilo ne take kallo ana kokarin kwacewa, ita ko da Aise ce Haris ya aura ba zataso ace ya tafi Kano da ita ba, yayiwa idanuwanta nisa, balle kuma wata Maryama.
Yanda taci burin bikin Haris, irin shagulgulan data dinga hangowa zatayi shikenan? Sunbi ruwa ake nufi fa, inda hawaye na karewa da tuni nata sun kare saboda yawan data zubar daga daura auren nan zuwa yanzun da take ganin da gaske babu yanda zatayi da Haris, da gaske yaki saurarenta, dan kar yaga fushin da tayi ma saiya dauke kafarshi daga shigowa sashin nata gabaki daya. Batasan yana can yana fama da zuciyarshi da kuma Aise ba, tunda ya siyi sabon layi, ya saka kudi a ciki sosai ya kirata, tanajin shine kuma ta fara dariya tana fadin
"Kiranka nake ta jira..."
Tana cigaba da dariya, wai Binta ta zuga Alhaji Modu, tun jiya daya dawo ya fada mata wata magana da ta kasa daina dariya
"Basu san da gaske babu wani abu da zasuyi da zai rabamu ba ko?"
Ya numfasa, kai tsaye yace mata
"Ba karya bane Aise, Baba yaje Maiduguri nema mun aurenki Uncle Modu ya hanashi, shine ya dauramun aure da 'yar abokinshi...amman da gaske ne, babu wani abu da zasuyi da zai rabamu, ni dake mun san hakan"
Sai ta sake kwashewa da dariya
"Saboda na gaya maka inka auri wata bayan ni zan iya mutuwa shine kaima abin ya zame maka wanda zakayi amfani dashi ka tsokane ni ko? Zaka dawo...zaka san ka fadamun maganar nan Allaah"
Cikin wata sabuwar damuwar yace
"Ba wasa nakeyi ba, ba wasa nakeyi miki ba, an daura aurena"
Kawai saita kashe masa waya, ya sake kira wajen sau biyar tana kashewa, saiya kyaleta, da kanta ta kirashi da daddare ya sake tabbatar mata da ba wasa yakeyi ba, an daura masa aure
"Ka sake ta"
Ta fadi cikin wata irin murya data sa kirjinshi bugawa
"Ba zan iya ba"
Ya furta kai tsaye
"Me yasa?"
Itama ta tambayeshi
"Saboda Baba...ba zan iya ba saboda shi Aise, dan Allaah ki fahimce ni"
Cikin ihu tace masa
"Taya zan fahimceka? Baban ne zai zauna da ita ko kai?"
Shima da hargowar ya amsa
"Karki fara, Babana nace, karki fara Aise"
Yanda take sauke numfashi yasan kuka takeyi
"Ka zaba, ni ko ita, wallahi sai dai ka zabi daya a yau din nan"
Duk wasu kalmomi da ya furta abu daya Aise ta dinga maimaitawa
"Ni ko ita?"
Daya kashe wayar ganin ba zata saurare shi ba saita dinga jera masa sako iri daya, tambaya daya amman ta tura masa ita tafi sau hamsin, har email dinshi tabi. Kuma tun ranar in ya kirata tana dagawa abinda zata furta kenan, ba zata taba bari suyi wata magana ba, kirjinshi yayi masa nauyin da baisan ya zaiyi dashi ba, ko baccin kirki baya samu, a wannan lokacin ba zaice ga adadin wiwin daya bankadawa cikinshi ba, abinda yake fitar dashi daga gidan kenan a wannan lokacin, saboda bayajin ma fita sam, duk yanayin da yake ciki ba zai taba yarda yasha wani abu a cikin gida ba.
Wai kuma a wannan yanayin ne Alhaji Mustafa ya kalle shi yace masa
"Sa'idu yayi mun magana kan karatun Maryam, kasan aji shida ta shiga, shekarar nan ne ya kamata ta zana WAEC dinta..."
Shikuwa ina zai sani, yarinyar da baima san ya take ba, ta ina zai san wani matakin karatunta, to wai akan me ma su duka suke tunanin abinda suke so zaiyi bayan shi suna neman yi masa katanga da abinda yake so?
"Kaga da anan ne saita cigaba da zuwa makarantarta, amman tunda Kano zaku zauna sai dai ka nema mata wata makarantar acan"
Ya amsa da
"To Baba"
Kuma shima Alhaji Sa'id din, Hajja ce tayi masa maganar bayan ya gaya mata suyi kokarin kammala duk wata siyayya da zasuyi, Kano za'a kai Maryam
"Kayi musu maganar karatunta, dan Allaah karya zamana karatunta ya tsaya, tunda kaga auren nata yazo daban dana 'yan uwanta"
Yanata juya abin a ranshi daman, sai suka samu natsuwa su duka da Alhaji Mustafa yace
"Haba wannan ai ba abin damuwa bane ba, In Shaa Allaah zata cigaba da karatunta, abinda shima Haris din yace mun yanaso ya dora Masters dinshi"
Yanda dai Hajjan taso su Zahra suyi fatan alkhairi, amman kowa saiya nuna mata hankalinshi ya tashi da maganar kai Maryam Kano, saida tayi musu jan ido tukunna sukayi shiru, kuma yanda akaje akayi jere aka dawo anata koda gidan su bata gani ba ko a fuskokinsu, ta kara dagewa, ta kara rage bacci tana ta kaiwa Allaah kukanta, bata san me yaran suke jiwa 'yar uwarsu tsoro ba, amman tana addu'a koma menene ya juye ta zame mata alkhairi, ita nata hankalin bai tashi ba saida aka shirya Maryaman cikin wani laffaya da Zahra ce ta siye shi da kudinta, ita tayi tsaye har kunshi saida akayiwa Maryam, kuma tun kwanaki uku data mayar da hankali akanta, kallo daya zakayi mata kaga ta fito a amaryarta.
"Allaah Yasa kije gidanki cikin aminci Maryama, Allaah Yasa auren nan ya zame miki alkhairi kinji ko? Allaah Yayi miki albarka..."
Ta karashe tana jin muryarta na karyewa, da aka daga Maryam din tsaye, saita karbe hannunta taje ta fada jikin Hajjan
"Dan Allaah Hajja...dan Allaah"
Take furtawa cikin wata karamar murya da kuka ya zuke, kukan da ta kasa ne a cikin kwanakin ya taso mata gabaki daya, tsoro da firgici na lullubeta, da gaske dai auren akayi mata, da gaske rabata za'ayi da gidansu akaita ta zauna da mutumin da bata taba gani ba, har garin Kano da tunda take a rayuwarta sau biyu suka taba zuwa, kuma da yake tana da kulafacin gida, hutun data taba cewa zata raka Khairi gidansu, kwananta daya ta makale aka juya Kaduna da ita. Gata yau zata bar gidan gabaki daya
"Ki tashi Maryama, ki tashi ku tafi"
Sai ta kara rike Hajjan gam, dole ta mike da ita, ta kuma riketa har dakin Alhaji Sa'id da yake tsaye ya rasa inda zaisa kanshi, wani irin rashin natsuwa ne yake ta ratsa shi, a kasa Maryam din ta durkushe, har gwiwoyinta na taba kafarshi
"Abbaa..."
Ta kira cikin karyayyar murya, tunda can shi mutum ne mai matukar rauni akan lamarin yaranshi, bashi da wasu kalmomi da zaice
"Allaah Yayi miki albarka Mairamata, Allaah Ya kula dake da al'amuranki, Nagode. Ki daina kukan nan, ga Yayyenki can a waje sunce sune zasu wakilceni yau, sune zasu rakamun ke har cikin gidanki..."
Ta daga masa kai, watakila akwai wani abu a tare da kalamanshi shisa wannan karin batayi wani gardama ba da taji an kamata ta mike, nan Hajja ta tsaya bangaren Alhaji Sa'id, sai ajiyar zuciya takeyi kuwa, idanuwanta na mata yaji, ta cikin mayafin da aka ja mata ya rufe mata fuska take hangensu, da yake ba mai kauri bane, wani abu ya daki zuciyarta, duka mazan gidansu ne. Ahmad, Khalifa, AbdulKarim, Yazid, Sagir, Adnan, sai kuma Saifullah. Fararen shaddojine a jikinsu, kowa yasha babbar riga da hula, kukan da takeyi bai hanata jin yanda kamshin