Advertisements
Chapter 45 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   45 / 54

132K to 135K   out of 160.3K words

wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*



4⃣3⃣


Haka Alhaji M. Sanda yayi ta zagaye a d'akinshi sam ya kasa kwanciya, duk bayan mintuna sai ya kira Lucky amma amsar d'aya ce ba'a dace ba, dole tasa ya hak'ura ya kwanta ranshi a b'ace.


**** ****

Milo kaga abinda nake fad'a maka ko, nace maka Dady yace kada na fita amma kace na fito gashinan an kama mu, gara kai nasan sakin ka za'ayi ni ko kamani zasuyi zuwa kotu kuma kashe ni za'ayi.


Milo yace yanzu meye amfanin b'oyewar, ko ka tafi idan aka gano kana da laifi ko birnin sin kaje kotu tana da ikon maido ka, shawarar da zan baka kawai kaje ka fad'i iya abinda ka sani zaifi maka.


Hawaye ne suka zubo ma Fawwaz yace yanzu Milo kaine kake bani shawarar naje akashe ni? Dafashi Milo yayi yana fad'in ka fahimce ni abokina, wallahi ban tab'a jin na tsani rayuwar da nakeyi ba sai yanzu, tunda ka bani wannan labarin hankalina ya tashi, ayanzu da ka fad'a mani shari'ar da za'ayi sai nayi nadamar abubuwan dana aikata, kuma insha Allahu daga yau na bar shirmen da nakeyi, shaye-shaye kuwa dole zan barshi domin shine yake samu aikata sauran laifukan.


Kwanciya Fawwaz yayi yasa kuka. Matsowa Milo yayi yana rarrashinsa tare da kwantar masa da hankali.


**** ****

Wajen k'arfe goma motar su Alhaji Marusa ta shigo cikin gidanshi, masu aikin gidan ne suka zo suna masa sannu da zuwa, Mr. Kallah ne ya bud'e mashi mota ya fito tare da sandar da yake dogarawa, duk ya rame sai dai yayi haske.


Har cikin falonshi suka rakashi shida Alhaji Barau dan shine ya d'auko su. Ruwa Mai aikin gidan ta kawo masu, bayan ta aje ta duk'a tana sake gaishe su tana tambayar mai jiki.


Alhaji Marusa yace ina Hajiya fa na kira wayarta akashe? Mai aikin tace ai Hajiya bata da lafiya jiya sai wajen k'arfe d'aya muka dawo daga asibiti dan tace bata son kwana acan shine aka sallameta amma tana can kwance tana cikin ciwo ko magana batayi sai kuka.


Alhaji Marusa yace meya sameta ne? Wallahi ina aiki kawai naji ihunta, kafin nazo na iske ta suma, haka na kira sauran muka kaita asibiti, sai dai lokacin data farfad'o tasa kuka tana fad'in wayyo kud'inta tana kuma kiran sunan Nuress.


Alhaji Marusa yace to Allah ya kyauta, idan na huta na shiga. Da sauri Alhaji Barau yace ba haka za'ayi ba, kana ji fa tace tana ambaton kud'i hada sunan namiji, ke wanene Nuress? Wiki wiki mai aikin tayi da ido.



Alhaji Barau yace magana zakiyi dan musan abinda yake faruwa, domin daga bayanin ki na fara fahimtar bakin zaren gara ma ki fad'i abinda kika sani ko nasa a kulle ki.


Mr. Kallah yace wai Alhaji Barau ina ruwanka, wannan fa maganar cikin gida ce. Alhaji Marusa yace barshi yacigaba nima naji ina son naji komai. Mr. Kallah yace kasan fa ba wata lafiya kake da ita ba meyasa zaka damu kanka.


Alhaji Marusa yace muna jinki. Kai a k'asa ta fad'a masu waye Nuress har zamanshi a gidan bayan tafiyarsu da irin alak'ar da sukeyi da Hajiya, sai dai batasan abinda ya had'asu ba.



Mamaki sosai ya kamasu Alhaji Barau, Alhaji Marusa kuwa murmushi ya saki yana fad'in ashe dai maganganun da ake fad'a mani gaskiya ne nine ban yarda ba, lallai Karimatu kin cika butulu, koda yake dama ai nasan za'a rina dama can butulu ce ita, shikenan tayima kanta domin ni mace bata isa ta sani damuwa ba, abu d'aya ne zan rasa nashiga tashin hankali shine kud'i domin sune nasa araina fiye da komai, ko Marwan da naji yaki tsayawa yayi jinyata banji haushi ba, domin dama can ban sasu araina ba dan nasan zasu iya sani ciwon kai.


Mr. Kallah yace baza'ayi haka ba Alhaji, yakamata kaji abinda ya faru domin ka taimaka mata, muna can fa take fada maka kayanta sun salwanta, kaga kila shima yaron yaudararta yayi.


Tsaki Alhaji Marusa yayi yana fad'in wallahi babu abinda zan mata, kai na saketa ma saki ukku tazo ta barmin gidana bana buk'atar ta ayanzu.


Alhaji Barau zeyi magana sukaji an saki kuka, ganin Hajiya sukayi ta shigo tana takawa da kyar, dama daurewa tayi jin ya dawo tazo tayi masa sannu da zuwa.



Cikin sauri ta shigo tana fad'in Alhaji ka rufa mani asiri, wallahi zan shiga damuwa idan ka rabu dani, duk tarin kud'in da kake bani ban tab'a tunanin siyen kadara ba, abu d'aya nasan ina tarawa sune gwalagwalai, sai kuma kud'ad'e da nake ajewa a banki suma na kwashe su na saro kaya gashi nayi asara, sauran kud'in kuma an sace su da gwalagwalai na, ga Marwan jami'an Madina sun kamashi da kayan kwayoyi yana can dama jiran dawowar ka nakeyi, dan Allah ka rufa mani asiri wallahi sharrin shed'an ne, gaba d'aya Nuress ya takaitani.


Shiru sukayi suna kallonta da jin irin abinda take fad'a. Alhaji Barau yace to a ina za'a samu shi Nuress d'in? Cikin kuka take fad'in nima ga sakon daya rubuto mani nan, ashe d'aukar fansa ce ta kawoshi waje na......


Tsab ta fad'a masu abinda ya faru. Shiru wajen yayi sai sautin kukanta. Alhaji Marusa ne yayi gyaran murya yana fad'in wallahi da zanga wannan yaron sai nayi masa babbar kyauta, wannan yaro shi ake kira da d'an halak, kuma yayi dai-dai, to bari kiji, wallahi babu wanda zai b'ata lokacinsa wajen tayaki nemoshi, kema yanzu ba anjima ba zaki bar mani gidana, suturarki kad'ai zaki d'auka amma ko mota bazaki d'auka ba wallahi, taimako d'aya zansa direba ya kaiki tasha zan baki kud'in mota kitafi, dama bakizo da komai ba.


Ihu tasa tana fad'in Alhaji kodan Yaranmu da suka girma kada kamun haka wallahi zan gyara, idan ma ka sake ni naji ka barni nayi zaman yarana.



Tsaki yayi yana fad'in ni yanzu yaro d'aya nake dashi domin nasan Marwan tashi ta k'are dan saudiya hukuncin kisa suke ma duk wanda suka kama yana siyarda miyagun kaya, ni ko wallahi bazan b'ata kwabo na wajen amsoshi ba, shima Khalil idan ya dawo to, idan kuma ya zauna acan zan cigaba da kula dashi.


Alhaji Barau zeyi magana yayi saurin tashi yana kwalama direba kira, kallonta yayi yana fad'in na baki mintuna ashirin, idan baki shirya ba zaki tafi haka. Jiki na rawa tayi saurin tashi dan tasan halinshi.


Haka taje ta had'a kayanta kusan akwati bakwai, sai kuka takeyi, Nuress ya cuceta, amma tasan alhakin Hambali ne, ashe dama irin wannan rayuwar zata risketa, yau kusan shekaru talatin da wani abu tana cikin jin dad'i amma rana d'aya komai ya tafi, sam bata tab'a tunanin ta gyara gidansu ba, batayi tunanin ta taimaki wani nata ba, asalima bata cika zuwa gida ba, sai tayi shekara bata leka ba, idan taje ma bata wuce kwana biyu, shima har ta baro gidan bata cin komai na gidan, gashi yanzu zata koma can da zama.


Haka ta fito masu aiki suka d'aukar mata kaya sai kuka takeyi. Dubu hamsin Alhaji Marusa ya bata, Mr. Kallah ya ciro tubu talatin ya k'ara mata yana bata hakuri, Alhaji Barau kuwa wajen ya bari yana yamutsa fuska.



Bayan sun tafi Mr. Kallah yace Alhaji ya za'ayi da Marwan? Alhaji Marusa yace Allah yaji k'ansa, yanzu ta Khalil nake kuma kada ku sake tuna mani dashi. Mr. Kallah yace kada kace haka.... Hannu ya d'aga mashi yana fad'in dan Allah.


Kai Mr. Kallah ya jinjina yana fad'in muje ciki kayi wanka ka huta zamu wuce. Hannu ya mik'a masu yana masu godiya. Alhaji Barau yace zan wuce dan tun d'azu Alhaji M. Sanda yamun waya yana nemana sai munyi waya. Godiya yayi masu suka wuce.


**** ****


Ido awaje Alhaji Barau yake kallon Alhaji M. Sanda jin abinda yake fad'a. Hannu yasa ya goge zufar data zubo mashi yana fad'in Lucky d'in yace basu ganshi ba? Alhaji yace har yanzu babu labari.


Gyara zama Alhaji Barau yayi yana fad'in ana wata ga wata, nasan dole su Ra'eez ne zasu sa a d'aukeshi, yanzu ya zamuyi? Alhaji yace nasan Fawwaz bazai tab'a amsa laifinsa ba, kai kuma ina so kayi saurin yanke hukunci da zaran Fawwaz yaki amsa laifinsa shikenan magana ta wuce, domin dole jawabinshi ne kad'ai zai tabbatar da gaskiya, nasan kuma bazai fad'i gaskiya ba, kaga babu Adnan, babu Alhaji Sulaiman, kuma su kad'ai ne suka san gaskiya, kai ko suna nan basu da hujja ahannu iyakarta abaki, kotu kuma da hujjar zahiri take amfani, sannan kuma basu kai su ukku ba.


Ajiyar zuciya Alhaji Barau yayi yana fad'in hakan ma yayi kuma yasa naji sauki, gara ma Fawwaz d'in yaje kotun hakan zaisa kowa ya yarda dashi tunda bazai fad'i gaskiya ba.



Alhaji yace magana ta wuce, anjima zanje na duba Alhaji Marusa, bazan sake damuwa akan a nemoshi ba, mubarshi yaje kotun ba shikenan ba. Alhaji Barau yace haka ne. Sallama yayi mashi ya fita.


**** ****

Rumaisa leka naji ana sallama. Fitowa Rumaisa tayi tana amsawa, cike da mamaki take kallonta. Murmushi Raheena tayi tana fad'in K'anwarmu ko na koma? Murmushi Rumaisa ta saki tana fad'in kishigo mana.


A falo ta zauna, fita tayi ta kawo mata ruwa tana fad'in sannu da zuwa. Raheena tace kin ganni ko azahar ban bari tayi ba, dole tasani fitowa tun d'azu ma naso zuwa naga safiya tayi da yawa shiyasa na daure har shabiyu tayi.


Rumaisa tace amma Yaya besan zaki zo ba ko? Raheena tace shine ma silar zuwana, kwana biyu idan nakirashi baya d'auka, duk da nasan yana kan aiki ne amma ko beje ba ai sai muyi waya ko.


Murmushi Rumaisa tayi tana fad'in sosai kuwa. Mama ce tashigo da sallama, saurin risnawa Raheena tayi tana gaisheta. Amsawa Mama tayi cikin sakin fuska, fita tayi ta basu waje.


Ganin sunyi shiru Rumaisa tace Aunty bara naje na d'ora abincin rana kada na bar Mama da aiki, kiyi kallo kafin na gama. Tashi Raheena tayi tana murmushi tace haba muje muyi aikin tare. Rumaisa tace ki barshi zanyi. Wucewa tayi tana fad'in Allah tare zamuyi. Fita Rumaisa tayi tana mamkin karfin halin Raheena, dole haka suka had'u sukayi aikin, Mama kuwa tausayin Raheenar ma takeji.


**** ****


Shiru sukayi suna jiran fitowar likita daga d'akin gwajin da aka shigar da Ummu, Ra'eez addu'a kawai yake Allah yasa Ummunsa ta samu sauki. Jabeer ne ya dafashi yana fad'in insha Allahu zata samu sauki.


Fitowar likita yasa su saurin tashi. Hannu ya mik'a ma Alhaji Mansur suka gaisa. Kasa hakuri Ra'eez yayi yana fad'in an dace likita? Zama yayi yana murmushi, gaba d'aya suka zauna suna kallonshi.


Takardar da take hannunsa ya kalla yana fad'in da farko zan fara da godema Allah, domin shine mai kwantarwa kuma ya tayar, Alhamdulillahi Allah shine abin godiya, yau kam Allah ya kawo mana saukin al'amauran da suka shige mana gaba, acikin mutane goma da aka d'aukesu a wannan asibitin a shekarar 2008 tare da Hajiya yau Allah ya nufa itama ta samu lafiya kamar yanda biyar daga cikinsu tuni an sallamesu.


Cikin farin ciki Ra'eez ya zube k'asa, goshinsa ya kai yana mai sujudar godiya ga ubangiji. Gaba d'ayansu kallonshi sukayi cike da tausayi. 'Dagowa yayi yaje ya rungume likita yana hawaye.


Alhaji Mansur yace ai babu sauran kuka kuma sai farin ciki, gaskiya nayi matuk'ar farin ciki, likita babu abinda zamuce maka sai godiya kai da Alhaji Usman, hakika kun bada gudummuwa akan Hajiya Bilkisu, Allah ya saka maku da alkhairi.


Zama Ra'eez yayi yana fad'in amin Abbah, wallahi na rasa bakin godiyar ma. Likita yace ai kayi abinda akeso, domin wannan sujadar da kayi ta wadatar, sai kuma aje ayi sadaka.


Jabeer yace wannan kam kullun cikin yinta akeyi, amma dole ta yau ta zama ta musamman. Alhaji Mansur yace ya jikin nata yanzu? Likita yace babu abinda yake damunta yanzu sai rashin kwarin jiki, ina ganin nan da juma'a zaku iya tafiya da ita, dalilin da yasa nace zan riketa anan nafison ku kammala wannan shari'a hankalin ku zaifi kwanciya, kafin nan ta k'ara warwarewa.


Ra'eez yace yanzu zamu iya ganinta? Kai likita ya d'aga yana fad'in kaje ka ganta idonta biyu. Hannun Jabeer yaja sukayi waje da sauri. Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in bawan Allah, koba komai yanzu zaiji sanyi a ziciyarshi. Likita yace sosai ma.



A hankali ya tura k'ofar d'akin, Ummu tana kwance tayi saurin tashi tana kallon Ra'eez, cikin sauri yaje ya shige jikinta yana sakin kuka. Rungumeshi tayi itama hawaye suka zubo mata, duk da iya abinda ya faru alokacin da Malan Sani yazo kawai zata iya tunawa amma tasan tabbas wani abu marar dad'i ya faru da Abbun Ra'eez.


Shigowar Alhaji Mansur yasa suka nutsu. Zama yayi yana fad'in Ra'eez kai da zaka kwantar mata da hankali shine zakasa mata kuka. Murmushi yayi yana goge idonshi.


Kallon Ummu yayi yana fad'in sannu Hajiya Bilkisu, Allah ya k'ara lafiya yasa iya wahalar kenan. Murmushi tayi tana amsawa, tana son ta tambayeshi amma kawaici ya hanata.


Kamar yasan abinda take tunani yace abinda nakeso dake kisa aranki kome ya faru muk'addari ne daga Allah, nasan akwai tarin tambayoyi a zuciyar ki, amma ki sani yanzu ne kika warke daga ciwo, kuma ciwonki yana buk'atar natsuwa domin abu ne daya had'a da kwakwalwa, dan haka ki adana tambayoyinki insha Allahu ranar juma'a idan muka koma gida zakiji komai, amma inaso kisa jarumta aranki, sannan ki godema Allah bisa baiwar da yayi maki na baki lafiya da yayi.


Kai ta jinjina tana kok'arin maida kwallar idonta. Tashi yayi yana fad'in bara naje Alhaji Kamal yana jira na, Ra'eez ku dawo gida dawuri saboda an kawo wannan sakon na Kano ina so mu bincikeshi. Kai Ra'eez ya d'aga.


Tashi Jabeer yayi yana fad'in bara na koma wajen aiki kai ka zauna anan. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in nagode. Haka suka fita suka barsu, gyara zama Ra'eez yayi yashiga bama Ummu labarin karatunshi.


**** ****


Yauwa kana ji na ko, kada ka bari su b'ace maka gani nan zuwa, inaso kayi amfani da hankali kasan manyan 'yan fashi ne zasu iya gane kana binsu, shikenan gani nan zuwa.


Cikin mintuna ashirin Hamza ya isa bayan gari, da sauri d'an sandan ya fito daga inda ya b'oye. Hamza yace yauwa sannu Hassan ina ne suka shiga? Hassan yace cikin wancan lungun naga sun shige, sai dai su biyu ne kawai.


Hamza yace kai da sauran ku biyo ta baya, ni kuma zan shiga ta gaba amma kuyi ahankali. Su ukku suka zagaya ta baya yayin da Hamza yawuce ta gaba.



Ruwa suka watsama Adnan wanda yake a sume saboda tsab'ar kishir ruwa da wahalar d'aurin da akayi masa, Abban Nabeel yana d'aure a saman kujera cike da tausayin Adnan, saboda sunfi bashi wahala shi a zaune yake kan kujera yayin da Adnan yake d'aure atsaye, sannan shi Abbah ana bashi abinci da ruwa amma basa bama Adnan.


A firgice Adnan ya farka yana sakin ajiyar zuciya. Abbah yace haba bayin Allah wace irin zuciya ce da ku, idanshi Ogan ku beda d'igon Imani da hasken musulunci ai ku musulmai ne, meyasa zaku biye mashi bazaku bama wannan Yaron ruwa yasha ba, ko babu abinci ai zai iya rayuwa da ruwa.


Dariya d'aya daga cikinsu yasa yana fad'in idan baka sani ba kome mukeyi Oga Lucky yana kallon mu a gidanshi, ko baya zaune yana zuwa zai kunna yaga abinda ya faru, idan ma mun kashe kemarar zai gane, dan haka bazamu b'ata aikin mu ba saboda kud'i muke so.


'Dayan zeyi magana yaji saukar k'asan bindiga akanshi, k'ara ya saki ya zube a sume, rarumar bindiga d'ayan yayi amma Hamza yarigashi kwad'a masa sanda, fad'uwa yayi yana nishi, saurin shigowa su Hassan sukayi, kama su sukayi suka d'aure suka fita dasu.


Saurin kwance Adnan da Abbah Hamza yayi, sai dai tuni Adnan ya faad'i saboda babu kwari ajikinshi. Ruwa Hamza ya d'auko ya kamoshi, saurin amsa yayi ya fara sha, yana gama sha ya fara amai. Abbah yace muyi saurin barin wajen nan domin Ogansu zai iya zuwa dan yana ganin duk abinda akeyi. 'Daukar Adnan Hamza yayi sukayi saurin barin wajen.


**** ****


Ra'eez goge flash d'in kafin ka saka shi nasan yayi kura, Ra'eez yace Jabeer wurgomun gashinan gefen ka, d'aukowa Jabeer yayi yana fad'in bara muga ka iya kwallo.


Murmushi Rafeek yayi yana fad'in duk wanda yayi makaranta ai ya iya buga kwallo sai dai matsoraci. Wurga masa Jabeer yayi yana dariya, hannu Ra'eez yasa zai cab'e sai dai bezo a dai-dai ba sai ya fad'a k'asan gado.


Alhaji Mansur yace lallai Ra'eez beyi kwallo ba. Ra'eez yace Allah mugunta yamun. Jabeer zeyi magana wayar Rafeek tayi k'ara, saurin d'auka yayi ganin Hamza.


Saurin tashi yayi yana fad'in amma mungode Hamza, shikenan kayi yanda kace, bana so akaishi asibiti subi bayanshi, shikenan nagode sai mun had'u goben.


Zama yayi yana fad'in Allah maji rokon bawansa, su Hamza

45 / 54