Author : Lubabatu Sufyan Category : Complete Novels
ya siyo, sannan suka dauki jakunkunan shi da Alhaji Sa'id suka sake ficewa badan yaso hakan ba. Lokacin da Haris yayi wata dawowa daga makarantar kwana, ya ganshi, lokacin farko daya fara kai ziyara makarantarsu, akwai wani abu tattare da Haris din da bai kwanta masa a rai ba, wani abu daya dinga damunshi, irin wannan abin yake gani yau. A kasan yanayin kamar akwai firgici kwance cikin idanuwan Haris, ko meye yake gani yasa shi son yin magana da Maryama. Shisa bayan sun fita ya samu inda ya kara wanke hannuwanshi, yazo ya zauna yaci iya abinda zai iya, ya zubar da sauran a shara.
Cikin sa'a lokacin daya leka ta window din dakin da Maryama take sai yaga ta tashi, kafin ma wani cikin sarakan iyayin Nurses din nan ko likita suzo da wata tsirfar tasu ta kasar waje da zasu hanashi shiga wajenta ya murda hannun kofar da sallama dauke a bakinshi, idan ma Maryama data amsa sallamar a hankali tayi mamakin ganinshi to ko a fuskarta bata nuna hakan ba. Ya shiga ciki sosai, yaja kujera ya zauna
"Maryama"
Ya kira cikin taushin murya
"Baba...sannu da zuwa"
Ta tsinci kanta da furtawa tata muryar na fitowa a hankali
"Ya jikin naki?"
Ciwon da takeji yanzun kawai a zuciyarta ne da kwakwalwarta da koya zata rufe ido babu abinda take gani sai Haris da Autumn, ko alluran baccin da suke ta dankara mata, tana baccin tana ganin wannan kazantar, duk wani bayanshi mai saukine, inda zata goge hoton nan, inda zata samu hanyar da zata cire shi daga kwakwalwarta, watakila da ta fara samun salama
"Alhamdulillah"
Ta amsa sauran kalaman na makale mata
"Tare da Sa'idu mukazo, sun fita shi da Haris, na zauna ne saboda ina so inyi magana dake"
Kallonshi takeyi, sai taji gabanta yana faduwa
"Lafiya kuke? Karkice mun bakomai Maryama, yanayin Haris, yanayinki yanzun, baiyi mun kama da babu komai ba"
Tasan tayi shiru, shiru mai yawa, kuma magana ce ake cewa kana cikin yi ko zakayi an katse maka, Alhaji Mustafa baiyi wani yunkurin katse mata wannan shirun ba, ya barta, kamar mai bata lokaci ta tattara kalamanta, ko ta zabi iya abinda take so ya sani. Maryama ta bude bakinta yafi a kirga tana sake rufewa ta rasa ta inda zata fara, ta rasa me zatace, ta daisan ko meye zai fito ba zata taba iya kallon Alhaji Mustafa da yake zaune ta gaya masa matsalar nan ba, ko kirjinta za'a tsaga masa saita samu hanyar data rufe wannan abin, kafin a hankali tace
"Ni dashi ne Baba, matsalar, ni dashine kawai"
Alhaji Mustafa ya kalleta, sai tayi saurin karawa da
"Inaso inje gida dai, bana so in kara haihuwa anan, kuma ina so in dan huta, ina so inje gida Baba, dan Allaah, idan na zauna ciwon nan banajin zai warkemun, ina so inje gida"
Ta karasa maganar cikin karyewar murya, hawayen da batasan tana rike dasu ba suka zubo mata, ganinsu ya saukarwa da Alhaji Mustafa wani abu mai nauyi a cikin zuciyarshi
"Dan Allaah, kawai gida nake so"
Cewar Maryama ganin yanda yanayin Alhaji Mustafa ya canza gabaki daya, da saurinta kafin yayi magana ta kara da
"Idan na fadawa Abba zai bani hakuri, nasan hakuri zai bani yace in zauna, wallahi ba zan iya zama ba, kirjina yana mun zafi sosai Baba, duka zuciyata ciwo takeyi, ka tafi dani gida in huta"
Kai Alhaji Mustafa ya jinjina mata
"Yace wai ba zasu barni ba, asibiti ba zasuyi clearing dina fit to fly ba, kayi musu magana"
Kai ya sake daga mata, ya kasa magana, to me zaice mata? Me zai fada bayan ciwon da yake gani kwance cikin idanuwanta, ciwon da yake ganin ya girmi shekarun da take dashi, meye Haris din yayi mata? Me yakeyi mata? Daman ba lafiya suke zaune ba? Yanda yakejin su a waya ba haka abin yake ba? Ai idan Munira yazo ya samu tana wannan hawayen, ko batace masa komai ba yasan da 'yarshi zai tafi, kai tun ranar da sukaje duba Haris a asibiti yaji kalar ciwon daya kwantar dashi, bayajin zai iya barwa dan wiwi 'yarshi ya cigaba da aure, idan kuma ya dinga numfashi a kusa da ita ya goga mata wani ciwon fa? Ko ya dinga busa hayakin a cikin gidan itama tana shakewa, shisa har yau cikin kunyar Alhaji Sa'id yake, nauyin shine ya ninku a idanuwan Alhaji Mustafa, nauyi mai yawa kuwa.
A gefe daya duk addu'ar da zaiyi baya taba tashi bai roki Allaah Yafiya akan son kan da yakejin yayi ba, yana fatan auren Maryama da Haris yakeyi ya cigaba da zame masa rufin asiri, nagartar yarinyar da ta gada wajen mahaifinta ta shafi danshi, kuma akwai abubuwa da yawa na canji game da Haris din da yasan cewa sanadin zama da Maryama ne. To taya zai so su rabu? Bashi da wannan kawaicin irin na Alhaji Sa'id, bashi da wannan karar, kamar yanda yasan yaran Hajiya Rumana sune rauninta, to shima soyayyar da yakeyi musu itace rauninta. Abu daya dai zai iya wanda Alhaji Sa'id ba zai taba kamantawa ba, shine karbar rokon Maryama, wannan karon zaiyi ma Alhaji Sa'id abinda yasan zai tsaya yayiwa Haris ninkinshi.
"Tare zamu tafi...dake zamu koma"
Kai kawai Maryama ta iya daga masa saboda kukan da taji yana neman kwace mata, kuka ne da bataso tayi, kuka ne da inta fara batasan ko zata iya tsayawa ba, saboda tunda abin nan ya faru batayi kuka ba, kawai dai taji kamar amincewar da Alhaji Mustafa yayi ya daga mata wani abune mai nauyi da yake danne da kirjinta, zataje gida, zataje gida, shine kawai abinda yake mata yawo cikin kanta, abinda yake rufa mata wani bargon Rahma a duka ilahirin jikinta
"Nagode, nagode Baba"
Ta furta cikin rawar murya, nashi kan ya daga mata
"Bari in barki ki huta"
Wani irin tausayinta ne yake dukan zuciyarshi, watakila idan ya zauna anan tsaf zata saka shi hawayen da ya manta rabon da yayi su. Daya fita saiya kira Haris yake tambayarshi inda suke, ya fada masa, ya fita ya samu taxi ya hau yana samunsu a wajen, Alhaji Sa'id harya shiga wanka dan Haris ya kama musu daki
"Bari in koma asibitin Baba, karta tashi ko zata bukaci wani abin"
Haris ya fadi da saurinshi, wani kallo ne Alhaji Mustafa yakeyi masa da baigane ba
"Me kayi mata?"
Tambayar ta dake shi kamar ya kwada masa wani abu
"Kafin kayi tunanin bude bakinka kayi mun karya nasan kayi mata wani abu Haris, nayi magana da ita kafin in taho"
Haris ya sauke idanuwanshi zuciyarshi na bugawa kamar tana son fita ta gudu tabarshi da abinda yakeji shi kadai
"Me kayi mata?"
Alhaji Mustafa ya sake maimaitawa, yana saka Haris juya yanayin tambayar, yace yayi magana da Maryama, to in yayi magana da ita me yasa yake tambayar shi?
"Saboda bata fada masa ba"
Wani sashi na zuciyarshi ya bashi amsa, amsar ta sama masa natsuwa kadan
"Baba..."
Ya kira sai kuma ya rasa abinda zaice
"Na dauka kuna zaune lafiya, hankalins a kwance yake sanin kana rike da amanar dana karba maka da hannu na, ashe ba haka bane Haris? Ashe ka shirya kunyata ni? Ka shirya ka watsamun kasa a ido?"
Kai Haris yake girgizawa, shi duk yaushe yayi hakan?
"A'a Baba, na karba, aina fada maka na karbi auren"
Alhaji Mustafa ya jinjina kai
"Eh ka karba, ka fadamun ka karba, kuma ka nuna mun da gaske ka karba din, sai dai baka cemun zaka riqe da kyau ba, daka karba, shisa kayi mata abinda ya kwantar da ita, wannan 'yar yarinyar Haris, da karancin shekarunta yau a zaune naga bakin ciki a idanuwanta, bakin cikin da na tabbata kai kayi mata sanadinshi"
Ya kasa cewa komai, yasan abinda yayi ba dai-dai bane ba, amman a wannan lokacin bawai yana kallon abin ma ta fuskar addini bane ba, yana kallonshi ne ta fuskar zamantakewa
"He cheated on his wife"
Shine abinda ya sani, bai kyauta mata ba, sai dai har ranshi ai baiyi tunanin zata sani ba, yabi duk wasu matakai daya kamata wajen kareta daga sanin, ita ta dauko kafafuwanta taje har inda yake tagani, ya bata hakuri, zai kara bata hakuri, zaita bata hakuri har saita yafe masa, yanda Alhaji Mustafa yake maganar yana saka shi jin kamar abinda yayi wani gingimemen laifine da bai kamata a yafe masa ba
"Zamuyi magana Baba, komai zaiyi dai-dai, matsala ce muka samu, shima duka ba'a dade ba sai tazo bata da lafiya...ka daina cewa haka, kana magana kamar tunda mukayi auren nakeyi mata wani abu"
Hararashi Alhaji Mustafa yayi
"Yaushe zasu sallameta? Da ita zamu wuce? Dan zan zauna ne sai sun sallameta mu tafi"
Haris ya kalle shi da sauri
"Eh, tare zamu tafi da Maryam"
Kai ya girgiza
"Zamu zo ai, ta sani, idan ta haihu daman zamu zo"
Shima nashi kan Alhaji Mustafa ya girgiza
"Gida take son zuwa, kuma gida zan tafi da ita"
Wannan karin ba bugawa zuciyar Haris takeyi ba, ji yake tana kada masa da wani abu da baisan menene ba
"To me yasa? Saboda munyi fada? Baba ba'a fadane a tsakanin ma'aurata? Kuna fada da Mami, amman babu wanda yake zuwa ya dauketa sai dai ko idan itace ta tafi da kanta"
Bai cika sakin baki a gaban Alhaji Mustafa ba, ko yace ya manta rabon da yayi, tun lokacin kuruciya, da wannan sakin bakin ne abinda yasa duka ya fara giftawa a tsakaninsu, sai dai yanzun in yayi shiru zai cutu ne, ya za'ayi kawai ace za'a tafar masa da mata? Haka akeyi? Ina ake haka
"Waya baka Maryama?"
Cewar Alhaji Mustafa, bai kuma jira amsar Haris ba ya dora da
"Inace ni na nema maka aurenta ko? Inaso kasan yanda na nema maka shi cikin sauki zan iya kashe shi cikin sauki idan naga akwai cutarwa a ciki. Maryama tace mun tana so taje gida, da alama tana bukatar break, daga koma menene yake faruwa tsakaninku da bataso ta fada, saboda haka zata tafi gida"
Kai dai Haris yake ta girgizawa
"Ai ba tambayarka nakeyi ba, umarni ne nake baka"
Da yake dakin hotel din ciki da falo ne Haris ya kama musu, sai lokacin Alhaji Sa'id ya fito, ya sauya kaya, yaji dadin jikinshi, cikinshi nema a cushe, watakila gajiya ce ta hanashi cin abin kirki, Haris ya kalle shi, ya tsinci kanshi da fadin
"Abba kayiwa Baba magana"
Cikin rashin fahimta Alhaji Sa'id yake kallon su biyun
"Wai sai an tafi da Maryamm gida, kuma na gaya masa zamu zo, idan ta haihu zamu zo gida tare"
Alhaji Sa'id ya danyi murmushi yana kallon abokinshi, duk da ba wai ya gama fahimtar abinda yake faruwa bane, sai yace
"To ina ake haka kuwa? Yarinya ga mijinta ace za'ayi masa iko"
Shima nashi kason kallon ya samu a wajen Alhaji Mustafa
"Wallahi kafata kafar Maryama zamu bar kasar nan Haris, kuma tunda ba tsoronka nakeyi ba, ba zaka sakani azumin kaffara ba"
Da sauri Alhaji Sa'id yace
"Subhanallahi...haba Mustafa...kai Haris tafi abinka, kabarshi zamuyi magana kafin muzo asibitin anjima In Shaa Allaah"
Kamar Haris zaiyi gardama, saiya tuna ai a lokutta da dama idan Baban nashi ya murde, ita kanta Hajiya Rumana bata da wanda take kira ya shawo mata kanshi sai Alhaji Sa'id din, amman fa a yanda yakeji babu inda Maryama zata taka batare dashi ba, babu mai tafar masa da mata ko ina. Yayi shiru ne yabi maganar Alhaji Sa'id ya tafi. Haka kawai yaji ranshi yana baci, maimakon ya wuce asibitin, sai kawai ya fara yin gida, yana bukatar ya dan busa hayaki ko kanshi zai rage nauyin da yakeji yayi. Daya gama sai yayi wanka, ya kara sake kaya ya balbala turare saboda ya rasa irin hancin da Maryama take dashi wajen jin warin hayakin wiwi a jikinshi. Biyawa yayi ya bada uzurin da ya dauki Awwab tunda lokacin daukar baiyi ba, ya wuce asibitin tare dashi.
Mamaki ya dingayi, ganin Maryama a zaune, alamunta sun nuna tayi wanka, ta canza kaya, kuma da murmushi ta mikawa Awwab daya ruga da gudu hannu
"Dan albarka, ya kake?"
Ita Hausa takeyi masa, haka kawai kuma sai Haris yake yi masa Italian, gashi yanzun da yake cakuduwa da turawa, turanci akeyi, bakin yaron yayi nauyi, watakila kuma yana rasa yaren da zai farayi ne, yarukan sunyi masa yawa a cikin kwakwalwa, ya jima sosai kafin ya fara furta wasu abubuwan, wani abinma inya fada Maryama bata ganewa saboda zai fadane da yaren Italian, ita kuma bataji. Ko yanzun ma labari yake bata, yanata cakuda yarukan uku, tayi 'yar dariya, rabon da tajita sakat haka tun data farka a asibitin nan, yanzun bata da wani fata saina suzo su sallameta, taje gida ta fara hada kayanta. Dan in yau ma aka sallameta ba zataki ace yau zasu bi jirgin da suka samu zuwa Nigeria ba.
"Ya jikin?"
Muryar Haris ta ratso cikin surutun da Awwab yakeyi mata, yanda ta shareshi, kamar baya dakin, sai abin yakeyi masa wani iri
"Da sauki Alhamdulillah"
Ta amsa masa, zaiso ace yayi mata wata maganar daban, amman daya sake bude bakinshi sai yace
"Me yasa kika cewa Baba kinaso kije gida? Na fada miki zamuje tare, idan kin haihu"
Ta dago kai idanuwanta tar cikin nashi
"Saboda gida nake so in tafi, na gaya maka ba zan zauna ba ai"
Yayi shiru yana kallonta har saida ta kasa jurewa ta sauke idanuwanta
"Idan nace ba zakije bafa?"
Tasa hannuwanta biyu tana toshewa Awwab kunnuwa
"Ai baka isa bane ba Ganja, isar nan ta kare tun randa naga wata a samanka..."
Zaiyi magana ta saki kunnuwan Awwab tana cigaba dayi masa wasa kamar bata fada masa magana ba
"Maryamm"
Cike da kosawa tace
"Ni da zaka tafi kayi abinda ka sabama ya fiye mun wannan zaman da kakemun, dan ba son ganinka nakeyi ba"
Ta karasa maganar da dukkan gaskiyarta, wani irin tiririn bakin cikine yake taso mata data ganshi, data kalle shi saita ga komai yana dawo mata, kamar ta tashi ta shakare shi
"Maryamm"
Karamin tsaki taja, wani abu da ta gwada sau biyu kacal a iya zamansu basu kwasheta da dadi ba, bata sake giginyi masa tsaki ba sai yau, kuma taja shi irin da tsayin nan dan so takeyi yajita, aikuwa yaji, tagani a yanda yanayin fuskarshi ya canza zuwa bacin rai, bayason tsaki, tun tasowarshi yana cikin abinda bayaso, inya taba kwatanta yi to ya manta, saboda bayaso, ko sanda yake secondary abinda tsaki na daga cikin abinda zaija yayi maka dukan tsiya. Na farko data fara yi masa ya dalle mata bakine, na biyun ma haka, bayan yayi mata riqon da saida ta bashi hakuri jin kamar zai karyata, kuma fushi ya dauka sosai, ba karamin lallashi tayi ba kafin ya hakura da kashedi sosai, ta kuma dauka, amman yau raini yake gani karara a cikin idanuwanta, rainin da yake so ya dauke Awwab ya maidashi inda ya dauko shi, ya dawo ya murzawa dakin mukulli ya goge shi tas a tare da ita.
Babu daya a ciki da zai iya, dan Alhaji Mustafa ne ma yake kiranshi, dole ya daga wayar, tambaya yayi ko zasu iya zuwa, ya amsa musu a takaice. Ba'a kara mintina ashirin ba sai gasu, Maryama da gudunta taje ta fada jikin Alhaji Sa'id kamar ba ita bace bata da lafiya
"Mairama kice so kikeyi in taho babu shiri, shisa kuka hada baki da mijinki kukayi mun karyar ciwo"
Dariya tayi, daga zuciyarta
"Kai Abba"
Shima dariyar yayi, yaji dadin ganinta matuka, dan yayiwa Alhaji Mustafa maganar duniya bayan tafiyar Haris bai kulashi ba, bayan sun kara gaisawa da Alhaji Mustafa, sai yayi wa Haris ido, kan dole ya tashi yabi bayanshi suka bar Maryaman da Alhaji Sa'id
"Yanzun me yake ciwo?"
Kai ta girgiza masa, abinda ya rage da yake mata ciwo ba zata iya fada masa ba
"Babu komai, naji sauki sosai"
Ya sauke numfashi
"Alhamdulillah. Allaah Ya kara miki lafiya yayi miki albarka"
Ta amsa a hankali
"Babanki yace dake zamu koma, mijinki kuma yace saikin haihu, na dauka nima maganar da muka gama kenan, akwai matsala ne Mairama?"
Ta danyi jim, tana tauna abinda zata fada
"Eh Abba, fada mukayi, kuma inajin idan ba muba juna tazara ba zata iya yin girma"
Shima shiru yayi na dan lokaci
"Babu auren da ba'a samun matsala a cikinshi, amman ba ko da yaushe bane in an samu matsalar za'a guje mata maimakon a fuskance ta"
Sai taji kamar hawaye na shirin balle mata
"Ba gudu zanyi ba, ina bukatar hutun ne Abba..."
Suka sakeyin shiru, yasan Maryama na da kafiya, har Hajja takan kawo masa kararta, amman shi batayi masa, in yaja saki takeyi, shisa ya rasa abinda zaice saboda bayaso ya tauyeta, ba kuma yaso ace ya goyi bayanta ta fara gujema matsalolin aurenta, tunda har tayi shiru, itama tasan cewa matsala ce da sirrantawar yafi bayyanawar zama maslaha, kuma tana sa ran ita da Haris din zasu iya samun dai-daito batare da an shiga ciki ba.
"Kiyi hakuri Mairama"
Ya furta a hankali, taji hawaye ya balle mata
"Karkace baka isa dani ba Abba, dan Allaah kayi hakuri"
Sai kawai yace mata
"Na hakura, Allaah Yayi miki albarka"
Tasa hannu ta share hawayenta tana amsawa da
"Amin Abba"
Cike da wani irin rauni da yake shigarshi a hankali, duk wani kokarin hira da yake janta dashi ta kasa sakewa gabaki daya, ta kuma kasa daina kai hannu tana share hawayenta. Har sanda su Alhaji Mustafa suka dawo dakin kuwa bata daina share hawaye ba, zuciyar Haris har wani tsalle takeyi, ya kasa daga ido ya kalli Alhaji Sa'id, kamar ya zama gari yabi iska haka yakejin shi, taya Maryama zata dinga wannan kukan a gabanshi? Me take so yayi tunani? Bayaso ko kadan mutuncinshi ya zube a idanuwan Alhaji Sa'id din. Sanda zasu tafi kuwa dakyar ya rakasu. Yazo ya dauki Awwab suka koma gida dan yasan koya tsaya magana da Maryama ma ba zata kulashi ba, inta kulashi kuwa maganganun da zata fada masa zata bata masa raine. Washegari da safe aka sallameta da sharadin ta huta sosai, kar ta jijjiga jikinta, kuma suna komawa gida ta fara hada akwatinta kamar bataji kashedin da akayi mata na hutawa ba.
"Wai me kikeyi haka Maryamm?"
Haris ya tambaya, bata kulashi ba, duk maganar daya tsaya yanayi mata bata kula shi ba, sannan iya kayanta yaga ta hada, ta zage akwatin ta koma falo tana barinshi a bedroom din cikin rashin sanin abinyi. Kuma a ranar da yamma da su Alhaji Mustafa sukazo gidan take ce masa
"Baba harna hada kayana, passport dina yana wajenshi..."
Alhaji Mustafa ya daga mata kai yana kallon Haris
"Saika dauko mun, dan so nake mu samu mu juya, ina da abubuwan yi a gabana,