Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
meye dangantakarsu, Maryama tayi fadan, tayi dukan akan wannan halin nashi ta gaji tabarshi, ta daiyi kokari tana kanyi wajen ganin ya saka ladabi a yanayin tambayoyin da zai saka babba a gaba yana tsareshi dasu. Haka ta dinga kallonsu da irin kwalliyar da suka tsantsara, Haris sai murmushi yakeyi daya gansu. Maryama na gaisawa da Shatun Umma Fadime, ta wuceta zuwa wani teburi data hango wata kanwar Alhaji Mustafa dan ta gaisheta, Maryama ta dago kai, tayi mummunan gani, dan ba zata kirashi da kyakkyawa ba.
Tana nan, yanda take, a cikin jerin halittun da Maryama ta sani, ko tace ta gani daga fina-finai, vampires sune basa tsufa, idan a jariri ka zama vampire, to zakaita zama ne a jaririn nan ko da zaka shekara dubu a duniya. Batasan ko idanuwanta bane ba, amman yanda taga Aise a wannan hotunan nata da Haris, haka ta ganta a Maiduguri, haka kuma ta ganta a yau din nan, cikin wani leshi da bature kewa kalarshi lakabi da wine daya karbi bakar fatarta, dinkin bubu ne, sai tayi daurin data dan turo gaban goshinta kadan, tayi kwalliya mai sauki, haka dan kunne da siririyar sarkarta, tsinin takalminta kuwa ko a mafarki Maryama tasan sai anyi yawo da ita tsakanin asibitocin kashi na Nigeria kafin a samu inda zasu iya gyaran karayar da zatayi in tace zatayi amfani dashi.
Haka ta karaso har inda suke, inda Haris yake zaune, hannu ta mika masa
"Ciao..."
Da wani murmushi daya bayyana fararen hakoranta, hannu shima ya mika mata, sai dai a maimakon normal handshake da zama dasu yasa Maryama fahimtar ba wani abu bane, basu ma san zunubi bane tunda su din ba muharraman juna bane, balle kuma runguma da sumbatar kumatun juna, sai kawai duk wadannan shekarun da suka shafe, shekarun da ya saka tazara a tsakaninsu ya bace, sukayi wata gaisuwa da suka kirkira a tsakaninsu, da suka gaisa din, sai suka zame hannayen nasu a hankali, ta dan mari nashi ta baya, yayi mata, sai kuma suka dunkule hannuwan, kowa ya buga akan na kowo, bugun daya fada har zuciyar Maryama, musamman da Aise din tayi wata dariya mai sauti tana fadin
"Mi manchi..."
Maryama bata bukatar fassara, tasan ma'anar kalmomin, kuma dariyar da Haris din yayi shima, sai kawai ta dira a kunnuwan Maryama da fassarar
"Nima nayi kewarki"
Ba zatace ga abinda ya cigaba da faruwa ba, bayan Aise taja kujera a teburinsu ta zauna tana gaishe da Maryama da kalmar
"Sannu"
Wadda ta amsa mata da yin wani guntun murmushi kawai. Kuma kafin a tashi daga wannan sword crossing din, kamar lokacin ma da ake hotuna ne, tunda sunyi da Haris ba zasu zauna har a tashi ba, zasu dai zo yanda yake so, taji wata tana cewa Anisa
"Ba Aise bace waccen? Yaushe tazo Kaduna?"
Taji Anisan ta amsa da
"Suna Abuja ai..."
Waccen tayi saurin katse Anisa
"Nasani, nasan Uncle Modu ya dawo, ita daice nayi mamakin zuwanta"
Anisan ta danyi dariya
"Ai itama ta dan dade fa, kinsan bata tare da mijin, sun rabu, tam shine ta dawo...kaman dai tana so ta bude asibiti ne a Kaduna ko wani abu mai kama da wannan"
Maryama ta dafa matar dake kusa da ita saboda jirin da taji ya kwasheta, hall dinma juya mata yakeyi
"Kaji wata kakkaurar masifa"
Sarar 'yan ajinsu ce lokacin da take Islamiyya, idan anyi abu suce lukutar masifa, ita randa ta furta hakan, tayiwa nata ado da kakkaura, haka Hajja ta watsa mata wani kakkauran mari da saida bakinta yayi jini, ko wani ya fada a kusa da ita sai taga kamar hannun Hajja zaiyo fuffuke ya samesu, amman yau sai abin ya fado mata a rai, ashe kishinta yana nan, babu inda yaje. Dan har baki baki take gani, hannun da taji a bayanta, hannun Haris, hannun daya gama tuna tsohuwar soyayya ta hanyar rukunkume na Aise, ta kuwa matsa gaba tana janye jikinta, amman ya sake matsowa yana nanike mata, a daddafe suka gama hotunan suka bar wajen.
Lokacin data karasa gida, Khairi na mata kallo daya ta rufa mata baya, dan ita bataje sword crossing din ba, wani irin laulayi take fama dashi mai yawan amai, kamshin turaren da baiyi mata bama inta shaka sai ta dinga amai kamar hanjinta zai fito.
"Menene? Meya faru?"
Da wani irin yanayi Maryama tace
"Gaisawa yayi da Aise...hannunshi cikin nata Adda...aurenta ya mutu, ta dawo, aurenta ya mutu"
Cikin rudani da rashin fahimta Khairi tace
"Bangane ba, wacce Aise"
Maryama taji wasu hawaye sun zubo mata, takai hannu ta gogesu da sauri tana jan hanci
"Shikenan ba zan huta ba ko Adda? Aurenshi ya zame mun kamar wani tseren gudun da duk sanda na samu inuwa na fara numfasawa sai wani abin ya sake biyoni..."
Kamata Khairi tayi ta zaunar
"Na kasa fahimtarki Maryama, wai me yake faruwa"
Saida ta dauki wasu dakika sannan ta tattaro natsuwarta tana yiwa Khairi bayani, Khairi taja tsaki
"To shine me? Dan sun gaisa? Kinsan fa ba kintsi ne dasu ba, basu dauki wannan abubuwan wani abu ba, sannan aurenta daya mutu ke ina ruwanki? Kinga ki nutsu ki cire wani tunani daga ranki, kika san ko tun yaushe auren nata ya mutu? Tun yaushe ya sani?"
Maryama taji ta mike tsaye, tun yaushe ya sani to? Kenan suna magana kome?
"Maryama..."
Khairi ta kira a tausashe
"Babu abinda zai faru, In Shaa Allaah, ki natsu dan Allaah, ki natsu a gama hidimar nan, karki dagawa kanki hankali"
Ta daga mata kaine kawai, amman idan hankalinta yayi dubu, to kowanne a tashe yake.
Aise fa
Aise ce...
Koya zatayiwa Khairi bayani ba zata gane ba, a rashin Aise dinne aka aura masa ita. Bashi bane ya gaya mata, Anisa ce ta dankara mata, in bata manta ba haka tace
"Kinsan babu wanda ya dauka aurenku zaije wani waje, da yake Aise yaso kamar rai, da aka samu 'yar matsala shine Baba da garajen shi ya nema masa aurenki, yanda ya tubure ya nuna bayaso sai kiyi zaton ana kawoki zai koraki gida"
Kalaman sunyi mata ciwo harta rasa martani, ta kuma yi kuka da Anisan ta tafi, Haris ya rutsata da tambaya saida ta gaya masa abinda ya faru
"Karya takeyi..."
Ya fadi kanshi tsaye
"Baba ya nemar mun aurenki, kuma yana fadamun an daura na karbi auren da duka zuciyata, ko sanda na amsa, ban ganki ba, na dai san na karba, kuma babu abinda zaisani rabuwa dake, ko da Baban ne da kanshi kuwa..."
Da jajayen idanuwanta tace
"Aise din fa?"
Ya daga mata girarshi guda daya
"Maryamm"
Sai kawai tayi shiru tana karbar lallashin da yakeyi mata, inta matsa ba zaiyi mata karya ba, zai fada mata abinda tasan kunnuwanta ba zasu so ba balle kuma zuciyarta. A ranar batasan me yasa data bar dakin saita nufi bangarenshi, da yake gab da bikin suka dawo wannan gidan, gidan da ta dinga yi masa mitar yayi musu girma
"Mu da zamu rage yawa?"
Saiya ja hannunta, zuwa wani bangare, dakine babba, babba sosai irin mai hade da dan karamin falo da bedroom, kayan ciki ruwan kasa mai duhu, kalar da Fa'iza tafi so
"Ga dakinta nan"
Dariya tayi
"Kwana nawa zatayi a ciki..."
Ya daga kafadunshi
"Dakinta ne ko da Auwal zaiyi mata wani abu, saita dawo a share mata tayi zamanta...ita da Rauda, suna da dakunansu a duk wani gida da zanyi, yanda na kamokin nan na nuna miki haka zan riko Auwal in nuna masa, in fada masa ban bashi ita dan nagaji da ita ba, ko dan bata da waje a gidansu, ko da zaiyi tunanin yi mata wani abu, sai mun birkice garin Kaduna ni dashi kafin in dauko 'yata"
Haka ta dinga kallonshi tana rasa abinda zatace masa. Kamar dai yanzun data shigo dakin ta same shi harya kwanta
"Ke zan kira yanzun"
Ya fada shi, ta karasa ta zauna gefen gadon, tayi shiru
"Me ya faru?"
Ya tambaya yana tashi zaune shima, hadi da kunna kwai mai haske, dan da ya rage hasken dakin ne ya barshi dim
"Kuka kikayi? Meya faru? Menene?"
Tar ta saka idanuwanta cikin nashi
"Aise..."
Ta kira, ya dan kankance idanuwanshi, tana ganin wannan maikon na cikinsu kamar ya sauya launi, yana son boye mata wani abu
"Tun yaushe ka sani?"
Ya numfasa ta tare shi
"Inaso in sani, dan Allaah..."
Dan kamar sanin zai nutsar dashi
"Idan dawowarta Nigeria ne, an dade da naji Mami tayi maganar... mutuwar aurenta, lokacin da nasan ta dawo lokacin naji, zuwanta Kaduna...dazun, sanda tazo hall din nan"
Saiya riko hannunta, tabi hannuwan nasu da kallo, hannunshi ne na dama, wanda ya rike na Aise, ta zame hannunta tana gogewa a jikin kayanta
"Na wanke, na wanke hannuna, wanka nayi"
Yayi maganar da wani yanayi a muryarshi sanin abinda take tunani
"Babu komai Maryamm, banda gaisawar da mukayi, babu komai...in akwai kinsan zan fada miki"
Ya kamata kalamanshi su nutsar mata da zuciya, amman sai zuciyar tayi mata tambayar data subuce harta furtata
"Har zuwa yaushe? Babu komai har zuwa yaushe Ganja?"
Kai yake girgizawa
"Maryamm..."
Hawayen da suka cika mata ido suka zubo, haka kawai wani irin tsoro yake shigarta
"Dan Allaah karki daga mana hankalin akan abinda bai faru ba, abinda ba zai taba faruwa ba"
So take tace yayi mata alkawari, babu abinda zai faru, tsakaninshi da Aise, amman tana tsoro, wani abu yana fada mata
Ko yayi mata alkawarin nan zai karya...
46
"Harrasment"
Kalma ce da bature yake amfani da ita, kalma ce da in za'a rutsa Haris da bindiga ace ya fassarata sai dai ya lumshe idanuwanshi yayi fatan cikawa da imani, kalma ce da ita kadai tazo cikin kanshi wajen misalta abinda Aise takeyi masa. Ya rasa tsakanin Anisa da Munira waye ya bata address din HM Wheels, ranar da tazo haka ta wuce sakatarenshi da yake mata magana, ta bankada kofar ta shiga ciki, lokacin yana zaune yana sake duba lissafin kudin da suka shigar musu a watan da kuma wanda suka fita wajen yin gyare-gyaren wasu daga cikin motocinsu da suke bukatar service.
Har taja kujerar ta zauna bai daina abinda yakeyi ba
"Ban dauka akwai ranar da nice zan dinga binka inda kake kana mun wulakanci ba...saboda ina tuna lokacin da kaine kake biyoni kuma na rana daya ban taba wulakantaka ba"
Saida ya fara sauke numfashi tukunna ya daga kanshi yana kallonta
"Me kike so dani Aise? Me zanyi miki? Sau nawa zan fada miki ni da ke ya kare ne, koma menene muka taba sharing ya kare daga ranar da kika zabi ki auri wani a kaina!"
Itama kallonshi takeyi, wanne aure yake magana akai? Baiyi karya ba, tayi aure, amman kuma ba don ta zabi wani a kanshi ba, tana so tayi masa wannan bayanin, bakin kishinshi da takeyi ne yasa ta karbi zabin Alhaji Modu, ido rufe ta karbi auren nan, kuma idanuwanta basu bude ba sai bayan auren. Sai bayan komai ya faru, tana kwance a jikin Abdul, tukunna wani irin kuka ya kwace mata, kukan da yake ta lallashinta dan ya dauka shine sanadinshi, ko kadan baiyi tunanin kukan dana sani da nadama bane suka saukar mata. Dan data kalleshi duk hasken fatar nan tashi sai ta ganshi bakikirin, baki fiye da duhun daya lullube zuciyarta.
A ranar ta gane tayi kuskure, ta cuci kanta, ta cuci zuciyarta
"Aure kayi kaima"
Ta furta a hankali, muryarta na fitowa a karye
"Auren da kinsan yanda ya faru, sai kika kasa yimun uzuri..."
Kai take girgizawa, hawayenta na zubowa wannan karin
"Nace ka saketa ka aureni, na baka zabi Haris, saika zabeta"
Yayi shiru, da alama bashi da niyyar magana
"Kayi aure, nayi aure...yanzun na shirya, ka nemi aurena, babu wanda zai hanamu aure yanzun..."
Tasan Alhaji Modu a yanzun da gudu zai karbi Haris idan yazo neman aurenta, dan da kunnenta taji yana maganar yanda yaga Haris ya zama babban mutum. Kuma akwai dana sani mai yawa a tare dashi lokacin da aurenta ya kare ita da Abdul, yana ganin kamar shine yaja mata komai, dan idonshi ya rufe ya kasa tuna cewa ya kamata ya barwa Allaah zabi, duk da shine mahaifinta, ko da zai duba nagarta da cancanta to ya hada da nemar mata mafi alkhairi bawai shi ya yanke mata hukunci kai tsaye ba, bakowacce nagarta bace take tare da alkhairi, musamman a lokacin da ba'a nemi zabin Allaah a ciki ba.
Tabbas zai dauki wani kaso na laifin, amman mafi yawa itace da laifi, babu wani kokari da Abdul baiyi ba na ganin ya kyautata mata, zuciyarta ce bata tare dashi shisa batama ganin wannan kyautatawar, shisa suka dinga samun matsala, gashi yanda takeji da rawar kai, shima kan nashi rawa yakeyi, in suna fada har makota ke kira musu 'yan sanda saboda hayaniyarsu tana yawa, zata jawo abubuwa tana fasawa, shima kuma zai biye mata, akwai randa ya hankadata ta fada kan mudubin data fasa.
Ba zatace ga takaimaiman abinda ya hanata pressing charges ba lokacin da sukaje gaban 'yan sanda, amman ta tafi gida, kuma bayyanar cikinta ne yasa suka dan samu dai-daito ta koma. Yaransu biyu da Abdul, duka maza, yaran ma suna wajenshi, zamansu baiyi dadi ba ko kadan, haka ba rabuwar dadi akayi ba, tunda har saida akayi fadama da Alhaji Modu da abokin nashi, kuma ita batayi fada dashi ba akan full custody na yaranshi daya nema, ita yara ba wani sakasu tayi a rai ba, cikinta na biyunma kusan zatace accident ne, tana shan kwayoyin planning, mantawa tayi na rana daya bata sha akan lokaci ba, babu wata shakuwa ta kirki tsakaninta da yaran, tafi bawa aikinta muhimmanci, tasan suma ba zasu so su zauna da ita ba.
Ko sanda su Alhaji Modu suka dawo Nigeria, ba nan take ta biyosu ba, zamanta tayi acan Italy tana cigaba da aikinta, sai dai inta samu sarari ta shigo ta sake komawa, a shekaru biyar din nan bayan mutuwar aurenta, Haris ya fado mata sau babu adadi, ko yatsanta ta kalla da har lokacin ta kasa goge sunanshi daga jiki, duk irin tashin hankalin da suka dinga kwasa da Abdul akan sunan kuwa, data tuno yanda ya kalleta a haduwarsu ta Maiduguri, yanda ta ganshi da matarshi, da kuma yanda kafin su Haris din su bar Maiduguri, babu wanda baya maganar irin son da akaga Haris nayiwa Maryaman, son da baya boyewa a gaban kowa, sai taji zuciyarta ta takure waje daya, tsoro da fargaba su dirar mata.
Sai dai a shekarar nan da tazo Najeriya, da niyyar sati hudu tazo, sai dai batason zama haka kawai bata komai sai fita yawo, kusan jikinta ya riga ya saba da aiki. Saita fara duba hanyoyin da zata taimaka, akwai kungiyoyin da tayi aiki dasu a kasar Italy, da yake tasan kan komai sai gashi ta fara magana da wasu NGO's masu zaman kansu, sai kawai abin ya shiga ranta sosai, ganin irin wahalar da mata suke ciki, musamman a kauyuka anan Nigeria, wani kauyen Abuja da sukaje sai da tayi hawaye ganin macen da bata rufa shekaru ashirin da biyar ba da yara shida, shi kanshi na farkon bukatar goyo yakeyi, ita kuwa kamar ta shekara arba'in saboda wahala, babu ko wutar nepa a garin, ta dinga kallonsu tana mamakin yanda suke jin dadin zaman duniya.
Inda za'ace mata akwai mutanen da tunda suke a rayuwarsu basu taba shan iskar fanka ba, balle ayi maganar sauran jin dadin rayuwa sai ta karyata, sai gashi ta gani da idanuwanta. Data koma gida sai kawai ta rubuta takardar ajiye aiki ta tura ma asibitin da take aiki dasu a can Italy, ta yanke hukuncin zama anan Nigeria na wani lokaci. A cikin irin wannan ayyukan da sukeyi ne sukazo Kaduna, a hotel suka sauka kamar ko da yaushe ita da abokan aikin nata, tunanin ma ta nemi gidan 'yan uwa ko da a gaisa ne bai gifta mata ba, sai bayan sun fita, sun sha yawo, a mota suke amman zafin da akeyi yasa ta gaji likis, da suka koma hotel akwai wasu takardu da suka manta a wani waje, sai abokiyar aikinta Nana tace zata saka aje a karbo a kawo musu anan hotel din da suke.
"Wannan masu karbo sakon naku na Nigeria da bata lokaci, da mu muka fita kawai, inaso inyi scanning takardun nan in aika dasu dan zan kwanta da wuri"
Ranar da tayi order din abinci saida ranta ya baci a Abuja, sau nawa ma tayi order amman suna samun matsala da masu delivery, karshe abinma saiya fita daga ranta, gara ta dauki mota taje ta siyo abinda take so ta dawo
"A'a fa, banda masu delivery din HM Wheels...in dai nazo Kaduna su nake kira, ko da bana Kaduna inaso a karbo mun wani abu a aikomun dashi su nake kira, randa aka samu matsala, mai HM Wheels din da kanshi ya bani hakuri, ni muryarshi ma tasa na kara sonsu, balle kuma da naga hotonshi...har gwada kiran lambar nayi amman naji ta kamfanin ce bawai tashi ba..."
Dariya Aise tayi sosai
"Kina da karfin hali"
Nanan bazawara ce, mijinta ya rasu tun shekararsu ta farko da aure, kuma bata sake wani ba
"Daga ganin hoton mutum"
Sai kuwa Nanan tace
"Bari kiga me nake nufi"
Lokacin data mika mata wayar saida taji zuciyarta ta tsaya na wucin gadi, Haris ne, amman ba Haris dinta ba, Haris dinta babu komai a fuskarshi, wannan mutumin akwai saje ko tace kasumba da tasha gyara tana kara masa kyau, bakar fatar nan tashi har wani sheki takeyi saboda hutu, shekaru sun nuna a jikinshi, kamar kuma jikin nashi yayi maraba mai kyau da wannan shekarun, da gaske ne ya zama babban mutum, baiyi kiba ba, jikinshi ya murje dai, babu rama ko kadan a tare dashi. Sai kawai ma'anar HM Wheels ta haska mata da Haris Maryamm, yanda yake furtawa yana jan karshen sunan kamar an radashi ne dan ya gyarashi ya dinga furtawa ta sigar da zai kara dadi, ya kuma bakanta mata zuciya.
Batasan cewa soyayyar Haris waje ta samu ta kwanta tanata kara mirgina a zuciyarta ba sai da taje kwanciya, duk juyin da zatayi sai kawai ta dinga hangoshi, zuciyarta tace batasan wani abu su hadu suyi hakuri da Haris ba. Tunda dai tayi aure, to zata ari bakin bature tace
"We are even now Amore"
Sai dai harta bar Kaduna bata ga Haris ba, taje gidansu sau biyu, bata samu tarbar da tayi zato a wajen Hajiya Rumana ba, yi tayi kamar basu da wata dangantaka, a zuwan farko ma da ta rungumeta sai tayi dabara ta banbareta daga jikinta
"Ya Haris kuwa?"
Ta tambaya data kasa hakuri
"Yana lafiya, tare da matarshi, suna zamansu lafiya..."
Ta bata amsar da taji kamar ta kwada