Advertisements
Chapter 28 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   28 / 51

81K to 84K   out of 151K words

din yana kuma gutsira da cokalin da yake ciki, saima ya shige dashi daki, to tasan dadi yayi masa shisa yake ta kara diba

"Wai Maryamm ni kika daina yiwa magana?"

Tambayar da yayi mata kenan da safe

"Ba kaqi goge hotunan ba? Kafi so zunubinka na karuwa duk kallon da kayi, to ni me kake so ince maka?"

Shine amsar da ta bashi kamar zata tashi da mauje shi saboda takaicin daya cika mata ciki. Ficewa yayi batare da ya kara cewa komai ba, bai dawo gidan ba sai bayan Magriba, yana ta shige da fice yana daukar wasu manyan abubuwa da sukayi mata kama da frames, amman an nade kowannensu da takarda ta yanda ba zakasan menene a ciki ba. Ita dai sallar isha'i ta gabatar, taxi abincinta tayi zamanta a falo, duk da kallon ba sosai take fahimtarshi ba, kunnuwanta da hankalinta kacokan yana dakon fitowar Haris ne, tasan zaizo ya hada shayin da ta daina hada masa. Tana jin bude kofarshi, daya fito ba kitchen yayi ba, nan falon yazo ya sameta kan kujera ya kama hannunta, tayi kokarin fisgewa, amman rikon da yayi mata bana wasa bane shisa ta hakura ta mike kamar yanda yake so, janta yayi har dakinshi.

Da farko dariya ta bashi, harya kwanta ma ranar dariya ya dingayi, na karfin halin Maryama da kuma rikicinta. A gefe daya akwai wani abu mai nauyin gaske da ya danne masa zuciya da wannan hotunan nasu da Aise, kuma sai da ya bisu dayan bayan daya ya kalla, abinda tun ranar daya baro Italy bai kara barin kanshi yayi ba, ya kuwa kasa bacci, saboda yana tunanin zata kwanta a jikin wani bashi ba, wani daban zai riketa, hannuwanshi zaije har inda nashi a mafarkai kawai suka taba kaiwa. Amman wannan shirun na Maryama da ta tsiri yi masa sai ya dame shi, ya hana masa sukunin kirki, da ya fito take tsuke girarta da take a wargatse, kamar da gangan take saka hannu tana hargitsata, dan inya kalla ya dinga lissafin yanda zaisa hannunshi ya gyara mata gashin.

Wani lokacin kuma baki take murgudawa, inda tasan yanda yake kokari wajen rike kanshi intayi hakan data taimaka musu ta daina. Ko ta harareshi kamar idanuwanta zasu fado

"Ki hadamun shayi"

Yace mata, ta murguda bakinta tana gyara kwanciya, kuma ya jira yakai na minti talatin, daya fito ma bata falon, sai shi ya hada da kanshi. To tun shekaranjiya ma ruwan zafine a flask din, zallan ruwan zafin babu komai, babu wannan spices din masu kamshi da ta saba masa da dandanonsu. Yau kam ya gaji da fushin, ya gaji da rikicinta. Har dakinshi ya jata, ya dauko laptop din da take a kunne, ya zaunar da ita gefen gadonshi yanajin yanda take maida numfashi, kan cinyarta ya dora laptop din, data duba sai taga yana kan wannan folder din, folder din hotunansu shi da Aise

"Ki goge da kanki, ki goge ki daina mun rigima Maryamm"

Tayi masa wani kallo

"Bayan ka gama yin copying a wani wajen"

Shima kallon nata yakeyi, tunanin yayi copying ko kusa baizo masa ba, yaso ya goge da kanshi ne ya kasa, shisa ma yaje ya janyota, ganin hotunan wahalar masa da zuciya sukeyi ba kadan ba. Inta goge din zata taimaka masa

"Me yasa zanyi haka?"

Ta janye idanuwanta daga cikin nashi

"Su kadaine, babu wasu a ko ina"

A yanayin muryarshi ta karanci gaskiyarshi, yatsanta har rawa yakeyi lokacin da ta goge, ta koma recycling bin kamar yanda ya nuna mata, tabi ta goge acan

"Shikenan?"

Ya tambaya, ta tsinci kanta da daga masa kai, dan wani abu daya danne mata kirji ya daga, tana gogewa taji kamar iska na shiga kofofin jikinta da batasan lokacin da suka toshe ba

"Zan samu shayin yau?"

A kunyace tayi murmushi

"Bari in hado maka"

Ya sauke numfashi mai sauti

"Da sauran cake din nan in akwai dan Allaah, zan kira Adda Khairi saimu kara siya ko ina ta siye shi, ayi mana da yawa ko?"

Kai ta daga masa tana rufe laptop din ta ajiye hadi da mikewa, kitchen ta nufa, ta dan dauki lokaci saboda saida ta dafa shayin sannan, data kawo masa ya karba, ya sake juyawa, kamshin ya dake shi

"Dan Allaah ko munyi fada ki dinga hadamun shayi, ko ki dafamun irin wannan sai in hada da kaina"

Yanda yayi maganar saiya bata dariya

"Kinji"

Ta daga masa kai, ta kama hannun kofar yace mata

"Ina zakije?"

Da mamaki ta kalle shi

"Kallo nakeyi"

Da sigar umarni yace

"No...ki zauna, anan, ki zauna in sha shayina sai muyi editing wasu hotuna"

Ganin tana kallonshi yasa shi dan kankance mata idanuwanshi yana dorawa da

"Please..."

Batayi musu ba, tasan kan gadonshi zai zauna, ita saita zauna a kasa, kan kafet din dakin, yanda ta saba in dai ta shiga, sai dai shima ya biyota kasan yanda yayi yanzun. Ya gaji dayi mata tayin ta zauna akan gadon. Yana shan shayin yana nuna mata hotunan a dayar laptop dinshi, na bikine, daga ganin bikin kuma kasan na masu hannu da shuni ne, sai kallo takeyi, su dai masu kudi komai nasu ya fita daban, komai nasu a tsare, dinner ce, kaf babu wani da yayi kamar bai kamata ace yana wajen ba, haka shigar kowa ta burge

"Su masu kudi sai kaga dinner dinsu tayi kyau, tunda basu da dangi 'yan kauye da zasu zo su bata wajen"

Dariya Haris yayi

"Suka ce miki? Akwai wanda basu da kauye ne"

Ta dan kalle shi

"Kuma kuna da kauye ne?"

Idanma suna dashi bai sanshi ba, bai taba zuwa ba, rayuwarshi duka tsakanin Kaduna, Abuja sai Maiduguri ne, sai kuma Kano yanzun, shisa ya zabi ya amsa da wata tambayar

"Ke baku dasu?"

Aikuwa da sauri tace

"Muna dasu fa, da yawa sosai, sai dai suna da kirki, in zasu zo gida zaka ga sun kawo mana abubuwan kauye da yawa, harda su goruba ma suna kawo mana"

Yayi shiru yana tunanin yanda ita gorubar take, yanajinta, amman bayajin ya taba gani, daya gama shanye shayin, saiya tashi ya fita da komai da kanshi ya bar Maryama a dakin, lokacin daya dawo ya zauna sai yace mata

"Kinata fushi dani, baki bari na tayaki murnar birthday ba, shekara nawa kika cika?"

Ta gyara zamanta

"Sha bakwai"

Ya kalleta kamar bai yarda ba

"Anya? Ba sha biyar ba?"

Da sauri tace

"Sha biyar kuma, haba dai, ni da na wuce rabin talatin yanzun, inafa kusa da ashirin ne"

Lissafin nata ya bashi dariya

"Da zan baki gift, amman na fasa, ladan dafamun tsuran ruwan zafi da kikayi jiya da shekaranjiya"

Ashe ya kula, tayine dan yayi mata magana, ganin shima din ya shareta yanda ta shareshi a kwana biyun, har cake din taso ta cinye, mai chocolate din, saita kasa.

"Yi hakuri, ai mun shirya yanzun, ina gift din? Menene?"

Dan kuwa tana son kyauta, tana son kyautar bazata matuka

"Aina fasa"

Wannan magiyar yake so yaji tayi, kamar yarinya yar shekaru hudu in tana so ayi mata abu, kyau takeyi masa, yaso ta riko hannunshi, da kanta, yanda takeyi in tana rokonshi abu, amman batayi ba, ya kasa cigaba da hakuri yace mata

"Gasu can, tashi ki dauko"

Wannan frames dinne daya shigo dasu yau, guda goma ne a yanda Maryama ta lissafa su bayan ya nuna mata, sai dai manya ne, duk ya jingina su da bangon dakin, taji da nauyi, maimakon ta dauka takai inda yake, sai kawai ta tsugunna a wajen, ta janyo daya ta fara yage takardar da aka nade shi da ita. Hotonta ne, da kanta da babu kitso, ta kwance ranar, taji kwiyar zuwa saloon su wanke mata acan suyi mata wani kitson yanda takeyi, sai kawai ta wanke shi a gida, da yake a cike yake sosai, ta kasa tajewa da kyau, daya bushe sai yayi mata tudu, abaya ce a jikinta baka, dankwalin abayar ne ta daura ya zame, saita barshi kawai ta nemi wata farar hula da itama ta dinga zame mata saboda mai santsi ce, ga gashin nata a cike.

Haris ya dawo daga aikine, ya zauna a falon, ita waya take dannawa tana amsa sakon Khairi, ko kadan bata ga lokacin daya daga camera din daya fito da ita yanata wasa da ita ba balle sanda yayi mata hoton, yayi kusa dai ta yanda kafadunta ne zuwa sama kawai, gashi da girma, har tana iya ganin kwallin da ta saka na ranar ya fito radau dashi, duk da ya saka shi a black and white, batajin ta taba yin wani hoto da yayi mata kyan wannan, itace dai a jiki, amman ta kasa daina kallo. Dakyar ta ajiyeshi a gefe a hankali, kamar mai tsoron wani abu ya same shi, saita dauko wani ta bude, a kwance take, akan kujera one sitter, ta saka hannunta ta rufe idanuwanta dashi cikin son ragewa kanta hasken dakin dan bacci takeyi, dayan hannun ma ta dorashi akan wannan din.

Shi kana ganin alamun kanta, da wani sashi na fuskarta, amman hannuwanta su suka cika hoton, kuma ta kula da muhimmancin daya bayar wajen editing din hannuwan nata, kamar maison fito mata da abinda bata taba gani ba, haka ta bisu daya bayan daya, tana budewa, tana kallo, tana son karantar labarin da taga kamar kowanne hoto yana son bata, amman ta kasa, Haris kuma ita yake kallo, yanayinta nayi masa dadi har zuciyarshi. Ranar farko daya dauketa hoto, tana bacci ne, washegarin ranar da taje gidan Mummy, anyi mata lalle a yatsunta duka goman, jan lalle, ya shigo harya wuce ya dawo ya dauka. Haka ya saka hoton a gaba bayan yayi editing yana son gane meye a jikin wannan siraran yatsun nata, wannan siraran hannayen da bai saba gani a jikin na sauran mata ba, ko faratan ne, farare dasu, dogaye, ko kuma yanda suke a yanke ko da yaushe ne sabanin sauran da ko ba suyi fixing ba to sun tara oho?

Bayajin ya taba aikin wasu hotuna da suka sakashi nishadi kwatankwacin na Maryama, yanajin kuma yanda yake so ya kara daukar wasu, masu yawa, ya adana wannan kananun abubuwan da camera dinshi ce kawai take nuna masa, 'yan details din nan, scars din da suke son bacewa tare da lokacin a jikin hannuwanta, wani a gefen wuyanta, kananun abubuwa da inya kalleta saiya tsinci kanshi da yawatawa da idanuwanshi yana nemansu. Yanda ta dauki frames biyu tana mikewa yasa shi fadin

"Ina zakije?"

Ta dan juyo

"Dakina zan kai...ka tayani mu kwashe duka...sunyi kyau, duka zan jera"

Sai taga ya girgiza kanshi

"Ai gift din naki iya kigani ne ki ajiyemun kayana, waye yace zaki iya dauke su daga dakin nan?"

Da mamaki take kallonshi, dan bata gane ta ajiye masa kayanshi ba, hotunan nata ne suka zama kayanshi? Kuma saiya kara sakata kallonshi daya taso ya karbe na hannunta, ya sama ma kowanne waje a cikin dakin, a kasa ya ajiye yana jingina su da bangwayen dakin, cikin wani irin tsari da yayi mata kyau

"Kingani, kowanne yana da wajenshi..."

Wani abu da bashi da suna ya saukar mata

"Haka ake bada gift? Hotunana ne fa"

Ya hade space din da yake tsakaninsu, ta bayanta ya zagaya hannuwanshi yana riketa, kanshi a kafadarta, tanajin yanda yayi mata rumfa kamar mai shirin mayar da ita cikinshi

"Ke din gabaki daya ta wacece?"

Ya tambaya a hankali, amman sautin ya karade ko ina na jikinta saboda kamar cikin kunnenta yayi maganar

"An bani ke ko kin manta? Ke din duka tawa ce, sai hotunanki ne zasu kasa zama mallakina Maryamm?"

Tsikar jikinta ta tashi, tanajin shige da ficen numfashinshi, haka yake so, haka jikinshi gabaki daya yake muradi, ya riketa, yaji cewa tashi ce, rikon ya sake tabbatar masa da cewa an bashi ita

His to own

Wannan kalmomin uku da yake neman fassararsu ta bace masa bat

"Anan zaki kwana, anan zamu kwana"

Kuma yanda jikinta ya mutu gabaki daya saita kasa wani yunkuri, ji takeyi kamar ma daukarta yayi gabaki daya ya ajiyeta akan gadonshi, ya kuma bita kan gadon yana kwanciya, ko tace shi akan gadon tunda ita dai hannunta da wani sashi na hakarkarinta ne taji ya hadu da katifar, amman gabaki dayanta a jikin Haris take, yayi mata wani irin riko kamar ya kama barauniya, kamar yana tunanin inya sassauta zata subuce masa

"Ka matseni, ya zanyi bacci a haka"

Tayi karfin halin furtawa, yama zatayi bacci gabaki dayanta a jikin Haris? A daki daya dashi? Akan gado daya dashi?

"Zaki saba"

Ya furta a hankali saboda kamshin humrar data shafa a wuyanta da ya kara cika masa hanci yana saukar masa da wata irin natsuwa, ya rasa yanda za'ayi ace riketa kawai yana neman saka shi bacci a lokaci daya kuma yana masa barazana da wannan baccin? Ya za'ayi yarinya kamar Maryama ace itace take sakashi jin emotions fiye da kala daya haka? Me yasa ma tuntuni ya saka mata ido? Me yake jira? Me yasa tuntuni bai daukota ya kawota dakinshi ba? Mutsu-mutsu takeyi, tana son zamewa, ya sake riketa gam

"Stop...stop moving"

A hankali yayi maganar, muryarshi na karasawa kunnuwanta kamar yayi mata magana daga nesa, amman akwai wani yanayi a cikinta mai kama da kashedi, mai kama da roko da yasa ta daina kiciniyar da takeyi

"Allaah ka matseni"

Ta sake fadi, gabaki daya a takure take, banda bugun zuciyarta babu wani abu da take jinshi a sake a irin rikon da Haris yayi mata

"Zaki saba"

Ya sake maimaitawa

"Zaki saba Maryamm"

Kuma kamar yana duba,
Kwana nawa ya dauketa? Bata lissafa ba, amman anya an dade da yawa? An dade kafin ta saba din kamar yanda yace...!

29

Ya dauka ta hakura, tun jiyan, tunda har tayi bacci yanajin yanda take sauke ajiyar zuciya, kuka tayi har saida yaji tsoro

"To me yasa ba zamu tafi tare ba? Ni kadai zan zauna?"

Yanajin tayi masa tambayar nan yafi a kirga, duk da tunda ya tsaida ranar tafiya, kuma daga bangarenta babu wanda zaizo ya zauna da ita, aka yanke shawarar samo mata mai aiki. Babbace aka samo, dan zatayi shekara talatin da kusan bakwai, mijinta ne ya rasu ya barta da yara har biyar. Daga ganin matar da tace sunanta Sadiya, tun a jiyan da tazo kuma Maryama ta lankaya mata Mama Sadiya, dan tana tunanin zata iya haifarta. Haris ya dauka shikenan ta hakura, kukan ya kare, ya fada mata za'ayi mata passport, kuma za'a fara cuku-cukun yanda za'ayi ta bishi. Sai dai fa a wajen Maryama ba haka abin yake ba, wani irin sabone Haris yayi mata da kanshi a watanni biyun nan da suka kara ya tashi takwas da aurensu.

A jikinshi take kwana, sannan haka kawai ma in yana gidan duk wata dama da zai riketa baya bari ta subuce masa, shima har mamakin kanshi yakeyi, na irin yanda ya saba da ita haka, yanda yakejin kamar ya sakata a daya daga cikin jakunkunanshi su tafi tare. Yanzun da ya dauki jaka ta rike masa hannu tana kuka sai yakejin daman bai hakura da ita ba da safen nan, da ya bata dalili fiye dana tafiyarshi da zatayi kukan, amman saura mintina talatin jirginsu ya tashi, tun dazun ya kamata ya tafi, ta dagula masa lissafi

"Zamuyi waya kullum fa Maryamm, dan Allaah, ya zan tafi kina wannan kukan? Ni ya kike so inyi"

Taja hanci, ita ina ta sani? Ya fasa tafiyar kawai, ko ya jirata ko suyi zamansu, fuskarta ya rike cikin hannuwanshi, ya kara sumbatarta a karo na babu adadi daga wayewar gari zuwa lokacin, ya dauki dayar jakarshi, tunda ya saka sauran a motar Lalaye da yake jiranshi a waje, haka ya kauda kai ya bambare hannun Maryama ya fice batare da ta sake juyowa ba, inya tsaya tabbas zai rasa jirgin, zai kasa tafiya ne ya tsaya lallashinta. Dankwalin da babu a kanta ne ya hanata binshi waje, duk da tun da yake kai jakunkuna da zata fita ya hanata

"Bana ce miki Lalaye bane zai kaini airport? Yana waje cikin mota, ya za'ayi ki fita"

Ta fita ya ganta, yanda fuskarta din nan take cike da rauni, ga hawaye ne sababbi da wanda suka bushe, taya wani namiji zai ganar masa ita a haka? Maryama kuwa tunda ta koma dakinta, ko abinci bataci ba, da Mama Sadiya ma ta kwankwasa mata kofa haka tace kanta ne yake ciwo babu abinda zataci, bata fito ba sai bayan da tayi sallar isha'i. Agogo kawai take dubawa, tunda Haris yace mata kusan kwana daya ne daga nan Kano, dole saiya sauka zai kirata. A daren bacci barawo ne ya iya daukarta, dakinta ta kwanta, tanajin in taje dakinshi kewarshi ce zata sake danneta. Amman da yake komin yanda zai qure musu AC, dumin jikinshi yana hana mata wani tasiri a wajen Maryama, yau duk inda ta juya sai taji shi karara, bargonta kuma ba dumi daya suke fitarwa da Haris ba.

Washegari kuwa karar wayarta ce ta tasheta daga baccin data koma bayan sallar asuba

"Ganja"

Ta fadi tana kara rike wayar kamar zai fito ya rungumeta yanda ya saba

"Na sauka Maryamm, nagaji sosai, nagaji, yunwa nakeji"

Da sauri tace masa

"Baka siyi shayi ba?"

Ya amsa da

"Babu dadi, ba naki bane ba"

Ta saka masa tea spice din, taji hawaye ya cika mata idanuwa

"Ka dafa to, na saka maka tea spice din a cikin kayan, ka manta?"

Zata rantse kai Haris ya girgiza

"Na sani, ai hotel na kama, sai na gama hidimar makaranta duka zan samu waje"

Ta sauke numfashi

"To ka daure kasha a haka, ba shayi kadai ba kuma, kaci wani abu"

Kai ya daga, bai amsa ba, shisa tasan kai ya daga

"Kuma karka sha wiwi, dan Allaah, kaji? Nasan kana fita kasha kullum, kana sha har a bandaki, ban maka magana ba tunda naga kana boyemun, kuma Mu'allim yace wanda suke boyewa in suna aikata abinda bai kamata ba ana saka musu ran zasu bari, saboda suna jin kunya, dan Allaah karka sha"

Ta karasa muryarta na rawa

"Maryamm..."

Ya kira a hankali

"Dan Allaah"

Ta sakeyin maganar cikin sigar roko, babu yanda batayi dashi ba su koma asibiti kamar yanda akace yace mata ba zaije ba, kamar takai kararshi saita kasa, saboda batasan ta inda zata fara ba, kar ayi masa fada.

"Kaji...dan Allaah"

Ya sauke numfashi

"Banyi alkawari ba, amman zan rage, zanyi kokari in rage"

Da sanyi a muryarta tace

"Hakanma nagode, in kana ragewa a hankali zaka daina...kaje kasha shayin saika huta sosai"

Tanajin gajiya har a muryarshi

"To, amman zan kara kiranki, mu nan dare ne ma, zan kara jin muryarki sai in kwanta"

Itace ta daga masa kan wannan karin, muryarshi ta bata karfin gwiwar tashi tayi wanka, taji dadin jikinta, ta fita falon suka gaisa da Mama Sadiya, data bita kitchen

28 / 51