Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
cikin kunnenta
"Hot chocolate ne"
Yace mata, ta jinjina masa kai kawai, koma menene dai, tabbas kudadenshi zasu dinga ji a jikinsu wajen siya mata shi, dan yayi mata dadi matuka. Taxi taga ya tare musu, aka saka akwatinta a baya, jakar kuma suka shiga da ita bayan Haris ya bude mata bayan motar, hot chocolate dinta take ta kurba
"Daman guda biyu ka siyamun"
Ta fadi jin nauyin kofin na raguwa
"Ba kici komai ba, yayi zaki da yawa, cikinki zai iyayin ciwo"
Da sauri tace
"Inji wa?"
Ya dan gyara zamanshi
"Inji ni"
Sai tayi shiru kawai, ko dai zai sakata ciwon ciki ai bakinta ya more dadin, balle tasan babu abinda cikinta zaiyi banda gode mata. Tafiya sukayi da Maryama take kula da nisanta saboda abinda take sha din ya kare, tana ta juya dan kofin ne a hannunta, yunwar da takeji tana dawowa sabuwa, ita duk abinda aka basu cikin jirgin wani orange juice da dan biskit kadai ta iya sakawa a cikin nata, sai kuma ruwa, zuciyarta ta dinga gaya mata data sani ta dafa wani abinma ta jeho a jaka. Ba karamin dadi taji ba lokacin da taxi din nan ta tsaya a wata unguwa mai dauke da gidaje masu matukar tsari, haka bishiyoyin ma ba'a hargitse suke ba, ga babban titi, sai dai babu wata zirga-zirga akanshi.
Tanata kallon yanayin unguwar ne da ta fito, sai ganin mai taxi din tayi yaja motarshi baya yayi reverse, har Haris kuma ya fito da akwatinta.
"Barka da zuwa New York Maryamm...muje"
Ta danyi murmushi tana binshi a baya, suka taka matattakala guda biyu na dan matsakaicin gidan, ba mukulli ya saka bama, wasu yan abubuwane taga ya daddana sai kofar ta bude, ya shiga ta rufa masa baya, dan lungune a wajen karami, sai inda taga ya cire takalminshi ya ajiye, itama ta ajiye nata, ya sauka step daya, saiga falon ya bayyana, tsarinshi yayiwa Maryama kyau sosai, irin gidajen da take gani a fina-finai, tunda daga gefen falon ga kitchen din nan, babu wata kofa ko katanga da ta rabasu da falon, kawai a gefe akayi shi.
"Zakiyi wanka ne?"
Ta kalle shi tana cire jacket din jikinta ta ajiye kan kujerar da take tsaye a gefenta, dan taji dakin da dumi sosai, alamar akwai na'urar da take dumama waje
"Wanka? Yunwa nakeji, kuma idan naci abinci ma saina fara rama sallolina"
Baice komai ba taga ya nufi kitchen din nan, ya kuma bude fridge din yana fito da abubuwa, ita dai guri ta samu ta zauna, kafafuwanta duk sunyi tsami. Duk abubuwan da ya riga yayi order ne yake microwaving, abubuwan da yake tunanin zataci, kaza, dankali, taliya sai kuma pizza. Tana zaune tana kallonshi harya gama komai ya kwaso ya kawo ya ajiye mata anan kan kafet din falon. Ta cire gyalenta ta ajiyeshi, saima kawai ta mike taje kitchen din ta wanko hannunta ta dawo ta zauna kasa, da yake Haris yasan nan zata zauna daman, shima akan kafet din yake zaune.
Taliyar a wani kwali take, haka ma kazar da chips din, sai Pizza dinma
"A ina zan juye? Kabani plate"
Ya kalleta, sai kuma ya mike ya dubo mata plate din ya dauraye shi ya kawo mata, ta juye da taliyar da dankalin da kazar, tayi Bismillah ta fara aikawa cikinta, taliyar tayi mata dadi sosai, akwai wani zaki-zaki dama tsami da bata taba tunanin zai hadu waje daya ba a dandanon, ganin yanda Haris yake kallonta yasa ta fadin
"Nasan ba ci zakayi ba...ko zakaci?"
Ya girgiza mata kai, yayi kewar kallonta tana cin abinci, yanda kuma bata kiba duk tarin abincin da takeci har mamaki abin yake bashi, kamar ya fadawa Mami, ya gaya mata ba abinci bane yake saka wasu mutanen kiba kamar yanda take tunani, amman a halin yanzun ma tafi sati bata daga wayarshi, duk akan zuwan Maryama, rigima akayi da ita da Alhaji Mustafa ba 'yar kadan ba, rigimar da taso ta saka shi a tsakiyarta ta hanyar saka shi yace ya fasa dauko Maryama ta biyoshi
"Ubanka zatayi maka inta zo nan? Wato kai Haris duk abinda nake hango maka ka rufe ido ko? Ka rantse da Allaah sai naga abinda banaso, saika likamun jinin Sa'idu a cikin zuri'a fiye da yanda nake fama dashi a yanzun"
So yake ta kwantar da hankalinta, ta nutsar da zuciyarta akan zamanshi da Maryama, saboda bai karbi aurenta dan ya sake shi ba
"Kiyi hakuri Mami, ki karbi auren nan kamar yanda nayi...saboda..."
Katse shi tayi a hasale
"Ba zan karba ba din, kana jina, akan me? Ga mata nan kala-kala"
Cikin wata irin murya yace
"Wadda kikayi mun alkawarin zaki sama mun din kin cikamun ne Mami? A danginki fa na nema aka hanani, kina kallo baki iyayin komai akai ba, bayan kinmun alkawari, ke da kanki kikayi mun alkawari, sai Baba ya miko mun wata matar a madadin wadda nace inaso kika kasa samamun inki karba? Mami so kike in kunyata shi yanda dan uwanki yayi masa?"
Yaji shirunta, shiru tayi mai yawa kafin ta kashe kiran batare da tace komai ba, kuma shine har yau bata dagawa, bai fasa kiranta ba, fushine zatayi ta gama, a hankali kuma zata gane babu wani abu da zai rabashi da Maryama in ba mutuwa ba
Haka tunanin shi ya fada masa,
A gefe kuma kaddara ta girgiza masa kai cikin yanayin rashin tabbaci
"Nifa wannan abin ba lallai in iya cinshi ba"
Maganar Maryama ta kutsa ta cikin tunaninshi tana saka shi kallon Pizza din data nuna, a fina-finai kawai ta taba ganinshi, kuma baiyi mata kama da abinda take so taci ba, ko abinda in taci zaiyi mata dadi
"Akwai dadi"
Ya fadi, ta kalle shi kamar bata yarda ba
"Baki yarda bane"
Ta dan numfasa
"Inda wani ya fada, da harshenshi ya saba da dandanon abubuwa da sai in yarda, amman kai...sau nawa ma ya taba zuwa bakinka da zakace akwai dadi"
Da gaske yayi kewarta, sosai
"Kici kiji mana saiki yanke hukunci"
Ta makale kafada, cikinta ma ya cika, data fara gani takeyi abincin duka yayi mata kadan, amman ko rabinshi bata cinye ba.
"Nifa na koshi ma, na koshi kuma bacci nakeji"
Ta karasa maganar tana mikewa, hannu taje ta wanke
"Ina zanyi alwala? Ina ne gabas kuma? Ni bana ganewa idan naje waje, ko can gidan su Adda ne suka nuna mun ranar da aka kaini"
Da kanshi Haris ya mike ya nuna mata bedroom din da bayan ta shiga ta nufi bandaki kanta tsaye, ta gama duk uzurin da zatayi ta fito, akwatinta ta dawo ta dauka ta bude, akwai hijabi a ciki ta dauka sannan ta rufe shi ta koma bedroom din ta gabatar da salolinta, dakyar take daga idanuwanta lokacin data idar, a haka take karewa dakin kallon, idanuwanta suka sauka daga can gefen gadon dakin, ta wani lungu, zuciyarta ta buga, hotonta ne, frame din hotonta, daya daga cikin hotunan nan da yace na birthday dinta, kanta babu dankwali, tshirt ce ma a jikinta ranar, wata jar tshirt saita saka wando, kuma a tsaye take da kofin da ba zama ta tuna menene a cikinshi ba, da alama kuma hankalinta kacokan yana kan tv ne, iya cikinta ne zuwa kanta aka dauki hoton, ta rasa hadinshi da black and white, tunda wannan dinma anan yake, da bata tuna rigar ba, babu yanda za'ayi ta gane kalarta.
"Baccin yazo ne?"
Haris daya leko kanshi ya tambayeta, ta danyi murmushi
"Kwanciya zanyi dai..."
Shima murmushin yayi
"Inzo mu kwanta?"
Taji kunya ta dirar mata, ta rasa amsar data kamata ta bashi, shisa ta zabi tayi shiru kawai, ita zataso ma ta rage kayan jikinta ne, amman inta kwanta, yanda Haris ya gayyaci kanshi din nan zuwa zaiyi ya kwanta shima, gashi ba dare bane balle tace duhun zai boyeta daga idanuwanshi ko da yabar masa gangar jikinta. Sai kawai ta mike ta hau gadon, tana kallonshi ya shiga cikin dakin, ya nayar da kofar ya rufe, shima ya zagaya ya hau gadon, lokacin daya saka hannunshi ya jata yana hadawa da jikinshi, taji wani irin numfashi daya sauke
"Nayi kewarki Maryamm, har bansan adadin sau nawa na kwanta akan gadon nan ina tunaninki a jikina ba"
Tayi luf tanajin duminshi da maganar da yayi sun hadar mata
"Amman da alama ni kadai nayi kewarki ko?"
Wannan karin ya fada cikin kunnenta, tayi shiru, ya dan kara karfin rikon da yayi mata saida ta motsa
"Bakiyi kewata ba Maryamm?"
Muryarta a hankali, tana rawa ta fito
"Nayi"
A hankali yace
"Karyane"
Yaune karo na biyu daya furta mata kalmar, ya karyatata kai tsaye, amman kuma ta rasa menene a yanayin yanda yayi maganar da maimakon haushi saita sakata murmushi
"Da gaske"
Sai ya sa karfi yana juyo da ita ta fuskance shi, idanuwanshi cikin nata sukayi mata nauyi ainun, dole ta sauke nata, amman saiya saka hannunshi ya dago da fuskarta
"Ban yarda ba Maryamm, ni kadai nayi kewarki"
Idanuwanta ta kara saukewa, ba zuciyarta kadai ke harbawa ba, duka jikinta bari yakeyi, sau nawa yake rungumeta suyi bacci, amman na yau yayi mata daban, batasan ko dan ya juyata ta fuskance shi bane ba, ko dan hasken da yake cike da dakin, ko kuma dumin numfashin shi da takeji akan fuskarta
"Barka da zuwa New York, duk da na fada miki dazun, yanzun inaso ince miki barka da shigowa rayuwata"
Saboda tun daya dora idanuwanshi akanta a airport din nan yaji yanda ta shigo rayuwarshi a yau din nan, kamar wancen karin, ranar da aka kawota, ya karbeta ne kawai, amman baijita ba, amman a yau wani abu ya canza, wani abu a tsakaninsu, koshi kadai yaji hakan ma ba matsala bane ba, amman Maryama ta shigo rayuwarshi, ya kuma bude hannuwanshi ya karbeta, itace dai yake so yanzun ta bude tata rayuwar ta karbeshi,
Rayuwarta
Jikinta
Zuciyarta, harma da ruhinta idan zai samu
So yake ta karbeshi yanda zata zama mallakinshi gabaki daya, amman ba yanzun nan ba, ba yanzun da yakejin bugun zuciyarta a kirjinshi ba, ba yanzun da jikinta ke kyarma haka ba
"Ba yanzun ba Maryamm, muna da lokaci mai yawa, ina da lokaci, ki huta yanzun, kiyi bacci"
Ta daga masa kai kawai dan ko ta bude bakinta ma ba zata iya magana ba, ya sumbaci goshinta, da saman idanuwanta data lumshe. Baccin tayi, da yanda numfashinta ya canza yasan bacci tayi, shima kuma nashi idanuwanta sun fara lumshewa alamar bacci, wata gajiya ta saukar masa, ya kara gyara mata kwanciya a jikinshi, ya rufa musu katon bargon da yake kan gadon, ya rufe nashi idanuwan wani irin bacci mai nauyin daya kwana biyu baiyi irinshi ba yayi gaba dashi.
Maryama ta rigashi tashi, na yan dakika ta manta inda take, ta dauka ma mafarki takeyi data bude idanuwanta akan fuskar Haris, kafin komai ya dawo mata, kaddara kenan, wai itace yau a wata kasa, itace ta hawo jirgi har wata kasa, Haris din take kallo, batajin ta taba samun damar kare masa kallo haka, wani haske ya ratso ta gilashin window din, shine ma ya shigar mata ido yana tashinta, da yake labulen window din ba'a jashi ba, kamar wata fitila ce dan baiyi kama da hasken rana ba, kuma yanayin nauyin jikinta ma tasan bacci tayi sosai, hasken ya haska wuyan Haris da bayan kanshi.
Ta tsinci kanta da kai yatsa ta dan dangwali kumatunshi, ta kalli yatsan nata, sai kuma dariya taso kwace mata, to ai inda bakin nashi mai zuba ne da ita zai fara batawa, kawai gani tayi yana wani kyalli-kyalli, fuskarshi da yanda yake baccin kamar an jikata cikin wani mai da yake da saukin maiko, ko haka duk bakar fata inta hadu da hutu takeyi? Kuma kilan kallon ne yaji yayi masa yawa yasa shi bude idanuwanshi da suka sauka cikin nata
"Me kike nema?"
Ya tambaya, tun da ta motsa ya tashi, bai bude idanuwanshi ba
"A ina?"
Ta tambaya a diririce
"A jikin fuskata, me kika shafamun a kumatu?"
Ta girgiza kai da sauri, yaji kenan? Idonshi biyu? Allaah ne ya rufa mata asiri da bata dangwalar masa lebe ba kenan
"Bakomai ba, ban gani bane nazo gyara kwanciya, ka matseni"
Ya danyi murmushi yana sauke numfashi, sai kawai ya saketa ya mirgina gefe, tunda kokarin mallakar kanshi yakeyi, yanda ta diririce din nan so yake ya kara cika wannan idanuwan nata da bacci ya canzawa launi da wani abu na daban. Bandaki ya shige, yabarta kwance zuciyarta nata bugawa, daya fito sai itama ta tashi, yanzun wankan da batayi ba ta samu tayi, ta fito taga Haris ya janyo akwatinta ya shigo dashi dakin, ya kuma bude yana fito da kayayyakinta daya bayan daya, da saurinta ta karaso ganin abinda yake shirin daukowa
"Dan Allaah..."
Ta fadi da sauri, ita batama san me zaiyi da kayan ba
"Zan jera miki ne a wardrobe"
Ya amsa kamar yaji me tace
"Baga ta can ba, zan jera, kawai saika budewa mutum kayanshi, dan Allaah kabari, karka fito da komai, waye yake taba akwatin mace?"
Yayi murmushi
"Meye a ciki da bakya so ingani"
Ya fada yana kallon akwatin, takai hannu zata janye ya rigata ta hanyar daga abinda bataso ya dauka din, kuma saiya kwashe da dariya
"Size nawa ne wannan?"
Ya tambaya yana kokarin juyawa ya duba, ta fisge tanajin wani abu bayan tsananin kunya na dirar mata
"Wallahi banaso, kabari, ina ruwanka? Me yasa zaka daukar mun?"
Ta karasa da rawar murya, taji kunya irin wadda bata taba sani ba tunda take a rayuwarta, kuma saiya kara yin dariya, mai sauti, yanda idanuwanshi ke yawatawa a jikinta sai kawai taga ma waje daya suka tsaya, taja akwatin gefe tana juya masa baya, ya girgiza kanshi kawai yana murmushi, in dai ita dashine, su kadai a kasar nan, a hankali zata gane bata da wani abu da zata boye masa
Ita da komai nata nashi ne...
Duk da shi kanshi bai hango tazarar faruwar hakan bata da yawa ba...Maryaman zata zama tashi, zata zama tashi ta yanda kowa ma zai shaida hakan...
31
"Dan Allaah ka matsa"
Maryama tayi maganar muryarta na rawa, hawayen da take ta rikewa suka zubo mata, komai ya isheta, duniyar duka batajin dadinta, inda ace mutum ya san ranar mutuwarshi, to da sai tace watakila watan nata mutuwar ne ya tsaya, shisa komai ya hargitse mata haka. Dazun da safe sai da ta kara lissafawa, kwananta hamsin da hudu da zuwa, kuma a kwanaki hamsin din nan, ita dai zatace hudun farko ne tayi su cikin jin dadi da walwala. Saboda a daren kwana na biyar dinne daga irin rikon da Haris yayi mata da yawon da hannuwanshi sukeyi a jikinta tasan cewa zaman zurun da yakeyi mata ya kare. Jiki da zuciyarta na rawa ta rike hannun nashi da ya kwace
"Dan Allaah, Ganja, dan Allaah, ba muyi sallah ba, ba muyi sallah ba"
Ta furta tana kara maimaitawa
"Nayi har isha'i"
Ya amsa mata da muryarshi da ta dishe
"Sallar Nafila, ba muyi Salatul Shukr ba..."
Taji yanda ya dakata da komai na wasu dakiku, kamar mai nazarin maganar da tayi, zaice rabonshi da cikakkiyar Islamiyya tunda ya gama primary, a boarding din da yayi kuwa ko an korasu ba wani maida hankali yakeyi ba, yana da haddar izu goma daga kasa, shima albarkacin jajircewar Malamansu ne lokacin kuruciya, itama haddar idan aka tsare shi yasan ba zai iya kawota gabaki daya ba. A secondary kuma, a ranakun da ya zauna a Islamiyyar dan abinda yake tsinta ba wani mai yawa bane ba, ya gane Shukr, ai godiya kenan, Sallar godiya take nufi
"Farilla ce? Salatul Shukr din?"
Ta girgiza masa kai, asalima Malamai da yawa sun sakata a jerin Mustahabbi ne, amman abune mai kyau, tunda har Salatul Hajah ma saida Adda Maimunatu ta saka tayi ana gobe daurin aure
"In kin idar ki roki Allaah Ya saka miki salama a auren nan, Allaah Yasa komai na cikinshi yazo miki da sauki"
Tayi sallar dai, saboda a lokacin bataso ta dameta da wani wa'azi, amman data idar ta zauna babu addu'ar da tayi. Watakila yanzun dinma tsoron daya cika kirjinta ne ya tuna mata da ba suyi sallar da duk da ba farilla bace ta zamewa kowanne sababbin ma'aurata farilla
"Dan Allaah..."
Tayi maganar cike da roko, bakin da take magana dashi ya rufe mata da nashi, data lumshe idanuwanta sai ta dora hannunta saman kanshi a hankali tana furta
"Allahumma inni as’aluka khairahu, wa khaira ma jabaltahu ‘alayhi, wa a’udhu bika min sharrihi, wa sharri ma jabaltahu ‘alayhi"
A wannan daren ne Haris yayi hannun riga da duk wani kirki data dade tana dangantashi dashi. Idan yaji kukanta bai nuna alama ba, idan yaji magiyarta to ya zabi ya share ne, shisa ta daina magiyar, ta koma karanto duk wata addu'a da tazo cikin kanta, saboda taga alama rayuwarta Haris ya nema a wannan daren. Kuma washegari haka ya sake maimaita mata fiye dana farkon, sai gashi ta tashi da zazzabin da bai taba zauna mata a kai ba inta karanta a littafinta, to zazzabin menene zakayi? Su marubuta karyarsu ba sallah takeyi ba, ashe a wannan karin ainahin gaskiya ce basu haskawa 'yan mata irinta ba, kamata yayi ace babu wani sakaye-sakaye sun fito fili sunci rayuwarka namiji zai nema, saika san irin shirin da zakayi.
"Allaah Ganja kabari karfina ya dawo, ba yarda zanyi ba, dan kaga karfina ya tafi shisa"
Ta fadi cikin kukan da takeyi, saida ta saka murmushi ya kwace masa, amman da safen ba karamin rikicewa yayi ba jin yanda jikinta yayi zafi rau, danma Allaah Ya rufa masa asiri ko da ta kama ya kaita asibiti ne babu mai garqame shi tunda abinda yaja jinkirin samun izininta na biyoshi shine shekarun nata, kasar New York suna da tsauri matuka akan maganar Legal age, ko da kuwa ga bakine, zasu girmama auren da yake tsakanin Haris da Maryama ne, su kuma yarda dashi idan shekarunta suka kai sha takwas. To dan after care dinma Maryama taki barinshi ya nuna mata, daya riketa a jikinshi zata gartsa masa cizo, ko yanzun ma yayi tunanin zatayi masa musu daya bata magani da ruwa, sai ta karba tasha.
Yanda tayi laushi ne kadai yasa ta yarda Haris ya taimaka mata tayi wanka, ta sake kaya, daga zaune tayi sallar asuba, dan kafafuwanta rawa sukeyi, ga jiri-jiri da take gani, kwana biyu tayi tana fama da zazzabin nan kafin ta samu kanta. Bata tabajin dadin kadaici irin na kwana hudun da Haris yayi a makaranta ya barta ita kadai ba. Sai dai tayi kallo, ta dafa duk abinda ya samu, ta kuma kwanta. Da sukayi waya da Adda Zahra ne ma taji yanayinta, duk da ba wasu tambayoyi