Advertisements
Chapter 31 Reading LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

LABULE A Bayan Labule by Lubabatu Sufyan

Author :  Lubabatu Sufyan Category :  Complete Novels

Chapter   31 / 51

90K to 93K   out of 151K words

tayi mata ba tace

"Kiyi farfesu Maryama, ki shanye romon duka, ki dinga yawan yi kinji?"

Ta daga kai

"Kuna samun zuma anan?"

Kai ta girgiza tana dorawa da

"Bansani ba sai dai in tambayeshi"

Tunda dai komai ma shine ya fita yaje ya siyo musu

"Tam kice ya siyo miki, ya hado miki da lemon zaki ma, in ana samun kanamfari saiya hado miki, ki matse ruwan lemon da abin ciki, fatar da kwallayen kawai zaki zubar, kanamfarin 'yan pieces, ko hudu haka ki daka sosai ki zuba ki saka zumar sai kisha da daddare, in kin samu dama kullum kiyi kinji? Ko yana nan ko baya nan....ki kuma dinga shiga ruwan zafi, zan tura miki wasu abubuwan ta text"

Da ta wuni tana shiga ruwan zafi, tasha farfesun da shayi, sai gashi taji dadin jikinta. Randa Haris ya dawo zuciyarta har makoshinta, kuma shi ta bangarenshi bai dawo gidan da niyyar yayi mata komai ba, shisa ma yayi kokarin sauke duk wani abu da yakeji akan wasu matan, sai dai yana ganinta, yana ganin yanda idanuwanta suka kara girma da tsoronshi sai yaji babu abinda yake so irin ya rabata da wannan tsoron, ta saba dashi. Ta kuma gane shifa wannan harkar na daga cikin abubuwan da yake so, shisa ya ba kanshi mamaki matuka na yanda ya daga mata kafa, wai shine aka ajiyewa mace, kuma ya dinga kwana yana tashi daki daya da ita batare daya tabata ba, baima san yana da wannan self-control din ba sai akan Maryama.

Yanzun kuma daya rasa shi, baisan ta yanda zai sake dawo dashi ba, to ta ina ma zai fara idan tana nuna masa wannan raunin? Ya zai hakura da ita bayan zama kusa da ita kawai idan yayi sai yanayin fitar numfashinta ya canza? To shi da yake so ya mallaketa dukanta, taya zai iya rike kanshi? Ko da ta kalle shi tace masa

"Daman kasa na biyoka ne saboda ka kashewa iyayena ni?"

Saiya girgiza mata kai

"To me yasa ba zaka kyaleni ba kona roke ka?"

Ya riko hannunta, bata hanashi ba kuma

"Saboda ki saba, ina so ki saba dani Maryamm..."

Zaiso ace ya kara mata da

"Saboda ina son mata, saboda kin hada duk wani abu da banyi zaton zanso a jikin mace ba"

Amman sai yayi shiru

"Kome zance ba zaka kyaleni ba ko?"

Ya daga mata kai

"Da kin saba shikenan, kilanma kece zaki dinga damuna"

Batace komai ba, bata jinma ta gane me yake nufi, amman bata sake kokarin kwatar kanta a hannunshi ba

"Smettila di resistermi..."

Haka yace mata, kamar ya tuna ba zata gane ba ya dora da

"Stop fighting me, kibari Maryamm, kar inji miki ciwo"

To ya daina wahalar da kanshi, taji, ta daina kokarin kwatar kanta, ta daina gudunshi, gabaki daya tayi wani irin sanyi saboda fitinar Haris, shisa randa yace mata zasu fita batama yi wata murna ba, sai bayan sun fitan ne sauyin yanayin data samu yayi mata dadi, wani coffee place ne sukaje, wajen yayi mata kyau, daga kamshin shi zuwa yanayin setting din, shi yayi musu order din komai, kuma taji dadin abinda yayi mata order

"Ya sunan abin nan?"

Maryama ta tambayeshi tana kara zuka

"Frappuccino....a karo ne?"

Da sauri ta daga masa kai, yayi mata dadi sosai, sai da tasha kofi hudu, har mamakin kanta tayi, da zasu tafi ma ya sake siya mata kofi daya suka tafi tana rike dashi a hannunta

"Mu koma gida ko muje wani wajen?"

Gajiya takeji, kwana biyun jikinta nayi mata ciwo fiye da misali, shisa ta girgiza masa

"Muje gida kawai, ni jikina ciwo yakeyi mun, kullum ma jikina ciwo yakeyi saboda kai"

Dariya yayi

"Ni kuma? Ni dai yanzun bana gajiya da yi miki laifi, komai sai kice ni"

Ta harareshi

"Kaine mana"

Ya tsareta da idanuwa

"Me nayi? Ki fadi me nayi da bakinki inji"

Ta dan murguda bakinta

"Komai da komai, meye da meye ma bakayi ba?"

Ya karayin dariya, komai nata yayi masa, komai, musamman kananun abubuwa kamar yanda tayi maganar nan yanzun, yanda muryarta take canzawa da abubuwan da takeji, idan ranta ya baci, in tana cikin nishadi, in taji dadi, kowanne yanayi yana zuwa mata da canjin murya. Sai kawai yakai hannunshi yana matsa mata kumatu, ta janye fuskarta tana harararshi

"Wannan Maryamm din, nayi kewarta"

Shisa yace su fito, ko zata dan warware, ko surutun nan bata cikayi masa ba kwana biyu

"Bawani nan, ai kaine"

Ya sakeyin dariya, aifa ba zai huta ba, tunda ya tabata ta, daman yasan da ta gama mashau-mashau din ta warware sai yasha surutu, to ta fara, danma yana da abubuwan da shima zai tsokaneta dasu, abubuwan da zaisa ta rufe bakinta ta kyaleshi. Ashe surutun da zaisha da rikicin da zai kwasa na abu daban ne, dan a satin yanda take ce masa jikinta na ciwo saida ya fara bashi tsoro

"Dai-dai ina Maryamm?"

Ya tambaya

"Ko ina, har fatar kaina ma ciwo takeyi"

Kuma da gaske takeyi, ko ina ciwo yakeyi mata, wani irin ciwon jikine da bata taba sanin akwai irinshi a duniya ba, batama taba jin labarinshi ba

"Ki tashi, bari in kira uber sai mu tafi asibiti"

Ita ba son asibiti takeyi ba, amman dai a yanda take jin jikinta tana bukatar taimako, ta dauka asibitocin Najeriya ne kawai za'a iya samun layi irin wanda suka samu, shima kuma ma gwammati, tunda na kudi ai ba zakayi wannan jiran ba

"Wai layi baizo kanmu ba har yanzun?"

Ta tambayi Haris, dan ta jingina da kafadarshi ne, sai kawai ya gyara mata zamanta yanda ta kwanta a jikinshi, tunda ta kula babu wanda ya damu da harkar wani balle taji kunya.

"Ai su nan ba layi bane bafa, suna duba wanda yafi wani jigata ne"

Abin ya bata mamaki, tunda itama a jigacen take jinta, ko dai jikinta bai nuna irin wahalar da takeji bane ba? Kawai dai tayi mamaki ne matuka, yanda taga Haris nata cike form din da aka basu, ita bata masan menene rukunin jininta ba, an daiyi mata aune-aune kafin tahowarta, sai taga ya rubuta O+, haka ya gama cikewa batare da yayi mata tambaya ko guda daya ba. Tana ta kallonshi, harya kamata suka shiga wajen likitar, macece ma, kuma tunda aka gama mata duk wani gwaji da aka rubuta, saita tsinci kanta da kasa kallon dan karamin screen din abin gwajin da ake kira da scanner, saboda ta daina gane komai bayan kalmar

"Ina tayaku murna, tana da ciki..."

Kalmar ciki ce take ta amsawa tana sake maimaitawa a kunnuwan Maryama, lokacin da Haris ya zagayo kuma ya rike hannunta saita kalle shi

"Ciki kayi mun Ganja"

Ta furta a hankali, kamar mai son tabbatarwa da kanta maganar

"Cikina ne a jikinki Maryamm"

Yace yana kara dumtsa hannunta da yake rike dashi, a wannan lokacin daga ita harshi ba zasuce ga yanayin da suke ciki ba, amman mamaki ya rinjayi komai. A hanyarsu ta komawa hannunshi na cikin na Maryamm, da suka karasa gida kuwa haka ya riketa gam kamar mai gudun ta taka kasa, sannu kuwa tun tana iya amsashi har tayi shiru kawai

"Me kike so kici?"

Ta kalle shi

"Zaka dafamun ne?"

Ya ware mata idanuwan nan nashi da suketa maiko

"Ban iya ba ai, kin manta banda shayi ban iya dafa komai ba"

Cikin son ta tsokane shi tace

"Idan girkin naka nake so inci fa?"

Ya kara tausasa yanayin shi

"Sai in baki hakuri, ki zabi duk abinda kike so, idan akwai shi a NY, zan bazama komin nisan wajen in nemo miki"

Ta danyi murmushi

"Abin rannan, wanda ka saimun, mai dadin nan"

Ta bashi dariya

"Frappuccino?"

Ta daga kanta

"Shi, shi nake so"

In dai wannan ne ai ba zaiyi wahala ba. Kofi shida yayi mata order, duk da bai manta ba, akwai budurwar wani dan ajinsu lokacin da take da ciki, anan yasan ba'a son mai ciki ta yawaita shan Caffeine, dan haka decaf ne duka. Data kurba sai ta kalleshi

"Ba irin wancen bane ba, dandanon"

A hankali ya amsa da

"Akwai Caffeine a wancen, ba zaki iya shanshi ba saboda...saboda Babyn"

Ya karasa muryarshi na sauka kasa sosai, tare da idanuwanshi da suka tsaya kan cikinta, ta tura baki

"Wancen yafi dadi, ni wancen nake so"

Har lokacin idanuwan Haris na kan cikinta yace

"A'a"

Kalma daya, cikin yanayin da tasan duk wani abu da zata fada bayanta ba zaiyi tasiri ba. Haka tasha, tana gama kofin farko tasha na biyu, wani irin amai ya taso mata, da gudunta tayi bandaki, tayi amai kamar hanjinta zasu fito. Aman daya bude mata kofar wani irin laulayi mai zafin gaske. Laulayin da take cikinshi a halin yanzun, duk ta kara figewa tayi haske, idan Haris zai fita sai dai ya kwankwasawa makotansu guda biyu, dayar matar tsohuwace da zata kai shekaru 50 da karnukanta har hudu, dayan kuma ma'aurata ne da yaransu biyu yace musu dan Allaah matarshi tana ciki, su taimake shi su dan dinga dubata. Komai da zata bukata yake ajiye mata, ya dinga jaddada mata ta kira lambobin taimakon gaggawa da taji ba dai-dai ba, ta fara kiransu karta kirashi, kafin yazo idan wani abinne sun rigashi karaso su.

Ita duk ba burgeta yakeyi ba, tunda waye yaja mata wannan wahalar? Ji takeyi kamar mutuwa zatayi, shisa randa sukayi waya da Hajja, tana jin muryarta kawai ta fashe da kuka, aikuwa ba karamin dagawa Hajjan hankali tayi ba

"Wai dan ubanki ba zaki bude baki kiyi mun magana bane? Meye? Me yake faruwa"

Cewar Hajja cikin kosawa, Maryama na jan hanci da sauke ajiyar zuciya tace

"Bani da lafiya Hajja, dan Allaah kizo"

Hajjan ta dan sassauta murya daga can bangaren

"Subhanallah? Meya sameki? Kunje asibiti"

Tasa hannu ta share hawayen daya zubo mata

"Eh munje tun rannan, mun kara komawa, amman fa Hajja magani daya suka bani, kuma bani da lafiya sosai....dan Allaah kizo kar in mutu anan ni kadai, shi nace ya dawo dani gida yakiya..."

Maryama ta karasa wasu sababbin hawayen na kara balle mata

"Basu ce ga abinda yake damunki ba"

Batare da tunanin komai ba tace

"Ciki sukace fa Hajja, amman nace masa muje a kara dubawa ma jiya, tunda bani da lafiya, komai ciwo yake mun, har fatar kaina ma ciwo takeyi...idan cikine ai ba zan dinga ciwo haka ba ko? Dan Allaah kuzo"

Wani irin shiru Hajja tayi daga can bangaren, saida Maryama tayi tunanin kiran ya yanke ne tukunna taji tace

"Yanzun Maryama saboda baki da hankali sai ki bude baki ki fadamun kina da ciki?"

Maryama taji ta dan diririce, amman ta rasa abinda tayi na rashin hankalin, dan ta gaya mata? Hajja fa, in bata gaya mata ba wa zata fadawa?

"Zaki zo?"

Ta tambaya

"Tunda kasuwar bacci ne da zan dauki hijabi a kaini, kinga Maryama ki fita idona, Addanki zata kiraki"

Kafin tace wani abu ta yanke kiran, data kara kira bata daga ba, tasan Adda Zahra take nufi, sai kawai ta kirata da kanta, itace tace mata

"Zakiji sauki, In Shaa Allaah, da ya shiga wata na hudu zaki samu sauki...."

Duk wasu shawarwari ba wani shigar Maryama sukeyi ba, yanda ta saka Haris a gaba kuwa saida suka koma aka sake dubawa aka nuna mata, ta ware ido, ta sake warewa, harda kunnuwa dan ta fahimci turancin da likitar take tayi, da kuma abinda take nuna mata din, sai bayan sun koma gida, da daddare suna kwance ne ta cewa Haris

"Ganja..."

Tare da zame hannunshi daga rikon da yayi mata ta juya kwanciyarta tana kokarin ganin fuskarshi ta cikin duhun dakin

"Kayi bacci?"

Da muryarshi da tayi kasa saboda gajiya da kuma baccin daya dan fara yace mata

"Menene? Kina son wani abune? Ko jikin ne?"

Ta girgiza masa kai

"Dazun, kai kaga babyn? Da ake nuna mana, babyn cikina"

Ya dan numfasa

"Nagani...meya faru?"

Inda tama san yanda ya ajiye karatun daya kamata ace yanayi ya maida hankali akan karatun mai ciki da irin taimakon da take bukata zata sha mamaki, duk wani motsi da zaiyi zuciyarshi na kara tuna masa da cewar akwai cikinshi a jikin Maryama, shima yana gab da amsa sunan uba, kuma har lokacin abinda yakeji bashi da suna.

"Me yasa ni banga komai ba?"

Tana jinshi ya karasa sakinta, sai kuma taji ya mike, ya kunna kwan dakin, akwai hoton da aka kara basu, shiya sauka daga kan gadon yake falo ya dauko

"Tashi kigani"

Ya fadi, batayi musu ba ta tashi, yayi amfani da dan yatsanshi yana nuna mata

"Gashi nan...dai-dai nan"

Ta kura ido, ta karbi hoton ta sake dubawa

"Dai-dai ina dan Allaah? To ni me yasa bana gani"

Ya sake nuna mata

"Wannan farin abin mai kamar wake?"

Yaso ya danne, dariyar data taso masa, ko dan yanayin damuwar da yaga tayi, amman saiya kasa, dariya yakeyi ba 'yar kadan ba, itama kuma sai abin ya bata dariya

"Allaah ni na kasa gani, to ina kan? Da kafafuwan? Ina hannuwan?"

So yake yayi mata bayanin da sauran lokaci kafin duk wannan abubuwan su bayyana amman dariya ta hanashi, sai kara duba hoton hannunta takeyi tana son ganin alamar kai, ko hannuwa

"Ai shikenan, ni kam dai banda wannan wake-waken babu abinda nagani..."

Da alamar dariya a muryarshi yace

"Karki damu, zaki gani...ke da ma zaki ga babyn gabaki daya, ki rike a hannunki"

Tayi shiru, maganar ta shigeta, ita da yaro ko yarinya? Kuma ace nata ne duka, itace zata kula dasu, zatayi musu komai, babu wanda zaizo ya kwace mata, yaranta, ko yarinyarta

Allaah Kenan...
Mai kyauta da kari,
Sai dai kuma ai yanzun ne ta fara, kaddarar rabon da yake tsakaninsu.

32

"Ganjaa!!!"

Maryama take kira, kuma kusan duk wanda yake taku ashirin daga dakin naqudar da take, yaji yanda ta kira sunan nan harya bace lissafi, wani ma sai yayi zaton ko addu'a ce ta samu ta rike, ko kuma Haris din baya dakin tare da ita, hannunshi cikin nata yana jera mata sannu

"Ina ganin girmanka, banaso in zageka, ka daina mun sannu kamar bakai kaja mun ba"

Ta fadi tana karayin wani nishi da yaji har cikin ruhinshi, yana makaranta makociyarsu Chloe ta kirashi akan yazo, dan suna tsaye ne a kofar gida suna dan hira lokacin da Maryama taji wani abu mai dumin gaske nabin kafafuwanta, ta dauka ma fitsarin da tunda cikinta ya shiga wata bakwai bata iya rikewa sosai ne ya kubce mata, sai dai ai bataji alamar fitsari ba, kafin ta bude baki tayi magana wani abu ya soketa a gadon baya daya sakata rike karfen da akayi ado dashi a kofar gidan nata

"Her water just broke..."

Haka Chloe tace masa, kuma bai taba sanin mintina ashirin wasu mintina bane masu tsayin gaske sai a ranar, gani yakeyi kamar zata iya haihuwa kafin yaje. Sai dai ko asibiti ma basu tafi ba harya karasa, yana ta yiwa Chloe data zauna da Maryaman godiya, tukunna suka dauki akwatin da sun jima da hadashi, tunda duk wata siyayya tare sukayi da Haris, da yake sunce basa son sanin gender, sai suka dinga daukar unisex a komai, kayan da kullum sai Haris ya budesu ya kalla sau nawa, ya daga wancen ya ajiye ya daga wannan ya ajiye

"Ko dai mu karo set of socks din nan? Kinsan akwai sanyi"

Abubuwa da yawa ita ta dinga hanashi kwasarsu, tunda Adda Zahra tace mata su siyia 0-3 months su jira, wasu yaran saurin girma sukeyi, kayan ma sai suyi musu kadan kafin suyi watannin. Ita dai a tsakanin azabar da take sha ma dokin da take ciki ya bace, ji takeyi kamar ta shako Haris su kacame da dambe. Amman bari dai ta haihu, ai ko riga ta gama yarda ya cire a gabanta balle wani abin ya hadasu, daki ma zasu raba, wannan azabar? Ba zata taba yarda ya kara sakata a cikinta ba. Amman kamar anyi ruwa an dauke, haka taji bayan babyn ya fito, kukan jariri ya karade kunnuwanta, kuma batasan meye yasa hawayenta ballewa a dai-dai wannan lokacin ba, da aka mika mata babyn, maimakon ta karba sai ta kalli Haris, idanuwan Haris

"Macece ko namiji?"

Cikin wata irin murya yace mata

"Namiji..."

Ta jinjina kanta wasu hawayen na sake zubo mata

"Ka fara daukarshi"

Yaso ya girgiza mata kai, ita da tasha wannan wahalar? Tayi dakon cikin? Sai shi ya fara dauka? Amman tun kafin tayi magana zuciyarshi ta jima sa barin kirjinshi ta lullube yaron dake hannun likitar nan, hannuwanshi na gaya masa ba zasu yafe masa ba idan ya kara dakika bai karba ba, shisa baiyi musu ba, ya karbi yaron, ya matsa kusa da Maryama, ya sakashi a jikinta, ta sauke ajiyar zuciya, kuka yakeyi har lokacin, ta rankwafo tana kai bakinta saitin kunnenshi

"Barka da zuwa, ina rokar maka kariyar Ubangiji daga sharrin da yake cikin duniya da kuma rudinta, Allaah Yayi maka albarka Ya hada rayuwarka da alkhairi daga yau har karshen numfashinka, Allaah Yasa raino da tarbiyarka suzo mana da sauki, Allaah Yasa mu sauke amanarka, Allaah Yasa ka zame mana daya daga cikin hanyoyin shiga aljanna"

Bata manta ba, bata taba mantawa ba, yanda ake jaddada musu tasirin addu'ar uwa a Islamiyya, yanda ake fada musu su roki yara nagartattu ba sai sunyi aure ba, su rokama yaransu tsari tun kafin su samesu, kuma addu'ar ma ta zame mata jiki, shisa yanzun data rike shi a hannunta tunanin daya fara zuwa mata kenan. Ta mikawa Haris shi

"Kayi masa addu'a"

Shima bai manta ba

"Kiran sallah a kunnen dama, Iqama a kunnen haggu...karfa ka manta da an miko maka babyn"

Ta fada masa baisan adadi ba, hakan yayi yanzun, tana kallonshi, amman gajiya takeji tana saukar mata sosai, idanuwanta ma sun fara mata nauyi, bacci takeji, akace Haris ya mika mata babyn dan ta bashi yasha. Ya mika mata, yaki barin dakin har aka karasa yi musu duk wani abu daya kamata, daga ita har Babyn bacci sukayi. Ya samu waje ya zauna, sai kallon yaron yakeyi, zaiso ya dauke shi daga inda aka kwantar dashi, amman kuma bayason ya tashe shi, yayi kuka ya tashi Maryama, tana bukatar ta huta ko da ba'a fada masa ba. Dakyar ya iya fita ya barsu, shima dan yana so yayi waya ne. Alhaji Mustafa ya fara kira ya gaya masa, ta cikin wayar yakeji irin farin cikin da labarin ya sakashi, sai addu'a yakeyi yana karawa.

Inda lafiya, zai fara kiran Hajiya Rumana ne, amman gabaki daya ta canza masa tun tahowarshi da Maryama, ko da ta gama fushin, saida tace masa

"Ba zan taba karbar auren nan naka ba Haris, banga ranar da zuciyata zata amince da 'yar Sa'idu a matsayin surika ba, tunda kafi karfina yanzun, babu wani abu da zan fada yayi tasiri akanka, inaso in zamuyi magana muyi maganar data shafemu, karka sakko mun matarka a ciki, bana son ji"

Amman haka ta kirashi ta balbale da taji labarin cikin a wajen Munira

"To meye

31 / 51