Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: 🖋🖋 *ALKALI NE* 🖋🖋
(A book of law case)
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
Nah
Marubuciyar Zamani
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady
0⃣1⃣
*Bismillahir Rahmanirrahim*.
Ina mik'a godiya ga dukkanin masoyana. Wannan littafin k'irk'irarre ne, banyishi dan cin zarafin wani ba, ina fatan Allah yasa kowa ya amfana da abinda yake ciki amin.
*LAGOS*
Cike babbar kotun garin Lagos take da jama'a, wasu basu da alak'a da wannan shari'ar, amma yanda ake fad'in yanayin shari'ar da kuma wanda aka maida shari'ar wajensa yasa kowa yake so yaje domin yaji yanda zata kasance.
Kasancewar lauyen da aka maida shari'ar wajensa sabon zuwa ne hakan yasa kowa yake son ya ganshi, domin an sanar cewa wannan zaman shine zama na k'arshe, saboda tsohon lauya ya kasa kawo kwararan shedu hakan yasa shari'ar ta gamsu da shedun abokin karawarsa.
Tsaye mutane suke a bakin kotun suna jiran abasu izinin shiga kafin Alkali ya iso. Wasu Matasa ne da suke gefe guda suke magana akan wannan shari'ar. 'Daya daga cikinsu yake fad'in abokina ko kasan nima ban gamsu cewar gaskiya ce wannan lauyen yake fad'a ba, taya za'ace bayan mutum ya mutu da wata biyar sannan ace matarsa tana da ciki har na wata ukku, kai da gaji ma kasan rainin hankali ne har sai sunzo wata kotu.
'Dayen yace kuma wannan shari'ar kotun musulunci yakamata ace an kaita ba wannan kotun ba, gashinan yau zuwa na ukku ne amma an kasa tsaida mafita, da kotun musulunci ce tuni an wuce wajen amma hada wani sake lauya, ai zaizo muji tashi basirar.
Murmushi wanda yake gefensu yayi yana fad'in wallahi kuna bani dariya, kunsan fa ance shari'a sab'anin hankali, abinda wani yayi ya kasa sai kuga wani yayi, koshi Alkalin sai ya kasa gano abinda wani lauyen zai gano, duk da ance sabon lauya ne babu wanda yasan basirar da Allah ya bashi, kuma ba jiya bane ya amshi shari'ar kusan sati guda kenan rabon mu da nan, kunga kuwa acikin sati d'aya zai iya had'a shedu masu kyau idan yana da basira, koda kotun musulunci aka kai wannan shari'ar ai dole sai da shedu, dan haka muyi masu fatan alkhairi shine zaifi, danni wallahi tausayin matar nakeyi, itace k'arama acikin matan Alhajin, kuma itace ta ukku fa, kasan unguwar mu d'aya dasu babu abinda ban sani ba akan irin zaman da sukeyi da abokan zamanta, kasan halin mata, akan kishi babu abinda bazasu iya ba, kuma nasan halin matar, duk da basu dad'e da Alhaji ba amma mutane suna fad'ar kyan halinta, shiyasa jikina be yarda da wancan lauyen ba, domin ina yawan ganinshi a unguwar mu yazo wajen sauran matan.
Jinjina kai sauran sukayi suna fad'in to Allah ya bayyana gaskiya. Yace amin. Tashi sukayi ganin an fara shiga ciki.
Kowa ya sami waje ya zauna ana jiran shigowar Alkali. Wani Matashin yaro ne wanda bazai wuce shekara 32 zuwa da 33 ba yashigo kotun yana sanye da kayan aikinshi, idanuwansa suna b'oye cikin farin gilashi hannunsa d'auke da k'aramar jaka.
Yanayin takunsa yaja hankulan mutanan da suke zaune a kotun, koda ganinshi kowa ya gane shine sabon lauyen da ake magana akanshi. Wasu da yawa suna mamakin ganinshi a haka, sun d'auka zasu ga wani babban mutum sai gashi sunga Matashi mai jini ajika.
Yana k'arasowa wajen da aka tanadar masu domin zama ya fara mik'a hannu ga sauran 'yan uwansa lauyoyi suna gaisawa. Ko da yazo kan mutum na k'arshe bayan ya bashi hannu sai yaji bai sakeshi ba, d'ago kai yayi yana kallonshi. Babban mutum ne, yasan ya girme mashi a shekaru. Kallon hannunshi ya sakeyi ganin har lokacin bai sakeshi ba kuma murmushi bai b'ace daga fuskar mutumin ba.
Murmushi shima ya sakar mashi yana kauda kai. Sunana *Brr. Nuhu Bajinta*, amma amfi kirana da *Brr. Bajinta*, nine wanda yake jagorantar wannan shari'a, wato abokin karawar ka. Murmushi yayi yana fad'in sunana *Brr. RA'EEZ HAMZA MWD*, nine sabon lauyen daya amshi wannan shari'a.
Jinjina kai Brr. Bajinta yayi yana fad'in muna maka maraba da shigowa wannan babbar kotu mai albarka, Allah ya baka sa'a a wannan aikin namu mai had'ari da wahala. Brr. Ra'eez yace amin nagode.
Zama sukayi suna jiran k'arasowar Alkali. Wanda yake kusa da Brr. Ra'eez ya sake bashi hannu yana fad'in sunana *Brr. JABEER USMAN*, ina aiki a wannan kotun kusan shekara d'aya da farawata kenan, ina maka fatan alkhairi da zuwa wannan kotu. Murmushi Brr. Ra'eez yayi yana fad'in nagode Jabeer Allah ya bamu zaman lafiya. Yace amin.
Shigowar Alkali yasa kowa ya tashi. Bayan ya zauna kowa ya zauna tare da natsuwa. Bayan da Alkali ya gama 'yan rubuce-rubucensa sannan ya bada izinin acigaba da gabatar da shari'ar.
Tashi magatakarda yayi yana fad'in, a yau sha hud'u ga watan oktoba shekara ta 2019, wannan kotu zata cigaba da sauraron k'arar da akeyi akan iyalan gidan Alhaji Bala wanda matanshi guda biyu suke k'arar amaryarsa Amina akan fitowar ciki a jikinta bayan mutuwar mijinsu wanda suka tabbatar ba nashi bane, wannan shari'ar da ake gabatarwa ta tashi daga hannun lauyen da yake kare wacce ake k'ara ta koma wajen sabon lauya mai suna Brr. Ra'eez Mai Wada wanda aka yimasa canjin aiki zuwa wannan kotu.
Risnawa yayi yana mik'ama Alkali takarda. Bayan daya gama dubawa yace ina sabon lauya kotu tana so ka gabatar da kanka.
Fitowa yayi yana fad'in sunana Brr. Ra'eez Hamza MWD, kuma nine lauyen daya amshi wannan shari'a a wajen abokin aikina. Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in lauyen da zai fara bismillah.
Komawa Brr. Ra'eez yayi ya zauna dan beyi niyar farawa ba, yafiso ya zauna yaga kamun Brr.. Bajinta. Fitowa Brr. Bajinta yayi yana fad'in ya mai shari'a, har yanzu Amina bata amsa laifin da ake zarginta ba, haka kuma taki furta sunan wanda yayi mata wannan cikin, duk da matanshi sun tabbatar da Alhaji bai tab'a haihuwa ba a duk zaman da suke dashi, kuma sun dad'e atare dashi bai haihu ba, dalilin rashin haihuwar ne yasa ya k'aro aure, har sukayi zaman kusan shekara Amina bata tab'a b'atan wata ba sai gashi bayan mutuwar Alhaji ciki ya bayyana a jikinta har na wata ukku wanda likita ya tabbatar Alhaji baya haihuwa, kuma kowa ya sheda bayan mutuwar Alhaji sannan cikin ya bayyana wanda Alhaji ya riga cikin barin duniya kafin ya bayyana.
Takowa yayi wajen da Amina take tsaye yana fad'in Malama Amina ya kamata zuwa yanzu ki bud'e baki ki fad'a mana gaskiyar wannan al'amari, be kamata kicigaba da wahalar da kotu ba, agabanki aka gabatar da manyan hujjoji, kowa ya aminta da hujjojin yakamata kema ki bayyana wanda yayi wannan cikin domin ki sauk'ak'a ma kotu wahala.
Tashi Brr. Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a, bai kamata lauya yarik'a takura wadda ake zargi ba, Amina tana da ikon ta fad'i gaskiya akan abinda ta sani, bai zaima dole dan kowa ya amince da abinda wani ya fad'a ba ace itama dole ta amince. Nagode ya mai shari'a.
Kallon Brr. Barjinta Alkali yayi yana fad'in ka gyara kalamanka. Risnawa yayi yana fad'in za'a kiyaye ya mai shari'a. Iya kar abinda zan fad'a kenan, ina rokon wannan kotu data yanke wannan hukunci domin magada su san halin da suke ciki. Nagode ya mai shari'a.
Tashi Brr. Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a inaso nayima Alhaji Kabir babban aminin marigayi wasu tambayoyi. Da sauri Brr. Bajinta ya kalli Brr. Ra'eez jin wata magana da yazo da ita, shi tunda aka fara shari'a beyi tunanin sako aminin Marigayi ba domin yasan beda wani amfani a shari'ar, sai gashi Ra'eez ya gayyatosa a cikin shari'ar.
Alhaji Kabir ya fito gaban kotu.
Brr. Ra'eez... Kotu zata so tasan alak'ar ka da Marigayi.
Alh. Kabir... E to, kowa dai yasan Alhaji bai da amini daya wuce ni, atare muka taso, abotar mu ta wuce abota ta koma ta 'yan uwantaka, sirrina na Alhaji ne, haka shima nashi nawa ne, babu abinda muke b'oyema juna.
Brr. Ra'eez.... A tsawon zamanka dashi ko ya tab'a fad'a maka yana da matsalar rashin haihuwa?
Brr. Bajinta... Ina da ja ya mai shari'a, be kamata Brr. Ra'eez ya maido mana da hannun agogo baya ba, kowa yasan munyi nisa a wannan shari'ar, dan yazo daga baya bai kamata ya maido da komai farko ba.
Alkali... K'orafi bai karb'u ba, Brr. Ra'eez yana da ikon sako wannan shari'a daga farko matuk'ar yana da tabbacin ya kawo hujjojin da zasu gamsar da kotu.
Brr. Ra'eez.. Murmushi yayi yana fad'in nagode ya mai shari'a. Ina jinka Alhaji.
Alh. Kabir... Gaskiya tunda muke da Alhaji be tab'a fad'a mani yana da matsalar rashin haihuwa ba, asali ma duk lokacin da zaije wajen duba lafiyarsa tare muke zuwa, duk lokacin daya tashi zuwa asibiti baya yarda ya tafi da direba, ko bana gari yana hak'ura har na dawo domin muje tare, abu d'aya na sani shine yana fama da damuwa akan rashin haihuwa da Allah be basa ba, wannan dalilin ne yasa shi aure har mata ukku, domin munsha zuwa wajen likitoci daban -daban suna tabbatar mana lafiyarsa kalau kawai lokaci ne beyi ba, wannan dalilin ne yasa na bashi shawarar ya k'ara aure kila adace, sai gashi har Allah yayi masa rasuwa bai samu haihuwa ba, a daren ranar da zai rasu bana gari ina hanyar dawowa ya kirani, tabbas alokacin muryarsa cike take da farin ciki, duk da yana cikin hali na rashin lafiya hakan bai hana farin cikinsa bayyana ba, bayan mungaisa nake tambayarsa dalilin farin cikinsa, jin hayaniya ya gane ina tafiya hakan yasa ya kashe wayar yana fad'in idan na sauka zamuyi waya, bamuyi wayar ba har Allah ya d'auki ransa.
Brr. Ra'eez... Jinjina kai yayi yana fad'in mungode zaka iya tafiya. Juyowa yayi yana fad'in ina so nayima Hajiya Binta uwar gida ga marigayi tambaya. Hajiya Binta ta fito gaban kotu.
Brr. Ra'eez.... Hajiya ko kin tab'a zuwa asibiti aka gwadaki domin a tabbatar da lafiyar ki?
Hajiya Binta... Kwarai kuwa, ni da Alhaji munsha zuwa asibitin nan garin har ma da k'asar waje, duk inda mukaje amsar d'aya ce, matsalar tana wajen Alhaji, sun tabbatar mana bazai tab'a haihuwa ba, alokacin yaso mu rabu amma nace masa ban yarda ba, aurena dashi na saurayi da budurwa ne, ban damu da haihuwa ba matuk'ar muna tare dashi, alokacin na fad'a masa kada ya yarda da maganar likitoci domin ba maganar Allah bace, nice nayi ta bashi kwarin guiwa akan yayi aure kila adace, nayi mamaki da Alhaji Kabir yace wai sunje asibiti ance lafiyarsa kalau, kuma so da yawa Alhaji yana zuwa asibiti shida direba, dan haka maganar Alhaji Kabir ba gaskiya bace.
Brr. Ra'eez. Mungode zaki iya tafiya. Ina so nayima likitan daya tabbatar da awon cikin Amina tambayoyi. Likita ya fito gaban kotu.
Brr. Ra'eez.... Kai ne likitan Alhaji ko?
Likita... E nine.
Brr. Ra'eez.. Amatsayin ka na likitanshi ya akayi baka tab'a fad'a mashi bazai iya haihuwa ba tun yana da ranshi sai bayan mutuwarsa ne kayi rubutu sannan ka kawo kotu? Sannan ya akayi alokacin da ka auna Amina iya cikin kawai ka gani baka gano komai ba?
Likita... Hannu yasa yana goge zufar data zubo mashi kafin ya furta, iya abinda aka umarceni na auna kenan a kotu, kuma dana auna na kawo sakamakon a kotu. Maganar Alhaji kuma kasan ana son a b'oye sharri a bayyana alkhairi, Alhaji ya manyanta, bazaiji dad'i yaji cewar bazai tab'a haihuwa ba, yana matuk'ar son haihuwa har hakan ya jawo yayi aure har so ukku, ganin haka yasa na kasa fad'a mashi gaskiya har sai da buk'atar hakan ta taso a kotu.
Brr. Ra'eez... Amma gashi Babban aminin Alhaji ya tabbatar da sunje asibiti an tabbatar da lafiyarsa kalau.
Likita... E to, ai kasan ko wane likita da yanayin aikinsa, kowa yasan yanda muka dad'e da Alhaji, kuma Alhaji ya yarda da aikina, to bazanyi mamaki ba dan wani likitan yace lafiyar Alhaji kalau ba, domin koni abinda na fad'a masa kenan, kasan mu likitoci masu ceto ne, muna iya b'oye gaskiya domin farin cikin marar lafiyar mu, wannan dalilin ne yasa na b'oye masa gaskiya.
Brr. Ra'eez... Mungode likita zaka iya tafiya. Ya mai shari'a zan so nayima *IYA* mai aikin gidan Alhaji wasu tambayoyi.
A firgice Hajiya Binta ta mik'e tana fad'in ya mai shari'a Iya ta dad'e da barin gidan mu, tun kafin ya rasu muka nemeta muka rasa acikin gidan wai bazata iya cigaba da aiki agidan ba, yau kusan wata bakwai kenan da barin ta gidan.
Bubbuga tebur Alkali yayi yana fad'in ki kama bakin ki nan kotu ce ba kasuwa ba, dan haka kada ki sake magana idan ba kiranki akayi ba. Zama Hajiya Binta tayi tana goge zufa, kallon kishiryata Zainab kawai take, ita kuma ta kasa fahimtar halin da Hajiyar tashiga dan ankira Iya bayan tasan babu abinda ta sani Iyar tayi.
Brr. Ra'eez.... Iya ko zaki fad'ama kotu tsawon shekarun da kikayi agidan marigayi kina aiki?
Iya.... Gaskiya na dad'e ina aiki agidan Alhaji, tun bayan da Hajiya Binta ta cika shekara d'aya agidanshi tasa k'awarta ta samo mata mai aiki amma tafison Babbar mace, kuma bata son 'yar birni ta fison wacce za'a nemo a kauye, hakan yasa k'awarta taje har k'auyen mu da yake katsina wato 'Danja ta samo ni, tun daga lokacin na fara aiki agidan, sosai Hajiya take mani kirki, na d'auketa 'yar uwa, duk da na girmeta amma haka nake bauta mata, itama kuma tana bani hakki na sosai.
Brr. Ra'eez... Amma ya akayi aka wayi gari ba'a sameki agidan ba?
Iya.... Hannu tasa tana goge hawayen da suka zubo mata, kafin tace tabbas na cutar da Amina da Alhaji, nayi kuka wanda beda amfani, naso na nemi yafiyar Alhaji amma Allah be bani iko ba, abu d'aya nasan nayi mashi wanda idan na tunashi nake jin sauki. Kamar yanda na fad'a maka aiki nake ma Hajiya Binta, bayan shekara ukku sai Alhaji ya sake aure, sosai hankalin Hajiya Binta ya tashi, domin likita ya tabbatar mata bazata iya haihuwa ba, alokacin atare mukaje da ita, domin Hajiya ta aminta dani, lokacin da ta fad'a mani abinda likita ya fad'a sai tace na rufe maganar bata so kowa yaji. Bayan da aka kawo amarya Hajiya Zainab sai tazo ba kamar yanda mukayi zato ba, ta kasance mace mai kwantar da kai awajen Hajiya Binta, ganin