Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
miki ai ko?"
Ta daga mata kai kawai badan ta tuna me tace ba
"Wayar da na gaya miki tana nan cikin jakarki, zan dinga kiranki muna magana"
Ta sake daga kai tana kai hannu tana share hawayen da sukaqi tsaya mata, tana kallon Adda Zahra ta fice daga dakin taja kofar ta rufe, karar na dirarwa Maryam har cikin ruhi, kamar an rufe da wani bangare na rayuwarta haka takeji, sai ta koma kan gadon ta kwanta kawai, tana jin tashin motocinsu, kuka takeyi har sautinta ya dishe, akan idonta dakin yayi duhu, ta kuma jiyo kiran sallar Magriba, shine ma ya tasheta, ta wanke fuskarta, ta dauro alwala, inda tayi la'asar, dardumar dama hijabin suna nan, dankwalin da aka kinkima matane ta kwance ta jefar anan kasa, tai sallar, tayi kwanciyarta a wajen har aka kira isha'i tayi, ta mayar da Shafi'i da Wutr da ya zame mata jiki saboda tunda suka taso suka ga Hajja nayi, itama duk ta saka musu sha'awar hakan.
Ta ga gaske ya gauraye dakin, a hankali kuma kunnuwanta suke jiyo mata karar generator kadan-kadan, ta sauke ajiyar zuciya, kishin ruwa ma takeji, dole ta mike badan tana so ba, fuskarta tayi fayau, hawaye ya wanke mata komai, tama manta babu ko hijabi a jikinta, data bude kofar dakin saita leka kanta kamar mai tsoron wani abu, zuciyarta sai bugawa takeyi, to idan ta ganshi fa? Suka hadu? Ya zatayi? Tasan dole zata ganshi, amman kuma tanajin kamar bata shirya ba, kamar ba yanzun take so su hadu ba, saita yanke shawarar dubawa zatayi ta dauko abubuwan bukata, ruwan ma da yawa saita koma dakin nan ta rufe da mukulli yanda zatayi kwanaki bata fito ba.
Amman dole saita dudduba tunda inma akwai ruwan batasan ina yake ba, taje tsakiyar falon kenan taji motsi, a tsorace ta daga kanta, ta kuwa saka idanuwanta cikin na Haris, da yake su Lalaye suka hana ya bisu, a cewarsu zasu raka su Adda Zahra har wajen gari, ya zauna da amarya, wasu ledoji ne suka bashi, daya karba haka yaje ya samu fridge din kwance da aka ajiye a kitchen ya bude ya saka su a ciki, daya fita sallar isha'i ya dawone yaga babu wuta yasa aka kunna generator, so yakeyi ya kwanta, kanshi yayi wani irin nauyi, harma ya kwantan yaji cikinshi na neman agaji, yasan zai iyayin aman da zai bashi wahala in ya kara bankar hayaqi baici komai ba.
Shayi yaso ya samu, amman baisan ta ina zai fara ba, tunda baiga lipton ba balle kettle din da zai dora ruwan zafin, sai kawai ya dauki lemo da wani cake, anan kitchen din ya tsaya ya ci badon sunyi masa dadi ba, ya dauko ruwa ya fito kenan ya ganta, ko yace kanta, kitson da yake kanta, kananun kitsonta shiya fara gani, sannan ta dago kai, idanuwanta tar akanshi cikin hasken dakin, abu na farko daya fara gani shine sirantarta, rashin kibarta, amman yaga fuskar nan tata a cikin ta 'yan uwanta dazun, ko yace wasu abubuwa na fuskar a tare da kowannensu, kafin ma ya gama kare mata kallo ta kwashe da wata irin dariya.
Farin kwaine a falon, kuma a yanayin hasken zaka san ba guda daya bane, kwayayena dan ko allura ka yadda zaka dauki kayanka, sai taga Haris yafi duka 'yan uwanshi data gani baki, yamafi ita Hajiya Rumanan baki, ita da tafi su Anisa kenan, kawai irin kukan da ta gamayi dazun ne yake dawo mata, tana jin wai daman akan wannan danduqununun ne ta zauna take ta asarar hawayenta? Ai da ta sani da ta sauya akalar kukanta, tayi kukan yanda ta tabbata an gama kashe mata rayuwa tunda aka hadata dashi, ta jingine komai a gefe, idan akwai abinda Haris bayaso shine yaga ana dariyar da baisan dalilinta ba, balle kuma dariyar da aka kalleshi aka tuntsire da ita
"Lafiya?"
Ya tsinci kanshi da tambaya, kuma data samu ta tsagaita, yayi magana ta sake kallonshi sai kawai ta kara kwashewa da dariya, bakar tshirt ce a jikinshi da wani bakin wando da ya dan wuce gwiwarshi kadan, saboda tsabar karfin hali a tunanin Maryam kenan
"Maimakon kasa kayan da zaka dan haska, kai Subhanallahi..."
Ta fada batare data shirya ba, ya kankance mata idanuwanshi cikin rashin fahimta, ta numfasa, ita ta manta rabon da tayi dariya irin wannan
"Yi hakuri, ganinka nayi baqiqirin..."
Tace masa tana sake kwashewa da dariya...
16
Saida ya kwanta maganarta ta dawo masa, dan rabawa yayi ya wuce yana barinta a wajen
"Yi hakuri, ganinka nayi baqiqirin..."
Lokacin da yake Italy, mata da yawa suna yawan magana akan kalar fatarshi, suce bakinshi nayi musu kyau, duk da anfi yaba idanuwanshi fiye da komai, ko Aise tana ce masa idanuwanshi nayi mata kyau, sai dai yayi dariya, bai taba maida hankali akan irin kyan da ake fadar yana dashi ba, amman yau ba don gajiyar da yakeji ta zuciya da ruhi ba zai tashi ne yaje ya duba mudubi yaga abinda zaisa wancen yarinyar mai kama da sandar raken ta kalleshi ta kwashe da dariya, to wai mema ya samu bakin nashi? Baqiqirin tace, a cikin kan Haris abinda za'a danganta da wannan kalar sai dai gawayi ko bakar leda. Ya dago da hannunshi ya kalla, to bakin nashi ya shahara har hakane?
Yaja karamin tsaki kawai yana rasa abinda ya kamata yaji, ya kalli wayarshi da take ajiye can nesa, sai yaji kewar Aise na nukurkusarshi, ya kara jan wani tsakin, ya rufe idanuwanshi kawai, bacci ya dauke shi, sai dai ko sha biyun dare batayi ba ya farka saboda mafarkin Aise da yayi tana tsaye tana kallon shi, tashi yayi yaje ya watsa ruwa ko zai samu sauki, daya fito ya samu t-shirt ya dora akan gajeran wandon da yake jikinshi, ya dauko laptop dinshi da charger, ya saka a jikin socket din kusa da gado ya janyota zuwa kan gadon ya saka laptop din a caji, sannan ya zauna ya budeta ya kunna, akwai wasu hotuna da zaiyi aikinsu, duk da yana da sauran kwanaki uku kafin ranar daya bayar na aikawa dasu ya cika, amman yana bukatar distraction din, aikin zai rage masa tunani.
Abinda yayi kenan har safe, tunda a gida yayi sallar asuba duk da yanaji anayi a masallaci, kuma yaga gida baifi bakwai bane tsakanin gidanshi da masallaci a unguwar, shi daman tun yana gida sallah a masallaci bata dame shi ba, Hajiya Rumanan da zatayi masa magana itama bata damu da zuwanshi masallaci ko akasin haka ba, a Italy kuwa wasu ranakun ma hada wasu sallolin yakeyi abinshi. Alhaji Mustafa ne kawai in yana gari yakanyi masa maganar zuwa wasu ranakun, amman shi a karan kanshi sai sa'a, in ba juma'a ba. Yau da yayi sallar saiya kwanta, lokacin ne kuma ya samu bacci.
Yanda ya kusan kwana a zaune, itama Maryama abinda ya faru da ita kenan, ta dauki ruwan ta koma daki, data kwanta sai Haris ya dinga dawo mata, ko ido ta rufe saita ganshi baqiqirin cikin bakaken kaya, tasan wasu in suna dariyar da ta kai dariya zakaga idonsu har hawaye yakeyi, amman ita dariyar da takeyi hawayenta bana nishadi bane sam, hawayenta na yanda duk tarin fararen mazan da suke duniya, ace babu mijinta a ciki, sai wannan bakin katon, ga baki ga muni, kamar ma hancinshi yayiwa fuskarshi tsayi ko itace bata gani ba sosai, kuma ta ga alama yanda baiyi mata ba, shima wannan auren kamar na dole ne a wajen shi, tunda taga idanuwanshi kamar cike suke da hawaye.
Allaah Ya taimake shi su farare ne, koya hakoranshi suke? Zata so ta gansu. Wannan tunane-tunanen shine abinda ya hana mata samun bacci, ko ya zata juya al'amarin sai taji shi babba a wajenta, mijinta fa, mijinta ne danduqununun nan, sai kawai ta girgiza kai hawaye su zubo mata, ashe da gaske ne ana kasheka da ranka? To da me yasa ma take tunanin zata kulle kofarta, shi da yake bakima bai boye mata ba, itace zata boye masa? Gara ta fita tayi harkar gabanta, ba zai yiwu ace ga auren bakin ciki ga takura ba, gara taji da abu daya. Da ta gaji da saka wasikar jaki ma, saita mike cikin daren ta binciko jakar da Adda Zahra tace mata akwai waya, ta kuwa ganta, Nokia, kirar C3 da ake yayi a shekarar, kamar zata fasa ihu saboda murna, nan da nan ta kunna, ta dauko cajar wayar ta ajiye akan gado, ta koma ta kwanta tunda taga a cike take.
Ta shiga nan ta fita can tana jinta kamar a gajimare, ita da take ta lissafin a siyawa Khairi wayar ta zama tata, tunda sai sun gama secondary harsun samu admission sannan Alhaji Sa'id yace zai sai musu wayoyi, to tasan Khairi zata rigata, kuma ita bata damu da waya yanda Maryaman take nacinta ba, ta tabbata bar mata zatayi, ashe zata mallaki tata a kurkusa, taga an saka mata lambar duka 'yan gidansu dake da waya, data duba taga ta Alhaji Sa'id da akayi saving da Abba, sai taji kamar ta kirashi, a lokacin karfe uku da mintina arba'in, amman ai zaiyi tunanin ba lafiya ba, zata bari sai da safe dan taga kudi a wayar, tabi kowa ta kira su gaisa.
Sai gashi da karsashi tayi sallar asuba, ta zauna tayi azkar kafin tasa wayar caji ta kwanta, bacci tayi kamar bata da wata matsala a rayuwarta. Yunwa ce ta tasheta wajen karfe goma da rabi, bayi ta shiga ta wanke fuskarta tayi brush, ta fito tana nufar kitchen kanta tsaye, haka ta dinga bin tsarin kitchen din da kallo dan jiya batashi takeyi ba, yayi kyau, ba wani babba bane ba, amman an kawata shi da kayayyaki da kalarsu take da sanyin kallo a idanuwa, tasan Adda Zahra batason kala mai hayaniya tunda canma, ko atamfofinta zaka gan kalar jikinsu bata taba wuce uku, wasu ma kala biyu ne, shisa kitchen din baiyi hayaniya ba. Taga kwan a kunne, kuma bata jiyo karar generator ba, alamar wutace aka dawo da ita.
Yunwa take ji ta gaske, amman batasan ta inda zata fara ba, kome zata dafa, taga wata kofa a cikin kitchen din, data shiga sai taga dan karamin store ne, kuma akwai kayan abinci a ciki daga kan shinkafa har zuwa indomie, sai ta shiga ta fasa kwalin indomie din, kananu ne, ta dauko kwara biyu, ta fito ta ajiye, manyan bokatan dai tasan su dublan ne, tana sonsu, amman ta rasa dalilin da yasa su basa sonta, duk sanda zata saki jiki taci sai cikinta ya dingayi mata ciwo, akwai albasa da aka zuba a wani kwando cikin kitchen din, saita dauko ta kara dawowa, tana ta faman bude-bude, bata ga ashana ba, kuma ta kunna gas din taga ba irin na gidan Adda Maimunatu bane, dole sai tasa ashana. Gashi duka gida hudun burners ne babu electric.
Tayi tsaye cikin kitchen din ta rasa mafita, to ko dai zuwa zatayi ta duba ta ga idan yana nan ta tambayeshi ko shi yasan inda ashana take? Sai kuma taga ai dukansu bakine a gidan, sai dai tace masa ya siyo mata, tunda ba zata zauna yunwa ta kasheta ba. Ta fito da wannan niyyar kenan taga Haris din shima ya fito, bakar rigace dai a jikinshi, ya dai sake wando zuwa jeans ba irin wandon jiya ba, amman shima bakine, ita ta sake kayan jikinta dan batason takura in zata kwanta, wani material ta saka natane na gida, dinkin bubu ne kuma yadin bashi da nauyi, dashi ta kwanta, shine a jikinta yanzun. Bakin shi dai yana nan yanda tagani jiya, yau dai kamar ya shafa mai tunda har wani sheki-sheki taga yanayi.
Abinda bata gani ba jiya shine Haris na da tsayi, duk da bashi da wata cikar jiki, dan itama din ba gajera bace ba tana da matsakaicin tsayi, shisa daga inda take tana tunanin kanta zai kai kafadar Haris inda zasu jera, wayace a hannunshi yana dannawa, ya kalleta sau daya, saiya maida kanshi kan wayar yana cigaba da tafiya, da alama ficewa zaiyi ya bar gidan
"Harisu..."
Ta tsinci kanta da furtawa, sai kuma taji sunan ya danyi mata nauyi, ko dan basu saba kiran sunan wanda ya girmesu gatsau haka ba, yaji ta, shisa ya tsaya, kuma yanda ta kira sunan nashi ne yasa shi juyawa yana kallonta
"Harisu kuma?"
Ya maimaita cikin wani yanayi, yana kuma kara maimaitawa cikin kanshi, wanne irin Harisu? Kallonta yakeyi yana so ya gane matsalarta, dan tabbas tana da matsala, babu yanda za'ayi ta rasa matsala
"Ina as...ina kwana"
Tayi saurin canza akalar tambayar ganin yanda yake kallonta, bai amsa ba sai girarshi daya daya daga sama
"Daman...daman..."
Ta rasa me yasa taji kallon da yake mata yana neman daburta mata lissafi
"Ashana zaka siyomun"
Taga lokacin daya dage dayar girar
"Ashana? Ni zan siyo miki ashana?"
Idan bashi zai siyo mata ba waye zai siyo mata to? Ita bata da ko sisi ma balle tayi tunanin fita ta siya, kuma in tana da kudin ai batasan ina zata nufa ba
"Yunwa nakeji, babu ashana da zan kunna gas...bani da kudi, kuma bansan inda zanje in siyo ba ko ina da kudi"
Shifa yanda take tsaye a gabanshi tana masa magana kamar wanda suka saba da juna mamaki yake bashi, babu wani alamar bakunta a tare da ita, kamar ta sanshi, abinda bai sani ba, Maryama na daga cikin mutanen da basa bakunta, in yau ta fara ganinka to zata gaya maka abinda yake ranta batare da wani dar ba, duk gidansu ita da Khalifa ne suke da wannan halin, shisa suka fi jituwa, ta kuma fi cin dukanshi fiye da kowa saboda yanda yake gatse-gatse itama haka take, zasu zauna amman da wahala a watse bai kai mata duka ba saboda wata maganar da zata yaba masa
"In kuma akwai goma a wajenka saika nuna mun wajen dan Allaah, cikina sai kullewa yakeyi"
Ya numfasa
"Wai wacce irin goma kuma? Ina zan nuna miki?"
Kanta tsaye tace
"Wacce irin goma zan tambaya dan Allaah, Naira goma mana, shagon da ake saida ashana zamu fita ka nuna mun, tunda kaga ni ba sanin waje nayi ba"
Idan ya tsaya, ba mamaki bane abinda zai sandarar dashi, ciwon kan da ya tashi babu shine wannan yarinyar zata dawo masa dashi, shisa yasa hannu a aljihunshi, yana da lighter, ya riga ya saba ma tana daga cikin abinda yake dauka ya saka a aljihu duk idan zai fita, kuma da yabar kasar sai ta zamana wani abu da saiya duba mai kyau zai cire kudi ya siya, wannan dinma wata irice ta silver, in ba budewa yayi ba, ba zakayi zaton lighter bace ba.
"Ga lighter"
Ta karba, amman bakinta da bai saba shiru bane yace masa
"Lighter? Wannan lighter ce? To kai me kakeyi da lighter?"
A iya saninta ba haka lighter take ba, kuma babu masu amfani da ita sai masu shan sigari, taji gabanta ya yanke ya fadi, ta kalli labbanshi da suke da duhu suma kamar sauran jikinshi, tunda ai masu shan sigari zakaga bakinsu bakikirin haka tafukan hannuwansu
"Ban sani ba"
Haris ya tsinci kanshi da amsa mata
"Ki kunna ki bani fita zanyi"
Ta kuwa wuce, amman da taje saita rasa yanda zatayi ta kunna, daga kitchen din ta bude murya tana fadin
"Nifa na kasa kunnawa..."
Ya jita, ya numfasa
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Haris ya furta kasan numfashinshi, fita yayi niyyar yi, akwai wani tea joint da sukaje da Lalaye, can yayi niyyar zuwa ya zauna ya sha shayin saiya dawo ya cigaba da aikin gyara hotunan da yakeyi, amman yaga alamar ita ciwon kai take son hadashi dashi
"Kaji?"
Ta sake fadi, bai motsa ba
"Harisu!"
Yaji kamar ta kwada masa sanda, yanda yakejin dadin sunanshi, amman yau tana neman ta fitar masa dashi daga rai, baisan ya tsohon wake yake ba, amman da tace Harisun nan shine abinda ya fara hangowa, kitchen din ya nufa
"Karki kara cemun Harisu, sunana Haris, bani?"
Ya karasa maganar yana fisge lighter din daga hannunshi, ta kalle shi ya hade girar sama da ta kasa ya tsuke bakar fuskar nan, ta matsa gefe, daya kunna lighter din saiya rasa me zai murda kuma, ya juya ya kalleta ta zuba masa ido
"Ina zan kunna miki?"
Kamar tace masa
"Ai bari nayi inga gudun ruwanka"
Saita cije rike bakinta
"Kinsan Allaah zan tafiyata"
Da sauri tace
"Yi hakuri, saika matsa ai"
Ya matsa din, yaga tana kikiniyar murdawa
"In baki iya ba karki hada mana gobara ki babbake mun gida, ki bari fita zanyi sai in taho miki da wani abin"
Ta karbi lighter din tunda taga yanda ya kunna, ta murda gas din ta kunna, tana mika masa, kuma da yake rowa ba halinta bace sai tace masa
"Indomie zan dafa inyi da kai?"
Da saurinshi ya girgiza mata kai
"Jagwalgwala kayanki, aci lafiya"
Yayi maganar yana takawa ya fice daga kitchen din, kafin tace wani abu ya riga ya fita, ta jinjina kai, ai daya tsaya ta gama dafawa yasha mamaki, ita zaice zatayi jagwalgwalo, ita da take dafa abubuwa, danma ba son girki takeyi ba, ko sakasu akayi zatayi gyaran kayan miya, da kananun abubuwa ta bar Khairi da sauran aikin, tana son abinci, amman tafi fahimtar ta aikashi cikinta fiye da ta sarrafashi, duk da haka babu yanda za'ayi a kira girkinta da jagwalgwalo
"Kayiwa bakin cikinka"
Tayi maganar a fili, tasan yanda wajenshi yake bakikirin haka cikinshi ma yake. Tukunya ta samu karama ta tari ruwa ta daurayeta, ta zuba wanda take tunanin zai isheta ta dora. Shi Haris daya fita, joint din bashi da nisa sosai da unguwar tasu, saiya ga wajen a rufe, ya kira Lalaye yake fada masa
"Ai basa budewa da safe sai karfe takwas na dare"
Takaici ya kamashi, saiya juyo kawai yana fatan Maryama na kitchen ko ta shige dakinta, bayason wata magana, sai dai shayin yake bukata sosai, daya shiga bata falon, ya juyo maganarta a kitchen din dai, da alama waya takeyi cikin nishadi hadi da shagwaba kuma
"Kai Hajja, ni da Abba yace yanzun nama kusa in fi su Adda Asiya hankali..."
Wani numfashi mai dan sauti ya subucewa Haris, wai hankali, kamar ya leka kitchen din, sai kuma ya wuce dakinshi, ya sake fitowa, ko ita zaice ta dafa masa shayin? Bayason saka wani abu mai sanyi a cikin nashi daya hakura ya dauki lemo, haka kuma bayason yin wata doguwar magana da ita, da yake hankalinta na