Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
turarukan suna saka mata mura, amman wannan lafiya kalau takeyin amfani dashi, sai tayi tunanin ta fesa shi da yawa ne, dan kamar har kirjinta da ya kulle ya shiga, ta danyi tari tana dan murza kirjin nata, wayarta tayi haske, saita kalli wayar, ta daga ido ta kalli traffic din, wasu motocin na gabanta sun fara wucewa, amman ganin sakone ta Snapchat saita daga wayar da sauri, tana fatan Haris ne.
Ta daga wayar, ta kalli wayar, kirjinta ya sake daurewa ganinta na daukewa, a shekarun da tayi a asibiti, ba zata kirga adadin mutuwar da ta gani ba, a farko-farko abin yake damunta, amman sai tazo ta saba, zuciyarta ta kekashe, sai dai in akayi mutuwar, taga an dauke gawar, an nade zannuwan gadon, ta kuma san zuwa za'ayi a wankesu, inta zauna shiru saita dinga tunani, to me ake so a wanke?
Cutar?
Daudar?
Ko kuma mutuwar?
Idan mutuwar ce taya za'a wanke mutuwa ta fita? Wanda aka sake kawowa aka dora akan wannan zanin gadon ko ya sukeji? Ko suna ganewa? Ko sunaji a jikinsu wani ya mutu akai? Ko yana warin gawa idan gawa nada wani wari a ranar da ruhi yabar gangar jiki kenan, tambayoyin da bata da amsarsu, taga mutuwa a yanayi daban-daban, amman batasan mutuwa ba sai yau data risketa, sai da ta sameta a cikin motarta, ta bude bakinta da niyyar neman yafiyar Allaah sai dai
"Ast..."
Shine sautin daya fito, lokaci yayi abinda ya saba, ya cika akanta
Rai baya jiran buri!
Mutane nawa ne irin Aise? Mutane nawa ne suka fita daga gida da niyyar marar kyau lokaci ya kare musu kafin su aiwatar? Inama inama? Inama ace mutuwa sallama takeyi, saboda ka shirya, ka samu wannan dan taqin, ko da bai isheka furta shahada ba, kalmarka ta karshe a harshe da zuciya ya zama neman yafiyar Ubangiji ce...
Haka mutanen da suke cikin motocin da suke bayan Aise suka dinga danna mata hon, harda masu leko kai suna hadawa da zagi, wasu ma nayi cikin zukatansu, yayin da wasu suka dinga rabewa suna wucewa da tunanin karfen nasara ne da akace bashi da tabbas yayi mata halin, motar ce ta samu matsala, haka aka dinga rabewa ana wuce Aise, har saida wasu masu POS a tsallaken titin da masu saide-saide suka kula da matar da take ciki kamar bata motsi, sanann kanta ya langabo tunda tana daure ne da seatbelt, aka taso aka tsallako ana dubawa, mai POS din nan shiya fara zira hannunshi ya dauko wayar Aise din da akaci sa'a babu mukulli a jiki, dan yasan a yanayi irin wannan wasu sun zagaye motar ne saboda su samu abinda zasu sace.
Lambar karshe da aka kira, ita ya kira, sau biyu ba'a daga ba, sai ana ukun daya saka ranshi in ba'a daga ba zai sake duba wata lambar ne tukunna aka daga kiran kusan a tare sukayi magana, shi sallama yayi, Haris kuma ta dayan bangaren yace
"Aisee...."
Yana jan sunan da yanayi na kosawa a cikin muryarshi, jin ba ita bace yasa shi tsayawa cak, ya sauke wayar daga kunnenshi ya duba, lambarta ce, ya sake mayarwa yana fadin
"Hello..."
Aka sake maimaita sallamar, bai amsa ba
"Waye?"
Ya furta, baisan dalili ba, muryarshi yaji tana rawa
"Sunana Isa, munga wannan ce lamba ta karshe da mai wayar ta kira...Allaah Yayi mata rasuwa...t...."
Duk wani abu da ya cigaba da fada baya karasawa kunnuwan Haris da sukayi kamar an tashi bomb a cikinsu da kalmomin
"Allaah Yayi mata rasuwa"
Sune suke juya kansu cikin kwakwalwarshi, suna samun waje a zuciyarshi da take wani irin bugawa da sauri-sauri, wayar da take hannunshi ta subuce ta fadi kasa, yasan ya koma cikin falon nan da kafafuwanshi da sukayi masa kama da taliya saboda rawar da sukeyi, baiga tarin matan da suke falon nan ba, baiga kowa ba sai Maryama da itama take kallonshi ganin yanda jikinshi yake rawa
"Maryamm..."
Ya furta kalaman na komawa cikin kunnuwanshi da wani irin sauti, saboda yanda yakejin makoshinshi ya bushe kamar wanda yasha bokitin kasa, ya kuma ga tasowar Maryaman, amman zuciyarshi da take bugawa tasa wani irin duhu gilma masa, sama-sama yakejin kamar hannuwan Maryama na girgiza shi, amman dan hasken da yake gani ma saiya dauke masa. Abinda ya sake gani shine bude idonshi da yayi a asibiti, rudewa sukayi lokacin da suka ga ya fadi, banda Adda Zahra data karasa bakin kofar ta dauko wayarshi da take ta kara, ita ta daga kiran duk da babu suna a jiki.
"Wata ce ta rasu, cikin 'yan uwanshi waye a Kaduna?"
Kai Maryama ta girgiza musu, dukansu sai in sunzo Kadunan ne, kuma baice mata wani yazo ba, zuciyarta sai bugawa takeyi kamar zata fito daga kirjinta, ta nemi hawayenta ta rasa, abinda yake nutsar da ita shine jin bugun zuciyar Haris a tafin hannunta da yake kan kirjinshi, tasan yana da rai, koma waye ya rasu a wannan lokacin, mai saukine a wajenta, tunda ba Haris bane ba. Su hudu suka hadu amman da yake duk taron matane sai suka kasa daga shi, saida suka nemo taimakon maigadinsu da ya kira wasu mutum biyu sannan aka saka Haris din a mota, Khairi ta goya Aalim, Adda Maimunatu itace ta tuka motar bayan Adda Zahra ta ba Maryama wayar tana fada mata tayi kokari ta kira wani a gidansu Haris din ta sanar musu da abinda yake faruwa. Da wayar Haris din tayi amfani ta kira Hajiya Rumana, sai lokacin ne hawaye ya balle mata
"Rasuwa kuma? Waye ya rasu to?"
Ta tambaya a kidime, tana kashe wayar kafin ma Maryaman ta samu damar amsawa, sanda suka karya kwanar da zata hadasu da asibitin Frontiers saiga kiran Anisa
"Babu suna a jikin lambar?"
Ta tambaya, Maryama tace mata
"Babu..."
Ca tayi ta tura mata, ta kuwa yi copy ta aikata mata, bataji ta samu natsuwa ba saida aka karbi Haris, aka duba shi, likitan yace musu babu wata damuwa, sunyi masa allura da zai dai-daita bugun zuciyarshi, shock ne kawai ya shiga. A asibitin Hajiya Rumana tazo ta samesu, daga gani a kidime take, idanuwanta sunyi kozai-kozai, karo na farko da Maryama zatace taganta babu ko alamar hoda fuskarta, dan a shekarunta, yar gayuce ta kwatance, da alama kuka tasha, cikin wata irin murya mai sanyin gaske ta cewa Maryama
"Ya Haris din?"
Maryama ta amsa da
"Bacci yakeyi, sunce babu wata matsala...waye ya rasu Mami?"
Hawaye suka cika idanuwan Hajiya Rumanan
"Aise ce..."
Ta amsa tana kai hannu ta share hawayen, mutuwar ba karamin gigitata tayi ba, dan ta goge duk wani shekaru na rashin jituwar da take tsakaninta da dan uwanta, da yake bayan sunga kamar ba'a dauki maganar da muhimmanci ba sai suka duba lambar da akasa Mummy a jiki suka kira mahaifiyar Aise suka sanar mata, dan haka kafin ta fito daga gidanma Alhaji Modu ya kirata
"Na kira Alhaji Mustafa ban sameshi ba, kuje ku dauko mun ita Rumana...zamu taho yanzun"
Yanayin muryarshi ya tuno mata yarintarsu, shakuwarsu, ya dawo mata da komai, a muryar dan uwanta takejin yanda zuciyarshi take a rarrabe da rashin da yayi, tayi kokarin saka kanta a halin da yake ciki amman ta kasa, hankalinta yaki daukar rashi irin wannan, ace Munira ce ko Anisa, ko Haris, watakila ba zata iya dangana ba, zuciyarta ce zata buga a hada a binnesu a tare
"Yana gida, yanzun zan fada masa, zamu tafi sai mu wuce da ita asibiti..."
A hankali yace
"Ta rasu Rumana, Aise ta rasu, naji a zuciyata, 'yata ta rasu, ku dauko mun gawarta kawai"
Sai kuka ya kwace mata, kukan da ya kara dawo mata yanzun, da Alhaji Mustafa yace ba za'a tafi da ita ba, shine tace masa zata taho nan wajen Haris, mutuwar saida ta daki Maryama yanda batayi zato ba
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Take fada tana maimaita, rai bakon duniya, tana nan gefe ta hana kanta da zuciyarta zaman lafiya akan Aise, ashe ma taqin daya rage mata a duniyar ba mai yawa bane, wani irin tsoro ya tsirgawa Maryama yana saka hawaye suka zubo mata, shikenan fa ko? Yanda suke tsayen nan suna jimanta rasuwar Aise, suma babu tabbas anjima ba za'a jimanta ta wani a cikinsu ba
"Astagfirullah"
Ta furta tana cigaba da maimaitawa
"Bari in tafi gida Maryama, tunda jikin nashi da sauki..."
Tafiyar tayi, Adda Maimunatu ma bar musu mukullin motar tayi ta samu napep ta koma gidan Maryaman dan ta dauki motarta, aka barta ita da Khairi
"Kinga rayuwa ko Adda? Kai La hawla wala quwwata illa billah..."
Ita kanta Khairi jikinta yayi sanyi sosai, haka suka dinga jimanta abin, har Haris ya tashi, Khairi ta fice tana basu waje, ya dade yana kallon bangon dakin, yanajin tsikar jikinshi na tashi, ba don sanyin dakin ba, wani abune yake shigarshi da ba zaice menene ba
"Allaah Yayiwa mata rasuwa"
Shine abinda yakeji cikin kunnuwanshi, ya kalli Maryama da yaji ya rike hannunshi
"Allaah Yayi mata rasuwa akace Maryamm, mutuwa kenan ko? Ta mutu ake nufi, Aise ta mutu..."
Ya karasa maganar yana tambaya yana kuma amsawa kanshi wannan tambayar, ta sake dumtse hannunshi kafin ta daga masa kai a hankali
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, kace Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Ya kuwa fada din, kalmomin da ma'anarsu na danneshi, tun yana fada a hankali harya fara fitowa fili
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Aise ta rasu
Aise ta mutu
Da haihuwa batazo ma Maryama ba, da a tare dashi zata rasu, a dakin hotel din da ita ta kama musu, da shine zai kira waya bashi za'a kira ba, yace musu ta rasu! Yanzun kam wani abune yake mikewa a bayan kanshi
"Me kuke a hotel tare?"
Haka fa za'a tambaya ko? Me sukeyi tare? Ta ina zai fara yi musu bayani
"Kowanne sakan da kayi a doron kasa sai an tambayeka akanshi, sai kayi bayanin abinda ka aikata da lafiyar da Allaah Ya ara maka da damar daka samu"
Maganganun Malam suka dawo masa
"Ai yi musu bayani mai saukine, babban tashin hankalinka bayanin da zakayiwa Allaah"
Zuciyarshi ta fada masa
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ya furta a firgice yana tashi zaune har yana fisge karin ruwan da aka saka masa, ya riko Maryama a jikinshi, wani yaro ya rasu kwanaki anan unguwar, ya dawo masallaci aka fada masa, sai suka wuce akayiwa yaron sallah, karamine ance baifi shekara uku ba, suka tafi makabarta aka kaishi, sai yanzun yanayin kabarin yake dawo masa, yanda aka hakashi na kasan karami inda aka zira yaron, saina saman, sannan akabi da kasa harda wasu tukwane aka rufe ko ina, can za'a kai Aise itama ko? Cikin kasar nan, a barota ita kadai, to wai daman mutuwar haka take? Da wayonshi dai bai taba rasa wani makusanci ba, sai yanzun, lafiyarta kalau fa, sai kawai ace ta rasu? To me yafi wannan tashin hankali?
"Idan nima na mutu fa Maryamm?"
Ya tambaya cikin firgici yana kara riketa kamar maison komawa cikinta dan ya boyewa mutuwar
"Dan Allaah... Inalillahi wa ina ilaihi raji'un, to ya zanyi? Idan na mutu ya zanyi? Idan Allaah Ya tambayeni zunubaina ya zanyi Maryamm? Idan na tuba komawa nakeyi, komawa nakeyi, Allaah Zai yafe mun kuwa? Ina cikin mutanen da suka shiga uku ko? Mutanen da zasuyi ihu suce Allaah Ya dawo dasu duniya, mutanen da Malam ya bamu labari a makaranta..."
Jin yanda muryarshi take rawa yasa ta kara rikeshi itama, tana rasa abinda zatace masa
"Kace Astagfirullah, Allaah Mai Rahma ne...dan Allaah ka nutsu"
Ya daga mata kai, amman a wannan ranar shi da nutsuwa sunyi hannun riga, saboda a ranar ne addu'ar Maryama ta amsu, Allaah Ya nunama Haris girman IkonShi, Aise ta dawo rayuwarshi ne don ta zame masa silar shiriya
"Astagfirullah, ba zan kara ba, na daina, Astagfirullah..."
Ya kara fada, a karo na farko idanuwanshi suka cika taf da hawaye, hawayen tsoron Allaah, hawayen tsoron mutuwa, hawayen tsoron kwanciyar kabari, hawayen tarin zunubanshi da sai yanzun yake hangosu, maganganinshi kuma a gefe guda suna tsorata Maryama, sai ta lumshe idanuwanta, hawaye na zubo mata, a cikin zuciyarta ta furta
"Allaah Kayi mana Rahma da kyakkyawan karshe, Allaah Kasa in mun mutu mu huta..."
Wani abu mai sanyi ya saukar mata a zuciya, kamar taji lokacin da kaddara tace mata
A duniya dai, akan auren Haris, ki huta haka Maryama...!
Epilogue
A shekaru talatin da biyu, shekaru goma sha biyar harda doriya da aure, bayan ni'imar yara har hudu, zata kara godewa Allaah da sauran ni'imomin daya cika rayuwarta dasu. In zata daga Labulen da yake lullube da aurenta daga farkonshi zuwa yau, mata da yawa zasu samu abin fada, wasu zasu bude baki ne suyi mamaki, harma ba za'a rasa wanda zasu tambayeta
"Kuma kika zauna da dan wiwi?"
To mata nawa ne suke zaune da 'yan shaye-shaye? Babu alamar zasu bari, sannan a gefen wannan shaye-shayen ba dadin auren sukeji ba, babu abinci balle suttura, babu kulawar miji. Ita kuwa zatace taga ribar biyayyar da tayiwa mahaifinta, taga wannan ribar a irin kulawar da Haris yake bata, watakila da auren soyayya tayi, da zabin zuciyarta ta samu, ba lallai wannan zabin nata yazo da irin wannan kulawar ba. Sannan akwai macen da zatace babu wani kalubale da take fuskanta a gidan aurenta?
Wasu kuma zasuce ina su Anisa da Munira? Ya alakarta da Hajiya Rumana? Ta saduda? Yau da gobe ta tafiyar da ita? In akayi mata wannan tambayar, dariya zatayi, tunda ai tsanar da sukayi mata bata da wani dalili, to me yasa za'ayi tunanin zasu samu dalilin da zasu daina? Har yau din nan Hajiya Rumana bata sonta, har yau bata maraba da ita in taje gaisheta, in taga hakoranta a waje to jikokinta take yiwa dariya, tun yaranta basu da wayon da zasu fahimci cewa babu jituwa a tsakaninsu har Awwab da Rauda sun gane
"Me yasa Mami bata sonki? Kin mata laifi ne?"
Rauda ta taba tambayarta, ta rasa abinda zatace mata
"Waye yace miki bata sona?"
Sai ta daga mata kafadu, da yake ba surutu take dashi ba
"Akwai kunya a al'adarmu, tsakanin surukai, shisa zaki ga kaman bata sona"
Batasan ko Rauda ta gane bayanin da tayi mata ba ballantana ta rike shi a ranta, kamar yanda bata sake tambayarta ba, amman in dai zasu shirya zuwa gidan, kuma harda Maryama sai tace mata
"Dama kiyi zamanki"
Bata dai kulata ne, tsakanin Rauda da Anisa kuwa basa wani shiri ko tace Rauda bata shiri da Anisa, duk yanda Anisan take zuwa mata da tarkace kala-kala in zata zo, ko in su sunje take hadota dashi, da kuka take zuwa gidanta, sai Maryama tayi mata jan ido tukunna, kuma hakan ba zai rasa nasaba da yanda Anisa take gwaba mata magana har a gaban yaran ba
"Duk tsanarmu da zaki cusawa yaran nan fa ba zai canza matsayinmu a wajensu ba wallahi"
Haka Anisan ta taba ce mata, sai tayi dariya kawai. Inda a littafi ne, sai ace su Anisa sun girbi abinda suka shuka yanzun da shekaru suka ja, yanda suka so su hadu ayi mata kishiya, anyiwa daya daga cikinsu, yanda suka dora mata karan tsana to suma dangin miji suna gallazawa wani a cikinsu, za'a dai samu wani abune a lika musu da zaisa su saduda su kuma yi nadamar abinda suka aikata. Amman babu daya a ciki, saboda ba haka rayuwar take tafiya ba, wata shari'ar sai a lahira. In dai itace ma, a yanda ta samu Rahmar Ubangiji Ya shirya mata mijinta, idan akwai wani hakki tsakaninta dasu, to har ranta takejin ta yafe musu.
Duk wanda yayi mata wani laifi ma ta yafe masa, bata fatan tsayawa da kowa a gaban Ubangiji da sunan shari'a, taji da kanta ma da tsayuwar nata zunuban. Cikin 'yan uwanta mata kuwa, musamman Adda Zahra, in dai zasu hadu gabaki daya a gida sai tayi mata zancen makaranta yanzun
"Bafa ki makara ba Maryama, ko yanzun zaki iya komawa makaranta, shi ilimi bawai sai zakayi aiki ba, dadine dashi, gara ace ki janyo drawer kiga takardunki, ki dauko ki kakkabe kura ki sake mayarwa, inajin takaicin yanda a cikinmu ke kadaice ko kwalin sakandiri baki dashi"
Sai dai tayi murmushi, tasan lokaci bai kure mata ba, shi ilimi ba'a girma da nemanshi, amman ta riga ta hakura da karatun boko, tun da Alhaji Sa'id da kanshi yace mata tayi hakuri, ta cire abin a ranta gabaki daya, amman da inta kafawa Haris naci saiya san yanda zaiyi da ita. A yanzun haka tana zuwa Islamiyya, shekaru hudu kenan data fara zuwa, tana yaye Aalim ta samu Haris ya barta, daga karfe goma na safe ne zuwa karfe daya na rana. Gashi nan tana shirin hada haddar Al-Qur'ani, dan sun wuce rabi, da yake hadda sukeyi ta gaske, ga sauran litattafai wanda da yawa ma ta gama wasu, wasu ta haddace su tun lokacin da Haris ya daukar mata Malamar da take zuwa tana karantar da ita a gida.
"Ni idan ma ba zatayi karatun ba, to ta samu wata sana'ar ta fara"
Inji Adda Maimunatu kenan, murmushin dai Maryama takanyi musu. Har yanzun Haris na daukar hoto, har kasar wannan bangaren na aikin shi yake daukarshi, kuma yanda komai yake tafiya da zamani, haka shima yake tafiyar da ita ta hanyar koya mata, saboda in zai samu aiki, to itama zai bata aikin tayashi editing koma wani abin da ta iya, sannan zai biyata, bayan biyan zai dauki kudi haka kawai ya bata. A shekarun nan da kudinta ta kai Alhaji Sa'id Umrah, ta kuma kai Hajja. Ko da tana so tayi wani business batasan ta inda zata fara ba, banda yan uwanta, kawarta Khairi ce, sai wasu tsirarun da suka hadu a Islamiyya, sai kuma makota anan unguwarsu da suke mutunci, to ta ina zata fara? Me ma zata siyar? Me zatayi da kudin bayan wanda suke shakare a cikin asusun bankunanta?
In dai ta wannen bangaren ne, ko su da suke aiki suke kuma kasuwanci, babu abinda zasu nuna mata, idan ma aka tsaya filla-filla to ta fisu kudi, bata san yanda zatayi musu bayanin cewa kamar yanda suke tunanin ta rasa abubuwa da yawa a aurenta da Haris, haka kuma ta samu abubuwan da mata da yawa basu samu ba, ciki kuwa harda su, bama zasu fahimceta ba, Khairi ce kawai take fahimtarta, saboda ita tata jarabawar shine miji mai son abin hannunshi, mijin Khairi komai nashi a kididdige yake, yana da halin da zai wadatasu, sufi karfin bukatun yau da gobe, amman saboda idonshi nakan kasuwancin da takeyi na kayan yara, da kuma kayan kitchen tunda ya nuna bashi da ra'ayin tayi aiki, sai