Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
nauyi da baisan daga inda ya taso ba yana danne shi. Ya ajiye wayar akan gado ya shiga bandaki ya dauro alwala dan baiyi sallar azahar ba, kuma yana so ya dan fita yasha iska. Saida ya fara yin sallar, ya tattare dakin nashi ya gyara ko ina, tukunna ya dauki mukullin motarshi da maigadi ya bashi tun dawowarsu, Maryama na inda ya barta a zaune
"Fita zanyi, akwai abinda zan taho miki dashi?"
Tayi masa kallon mamaki tukunna ta girgiza kanta a hankali tana dorawa da
"A dawo lafiya"
Shi da ya fito daga asibiti, batasan inda zai dauki kafa ya tafi ba da tsakar ranar, maimakon ya kwanta ko bacci ne yayi ya hutawa ranshi. Tana da sauran dankali tunda ta kula yanaso, shi zata fere ta soya masa da daddare, ai zai sha mamaki, babu surutun da zata zauna tanayi akan garjejen kato kamarshi, maganin da ba zai sha bane zata dinga zuba masa a shayi yana kwankwadewa sai ya kare. Kuma kamar yanda tace ne, da daddare ma haka ta sake hada masa shayin nan da magungunan shi a ciki
"Kinsan Allaah ba bakina bane ba, ko madarar ce ta lalace, kisha kiji yayi wani iri"
Ta kalle shi, da yake daki ta mika masa komai, yanzun ne ya fito mata daga shi sai gajeran wando da riga mai guntun hannu, dogayen kafafuwanshi na tuna mata da wani tseren gudu da ta taba samu mazan gidansu na kallo, da wani santalelen baki da akace shine wanda yayi na daya
"Dan kenya ne, kasan kaman aljanu haka suke da gudun tsiya, nifa dana gansu a wasa nake basu ci"
Bambancin shi wancen nashi kafafuwan sunfi na Haris kauri ne, amman haka ta gansu diqildiqil kamar wanda baya wanka da kyau, ta kula bayajin kunyar ta ganshi da gajeran wando
"Babu abinda ya samu madara, nima na sha shayin ai, tare na hada mana kuma lafiya lau najita, nace maka bakinka ne"
Kai ya girgiza
"To kisha kiji mana"
Ya mika mata kofin, haka kawai ana zaune lafiya ba zata kurbi wannan shayin ba, ta makale kafada, ya zuba mata wannan idanuwan nashi da batasan ya akayi tace
"Maganin da kaqi shane na zuba maka a ciki, kuma in baka sha a shayi ba zaka sha a ruwa, zan narka a duk inda zan iya in baka kasha, idan kaqiya zan kira su Baban Tudun Wada in fada musu maganin da aka baka a asibiti kace ba zaka sha ba"
Cikin wani yanayi yace
"Maganin ne kika zuba mun a tea Maryamm? Magani?"
Ta kuwa daga masa kai
"Zan zauna muna jan magana ne dan Allaah? Tunda ba iya danneka zanyi in matse bakinka in dura maka ba"
Ya rasa abinda zaiyi sai kawai ya sauke numfashi yace
"Ki hadamun wani shayin"
Ta kara gyara zamanta
"Maganin kuma asararshi za'ayi koya?"
Cikin kashedi yace
"Maryamm"
Ta tura labbanta gaba
"To in ballo maka maganin kasha sai in hada maka wani shayin"
Da sauri yace
"Bana sha"
Bai jirata ba ya nufi kitchen, da gudunta ta rufa masa baya, ta tare wajen sink din
"Allaah ka shanye shi, kaga zan kira Baba, da gaske nake"
Ya harareta
"Matsa daga nan, tunda ba zaki hada mun wani ba, zan hada da kaina, dankalina yana hucewa, kuma kaina ya mun nauyi, bana son surutu"
Da gaske yake, shayin yake so ya gama sha, ya dan busa wiwin shi ko nadi biyu ne saiya kwanta yaga ko zai samu bacci ya dauke shi. Tazo tana zuba masa magani a cikin shayi saboda karfin hali irin nata, ganin taki matsawa yasa ya kamo hannunta da nufin ya janyeta daga wajen, sai kawai ta bude kafafuwanta tana tirjewa, dayan hannunta ta rike abin sink din, dariya ta kusan kwacewa Haris, gani takeyi tana da karfin da ba zai iya janyeta ba, saiya samu waje ya ajiye kofin shayin, ya saki hannunta ya kamata cancakat yana ajiyeta a gefe. Tana kallon shi ya dauki kofin yana kokarin juye shayin, tayi wuf ta rike masa hannu da nata duka biyun, Abba yace mata sai tayi jarumta, ta kula da Haris, itace babba idan akazo batun lafiyarshi, to da alama Abba gaskiya ya fada, sai tayiwa Haris jan ido yaga da gaske take tukunna.
"Bafa zaka zubar dashi ba, sai dai ko ka shanye, ko kuma in ballo maka magungunan ka hadiya..."
Mamaki ya kara kama Haris, yayi karamin tsaki yana amfani da karfinshi ya juye shayin
"Allaah sai kasha magani zaka hada wani"
Cewar Maryama, tana ture duk wani abu da takeji saboda rikon da tayi masa da yanda jikinsu yake ta haduwa, tureta yayi yana nufar inda flask yake da kuma kayan shayin daya gani, dan bata ma mayar dasu wajensu ba, ta bishi, ya juyo yana mata kallon kashedi, bataji ba ta rufa masa baya
"In ballo maka maganin?"
Yana bude gwangwanin madara yace
"Ba zan sha ba"
Duk surutun da take ta masa tana fadin
"Kaji, dan Allaah, kaji, haba Ganja, minti biyu fa harka hadiye, minti daya ma, ina da iloka wallahi zan sammaka, Mummy ce ta kawomun kuma tayi dadi"
Banza yayi yana kyaleta, akwai yanda take furta Ganjan da yake bashi dariya, itama sunan dariya kawai yake bata
"Wai meye Ganja dan Allaah? Ni ban taba jin sunan ba"
Ta furta, haka kawai takejin dadi data kirashi da Ganja, tun da taji sunan bakinta yake mata kaikayi, kuma yafi tace masa Haris din aiko? Tunda batasan me zata kirashi ba, Ganjan kuma yayi mata dadi, ya rufe gwangwanin daya bude, ya ajiye ya zuba Milo
"Maganin fa, kaji...in dauko maka? Kaji? Kana jina fa"
Bakinta baiyi shiru ba harya gama hada shayin nashi, da taga yana motsawa saita ruga ta tare kofar kitchen din, saida murmushi ya kwace masa, da jikinshi yayi amfani ya bangajeta yana wucewa, sai yayi tsaye, cak, ba jikinshi kadai ba harda wani abu a cikin kanshi da baisan menene ba, saboda Maryama data zagaya hannuwanta, siraran hannuwanta a kugunshi tana rike shi gam
"Allaah ba zaka shiga daki ba sai kasha magani"
Muryarshi can kasan makoshi yace
"Sakeni"
Ta kara karfin matsar da tayi masa tana jan jikinta baya a kokarinta na jan Haris din
"Wai meye haka? Ki sakeni nace"
Dan shayin hannunshi ya cika kofin ne, kuma yanda yakeji hannuwanshi sun fara rawa, saida shayin ma ya dan zubar masa
"Sai kinsa na kone"
Da sauri tace
"Zaka sha maganin?"
Baisan lokacin daya furta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Rike shi takeyi tana janshi baya, baiyi tunanin tana da wannan karfin ba, ko jikinshi ne da yakeji kamar ba nashi ba shisa ta samu damar janshi haka
"Dawo nan kasha maganinka saika tafi"
Bayajin ya taba ganin mai karfin halinta
"Jeki kawo"
Ta zagaya da kanta batare da ta kalle shi ba tace
"Da gaske? In kawo dan Allaah?"
Ya harareta
"Zan watsa miki shayin nan, ki wuce ki kawomun maganin kafin in fasa"
Sakin nashi tayi, tana juyawa ya kurbi shayin da sauri-sauri kaman sau biyar a lokaci daya, kafin ya ruga da gudu zuwa hanyar dakinshi dan bayaso ya zubar a kasa, yaji ta, ta biyo shi, amman kafafuwanshi ai sunfi nata tsayi, yana shiga daki ya rufo kofar ya murza key. Sai dai bai samu ya kurbi shayin nan cikin dadin rai ba, saboda yanda Maryama tayi tsaye bakin kofar tana kwankwasawa tana fadin
"Kazo ka bude, Ganja, kaji..."
Ya dauka zata gaji da tsayuwa ta tafi, amman bata tafi ba
"Allaah anan zan zauna ko zamu kwana saika bude kofar"
Haka kawai zuciyarshi ta fada masa zata iya, daya bude kofar sai ya ganta zaune, da magungunan da robar ruwa, tama saka daya daga cikin filon kujerun falonta hankalinta a kwance kamar tana tsakiyar gado, sai tayi masa murmushi hakoranta a waje
"Ga maganin"
Ta fadi tana mikewa, karba yayi
"Anan zaka tsaya kasha, inaso ingani, wallahi inka koma ciki zama zanyi inta kwankwasawa"
Saiya bata ta ballo masa duka magungunan, ya daga kai ya watsa su a baki, yana jin tsikar kanshi na tashi, yabi da ruwa ya mika mata robar
"Haaa mugani"
Saida ya bude mata bakin, ta dinga daddashe da kafafuwanta tana so ta hango
"Bangani ba, kayi tsayi, ka sunkuyo"
Ya biye mata, ta leka ko ina cikin bakinshi
"Ko kaifa, saida safe. Allaah Ya kara lafiya"
Tana gama maganar ta juya abinta, sai wata kalma da bature yake yawan amfani da ita tazo wa Haris "pest"
Maryama is a pest...
26
Yau take cika shekaru goma sha bakwai, a yau dinne kuma tayi wata shida babu wasu 'yan kwanaki a gidan Haris. Wasu watanni da sukazo suka wuce mata da abubuwa mabanbanta, abubuwan da bata taba zato ba. Dan washegarin ranar da aka sallami Haris, Hajiya Rumana sukazo ita da Alhaji Mustafa, Haris bai fada mata zuwan nasu ba, shima yace mata baisan zasu zo ba, haka ta rikice ta rasa abinda zata basu, sai taliya tayi stir fry, Alhaji Mustafa yaci sosai, ya dinga saka mata albarka, amman Hajiya Rumana ko taba abincin batayi ba, ruwa ma da kayanta ta shigo gidan rike a hannu, bata sha wanda Maryaman ta ajiye musu ba, balle kuma ayi tunanin zataci wani abin.
Ta hakimce akan kujera tana ta faman hura hanci kamar wadda kunama ta ciza, Haris ne ya zauna kusa da kafarta akan kafet, shima da alama ranar haushin Maryama ne ya shafeshi tunda haka ta dinga amsa shi dai-dai. Suka zo suka wuce, kwana hudu tsakani kuma Haris yace mata Alhaji Mustafa zasu sake zuwa shi da Umma Fadime, su da yake tasan da zuwan nasu, tun ranar tayi wa Haris magana suka fita tare akayo cefane, shinkafa zatayi da miyar kaji sai ta hada salad, tayi tunanin tayi musu wani dan lemo na gida, sai kuma ta fasa ko ba zasu so shi ba. Tun da daddare ta rage aiki, ta dafa namanta, kayan miyar ma ta dafasu, duk saita saka a fridge.
"Nace miki ayi order din abinci, kinqi"
Cewar Haris daya shiga kitchen din ya dauki ruwa da daddaren
"Abincin gida yafi albarka, yanzun sai kaga kudin cefanen nan da mukayo ya shige a order din abincin, kuma ba lallai yayi dadi kamar wanda zakayi a gida ba, ni da zaka taimaka ma ka yanka mun albasa"
Yayi wata dariya mai sauti
"Ni zan yanka albasa? Ban iya ba..."
Kafin ma tace wani abu ya fice ya bar mata kitchen din, sai dai tayi mamaki sosai ganin ba iyasu Umma Fadime bane ba, harda duka yaranta guda shida, Mukhtar ne kawai banda shi, saboda baya kasar, kuma shima sai da ya kira Haris, baya ma kusa da wayar, da yazo yaga lambar kasar waje ya dinga mamakin waye tunda ba lambar Italy bace ko wata kasa da yake da wani, sai yaga text din Mukhtar
"Mukhtar ne Hamma, na kira inji ya jikinka ne daman, Baba ya fadamun baka da lafiya, Allaah Yasa kaffara ne"
Ya dinga juya sakon nan, da yazo reply ma saiya rasa abinda zaice, yaushe rabon daya sa Mukhtar din a ido balle ma har ace sunyi wata magana, gara ma su Adda Halima tunda Baba ya bashi lambobinsu, sukan kira shi a gaisa. Yanajin dadi, danma maganganun nasu basa tsayi, babu wata shakuwa a tsakani. Sai gashi sunzo su duka, harda yaransu, ita kanta Maryama taji dadi, Haris nata kallon yanda suke rungume juna kamar sun santa tuntuni, saboda baisan akwai shakuwa a tsakaninsu haka ba, lissafin girkinta ne ya sauya tunda sun kara yawa, danma dai tayi miyar ne da niyyar ta ajiye ragowar.
Da ta koma kitchen din sai Shatu ta bita, suka kara dora girki, haka suka cika falon nan Maryama najin kewar gidansu na danneta, sosai wani lokacin shirun gidan yake mata yawa, ta riga ta saba da kullum gidansu cikin mutane yake, duk da ba yawo sukeyi ba, banda makaranta fita sai ta zama dole, amman ko fitar za'ayi ma, ita da Khairi ne, wani lokacin ma su da yawa haka za'aje a dawo. Nan kuwa data gama 'yan aikace-aikacenta sai dai tayi kallo, babu inda take zuwa, a ranar sai taji gidan yayi dadi, kamar karsu tafi, kamar ace kwanaki suka zo suyi musu.
Tana kallon Alhaji Mustafa da Haris suka fita sallar azahar tare, da suka dawo kuma sai suka tsaya a waje
"Ga motar nan an taho mata da ita, takardun da komai suna ciki, ina binka cikon dubu dari biyu da saba'in"
Haris yayi murmushi yana kallon motar, kalar ja ce, tayi masa kyau, yasan da bakar kala ma aka daukar mata sai tafi haka kyau
"To Baba zan cika, tayi kyau sosai motar"
Alhaji Mustafa ya jinjina kai, shiru ya dan gifta a tsakaninsu kafin yace masa
"Likitanka ya bamu shawarar kana bukatar rehab, banji dadi ba Haris, saboda kullum mukayi magana ina kara jin yanda hankali yake zauna maka, sai nake kyautata maka zato matuka, nace Haris dina ya girma, babu kalar fargabar da banyi ba bayan na karba maka auren Maryama, da kace mun a Kano zaku zauna zuciyata cike take da tsoro, kullum ina jiran inji ko zaka bani kunya ne..."
Haris ya jingina bayanshi da motar da suke tsaye kusa da ita saboda yanda yaji jikinshi ya dauki rawa, zuciyarshi har bugawa takeyi, abu na karshe da yake so ya faru a tsakaninshi da Babanshi a yanzun shine alakar nan tasu da yake riritawa ta samu matsala
"Sai naji shiru, sai baka kunyatani ba, dan iya damuwar da take fuskar yarinyar nan randa mukaje asibiti nasan baka bani kunya ba Haris, kuma na yarda ka karbi auren nan da zuciyarka daya...me yasa zakayi mun haka? Idan baka duba yanda zanji ba mahaifiyarka fa? Baka tattalin lafiyarka? Ko bakasan tana da muhimmanci wajen mutane da yawa ba?"
Kan Haris a kasa, ai kamar Maryama tayi masa maganganu masu shigen wannan
"Bansan ya Rehab suke ba, amman nasan wajene da ake taimakawa mutane masu fama da irin abinda kake fama dashi, haka kuma nasan wajene da babu wanda zai iya taimaka maka in har baka shirya taimakon kanka ba, kome zasuyi maka in baka shirya bari ba inaji ba zasuyi nasara ba..."
Batare daya dago ba yace
"Kayi hakuri....dan Allaah kayi hakuri"
Saboda ya rasa abinda ya kamata ya fada bayan wannan, tsayin rayuwarshi yana jin kamar bai cika ba a idanuwan Alhaji Mustafa, musamman inya gansu shi da Mukhtar, yana da yakinin yanajin cewa Mukhtar kawai ya ishe shi, daya matso kusa yanzun, ya samu irin abinda yayi tunanin Mukhtar ne kadai yake dashi bayaso ya rasa, wannan kusancin da kaunar bayaso ya rasasu. Amman kuma a gefe daya har yanzun baiji yana so ya daina shan wiwi dinshi ba, saboda abubuwa nawa ake sha anaci da suke da illa ga lafiyar jiki kuma sanin hakan baisa an daina ba? Kawai suyi hakuri su fahimce shi, suyi hakuri karsu yi fushi, suyi hakuri karsu canza masa
"Banji dadi bane ba, saboda kana cutar da lafiyarka, bawai nace kayi mun wani abu bane"
Haris ya sauke wani gajeran numfashi
"In kun koma asibitin saiku sake magana da likitan kaji matakan daya kamata, bansan ko zaka so muje tare ba"
Sai lokacin ya dago kai da saurin shi
"Zanyi magana dashi Baba"
Alhaji Mustafa ya jinjina kai, idanuwanshi cike da damuwa
"Dan Allaah ka kokarta Haris, a halin yanzun wannan ne kawai nakasunka"
Ya jinjina kai, bayaso ya bude bakinshi yayi magana, bayaso yayi karya, bayaso ya fadi abinda baya hango yiwuwarshi, yaji dadi da suka koma cikin gidan, cikin 'yan uwanshi yau da suke ta tsokanar shi, har Aliya na cewa taga yayi haske, girkin Maryama ne ya karbeshi, kuma da Maryaman ta daga kai suka hada ido, baisan meye yasa ta dinga tuntsira dariya tana karawa ba. Tare dashi suka rakasu har saida suka fice daga gidan, kafin su koma cikine kuma Haris ya bata mamaki na farko a aurensu
"Motar nan tayi kyau?"
Ta sake kallon motar, dan tanata mamakin me yasa basu tafi da ita ba, har hannu ta dan saka ta shafa motar, sabuwa ce dal, daga gani
"Tayi kyau sosai, tun dazun nake ta kallo, mota ka kara siye?"
Saiya girgiza mata kai
"Taki ce, bana ce miki zaki fara koyon tuki ba? Ranar asabar zaki fara zuwa ba"
Kallonshi kawai takeyi tana so tagane abinda yace
"Ga mukullin? Baba yace takardun suna ciki"
Idanuwanta suka dan fito waje alamar mamaki, sai kuma tayi dariya ta girgiza kanta
"Ni zaka tsokana da mota Ganja"
Shima dariyar yayi
"Ba zaki daina kirana da Ganja ba ko?"
Ta makale kafadarta tana shigewa cikin gida, saida ya tsaya ya dauki takardun motar, sannan yabi ta cikin gidan, da yake har wanke-wanke saida suka tsaya sukayi tare sannan suka tafi, gidan a gyare yake kamar batayi baki ba. Tana zaune kan kujera, anan ya ajiye mata takardun da mukullin motar ya shige daki abinshi. Sai da ta duba taga sunanta baro-baro a jiki, da mukullin a hannunta, zuciyarta na bugawa ta dira daga kujerar tana nufar dakinshi, bata ko tsaya kwankwasawa ba, ta tura kofar
"Wai dan Allaah da gaske kake? Dan Allaah motata ce? Kai ka siyamun?"
Ya daga mata kai, ya numfasa ihun da tayi ya hanashi magana, kafin ma yayi wani yunkuri ta ruqunqume shi tana jijjigawa, ta sake shi ta fice daga dakin da gudu, ko a mafarki bata taba hangowa kanta mota ba, mota fa, ita Maryama da mota, ta rasa inda zata saka ranta dan farin ciki, ta sake rugawa cikin gida ta dauko wayarta, kuma sai taga babu wanda ya kamata ya sani sai Alhaji Sa'id, shine mutum na farko da ta kira ta fadawa, sannan ta dinga bin 'yan gidansu daya bayan daya tana gaya musu Haris ya siya mata mota. Sukace mata zasu hadu su saka lokaci suzo suyi mata Allaah Yasa alkhairi.
Ranar yanda batayi bacci da kyau ba, shima bata barshi yayi baccin ba, haka zata fito falo saita leka ta window taga ko motar na nan, daga falon kuma dakin shi zatayi ta kwankwasa
"Ganja...kayi bacci? Motata na leka inga ko tana nan"
Saida ya bude kofar ya rankwasheta saboda wani bacci mai dadi daya fara yaji ta kwankwasa
"Idan kika kara kwankwasa mun kofa saina cire miki kunne Maryamm, idan ma kika kara fitowa baki kwanta kinyi bacci ba da asuba zan kira azo a dauke motar"
Tana sosa kanta inda ya rankwasheta ta wuce bakinta data tura a gaba, dakyar ta samu tayi bacci, shima asubar fari ta bude ido. Mayar da hankali tayi ta koyi tukin, dan taba Haris mamaki, yanda yake ganinta da rawar kai, baiyi zaton zatayi tukin hankali ba, sai gashi bata yi wata biyu ba ya fara bari tana hawa babban titi, tunda sun fita tare kuma yaga yanda takeyin tukin. Danma bata da wajajen zuwa ne banda gidan Mummy, ko