Advertisements
Chapter 38 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   38 / 51

111K to 114K   out of 151K words

kawai ba, shayi da wani abu..."

Kamar baiji abinda tace ba

"Ni kadai ne, gidan yayi shiru, ni kadai ne Maryamm, ya zanyi? Ina so in biyoku"

Kai ta sake girgizawa duk da baya ganinta

"A'a, dan Allaah kaje kaci wani abu"

Bata ganinshi, amman tabbas yana tsaye, ko a zaune, maikon da idanuwanshi sukeyi kuma na gardama ne

"Tafiya kikayi, kika barni, banajin cin abinci, ina so in biyoku"

Haka kawai taji ta nemi komai ta rasa, kamar bata da wani emotions daya wuce ta ganta tsaye a gabanshi, da kofin shayi da wani abin da zai hada ta mika masa, saboda zaman nan nashi da yunwa, ta tabbata komai zai iya faruwa, bata manta gargadin likitanshi ba, da yayi wani tari sai gata ta mike tsaye

"Kaga ka fara tari, dan Allaah kaje kaci abinci Ganjaa, sai muyi maganar zuwan naka, kaje kaci abinci"

A hankali ya amsa da

"Bacci kikace zakiyi, ki kwanta, in kika tashi ki kirani"

Da sauri tace

"Kaci wani abu"

Ya amsa da

"Si..."

Tasan zaici amman sai ta kara da

"Dan Allaah, kaji"

Ya sake amsawa da

"Si..."

Yana dorawa da

"Maryamm"

Kafin ta amsa kuma ya sake cewa

"Kiyi bacci"

Kai kawai ta daga masa, ita ta kashe kiran daga nan, ta sauke daga kunnenta, tanajin kamar zazzabi zai rufeta, sai kawai ta kwanta, idan ma tayi addu'a to saboda ta sabane, amman baccin ne ta dauketa, mai nauyin gaske. Bata san lokacin da Khairi ta dawo dakin ba.

*

Washegari kuwa sai bayan tayi wanka ma sannan ta fita suka gaisa da Hajja, abin karinsu ma daki suka kwaso ita da Khairi, Awwab ko magana baiyi mata ba, yana makale da Hajja, duk inda ta cire kafarta nan yake mayar da tashi, da yake Allaah Ya amsawa Maryama addu'ar data dingayi karta haifi irin Haris, ba zata iya ta dinga fama dasu biyun akan abinci ba, Awwab baya wasa da cikinshi, ko yanzun ma batasan me yake ta tauna ba, amman batajin tun zuwansu bakinshi ya huta

"Dan Allaah kar cikin yaron nan ya baci, kila bai saba da wadannan ciye-ciyen abubuwan da kuke ta dirka masa ba"

Tanajin Hajja tayi magana, amman Awwab dinne yake binsu daya bayan daya yana mika hannu. Kuma suna karyawar suna maganar bikin Khairi din, sai lokacin ma Maryama ta kula da ba ita kadai bace take da damuwa

"Me yake faruwa?"

Khairi ta sauke numfashi

"Ke kinsan zaman da zanyi a Kano yana daga cikin manyan dalilin da yasa na zabi auren mutumin nan, wai sai yanzun yake gayamun transfer ta dawo dashi Kaduna, kuma shi ba zai yiwu ace yana da mata biyu duka sun tare a Kano shi yana nan shi kadai ba, kuma ita matar tashi ba zai yiwu ta baro Kano ba saboda nata karatun, sai nice zanyi hakuri in zauna anan din, ni kosu Hajja ban fadawa ba har yanzun saboda ba zan zauna a Kaduna ba, ba haka mukayi dashi ba"

Murmushi Maryama tayi, tasan Khairi tana da hakuri, amman in har ta kafe akan ra'ayinta tana da wahalar sha'ani

"Yafa fiki gaskiya, kuma kinyi shiru ne saboda kinsan su Hajja ma haka zasuce"

Khairi ta kalleta

"To ke kuma fa? Haka zamuyi nisa da juna? Kilan ba lallai bane shima ya dinga barina ina zuwa sanda nake so, balle kuma wannan mijin naki mai kullen tsiya...ke bama zai yiwu bane ba, hakuri zaiyi ya ajiyeni inda mukayi dashi"

Har kasan zuciyar Maryama dadi takeji, duk saboda ita, Khairi take so ta zauna a Kano, saboda itane take ta wannan bacin ran, ita dai tana so a damu da ita, tana so taga tana da muhimmanci mai yawa har haka

"Dan Allaah ki daina musu dashi, kibari wani tunani nakeyi...idan nagama zamuyi magana"

Harararta Khairi tayi tana hadawa da karamin tsaki

"Wanne tunani kuma? Nan zan zauna ina jiran tunaninki?"

Sosai Maryama taji dariya ta kamata, kuma dariyar saita sake kule Khairi, ta kara jan wani tsakin. Tare sukayi wanke-wanke da Khairi, suka dora girkin rana sunata hira, fitsarin da taji ya sakata komawa dakinsu, taji wayar Khairi nata ruri, da ta karasa ta dauka sai taga Haris ne, taji wani abu mai kama da fargaba ya saukar mata, tace zata kirashi, harga Allaah mantawa tayi saboda ta tashi da saukin zuciya yau din nan, kamar fadawa Khairi da tayi ya rage mata wani kaso mai girma na zafin da takeji a ranta, ta daga

"Maryamm"

Kafin ya kara da wani abu tace

"Zan kiraka daman"

Dan tasan fada zasuyi

"Karya ne"

Murmushi yaso kwace mata

"Idan na tuna, mantawa nayi, na manta ne Ganjaa"

Yayi shiru na wasu dakika

"Da me? Dame kika manta Maryamm? Ni ko kirana?"

Akwai yanayin da yayi maganar da yasa ta amsawa da

"Kiran, mantawa nayi zan kiraka"

Ya sakeyin shiru

"Kaci abincin?"

A takaice ya amsa

"Burger"

Ta jinjina kanta tana rasa abinda zatace masa

"Zanyi exams, amman ina so in biyoku"

Tasan daman maganar ya biyosu ba zata kare ba

"Kabari kagama exams dinka"

Ya dan numfasa

"To ki koma Kano...kinji, ki koma Kano, idan nasan kina Kano zanfi samun natsuwa, bansan ya zanyi da tunanina ba Maryamm, kina Kaduna ina nan, kina gidanku fa, nasan muna fada, kina fada dani, ki koma Kano in na dawo sai mu cigaba"

Kai take girgizawa tunda ya fara magana, kamar ya sani ya cigaba da magana

"Dan Allaah, ki kara wasu kwanaki yanda zaku gaisa dasu sosai saiki koma"

Taji kamar hawaye zasu balle mata, ita dashi, a karkashin inuwa daya, ya zata kalli Haris batare da taga Autumn ba? Ita dashi, daban-daban, numfashinta neman daukewa yakeyi da wannan tunanin ya dirar mata, amman kuma bata shirya ba, komawa Kano, ta zauna ita kadai, tana bukatar ta zauna cikin 'yan uwanta

"Dan Allaah"

Ya sake fada, tasan naci dabi'arta ne, ashe ta shafa masa, ta koya masa irin magiyarta akan abu

"Kinji Maryamm"

Hawayenta suka zubo, murmushi na kwace mata a lokaci daya

"Nifa saboda ke na zabi mutumin nan, saboda zai ajiyeni a Kano, zamu zauna gari daya"

Sai kawai taji tana furta

"Nagaji da Kano Ganjaa, bana son Kano, kadaici yana damuna a Kano, dan Allaah nagaji da Kano"

Yayi shiru, wani irin shiru har saida tayi zaton kiran ya yanke tukunna yace

"Idan na siyi gida a Kaduna kuma fa? Zaki bar gidanku ki koma nawan?"

Da saurinta take daga masa kai tana share hawayen da suke zubo mata

"Maryamm"

Ya kira, muryarta a dakushe ta amsa

"Ko kina Kaduna kinsan banda hakurin kina yawan yawo"

Kai ta sake dagawa, ko ita bai barta ta fita yanda take so ba, babu yanda za'a rufa sati biyu batare da taga wani nata ba

"Ina so ki bude baki ki amsani ne"

A hankali tace

"Banma san ko inaso in sake zama da kai ba Ganjaa"

Sai taji yayi dariya mai sauti

"Ni ina so in zauna dake, zai ishemu kafin ki dawo da son zama dani, ya ishemu Maryamm"

Tayi shiru kawai

"Zan siya mana gida a Kaduna"

Shirun ta sakeyi masa

"Ki siyi layi, karmu damu Adda Khairi, ki siyi layi saiki kirani"

Ta daga masa kai

"Zan fita, karkije ko ina kinji"

Itace tayi dariya tana girgiza kanta kawai, saita tuna da wani littafi na Aisha Shafi'i, Zanen dutse, da gaske ne hali zanen dutse. Ta ajiye wayar kawai tana sake fita, kuma ta gane wani abu daya

Ba wani abu ta manta a New York ba,
Ba wani abu bane na daban tabari take jin rashin shi,
Haris ne, shi tabari tare da wani kaso mai girma na zuciyarta.

Kuma satinta daya a garin Kaduna, Hajja tace mata ta tambayi Haris su shirya suje su gaishe da Hajiya Rumana

"Naga yanda baki da hankali, shima kamar baisan abinda ya kamata ba, wannan shirmen naku bansan sanda zaku gyara shi ba"

Daga ita har Khairin haka suka hadu suka dinga mitar zuwan tun kafin ma suje, gashi Hajja tace sai sun tafi da Awwab, kuma ta sakasu kwasar wasu manyan ledoji guda biyu, daya na Hajiya Rumana, dayar kuma ta na Umma Fadime, Khairi ta dinga dariya da suke hanya Maryama tace mata su bar ledar Hajiya Rumana a mota, in suka gama abinda sukeyi su biya su kaiwa Adda Zahra su fada mata

"Ba ruwana wallahi, ke kinsan Adda tsaf zata iya gayawa Hajja, kilan ke aure yasa ki wuce duka yanzun, amman ni bani da wannan kariyar"

Itama sai abin ya bata dariya

"Hajjan? Lallai, ai kema kinsan sai in banyi abin dukan ba, ina ruwan Hajja da wani aure na"

Sake kama kawunansu sukayi lokacin da suka shiga gidan, Khairi na sabe da Awwab har bangaren Hajiya Rumanan, dukansu Hijabai ne a jikinsu, dan hijabin Khairi ce ma Maryama ta saka, da yake mai hannu ce saita bayyana dan karamin cikin da yake jikinta daya fara nunawa. Da sallamarsu suka shiga gidan, wani kamshin gayu nayi musu maraba. Dole fa ka jinjinawa Hajiya Rumana, ko da yake kamshin ai yana tare da al'adarsu ne ta mutanen Maiduguri. Tana hakimce cikin wata atamfa, ta nade kafafuwanta duka saman kujera tana danna waya, haka ta dago da kanta bayan ta amsa sallamar tana sauke musu fararen idanuwanta da Maryama taga kamar na Haris.

Maikon nan ne kawai babu, a maimakonshi sai tarin izza da isar da takeji da ita, kuma ko da suka shiga cikin falon sosai, kan kujera Maryama tayi niyyar zama, Khairi taja mata hijabi sai suka zauna akan lallausan kafet din dakin suna jera mata gaisuwa, bata amsa ba, idanuwanta na kan Awwab, shi take kallo, ta ganshi a hoto, sau biyu, Haris ne ya tura mata, kuma a duka biyun batace komai ba, sai bai kara ba, tana so tace masa ina Awwab, amman sai taji kamar inta tambaya ta hadane ta tambaya harda Maryama.

"Awwab"

Ta tsinci kanta da fadi tana mika masa hannunta, saiya koma baya ta wajen kafadar Khairi yana makalewa, yanda yayi din, yasa taji zuciyarta ta takure waje daya, ya tuna mata da kuruciyar Haris, yanda yake makalewa a bayanta duk lokacin da wani yaso ya dauke shi, kuma har girmanshi in zasu fita tare to yana daga gefenta, ko da zai rike hannunta zata dinga jinshi ne a bayanta, ta gefenta, amman daga bayanta yana saka kafarshi inda ta daga tata, kamar wanda yake bukatar dukkan kariyar da zata iya bashi, Haris da a yanzun take jin ya matsa daga bayanta ya koma na Maryama shisa a duniya babu wanda ta tsana a halin yanzun sama da yarinyar nan, ta rabata da 'danta, tasa yayi mata nisa.

Awwab din take ta kallo, shima ita yake kallo

"Yana kwiya ne?"

Ta tambaya tana sauko kafafuwanta daga kujerar

"Zo mu gaisa"

Tayi maganar cikin yaren Kanuri, saiya kalli Maryama, kamar mai jiran umarni

"Kaje Awwab, kaje ka gaisheta"

Kuma saiya tafi din, duk wani taku da yake da kananun kafafuwanshi da suke sanye da takalmi Hajiya Rumana naji kamar a cikin zuciyarta yakeyin shi, daya karasa ta kama shi, kamshin turaren da yakeyi ya cika mata hanci saita manta anyi masa takwara da sunan babban makiyinta, ta manta daga jikin Maryama ya fito, ta rike jikanta, yaron danta mafi soyuwa a ranta, tana jin kofofin da batasan dasu ba suna budewa da tarin soyayyarshi, ta manta dasu Maryama suna zaune a wajen nan, ta manta da komai sai yaron da take yiwa magana da yaren Kanuri a hankali.

Ganin sun kusan shafe mintina sha biyar a zaune, yasa Maryama cewa

"Bari mu gaishe da Umma"

Bata ko kallesu ba, saida suka mike, Awwab ya nemi ya zame daga jikinta yana shirin saka kuka tukunna ta lura dasu

"Tafiya zakuyi?"

Ta fadi da saurinta, dan bata gaji da ganin Awwab ba, to duka ma yaushe ta rike shi a hannunta? Dan Haris fa, shine take rikewa a karo na farko yau bayan shekaru biyu da wani abu, to wai me ma ya hanata zuwa New York din ta ganshi? Duk da Maryama ce ta haifeshi ai dan Haris ne, kuma Haris da duk wani abu nashi nata ne

"Eh Mami, daman munzo gaishe dake ne, kuma in kawo Awwab"

Hajiya Rumana ta jinjina kanta

"Gashi naga kuka zaiyi in kuka tafi, yaushe za'a kara kawo shi?"

Maryama ta dan kalli Khairi da tayi mata alamar

"Ba ruwana"

Da nata idanuwan

"Ko yaushe ma kikace Mami"

Hajiya Rumana ta jinjina kai

"Zan dinga aikowa ana daukar mun shi"

Har bakin kofa ta taka musu batare data sani ba, saboda Awwab din, dukansu kamar su tunstire da dariya yanda takeyi kamar ta kwace shi daga hannun Khairi, saida ta shafa kanshi, ta rike hannunshi, Khairi da taji ta fara gajiya da tsayuwar dan Maryama harta fice abinta sai kawai tayi dabarar zakuda Awwab din tana fige hannunshi daga rikon da Hajiya Rumana tayi masa tana ficewa itama

"Mata sai gulmar tsiya, ashe zaki so abinda Maryama ta haifa, karyar kiyayya kikeyi ai, zanga inda za'a dinga daukar shi ana kawo miki"

Cewar Khairi cikin zuciyarta tana makawa Hajiya Rumana hararar da ba gani zatayi ba, ba karamar dariya ta bawa Maryama ba da take mata zancen

"Inta aiko a dauke shi ai dole a bata shi"

Nata kason hararar ta samu

"Babu inda zaije a goga masa bakin hali"

Maryama ta kada kai kawai tana fadin

"Kayya Adda"

Tana jin wani abu mai nauyin gaske na danne mata zuciya, to bakin hali na nawa kuma? Idan har Awwab zai goga a wajen Hajiya Rumana, to tabbas ya fara bin Haris ne, ta kalli yaron, kallo na sosai, sai taji wani abu mai kama da tsoro ya tsirga mata.

"Allaah ka karemun Awwab, Allaah Ka karemun yarana"

Take furtawa cikin zuciyarta tana dafe cikinta da hannunta guda daya

"Allaah Karka kamasu da laifukan da mu iyayensu zamu aikata, Allaah Karka duba ayyukanmu, Allaah cikin tarin Rahmarka Ka karemun yarana. Allaah Ka shirya mahaifinsu..."

Saboda ta sani, babu wani abu da zai kwaceta a wannan gabar, bata da wata dabara, bata da inda zata juya sai wajen wanda Ya hada kaddararta da Haris waje daya...!

38

"Yanzun ya zakiyi?"

Shine tambayar da Khairi tayi mata, kuma tambaya ce da ta yiwa kanta sau babu adadi, amman wasu tambayoyin anayin sune ba don suna da amsa ba, a wajen Maryama wannan na daya daga cikin irin tambayoyin nan. Gashi dai kalmomi uku ne, amman kuma tambaya ce da inta zauna sai taji tana samar da wasu tambayoyin a karkashinta

Ya zatayi da Haris?
Ya zatayi da abinda ta gani?
Ya zatayi da abinda ta sani?
Ya zatayi...

A cikin duka tambayoyin, amsar da take da ita, amsa ce ta tambayar da babu wanda yayi mata, ba zata kara bin Haris wata kasa ba, kome zai faru ba zata kara binshi ko ina ba, wannan kadaicin, ba zata kara fuskantarshi ba, amman inta zauna a Kaduna, dole zata fuskanci Haris, shima kuma wani abune da bata shirya masa ba. Satinta uku kenan da dawowa, a kwanaki goma sha na satikan nan suna waya da Haris da ba zata iya kirga sau nawa ba a rana, har tunani takeyi yaushe yake samun lokacin yin wani abu a tsanake a yanda yake jera mata kira haka, tarin da yakeyi na damunta.

"Kaci abinci? Yaushe rabonka da abinci?"

Saboda wiwi ce, tasan ita yake ta bankadawa cikinshi, daga nan Kaduna kuwa bata da abinda zata fada masa ya rage ma ballantana kuma ya daina, amman in zaici abinci, ko yane zai taimaka masa wajen rage tasirin hadarin da yake kara jefa kanshi a ciki kullum.

"Ba zaka daina shan wiwi din nan ba ko?"

Tayi masa tambayar kwanaki biyu da suka wuce, yayi shiru, kuma a maimakon ya amsa sai yace

"Na siya mana gida, na cewa Baba 3 bedroom yace yayi mana kadan, saboda mun fara haihuwan namiji, zamu iya haifar mace, dole lokaci zaizo mu raba musu daki...daya daga cikin gidajen shine ya siyarmun, an gama gyarawa da komai, yanzun za'a zuba kayane a ciki"

Ta numfasa

"Sai a kwasomun kayana na Kano"

Yayi dariya

"Wannan kayan ai sun tsufa yanzun Maryamm, za'a sake komai ne kawai, zamu kyautar dasu kawai. Zan tura miki hotuna saiki duba abinda baiyi miki ba a canza, ina so a gama komai a satin nan"

Ita kam bata hango abinda kayanta sukayi ba, amman babu amfanin musu da Haris, kome zata fada ba zai canza masa ra'ayi ba, daya tura mata hotunan, komai ya burgeta, suka dai dinga dariya ita da Khairi, saboda kayan bakake ne

"Wai yanzun sai kawai mutum yasa bakaken kujeru, sai kace gidan mayu"

Inji Khairi, Maryama tayi dariya, in dai Haris ne to ba zaiki har fentin gidan ayi shi baki ba, ita dai ta zabi ruwan tokane mai duhu, sai yace mata ai falo biyu ne, saboda haka za'a saka ruwan tokan da take so, zaku ma a saka wancen bakaken dan sunyi masa kyau. Wani abinma bata san me yasa ya turo mata ba inya riga da ya yanke hukunci, ko dadin suyita musu yakeji bata sani ba. Yau dai da yamma ne yace mata

"Angama komai, zan tura miki kudi ko zaki kara siyan wani abin, kizo ki koma gidanmu"

Da yayi wannan maganar sai taji wani abu ya fada mata a ciki kamar dutse, yanayinta ya canza gabaki daya, hirar tasu ma batayi wani tsayi ba, ta zauna a daki kawai batare data san tunanin da takeyi ba. Awwab tun wajen karfe tara na safe Hajiya Rumana ta aiko direba ya dauke shi, haka takeyi tun washegarin zuwansu gidanta, kullum sai anzo an dauke shi, sai yamma likis za'a dawo dashi da tarin tarkacen da take ta tarawa, tasan dai kayan wasan nan har kannenshi sai sun samu a irin yanda Hajiya Rumana take siya masa su, shi Awwab din da wasa bai dame shi ba, wani jirgin kasane tun a New York, ta dauko masa kayanshi, kuma ko yanzun in dai zaiga jirgin babu wani abu na wasa da yake burgeshi.

A wannan yanayin Khairi ta sameta

"To meye matsalar?"

A hankali tace

"Nima ban sani ba..."

Suka danyi shiru, kafin Khairi tace

"Bari muyi maganar gaskiya Maryama, abinda kika gani, wani abune da har abada ba zai taba gogewa daga tunaninki ba, options din da kike dasu basu da yawa, bake kika zabi Haris ba, amman kuma cigaba da zama dashi a yanzun, wannan zabinki ne, zabin da babu wanda zai tayaki yinshi, zaki iya zama dashi bayan abinda kika gani? Zaki iya zama dashi bayan abinda kika sani?"

Taji hawaye sun ciko mata

"Inajin kamar ba zan iya ba, idan na tuna zuciyata zafi takeyi, idan kuma nayi tunanin rabuwa dashi ma zuciyar tawa zafi takeyi, kuma wani abu na fadamun zaifi mun sauki idan zuciyar namun zafi tare dashi akan ace bana tare dashi...to ya zanyi?"

Shirun suka sakeyi

"Ko kishiya bana so Adda, duk murnar da nakeyi ta bikinki dana tuna kina da kishiya sai inji murnata ta ragu, wannan fa

38 / 51