Advertisements
Chapter 24 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   24 / 51

69K to 72K   out of 151K words

da tarbiya? Ba zaki taso ki kawo masa ba?"

Kafin tace wani abu Haris dinma ya mike, da ya karasa kan kafet din kawai saiya samu waje a gefenta ya zauna, ya sake juya shayin ya kurba, bashi da zafi ma can, dan haka ya dauki kofin kawai ya cigaba da kurba

"Meye wannan kika zuba?"

Ya tambaya a hankali, itama a hankalin tace masa

"Alale"

Ya sake kallon plate din, da yake 'yar sauce din manja ce Mummyn tayi, ta zuba a gefe, tunani yakeyi idan ya taba ganin alale, ya dai san bata taba zuwa bakinshi ba, amman su Anisa na yawan maganar alalen, ko sun tabayi sun zubo a gabanshi ma ba zai tuna ba

"To kici, ko muci dankalin?"

Ta girgiza masa kai kawai, ta dauki nata filet din ta fara tura alalar da ta kasa gane dandanonta, kunun ya jima da hucewa, ba zata iya shanshi ba, dan batason kunu yayi sanyi. Hajiya Rumana kuwa kallonsu kawai takeyi tanajin kamar ana watsa mata ruwan zafi. Yanda Haris din ya tattara hankalinshi kan Maryama take kallo, da yanda itama Maryaman take amsa shi, batama jin me suke cewa daga inda take, sai tajita kamar bakuwa yau, bakuwa a rayuwar tilon danta, kamar wata da tazo ta tureta sai kawai ta zauna a wajen. Wani abu ya dinga tasowa yanayi mata rumfa, makoshinta ma daci yakeyi mata, da Maryama ta gama tura iya abinda zai shiga, sai ta mike tabar filet din a wajen. Ganin ta dauki hijabinta da yake gefe yasa Haris fadin

"Ina zakije?"

A hankali tace masa

"Coke zan siya, akwai shago a wajen asibitin, daga tsallake"

Kai yake girgiza mata

"Kece zaki tsallaka titi? Koma ki zauna"

Ta tura bakinta gaba

"Zan iya fa, ai zan kalli gefe da gefe"

Kai tsaye yace

"Ki samu wajen zama"

Sai kawai ta tafi inda ta ajiye ruwan dasu Alhaji Sa'id suka siyo musu jiya, ta dauki roba daya, akwai katan din holandia, amman ba sanyi,  akwai dan karamin fridge a dakin, ta saka fruits din da suka siyo ne dan karya lalace. Ta kuma karasa gefen Hajiya Rumana da take ta binsu da ido dan yau ne ta gane asalin abinda ake kira da

"Naga abinda yafi zare tsayi"

Wayarta da ta saka a caji ta cire tana nufar kofa

"Me nace miki?"

Muryar Haris ta fito cike da kashedi, ta juyo harda buga kafa

"Bafa zuwa zanyi ba, anan waje zan zauna zan kira Abba ne ba muyi magana ba"

Tayi tsaye tana kallonshi, ta kasa fita saida ya dan daga mata kai tukunna ta fice daga dakin. Shikuma ya mayar da hankalinshi akan shayin da yake sha, dankalin ma yaci kusan rabi, kwan ne bai taba ba

"Haris..."

Hajiya Rumana ta kira muryarta can kasan makoshi, wani abune mai kama da tsoro yake neman saukar mata

"Mami dan Allaah, idan kina da matsala da Maryamm kiyi mun magana, kiyi mun fada, saboda ba ita ta saka kanta a rayuwata ba, Baba ne ya daukota ya kawo, nikuma nayi masa alkawari cewa na karba...ko ba zaki karbeta bake, to hakan ya tsaya tsakanin ni dake, bana so ki dinga abinda zaisa mutuncinki ya ragu a idanuwanta, bana so ta raina ki"

Ta furzar da numfashi

"Idan ni banyi abinda zata rainani ba ai kai ka riga ka girma yanzun Haris, ka nuna mata ni din ba komai bace a wajenka, shisa zan dauko kafa inzo dubaka, in kawo maka abinci kaqi ci, sai wanda ta roko muku, sannan a gabanta nayi magana ta kawo maka nan, ka tashi kaje ka sameta kuka zauna waje daya, a gabana..."

Yayi shiru, tunda ya riga yasan halinta, yasan kuma yanda ranta yake a bace ba zatayi shiru ba, fadan ta cigaba dayi kamar zata taso ta rufeshi da duka, baiko motsa ba, data mike tana fadin

"Ai banga zaman da zan zauna inyi maka ba, gara in barka da wannan kaddararriyar yarinyar, daman saida Babanka yace inyi zamana ashe rabon inga abinda zai dasamun ciwone"

Cikin karamar murya yace

"Allaah Ya tsare hanya Mami, wayata na gida, amman zan kiraki da tata kafin mu koma in dauka dan inji ya kika sauka"

A hasale tace

"Inka kirani da wayarta sai naci ubanka Haris"

Ya kurbe sauran shayin shi yana ajiye kofin

"Zansa ta dauko mun wayar inta koma gida to sai in kiraki da tawa, I love you, Allaah Ya saukeku lafiya"

Taja tsaki tana ficewa abinta, yanda ta banko kofar saida kunnuwanshi suka amsa, ta kalli Maryama dake zaune a kujerun karfe da suke corridor din tana waya ta nata dariya, taji kamar ta karasa ta shaketa, ta wuce kawai, Maryama ta ganta, tun data ja kofar ta ganta, shisa ta kara waya a kunne tana dariya, ta kuma yi kamar bata ga fitowarta ba, data wuce tana tayar da iska Maryaman taja siririn tsaki

"Allaah Ya raka taki gona"

Ta fadi a ranta tana mikewa ta koma cikin dakin, ta samu Haris a zaune inda ta barshi

"Naga harta tafi, zataje ta dawo ne?"

Ya girgiza mata kai kawai, kafin kuma a hankali yace

"Mami tana da fada, haka take, amman ba duka abinda ta fada bane yake fitowa daga zuciyarta, banaso ki dinga rike maganganunta"

Cikin ido ta kalle shi

"Abinda ta fada daga zuciyarta ya fito, kuma gaskiya ta fada, Abba yayi yawon bara"

Yanda tayi maganar yaji baiyi masa dadi ba sam, shisa ya rasa abinda zai kara cewa, sai yayi shiru, ta wuce dan tana so ta maida cajin wayarta, tunda da safen ta saka daman, a wajen dai ta tsaya ta kira Mummy tace mata karta saka abinci dasu, ta gaya mata Hajiya Rumana tazo kuma ta kawo abinci da yawa. Babu wata hira mai yawa da ta sake giftawa a tsakaninsu, shi yanaso yayi mata magana, amman baisan me zaice ba, ita kuma zafin maganganun da bata mayarwa Hajiya Rumana ba shine ya rufe mata baki, da suka sakeyi masa allurai yayi bacci, itama saita samu ta kwanta.

Mummy bata dawo ba sai la'asar, Haris nata bacci, ita ta sake raka Maryama gida, ta tafi da wannan kayayyakin da Hajiya Rumana tazo dasu, ta saka a fridge, ta ajiye kayan da suka cire harda na Haris din, ta sake dauko musu kala dai-dai, suka dawo tare har asibitin, sannan sukayi sallama ta tafi. Ba'a sallamesu ba sai washegari wajen karfe sha biyu, batasan waya kai motar Haris gida ba, dan Mummy ta dawo, tana nan akayi sallamar, suka karbi magungunan da aka bashi na kwana bakwai, dan ance su sake dawowa bayan kwana bakwai din idan ya gama shanye magungunan. Haka suka fito Haris na mamakin abinda sukeyi tsaye a bakin titi, yaga Mummy ta tare musu adaidaita sahu, anata zabga ciniki.

Shi dai mamaki yakeyi, yaga Maryama ta shiga, sai aka loda kayayyakinsu a baya, kwandon da Mummyn ta kawo musu, basu ko taba ba, sai aka saka shi anan kusa da Maryama, da sauran wasu tarkace ma

"Ka shiga Haris, Allaah Ya kara sauki"

A hankali ya amsa da

"Amin. Mungode sosai"

Yana kallo ta zagaya gefen da Maryama take, shikuma ya shiga a darare, haka kawai zuciyarshi sai bugawa takeyi, shifa tunda yake ko mashin bai taba hawa ba, keke ma da yara sukeyi bai hau ba, daga mota sai jirgi, ko a sauran kasashe taxi ce. Dan shi bayason gudu da mota, shisa duk yawon da zasuyi in dai Barde ne zaiyi tuqi sai dai ya hakura da tafiyar, saboda Barde bashi da hankali inya rike mota, to yau gashi mai adaidaitar nan dan ta kife ne, dan yanda ya fisgeta saida Haris yayi gaba har kirjinshi na dukan karfen wajen

"Subhanallahi..."

Maryama ta fadi dan taga yanda Haris din ya bugu

"Ka shigar da jikinka ciki ka zauna sosai, wanne irin zamane kayi haka, sai kaje ka fada"

Ya kalleta

"Wanne irin zama zanyi, kina ganin gudun da yakeyi, gashi seat din yana da santsi, shine yake zamo dani"

Kallon da tayi masa bashi da fassara, tunda yayi mata magana ne kamar wanda bai taba hawa adaidaita ba

"Shikenan, karka zauna da kyau ka rike karfen wajen, inka sulmiya ka cire hakori babu ruwana"

Maganar ta shigeshi sosai, ya rike karfen da yaga hannunta yana kai da dukkan karfinshi

"Ka rage gudun nan fa"

Ya cewa mai adaidaita sahun, yanajin wata tsakuwa ta taso ta fada masa a ido

"Oga bafa gudu nake ba, dan naga na daukeku a asibiti shisa nake lallabawa"

Haris baima ji me yace ba yana ta faman murza idonshi da tsakuwa ta fada, daya kara bude bakinshi sai yaji kamar kasa ta shiga ciki, dole ya rufe, baisan me ya samu motarshi ba, amman ya tuna cewa Maryama bata iya tuki ba

"Wai a wannan abin kuka kawoni asibiti?"

Ya kasa hakuri saida ya tambaya, ta kalle shi da idonshi daya daya rine, dan akwai alamun danshin hawayen da idon yayi har lokacin

"Me ya samu idonka?"

Ya dan gyara zamanshi

"Wani abune ya shigo daga waje ya fada mun, anan kuka kawoni?"

Ya sake tambaya, sai kawai ta daga masa kai

"Baya muka sakaka"

Da saurin gaske yace

"Baya ina?"

Ta gimtse dariyarta

"Baya fa inda akasa kayan nan, to sai kafafuwanka sunyi tsayi, shine fa aka samu igiya aka kulleka a saman adaidaitar, da yake ba gudu yayi ba ya lallaba tunda da mutum akai, Allaah dai ya sauke mu lafiya"

Yaga tashin hankali kala-kala a Syria, amman saida yaji cikinshi ya hautsina, sama? Shi aka kulle a saman wannan abin aka kawo asibiti? Daya sulmiyo fa? Dariyar da yaji Maryaman ta kwashe da ita yasa shi sanin karya takeyi, ya mika hannun shi yana ja mata kunne, amman dariya takeyi har lokacin

"Zamuje gidane Maryamm"

Dariyar dai takeyi masa...
Abu dayane a ranshi har suka sauka, ba za'a rufe satin nan Maryama bata fara koyon mota ba, saboda ba zai kara hawa adaidaita sahu ba, yayi na farko, ya kuma yi na karshe, haka ya fadawa kanshi...

25

Wani abinci ne ta ga maigadinsu yana ci ranar da suka koma daga asibiti, dan da robar a hannunshi ya bude gate din, jikinshi har bari yakeyi lokacin daya gansu, yanata faman jera musu sannu, tana bashi abinci idan ta ga ba zata iya cinyewa ba, amman tunanin ta dinga bashi kullum bai taba zuwa ranta ba sai ranar, tunda su dai ba maigadi suke dashi a gidansu ba. Shiya tayasu shiga da kayayyakinsu ciki yanata yiwa Haris addu'o'in karin lafiya kafin ya koma bakin aikinshi. Daga ita har Haris din kowa nashi dakin ya wuce, dan ita kwanciya ma tayi tanajin gajiya na saukar mata, akan kafet take karasa baccinta a asibitin, tunda tana fara shine akan kujera, da kanta da take dorawa a jikin gadon Haris.

Yanzun da taji ta baje sai wani bacci-bacci yake neman kamata, amman dole ta tashi tayi sallar azahar. Data idar, tayi zamanta a dakin har karfe biyu tukunna ta fita dan Haris zai sha magani karfe biyun, saida ta dauki magungunan, tayi kitchen ta dauki robar ruwa da kofi ta samu tray ta dora akai taje ta kwankwasa masa daki, ya bude mata

"Karfe biyu, zaka sha magani"

Tana ganin yanda wani abu ya tattare a goshin shi, sannan ya yamutsa gabaki daya fuskarshi

"Magani?"

Kai ta daga masa

"Kala uku ne, karfe biyu akace zaka sha yau, sai kuma na dare, sai gobe idan Allaah Ya kaimu zaka sha sau uku a rana, harda na safe"

Shifa baya kaunar magani, da yake ma Allaah Ya taimake shi saiya dade baiyi rashin lafiya ba, yanzun tunanin shine zai hadiye wannan magungunan har kala uku kawai amai ke neman taso masa

"Bana sha, banajin wani ciwo a jikina"

Maryama tayi masa wani kallo

"Likitan daya rubutu maka yasan dalilin ai, ka dauki ruwan in ballo maka"

Ya girgiza mata kai

"Ke nifa ba zan sha wani magani ba"

Sai ta jinjina masa kai

"Ba matsala, in hado maka shayi? Kaga ance ka daina zama da yunwa"

Wannan dai zai sha

"Eh, amman ba da yawa ba, rabin kofi haka"

Ta daga masa kai sannan ta wuce kitchen din, ta gama hada shayin kenan Haris ya shigo, sai ta mika masa

"Nagode"

Ya furta yana gasa tafin hannunshi da yaji yayi sanyi a jikin kofin shayin, wanka yayi ya sake kaya. Sai ya kara jin karfin jikinshi sosai, Maryama batace komai ba ta bude fridge ta shiga fito da wasu manyan robobi, ta dinga bubbudesu, nama ne na rago da kuma kaji da baisan sanda ta dafasu ba, yaga ta dibi naman ragon ta saka a wata karamar tukunya, sannan ta dauko wata shinkafa da ta sha kayan lambu ta zuba a wata tukunyar daban. Ta rurrufe ta mayar tana janyo wata robar, kallonta kawai yakeyi tanata hidimarta, ya fara kurbar shayin shi a hankali, kamshin abincin da take dumamawa ya cika kitchen din

"Shayin nan yayi wani iri"

Ya fadi, tun a kurbar farko yaji haka

"Bakinka ne, kasan kayi rashin lafiya, bakinka bai gama dawowa dai-dai ba"

Cewar Maryama batare data juya ta kalle shi ba, ya sake kurba, yasan in mutum yayi rashin lafiya yana jin bakinshi ba dadi, amman ai jiya ma sau nawa ta hada masa shayi a asibiti

"Amman jiya lafiya kalau fa naji shi dana sha"

Kaman ba zata amsa ba sai kuma tace

"Wani lokacin saika dawo gida ai yake haka"

Bai sake magana ba ya cigaba da kurbar shayin, bama zaice ga abinda yakeyi a kitchen din ba da yayi tsaye, saida ta gama hada komai, harda meatpie yagani guda uku. Ta kuma hada abincin ne waje biyu, wanda shinkafar tafi yawa shi ta bashi tana fadin

"Dan Allaah ka mikawa maigadi mana"

Ya karasa kurbe shayin, ya dan yamutsa fuska saboda wani taste da yaji a karshen, ya ajiye kofin ya karbi babban bowl din data bashi taba dora murfinshi. Fita yayi ya mikawa maigadin, daya dawo saiya sameta a falo tana zaune kan kafet ta kuma kunna kallo, ga abincin nan a gabanta sai kuma lemon kwali data dauko, cikin wanda ma suka dawo dashine daga asibiti, ya zauna kan kujera, saita mika masa kwanon abincin, ya girgiza mata kai

"Zakayi loma daya ne ai, ka kuma ci nama guda daya, saika gutsiri meatpie din...ba abinda zai sameka dan kaci abinci"

Ya sake girgiza mata kai

"Wanda Mami ta kawo ne, abincin da na tabbata itace ta bata lokacinta ta shirya maka shi kala-kala, ta kuma dauko tun daga Kaduna zuwa Kano ka kalli idonta kace mata ba zakaci ba...bakaji komai ba kace mata ba zakaci ba, ai da saika bude ko cokali dayane kayi zataji dadi"

Kallonta yakeyi, yanda take maganar, kamar yayi wani gagarumin laifin da bai sani ba sai yanzun da ta sakashi a gaba tana zayyana masa su daya bayan daya

"Ka karba kaci kaji, saika kirata a waya ka gaya mata yanda komai yayi dadi"

Dan abincin yayi mata dadi, musamman ma meatpie din, shiya shigar mata ido ta fara gutsira, har yanzun tana jin dandanon shi akan harshenta, tun a asibitin bataji dadin yanda yaki cin abincin nan ba, saita dinga hango yanda hankalin Hajja baya taba kwanciya in basu da lafiya, yanda zatayi tsaye a kitchen da kanta ta dafa musu abinda suka fiso tazo ta sakasu a gaba da lallashi har sai sunci sannan hankalinta zai kwanta, ai taso Hajiya Rumanan ta dauki murfin daya daga cikin tsadaddun kulolin nata ta kwada masa. Ya karbi abincin, yayi loma daya kamar yanda tace, ya gutsiri meatpie din

"Bakaci naman ba"

Tace masa

"Nakoshi ne, kuma nama bai dameni ba"

Ta karbe kwanon abincinta

"Daman meye ma ya dameka kai? In dai abinci ne. Ka tashi kaje ka kirata"

Ga mamakin Haris saiya tashi din, ita kuma ta girgiza kanta kawai, inda dantane ai saita zane masa jikinshi akan abinci. Daya tafi dakin, ya dauki wayarshi ya kunna, Hajiya Rumanan ya fara kira, sai kace tana jiranshi bugun farko ta daga

"Mami...yanzun muka dawo babu dadewa"

Ya fadi

"Harka warware sosai? Kaji saukin da zasu sallameka? Naga shekaranjiya kamar jikin naka baiyi kwari bafa"

Ya danyi murmushi

"Naji sauki sosai, gashi har naci shinkafar da kika kawomun..."

Yanda tayi dariya yasan bata yarda ba

"Allaah naci, harda meatpie ma, yayi dadi, amman banci naman ba...zuwa anjima dai zan kara meatpie din da shayi"

Dariya tayi mai cike da nishadi, a yanda har suka karasa wayar batayi masa fada ko mitar komai ba yasan taji dadi

"Zamu sake dawowa duba jikinka... harda Babanka zamu zo shisa kaga ban dawo ba"

Ya jinjina mata kai, suka karayin hira ta fada masa Anisa ma tayi bari, baiji dadin labarin ba ko kadan, yace zai kirata. Daya sauke wayar saiya kira Alhaji Mustafa, suka gaisa yana karfin jikin, ya amsa yana dorawa da

"Ciniki nakeso muyi Baba"

Cikin alamun dariya Alhaji Mustafa yace

"Ciniki dai Haris?"

Ya daga kanshi kamar yana tare dashi

"Motata, dayar motata da take nan gida nake so in siyar maka"

Dariyar da Alhaji Mustafa yayi mai sauti ce

"Motar da na dauka na baka itace zaka siyar mun yau kuma?"

Shima dariyar yayi

"Har takardun fa ka bani Baba, kaga ta zama tawa, banaso cinikin ya wuceka ne shisa zan siyar maka"

Sukayi dariya a tare

"To kudin zan tura maka yanzun ko ya za'ayi"

Ya girgiza kai

"Inaso a samo mun wata motar ne, mai kyau, karama, ta mata, bansan ko kudin zai isa ba ko sai nayi ciko"

Jin shirun da Alhaji Mustafa yayi ne yasa Haris din cewa

"Zan siyawa Maryamm ne, inaso zata fara koyon tuki cikin satin nan In Shaa Allaah"

Shirun dai Alhaji Mustafa ya sakeyi, badan yanayin numfashin da yake saukewa ba sai Haris yayi zaton kiran ya yanke ne

"Na sake applying makaranta, na fada maka daman tun kwanaki, sai dai ba a Italy bane ba, banaso in barta ko da wani abu zai taso babu mota a hannunta ko saita jira wani yazo ya kaita"

Numfashi mai nauyi Alhaji Mustafa ya sauke

"Ba zaka tafi da ita ba Haris?"

A hankali ya amsa

"Sai na fara samun makarantar, idan naje nagama komai, na danyi settling, kafin nan anyi mata passport bansan ko tana dashi ba, sai inga yanda za'ayi ta bini ko in dawo mu tafi tare"

Da alama zancen ya zauna ma Alhaji Mustafa

"Zamu zo sake dubaka daman, sai a taho mata da motar"

Haris ya girgiza kanshi

"A'a Baba, ka siyi tawa din dai sai muga wadda aka samu ko zanyi ciko"

Dan haka kawai yaji bayaso Alhaji Mustafa yace zai bata motar kyauta, tashin dai yake so ya siyar ya sai mata da kudin

"Kar in ba 'yata mota kome kake nufi?"

Murmushi yayi

"Sai dai in zaka kara mata, amman nafison dai ka siyi tawan"

Bai ja maganar ba, yace duk yanda ake ciki zai kirashi su sake magana

"Dazun Abbanka Sa'idu yake tambayar jikinka, zan tura maka lambarshi saika kira ku gaisa"

Ya amsa da

"To"

Yanajin wani

24 / 51