Advertisements
Chapter 13 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   13 / 54

36K to 39K   out of 160.3K words

so suyima Alhaji tambaya hakan be samu ba dole suka hakura.

***

Zaune suke a falo Alhaji yana kwance saman doguwar kujera zazzab'i ya rufeshi. Alhaji Mansur ne yasa Ladi ta had'o masa shayi dan Ummu tana zaune kusa dashi sai kuka takeyi, sosai hankalinta ya tashi da abinda aka fad'a mata.


Malan Sani yana gefe ya kalli Alhaji Mansur yana fad'in Alhaji yanzu shikenan haka zamu kyalesu an yanke ma Alhaji hukuncin zalunci? Alhaji Mansur yace Malan Sani najeriyar kenan, gashi dai munsan sharri ne aka kulla masa amma babu yanda zamuyi, domin sun fimu hujja, kasan ita kotu da hujja take amfani, duk wasu hujjoji da zasu tabbatar Alhaji ne ya d'auki kayan Alhaji Marusa sun gabatar dasu, babban abinda yasa suka k'ara cin galaba akan Alhaji shine samun kayan a gidanshi, amma dan sun gabatar da irin ginin da yayi wannan ba hujja bace, sunyi amfani da hakan ne dan su k'ara ma hujjarsu girma, amma bakomai, akwai Allah, kuma shi kad'ai ne zai bayyana gaskiya.


Ummun Ra'eez tace wallahi na tsani garin nan, bana son wannan aikin na Abbun Ra'eez, tunda abun ya fara zuwa da haka dan Allah Abban Labiba kasa baki ya aje masu aikin su yazo mu koma Kano mucigaba da rayuwar mu, sun fara neman kassarashi ta hanyar dukiyarsa da goga masa bakin fenti, nan gaba wallahi rayuwarsa zasu nema, bani da kowa saishi, idan suka rabani dashi ina zansa kaina.


Rungumeta Maman Rumaisa tayi itama tana kuka. Alhaji Mansur da jikinsa yayi sanyi ya kamo Alhaji Maiwada yana mik'a masa kofin shayin.


Amsa yayi ya shanye dan yunwa yakeji saboda beci komai ba. Komawa yayi ya kwanta yana runtse idonshi. Alhaji Mansur ne ya kamashi suka mik'e tsaye, kallon su Malan Sani yayi yana fad'in bara nashigar dashi ciki nayi waya da likitansa zaizo ya dubashi yana buk'atar hutu saboda jininsa yana iya hawa.



Tashi Ummu tayi tana fad'in ko zaiyi wanka? Alhaji Mansur yace aa abarsa yayi bacci. Ciki suka nufa wani d'aki da yake ak'asa. Bayan sun kwantar dashi wayar Alhaji tayi k'ara, Alhaji Mansur ne ya duba sai ya ga likitan ne, fita yayi yana fad'in bara nashigo dashi.


Bayan ya gama dubashi ya bashi magunguna yayi masa allurar bacci, cikin lokaci kad'an bacci ya d'aukeshi. Fitowa sukayi likita yana fad'in jininsa ya hau, dole ya samu bacci mai yawa hakan zai taimaka masa. Godiya sukayi masa ya tafi.


Kallon Ummu Alhaji Mansur yayi yana fad'in ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru, abarshi ya samu hutu zuwa gobe zamuyi maganar. Ummu tace mungode Abban Labiba, kashiga ga d'akin baki can ka huta Ladi ta kai maka abinci. Jinjina kai yayi ya nufi wajen Malan Sani.


Bayan yayi masa bayanin da likita yayi masa Malan Sani yace shikenan abari zuwa goben sai muji abinda za'a yanke. Sallama sukayi masu suka tafi. Alhaji Mansur ya nufi d'akin da aka saukeshi.


***

Dariya ce take fitowa daga harabar gidan Alhaji Marusa inda suke hutawa, Mr. Kallah ne sai Brr. Barau, Adebayo, Umar sai Alhaji Marusa a zaune, daga gefe guda wasu manyan maza ne sunci sun k'oshi, fuskarsu babu alamun fara'a, d'aya daga cikinsu Peter ne, sai abokinsa na hannun damarsa.


Lemu Mr. Kallah ya kurb'a yana fad'in gaskiya Alhaji Marusa wannan karon bansan dame zan saka maka ba, rabon da muyi irin wannan samun har na manta, kodan an dad'e ba'a samu masu irin halin Alhaji Maiwada ba? Dariya Alhaji Marusa yasa yana fad'in ai dama haka irinsu suke k'arewa, yanzu gashinan ya rasa kimarsa, zai rasa dukiyarsa abanza, kaga mu gaba ta kaimu, wata kilama hukumar ku ta dakatar dashi.



Mr. Kallah yace baza'ayi haka ba, kasan dan an kama mutum da laifi so d'aya ba'a saurin dakatar dashi, tunda dai nasan abinda ya faru bazan bada goyon baya a dakatar dashi ba domin ya bani tausayi zafin zaiyi masa yawa, amma ranar litinin zan koma aiki hutuna ya k'are, zamu tattauna dole aja masa kunne kuma ya tsaya a aikinsa ya bar masu kula da sauran wajen suyi nasu aikin, idan ya kama dole saiya duba abu sai yaje amma ya tsaya a inda ya kamata.


Adebayo yace Wallayi Sir da an canza manashi kawai. Mr. Kallah yace kada ka damu da kanshi zai nemi canjin wajen aiki, yana nema kuma zamu masa sai mu kawo wanda mukeso. Umar yace shikenan ma mun huta.


Alhaji Marusa yace idan komai ya kammala kowa zaiji sak'o a asusunsa, Peter kunyi kok'ari dole wannan karon ku samu k'ari. Murmushi Peter yayi yana fad'in mungode Oga. Haka suka cigaba da tattaunawa suna shagalinsu.


***

*Alhaji Marusa da Mr. Kallah*, *menene labarin asalin su*?


Ur's.
Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*



1⃣2⃣


*Alhaji Job'e Marusa* d'an asalin garin *Mayo Barwa* ne, cikekken bafullata ni ne, duk cikin zuri'arsu shi kad'ai ne yayi karatun boko, shima wani Yayan Mahaifinsa *Bukar* ne ya d'aukeshi ya koma wajensa da zama a kudu, sana'ar Yayan Mahaifinsa shine siyar da Fata, babban dila ne kuma hamshakin mai kud'i ne, be tab'a haihuwa ba hakan yasa ya d'auki Alhaji Marusa ya koma dashi gidansa.


Baffa Bukar yana da mugun son kanshi, daga matansa sai masu masa fadanci kawai yake sakar ma bakin aljihunsa, sannan mugun mutum ne, sam baya so yaga wani ya fishi, zai iya kashe rai akan abun duniya, kuma be yarda da asara ba, zamansa a kudu ya k'ara masa rashin imani, yana da babban matsafi wanda yake masa aiki, yafiso akoda yaushe ya kasance shine a sama.


Haka Alhaji Marusa ya taso duk wani bakin hali na Baffansa ya d'aukeshi, a k'asar waje yayi karatunsa acan ya kara koyo mugayen halaye, sam ibada bata dameshi ba sai yaga dama, hatta da azumi ciyarwa yakeyi wai ulcer yake da ita.


Bayan daya kafu da kanshi sai Baffansa ya basa babban jari ya fara shigo da kaya daga k'asashen waje, cikin lokaci k'ank'ani Allah ya bashi abinda yake nema, hakan yasa ya tashi ya koma Lagos da zama, gidan da yake zaune kanshi abun kallo ne, domin shine ake kira da Aljannar duniya, dan Alhaji Marusa mutum ne mai son jin dad'i.


Wani zuwa da yayi k'asar waje acan ya had'u da wani abokinsa da sukayi karatu mai suna *Herry*, bature ne, sana'arsa siyar da miyagun k'wayoyi, bayan daya samu labarin Alhaji Marusa yana kasuwancin kai kaya k'asar najeriya sai ya bashi shawarar ya fara siyar da kwayoyi zaici riba sosai.


Jin harkar k'aruwa yasa Alhaji Marusa ya amince, nan ya fara saka miyagun kwayoyi acikin kayan da yake shigo dasu, yana shigo da shaddodi, su taliya da sauran kayan masarufi, acikin kwalayen ake saka miyagun kwayoyin ta yanda za'aga kamar kayan gaskiya ne a ciki, hakan yasa da wuya a kama kayan Alhaji Marusa da laifi, musamman da yake saye manyan kwastam da k'ananan su.


Sam beda matsala da bodar Lagos shiyasa yafi son shigo da kaya tanan, matarsa d'aya da yaransa biyu yasa aka cire mata mahaifa dan baya son haihuwa, ko kauyensu baya zuwa sai dai yayi masu aike, haka baya son wani nashi yazo inda yake, danshi be yarda da jininsa ba yafi son mutanan gari, acewarsa besan su ba idan sukayi masa abu zai iya masu rashin mutunci.


Brr. Barau tun yana k'aramin lauya yake masa aiki har ya zama babba, ya kware a harkar aikinsa, domin Allah yayi masa wata baiwa, ya iya tsara zance, idan yaso maida k'arya gaskiya babu wanda zai iya gano gaskiya, hakan yasa yayi saurin d'aukaka domin lauyen manyan mutane ne.


Zuwan Alhaji Maiwada bodar Lagos yasa Alhaji Marusa ya fara sanin meye damuwa akan shigo da kaya, gashi Baffansa ya jima da rasuwa da tuni ya kai sunan Alhaji an d'aure bakinsa, ganin zai caza masa kai yasa ya had'a masa wannan sharrin.


Shi da Mr. Kallah aminan juna ne, sunfi shekara goma sha atare, kowa yasan sirrin kowa, kuma Mr. Kallah shine yake goya masa baya a duk wani abu da zaiyi.

***

*Garba Bala* shine asalin sunansa, bamaguje ne daya fito daga garin *Malumfashi* cikin kauyen *K'afur*, yayi karatun boko sosai, yana da masifar kok'ari, ya rik'e muk'amai da yawa daga baya ne ya maida sunansa *Mr. Kallah*, idan ka ganshi bazaka tab'a cewa bamaguje bane, zaka masa d'aukar cikekkan musulmi, hausa abakinsa dama gadonsa ce, domin kowa yasan yanda maguzawa suke jin hausa, rashin hasken musulunci daya rasa shine ya banbantasa da musulmai, amma acikinsu yake komai, shigarsa da mu'amalarsa duk irin na musulmai ne.


Mr. Kallah yana da son kud'i, matuk'ar zaka yaga masa zai iya tsaya maka, sai dai yana da matuk'ar wayau, domin shi mutum ne mai aiki da kwakwalwa, duk yanda zaiyi abu baya bari aganosa, shiyasa a zahiri mutane suke masa kallon mai gaskiya da amana, wannan halin nasa yaja masa k'arin matsayi sosai, wanda a yanzu haka shine shugaban kwastam na k'asa, a Abuja yake zaune da matarsa ta farko, matarsa ta biyu kuma tana Lagos, gidansa na Lagos babban gida ne, waje guda ya ware ya gina katafaren ofis, idan yazo hutu anan yake aikinsa danshi mutum ne wanda baya son zaman banza.


Duk wani mai kasuwanci matuk'ar yana shigo da miyagun kaya to yana da alak'a da Mr. Kallah, saboda yana goya masu baya yasa suke cin karensu babu babbaka, sai wanda yaso yake ma k'arin matsayi, idan kuma yaga baka binsa yanzu zai canza ka da wani. Alokacin da aka kawo sunan Alhaji Maiwada akan abashi shugaban kwastam na lagos yaso ya hana saboda yasan halinshi, amma gudun maganar mutane yasa ya amince dashi, sai gashi yazo yana caza masu kai.


Wannan shine labarin *Mr. Kallah* da *Alhaji Marusa*


***** *****


Washe gari Alhaji Maiwada ya tashi da k'arfinsa, domin yaji sauki sosai, zugin da yake ji a zuciyarsa ma yayi sauki sai damuwar da baza'a rasa ba, bayan da likita yazo ya aunashi yaga jinin ya sauka.


Zaune suke a falo bayan sun gama karyawa. Alhaji Mansur ne ya kalli Alhaji yana fad'in naji dad'i dana ganka katashi ahaka yau, dama kuma haka akeson bawa ya kasance mai tawakkali da yarda da K'addara, Alhaji nafi kowa saninka, nasan abinda zakayi da wanda baza kayi ba, kada ka damu da kallon da mutane zasuyi maka, Allah yasan baka aikata abinda akace ba, kuma shine zai saka maka akan zaluncin da akayi maka, dan haka kada kasa damuwar komai aranka, ka d'auka wannan dukiyar Allah ne ya baka kuma gashi zai amshe abunsa, dan haka kada kaji komai zamu biyasu abinda kotu tace, insha Allahu sanadiyar wannan kud'i da zaka basu sune zasu zamo silar lalacewar tasu dukiyar.


Hannu yasa a aljihu ya ciro wata takarda, bud'eta yayi yana fad'in d'azu aka aikota daga hannun kwamishna, sunzo sai suka ba Madu, iya yawan kud'in da za'a biyasu ne aka rubuta aciki, kuma wata guda suka bada idan yacika ba'a basu ba zasu amsa da kansu.


Naira miliyan saba'in yace ya kashe akayan da suka b'ace hada kud'in daya kashe na zuwansu nan. Aje takardar yayi yana dafe kai. Murmushi Alhaji Maiwada yayi yasa hannu ya d'auki takardar yana kallo. Kuka kawai Ummun Ra'eez takeyi jin makudan kud'in da zasu biya.


Gyara zama Alhaji yayi yana fad'in Alhaji Mansur zansa wannan gidan nawa akasuwa. Da sauri Alhaji Mansur ya kalleshi jin abinda ya fad'a. Jinjina kai yayi yana fad'in wallahi gidan nan ya fitar mani arai, da nasan gina gidan nan zai jawo mani irin wannan zargin bazan tab'a ginashi ba, dama na ginashi ne saboda muji dad'in rayuwa nida iyali na, sai gashi hakan ya jawo mana tashin hankali, da zan samu wanda zai bani kud'in gidan nan ayanzu wallahi bazan sake kwana aciki ba.


Girgiza kai Alhaji Mansur yayi yana fad'in baza'ayi haka ba, dama abinda suke so kenan su rabaka da wannan gidan, idan sukaga kasa shi akasuwa burinsu zai cika, dan haka bazaka siyar dashi ba, zamusan yanda za'ayi.


Murmushin takaici Alhaji Maiwada yayi yana fad'in kayi hakuri Alhaji Mansur, ina d'aukar shawarar ka, amma a wannan karon ko Alhajina ne yace kada na siyar da gidan nan bazan jishi ba, kwanciyar hankalina shine nabar gidan nan, na ciresa araina hakan zaisa na samu natsuwa.


Cikin kuka Ummun Ra'eez tace dan Allah Abban Labiba ka barsa ya siyar dashi, kasashi ya aje har aikin mu koma kano da zama wallahi bana son garin nan. Hannu Alhaji yasa ya kamo hannunta yana fad'in kada ki sake fad'ar haka Bilkisu, idan na aje aikina kamar ban yarda da k'addara bane, kuma zuciyarsu zatayi sanyi tunda sun sa na aje aikina, idan kinga na bar aikina to takardar sallama aka bani, amma matuk'ar basu bani ba to mutuwa ce zatasa nabar aikina sai kuma idan lokacin aje aikin yayi, dan haka matuk'ar kina sona ki tayani cin wannan jarabawar da Allah ya d'ora mani.


Jinjina kai tayi tana goge ido tace shikenan Abbun Ra'eez, na amince ka siyar da gidan, ina maka addu'a akan Allah yayi maka sakayya akan zaluncin da akayi maka, kuma ya baka ikon cigaba da aikin ka.


Alhaji Mansur yace amin, nima na amince da abinda kace, bakomai Allah ya shige mana gaba. Alhaji Maiwada yace amin, ka kira DPO ka sanar masa zan siyar da gidana, nasan Alhaji Marusa ne zai siyeshi kaga sai ya fad'a masa, akira dillalai suzo suyima gidan kud'i, idan na biyasu zan sayi wani gidan sai mu koma can da zama.


Kwalla Alhaji Mansur ya goge yana fad'in Allah ya saka maka. Alhaji yace amin.


**** ****


Cikin kwana biyu aka gama komai, dillalai suka yima gida kud'i akan naira miliyon d'ari biyu, tayin farko wanda Alhaji Marusa ya aiko yace ya siya, haka aka gama komai aka mik'a masa takardun gida shedu suka sheda, dama acikin kwana biyun Alhaji ya kwashe kayansa, a unguwar *APAPA* ya samu wani gida mai kyau kuma aka sayar masa akan naira miliyon tamanin, nan take ya amince.


Bayan da aka mik'a masa kud'insa agaban 'yan sanda da hukumar bincike sukaje shida Alhaji Mansur da Malan Sani suka biya Alhaji Marusa naira miliyon saba'in da biyar da ya buk'ata, bayan da aka gama cike-cike suka bar wajen.


Kud'in gidansa ya biya sauran kud'in yasa a banki. Alhaji Mansur gudummuwar milayan d'aya ya bashi amma da kyar ya amsa, haka abokinsa Alhaji Usman wanda ya tab'a kwatoma kayansa shima sai da ya bashi dubu d'ari biyar, haka mutanan da suke mutunci suka rik'a kawo masa gudummuwa.


Bayan sun maida kayansu zuwa sabon gidansu suka gyara ko ina, gida ne mai kyau, sai dai ba me bene bane, bangare biyu ne, wanda d'ayan bangaren yake kamar d'akunan maza, sai babban b'arin mai d'auke da babban falo, sai kicin mai had'e da sito, sai wani d'aki akusa da kicin mai d'auke da band'aki wanda yake amatsayin na masu aiki, daga can kuma zaka shiga wata hanya mai d'auke da d'akuna biyu dukkansu da band'aki aciki, wannan shine b'angaren matar gidan, daga gefen falo akwai d'aki wanda shine na maigida, sai wajen teburin cin abinci. Daga waje kuma akwai d'akin mai gadi sai harabar gida da wajen aje motoci sai rumfa.


Sosai Ummun Ra'eez taji dad'in gidan dan ya burgeta, haka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki duk damuwar da take ciki sai ta tafi. Haka suka gyara komai dama gidan besha wahala ba, Ladi tasa kayanta a d'akin ta, kayan Ra'eez kuma aka aje masa a d'akin da yake na kusa da Ummunsa.

**

Bayan kwana biyu Alhaji Mansur yayi masu sallama ya koma yana mai sake kwantar ma Alhaji Maiwada da hankali, haka ya tafi cike da tausayin abokinsa.



Malan Sani yaji dad'i da suka samu gida a wannan unguwar saboda baya so ace sun bar unguwa mai kyau sun koma marar kyau, sai gashi itama wannan d'in tana da kyau.


Tunda wannan abu ya faru Alhaji be lek'a ofis ba, yana jiran yaji halin da yake ciki, babu inda yake zuwa sai masallaci, sosai hankalinsa ya kwanta dan ya dage da addu'a hakan yasa Allah ya yaye masa damuwar da take ransa yasa masa dangana, duk yanda yake tunanin mutanen gari zasu yaya tashi sai Allah ya kwantar da abun, wanda ba haka su Alhaji Marusa suka so ba.


Suna kwance ad'aki ya samu kira daga Mr. Kallah, bayan sun gaisa ya sake jajenta masa akan abinda ya faru, anan yake fad'a masa gobe ana nemansa a can abuja. Alhaji Maiwada yace nagode kuma zan zo akan lokaci. Sallama sukayi ya kashe wayar.


Ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in ya Allah ka zab'a mani abinda yafi alkhairi akan wannan aikin. Hannunsa Ummu ta kamo tana fad'in nemanka ake ko? Kai ya d'aga mata. Murmushi tayi tana fad'in nasan

13 / 54