Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
tafi gidan. Duk wani bayani da likita yayiwa Alhaji Sa'id shi yayiwa Hajja
"Sunce postpartum depression ne, amman basu gama tabbatarwa ba..."
Hajja ta jinjina kai
"Shi yaja ta kasa gane mu?"
Wannan sunce masa ta samu short term memory loss ne, amman bana komai da komai ba, tunda ta gane shi, ta kuma gane kanta, duk da bakomai ba, ta manta tana da aure, balle wasu yara. A hankali komai zai dawo mata, amman basu san yaushe hakan zai faru ba. Kai Hajja ta jinjina, cikin tarin karfin hali tace
"Allaah Ya dafa mana"
Tunda tasan babu abinda Yafi karfin Ubangiji daya dorawa Maryama wannan ciwon kowanne irine. Ciwon da zaka kasa gane mahaifiyarka, ka kasa gane yaranka? Ai ba karamin ciwo bane ba, tunda ita bata tabajin irinshi ba sam, tasan dai akwai hauka, amman wani ciwo daban na kwakwalwa bayan wannan, sabon abune a wajenta. Sabon abinda zata dukufa gaban Ubangiji akanshi. Aikuwa sai gashi dakyar aka samu Maryama take shayar da Naadir. Duk kuma yanda aka hana Haris shiga wajenta sai da ya rokesu suka barshi yake tsayawa ta window din dakin yana ganinta
"Ba zan shiga ba, Allaah ba zan shiga ba, kubarni anan ina ganinta, dan Allaah kubarni..."
Barinshi sukayi kuwa, wasu kwanakin bakwai Maryama ta sakeyi a asibitin kafin aka sallamesu da kashedi kala-kala dan har lokacin Alhaji Sa'id kawai take ganewa. Ko da akayi sallamar shiya kamata ya saka a motarshi, Haris na biye dasu a tashi, yanata mamakin dalilin da zaisa Alhaji Sa'id ya nufi hanyar gidanshi da Maryama, haka dai ya cigaba da binsu har suka isa. Ko inda yake Alhaji Sa'id bai kalla ba, ya sake kama hannun Maryama suka shiga ciki. Shima Haris ya rufa musu baya, nan falon suka zauna su duka, Haris nata kallon agogo, ganin har ana shirin yin azahar yasa shi fadin
"Abba zamu wuce gida..."
Alhaji Sa'id yayi masa wani kallo mai tarin ma'anoni kafin yace
"To madalla, ka gaida gida"
Yayi tsam yana rasa abinda zaice, dan likita da kanshi yayiwa Maryama bayani, ga Haris, shine mijinta, haka su Hajja, dama su Awwab, duk da bawai ta ganesu bane saita daga kai, ta rasa yanda zatace duk da bata gane Haris ba inta kalle shi sai taji kirjinta yana mata zafi. Mikewa Haris din yayi
"Maryamm muje"
Kafin ma ta amsa Alhaji Sa'id ya rigata da fadin
"Taje ina? Ai ita ta dawo gida kenan, kai dai ka tafi abinka"
Haris ya kalli Alhaji Sa'id, ya kalli Maryama data kara matsawa jikinshi, ya kuma kalli Hajja cikin neman taimako, data kalli Alhaji Sa'id sai yace mata
"Wallahi babu inda zataje"
Kuma yanda yayi maganar su duka sunsan ba zaiyi kaffara saboda su ba
"Kaje Haris zamuyi magana"
Haris ya daga mata kai batare da yace komai ba, ya dai dan kara tsayawa jim, ya kalli Maryaman da ta dauke idanuwanta. Sannan ya juya ya fice daga dakin. Sai dai daga nan gidan, makarantar yara yaje ya bada uzurin da yasa aka bashisu, ya biya ya dauki Fa'iza itama. Ya kaisu gida yana ce musu
"Fa'iza ki hada muku kayanku, Maryamm tana gida, an sallameta zan kaiku can wajenta"
Kayan nasu Fa'iza ta hada musu, harda extra uniform duk ta daukar musu. Sai dai ta tsaya ta dafa musu indomie, daga ita sai Awwab sukaci, Rauda sai anyi fada da ita, in ba Maryama ta zare mata ido ba, wata rana harda duka sannan zata yagi abinci, Fa'iza tasan ba zata iya sakata taci abinci ba, dan haka ma ta samar mata yoghurt a fridge ta bata, shima tanata jujjuyashine a hannunta batare data bude robar ba. Haka Haris ya fito ya samesu
"Kungama?"
Awwab yace
"Eh amman as usual, Rauda bataci komai ba, da safe ma da zamu fita black tea kawai tasha"
Rauda tayi saurin cewa
"Banajin yunwa...in munje zansha Tea a wajen Hajja"
Haris baya iya matsa mata, musamman akan abinci tunda Maryama na cewa ya bata mata yarinya gata nan kaman tsinke saboda batason cin abinci
"Tam"
Kawai ya iya cewa, yau bayama jin yin magana mai tsayi. Ya sakasu a gaba suka fice daga gidan, ba karamin mamaki Hajja tayi ba data gansu gabaki daya
"Hajja ina Abba?"
Haris ya tambaya
"Yanzun ya fita, sai dai bansan ko zai dawo da wuri ba, Maryama kuma tasha magungunanta ta samu bacci"
Kai Haris ya jinjina
"Zan jirashi"
Zaman yayi, anan gidan yayi sallar magriba da isha'i, kuma daga shi har Rauda duk wani tayin abinci da Hajja tayi musu basuci ba, shayin suka sha, shi da madara da komai, ita kuma tasha bakin ruwan shayi sai wani cracker biscuit da Hajjan ta matsa mata taci kwara hudu. Ta tashi taje ta kwanta, tunda sun san inda suke sauka in zasu kwana gidan Hajjan. Alhaji Sa'id bai shigo gidan ba sai tara saura, ya amsa gaisuwar Haris a daqile. Ganin bashi da niyyar saurarenshi yasa Haris din mikewa yabi bayan Alhaji Sa'id daya fito daga duha Maryama, tare suka taka har sashinshi, Haris ya samu waje kan kafet din dakin ya zauna yana fadin
"Abba yaushe zamu tafi gida da Maryama?"
Alhaji Sa'id ya kalleshi
"Sai ta warke"
Ya amsa a takaice, Haris ya jinjina kai
"Allaah Ya bata lafiya. Ni a ina zan zauna to?"
Kallonshi dai Alhaji Sa'id din ya sakeyi
"Baka da gidane Haris?"
Batare da wani shakku ba ya amsa da
"Bani da gida yanzun Abba, in da babu Maryamm ba gida bane a wajena"
Shirune ya ratsa dakin, shiru na wasu sakanni masu yawan gaske, shirun da Haris ya kora ta hanyar cewa
"Duka zamu zauna anan, inta warke saimu koma gida tare"
In dai dakuna ne akwaisu a gidan, tunda kullum cikin baki suke, sannan akwai samari har lokacin, wasu dakunan kuma a rufe suke a bangarensu, sai dai ana gyarawa kullum, a mayar a sake rufewa, na samarin gidan ne da sukayi aure. Sannan wani abu daya da Alhaji Sa'id ya sani shine, har yanzun matsayin Alhaji Mustafa bai canza ba a wajenshi, kawai dai zuciyarshi taje wani gejine daya daina fifita farin cikin Haris akan na Maryama, kuma kamar yanda ya rantse, sai Maryama ta warke tas ta dawo hayyacinta, sannan sai ta bude bakinta da kanta tace ta zabi cigaba da zama da Haris ne zai bashi ita, amman muddin ta kalle shi tace ta gaji da wannan auren, zai saka ma tarin biyayyar da tayi masa albarka, zai tsaya ya karbar mata takardar sakinta a hannun Haris.
Hakan kuma ba zai hana duk randa Haris yazo gidan a bude masa kofa kamar yanda za'ayiwa duk wani ahali na Alhaji Mustafa, kuma ko daga ina Haris ya fito to idan yana bukatar wajen zama, za'a share masa daki guda a bashi ya zauna
"Ai gidan nan nakune Haris, ko daga ina kake kana da masauki a cikinshi"
Magana ce daya kamata ta sanyayawa Haris rai, sai yaji zuciyarshi ta sake kuntata, sai yaji kamar yau Alhaji Sa'id nayi masa kallo dayane, kallon cewar danshi ne, dan wajen Alhaji Mustafa, bayan hakan babu wata alaka data sake hadasu, hakan kuma ba karamin tashin hankali bane a wajenshi. Dakin aka bashi, daya shiga ya kwanta sai ya karajin wani kunci ya lullubeshi, ya dauki waya ya kira Alhaji Mustafa, sai dai bayan sun gaisa saiya rasa me zaice masa.
"Muna nan gidan Abba tare da Maryamm"
Ya furta a hankali, Alhaji Mustafa yayi shiru, sai kuma sautin dariyarshi da yaba Haris matukar mamaki
"Da aka sallameta can kuka tafi? Yaran fa?"
Cewar Alhaji Mustafa
"Abba yace saita warke zata dawo gida, shine na daukosu muka dawo nan din, inta warke duka saimu tafi tare"
Dariya Alhaji Mustafa yayi ba 'yar kadan ba
"To madalla, Allaah Ya baku lafiya ku duka"
Ya fadi, dan da alama har Haris din yana bukatar yaga likitan kwakwalwa, daman yayiwa kanshi alkawari ba zai yiwa Alhaji Sa'id katsalandan ba, bama zaije ba balle yaji kunyarshi, yanata addu'a dai, ya kasa hana zuciyarshi yin wannan son kan, yana ma Haris addu'a karya rasa nagartacciyar mace kamar Maryama.
*
Kwananshi biyu gidan Alhaji Sa'id, duk kiran da Hajiya Rumana tayi masa a kwanakin nan biyu tana bankada masa zagi baije ba, sai rana ta biyun, shima daga wani aikine daya fita saiya biya ta gidan, yana shiga kuwa ta dora daga inda ta tsaya
"Ai bansan Sa'idu na haifawa kai ba sai yanzun Haris, saboda lalacewa sai ka koma gidansu mace ku tare, saboda abin kunya..."
Fadan takeyi kamar zata hadiye harshenta, har haki takeyi, saida ta gama tas, yana zaune yana kallonta, da ledar peanut a hannunshi, Awwab ne ya bashi, kuma tafi wata a cikin mota, sai yau ya dauka ya fasa, ita yake taci batare da yana gane dadinta ba, haka kawai yake taci, yanzun ma wata ya kara jefawa a bakinshi ya tauna, sai ya ajiye ledar a gefenshi, ya kalleta sosai
"Mami kinsan ya nakeji?"
Itama kallonshi takeyi, bai jira amsarta ba ya cigaba da magana
"Lokacin da Baba ya auramun Maryamm, na karbi aurenta ne da zuciyata duka, kuma ban taba hango ranar da zan rabu da ita ba, saboda Baba, amman yanzun inajin ba zan iya rabuwa da ita ba saboda ni Mami, saboda ina sonta..."
Yaja numfashi
"Saboda tana sona, tana sona Mami, Maryamm tana sona, Maryamm ta ganni da mace kuma ta cigaba da zama dani, randa kika zo gida, bashi bane na farko, kuma bansan ko shi bane na karshe, amman nasan Maryamm zata sake hakuri, zata dawo wajena...Mami inke ce zaki hakura? In Baba nine zaki...."
Da sauri tace
"Haris!"
Yayi shiru yana cigaba da kallonta
"Na hakura Mami, tuntuni na hakura ba zaki taba son Maryamm ba, ina so kema ki hakurane saboda ba zan taba rabuwa da ita ba..."
Sai bayan ya mike ne yaga Alhaji Mustafa tsaye a bakin kofa, ya karasa ya gaishe shi, sannan ya rabashi ya fice daga gidan
"Yau kinji abinda kike nema ko Rumana? Ai da kin amsa shi, wallahi nasan ba zanyi kaffara ba, idan nine nake da rabin halayyar danki ba zaki zauna dani ba, ba kuma zaki rufamun asiri irin yanda Maryama ta rufa masa ba...in da zaki zauna, ki ture wannan kiyayyar taki marar tushe, ki kalli danki, ki duba Rahmar daya samu ta sanadin auren Maryama, da zakice madalla da wannan auren Rumana. Ina miki addu'a Allaah Ya yaye miki abinda yake damunki..."
Yana gama maganar ya fice shima, sai wasu hawaye masu zafi suka zubo mata. Da gaske ne kiyayyarta bata da tushe? To in bata da tushe ya zatayi ta raba kanta da ita? Ya zatayi ta budema Maryama waje ko dan karami ne a zuciyarta? Tunda ta sani, gaskiya Alhaji Mustafa ya fada mata, gaskiya mai ciwo, Maryama matar rufin asiri ce, tun ranar da Haris ya bude bakinshi ya gaya mata meya aikata tasan Maryama rufin asiri ce da batayi masa terere ba, da zazzabi ta kwana saboda kaduwa da tashin hankali, amman girman kai irin nata ya hana ta saduda, ya hana ta rissina.
Amman ko taso ta hakura sai taji ta kasa, musamman idan taga yanda Haris yake fifita lamarin Maryaman akanta. In ba wanda aka shanye ba, ya za'ayi yaje gidansu Maryama ya tare? Taya zata ga farin Sa'idu da ahalinshi bayan sun maida mata da soko? Ita ko yau wannan auren ya qare zatayi murna da hakan
Sai dai kaddara ta riga fata...
Ya zatayi da sauran rabon da yake tsakanin Haris da Maryama?
44
HARIS
Kwananshi sittin da hudu, ko yace kwanansu sittin da hudu a gidan Alhaji Sa'id, shi da yaran da Maryama, a lissafe yake saboda kowacce rana jinta yakeyi kamar ba zata wuce masa ba. Kuma tun a kwana na 20 ya kalli Maryama data fito babban falon nasu, yana zaune da kofin shayi a hannunshi, yasan cewa ta dawo hayyacinta, sai dai yanda bata nuna masa ba, shima bai nuna mata ba. Tunda kafatalin 'yan gidansu, masu aure da marassa aure suka daina mamakin zaman da yakeyi a gidan, suka ma fara mantawa cewar shima ba dan gidan bane ba ya kyale Maryama, randa duk taji cewar ta gaji da zaman nasu, sai su tattara su koma.
Sai dai a duk wani mafarki da tunani da yakeyi, Maryama zata same shi, zasuyi rigima kamar yanda suka saba, za kuma su shirya, sannan zasu tattara kayansu su koma gida. Ko a mugun mafarki bai hango Maryama zatayi masa wannan gangamin ba, shisa tunda ya samu waje daga can nesa akan kafet a cikin falon da yake bangaren Alhaji Sa'id, yake kokarin ya hada ido da ita amman taki kallonshi, tana zaune ne daga kasa, kusa da kafafuwan Alhaji Sa'id din, Alhaji Mustafa na gefenshi, sai Hajja, sai kuma Hajiya Rumana da taketa hura hanci ta samu kujera mai zaman mutum daya. Ita inda tasan nan gidan zasu zo, babu yanda za'ayi ta biyo Alhaji Mustafa. Haka kawai yace mata ta shirya zasuje unguwa.
Shima kuma Alhaji Mustafa din, da daddare Alhaji Sa'id ya kirashi a waya, bayan Maryama ta sameshi a daki sun gaisa
"Mairama da magana a bakin nan naki"
Tayi murmushi, tare suke zaryar asibiti, shi yake daukarta a motarshi, sai dai Haris ya bisu a baya da tashi motar, kuma ya zauna ya jirasu a waje saboda Maryama ta nuna bata bukatar shiga ganin likita tare dashi. Tunda ko Alhaji Sa'id din idan yaje barinta yakeyi ita da likitan nata su tattauna. Kuma tunda suke zuwa duk wata dabara da zaiyi amfani da ita wajen ganin Maryama ta bude bakinta sunyi magana, yaji matsalarta saboda yafi gane yanda zai bullowa ciwon damuwar da take fama dashi abu ya faskara, daya hadata da Alhaji Sa'id ma sai tayi dariya tana ce masa
"Abba nifa na samu sauki, babu wani abu da yake damuna da zan gaya masa"
Da yake baya son matsa mata saiya kyaleta, ko data same shi a daki da kanta dinma maganar da tayi masa bata da yawa
"Zan koma gidana Abba, amman inaso mu zauna, dani dakai da Hajja, da kuma su Baban Tudun wada, da shi"
Bai tsaya yi mata doguwar tambaya ba ya amsa mata. Ta tashi ta koma cikin gida, kuma har daki Hajja ta sameta bayan Alhaji Sa'id ya gaya mata abinda Maryaman tace
"Inayi miki addu'a ko da yaushe Maryama, zan iya cewa addu'ar da nakeyi miki tafi ta kowa a cikin 'yan uwanki, bawai dan nafi sonki akansu ba, sai dan inaji a jikina taki jarabawar tafi tasu yawa, bana so in matsa miki Maryama, bana tambayarki ne saboda ina jiran ranar da zaki bude baki ki fadamun matsalarki, watakila ba zan rasa shawarar da zan baki ba"
Tunda abin nan ya faru, sai a lokacin ne Maryama taji hawaye masu dumi sun zubo mata, hawayen da in dai akan Haris ne ya kamata ace bata da saura
"Hajja..."
Ta kira cikin rawar murya, sai Hajjan ta riko hannunta
"Maryama zan cigaba dayi miki addu'a, ko da bansan ainahin abinda yake faruwa dake ba"
Ba gayawa Hajja bane bataso tayi, ta rasa ta inda zata bude bakinta ne ta kalli mahaifiyarta tace mata mijinta yana bin mata? Sunyi magana da Khairi, tasan duk abinda yake faruwa
d Khairi kinsan ko Kaduna da kewayenta zasu taru Mami ba zata bari in rike yarana ba, Abba kuma nasan ba zai goyamun baya ya tayani karbarsu ba, wa zan barwa tarbiyarsu? Mamin? Ko shi Baban nasu? Ni idan na bar auren ta ina zan fara?"
Ita kanta akwai matsalolin da inta gansu, ko da a social media ne, ko taji labarinsu sai ta ga auren ma in za'a tsaya a haska masa ka'idojin musulunci da wahalar gaske ace akwai shi, wani auren kuma sai ya sakata dinga tunanin to meye amfanin shi? Zaman me matan sukeyi? Sai a hankali da matsaloli suka fara kunnowa a nata gidan ne ta gane cewa, shifa lamarin aure abune mai cike da tarin sarkakiya, mata da yawa in zaka saka musu bindiga ba zasu ce maka ga dalili kwara daya da yake rike dasu a gidajen aurensu ba, wasu kuma in suka fada maka nasu dalilin sai kaji nauyinshi ya rinjayi matsalar da suke ciki.
Babban abinda Maryama zatace ta fahimta shine, daura aure yafi rabuwar shi sauki a lokutta da dama. Rabuwar aure ba abu bane mai sauki, da gaske ne aure yana da rai, ta yadda, dan duk yawan mutanen da zasu taru dan su kashe shi, idan lokacin shi baiyi ba, idan akwai sauran rabo, ko da rabon wahala ne haka za'a hakura. Ita dai inta duba, yaranta sune dalilinta na farko a yanzun, sannan inta hanga, bata iya ganin wata rayuwa da babu Haris a cikinta. To gani takeyi ma me ya rage mata? Duka kuruciyarta fa aka dauka aka mika masa, ta iya shanye halayenshi a lokacin da batasan inda yakeyi mata ciwo ba sai yanzun?
"Wannan son da kikeyi masa Allaah Yasa wata rana kiga ribar shi Maryama...Allaah Ya taqaita miki wahala"
Inama zata iya yiwa Khairi musu? Tace halayen Haris sun fitar mata dashi daga rai tas, sai dai ai ko harshenta ba zai bata hadin kai ta furta wannan gingimemiyar karyar ba, tana son Haris, son ne ma yasa damuwarshi tayi mata yawa, watakila wannan son ne yake kara rufe mata baki daga furta halinshi da tasan zai zubar masa da mutunci a idanuwan mutane, watakila shine yasa ta cewa Hajja
"Hajja ke kike yawan gaya mana zamu iya samun matsala da mazajenmu, mu yafi juna, harma mu manta, amman idan mun fadawa makusantanmun wannan fadan, zai wahala su manta...abinda nake gujewa kenan, bawai fada miki bane bana so inyi..."
Sai kuwa Hajjan tayi mata dan gajeran murmushi, irin murmushin nan na iyaye
"Allaah Yayi miki albarka Ya kara miki hakuri da juriya. Allaah kuma Ya dai-daita miki komai"
Kuma a yau da Alhaji Sa'id yayi mata yanda ta roka, sai takejin hawaye na neman balle mata, musamman yanda taji idanuwan Haris nata yawo a jikinta, sai ta zabi ta kalli Hajiya Rumana da idanuwan iyayenta bai hanata binta da kallon tsana ba, batasan me yasa Alhaji Mustafa ya kwasota suka zo gidan nan ba, to taron na menene? Bayan duk irin zagin da ta dinga yiwa Haris baiji ba balle yasa ya bar gidansu Maryaman. Da tayiwa Alhaji Mustafa magana sai yace mata
"Ko Haris baya auren Maryama ai gidan Sa'idu kamar nawa ne a wajenshi..."
Bakin ciki ya hanata magana, inta biye musu, zasu kassarama sauran yaranta da suke sonta itane, gara ta dauki ido ta saka musu
"Zan koma gidan Haris..."
Maryama ta fadi tana korar shirun da dakin ya dauka, ta cigaba
"Amman ina so ku zama shaidane, zan koma gidanshi