Advertisements
Chapter 17 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   17 / 54

48K to 51K   out of 160.3K words

ya miko masa yana fad'in jeka da ita, ka tabbatar ka fitar da Bilkisu, kace ta yafe mun kuma tayi hakuri da rayuwa, Allah ya albarkaci abinda zata haifa, kuma kuyi kok'arin barin garin nan kada kuzauna aciki dan Allah, ka shafa mani kan Rumaisa da Ra'eez.



Kuka kawai Malan Sani yake haka ya fita daga motar, kasancewar bata b'angaren da suke taho yake ba hakan yasa ya gangare basu ganshi ba, wani daga cikinsu ne ya hango giccensa nan ya fad'ama Peter.


Kafin su k'arasa ya kira Alhaji Marusa ya fad'a masa direban ya gudu hada jakar kamfuta a hannunsa. Alhaji yace nasan gidan Alhaii Maiwada zaije domin ya ceci matarsa, kuji da Alhajin zain tira su Lucky gidan yanzu, nasan zasu rigashi zuwa tunda da mota hannunsu shima zasu kasheshi.


Fito da Alhaji sukayi, yana rok'on su amma basu saurareshi ba, wani kyalle sukasa suka nad'e mashi wuya dashi har sai da yadena numfashi. Wurgashi cikin motar sukayi suka bar wajen.

**

Brr. Barau ne yayi kiransu Lucky ya basu umarnin kada su kashe Malan Sani su barshi sun canza shawara, kawai sujirashi agidan yazo su amso kamfutar su fito.


Ur's.
Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*



1⃣5⃣

Tsayawa Malan Sani yayi yana hutawa sai dube-dube yake, hawaye kawai suke zubo masa, shikenan yanzu sun kashe Alhaji, kai duniya. Hannu yasa ya ciro wayarsa, Alhaji Mansur ya kira, yana d'auka ya sake fashewa da kuka.


Hankali tashe Alhaji Mansur yake tambayarsa abinda yake faruwa. Tsagaita kukansa yayi ya fad'a masa abinda ya faru. Salati Alhaji Mansur yasa jikinsa yana rawa.



Malan Sani yace yanzu haka ina hanya inaso na k'arasa can gidansa na tafi da Hajiya. Alhaji Mansur yace kaga tana d'auke ta juna biyu, kayi yanda hankalinta bazai tashi ba dan Allah, kuma shima Alhajin insha Allahu babu abinda zasuyi masa, gobe da wuri zan iso, Allah ya tsare ku gaba d'aya.


Mota Malan Sani ya tare yana saka wayarsa aljihu. Gani yake kamar mai motar baya gudu, addu'a kawai yake Allah yasa basu yima Alhaji komai ba.


***

Ta bayan gidan suka shiga dan Alhaji Marusa yace baya so Maigadi yasan da zuwan su saboda Brr. Barau ya had'a wani shiri ta yanda zasu fita daga zargi.



Ummun Ra'eez tana zaune a falo sai gwada kiran wayar Alhaji take amma taki shiga, duk da tasan yana wuce haka bedawo ba amma kafin ya baro ofis sunyi waya yace ta dafa masa kwai guda ukku zaici abinci dasu.


Gashi Ladi bata nan taje Kauyensu ana biki sai litinin ma zata dawo. Wayar ta aje tana mai jin wani irin sanyi yana shigarta, rufe ido tayi tana karanto duk addu'ar data zo mata.


**

Madu ne ya bud'e k'ofa jin k'arar bugawa, mamaki yayi ganin Malan Sani shi kad'ai ga idanuwansa duk sun kumbura.


Shigowa Malan Sani yayi yana fad'in Madu akwai matsala fa. Madu yace matsalar me ina Alhajin? Malan Sani yace ina zuwa bara na fito. Be jira abinda zai fad'a ba yayi gaba. Zama Madu yayi yana fad'in ikon Allah, wace matsala ce kuma wannan? Taya Malan Sani zai dawo shi kad'ai kuma, ga jaka a hannunsa kamar ta kud'i, sannan idanuwanshi duk sunyi ja kamar wanda ya shawu, ko dai Alhajin ne ya aikosa? Amma da mamaki, Redionsa ya jawo yana fad'in bari ya fito muji.


Bayan Ummu ta bud'e k'ofar sai taji gabanta ya fad'i ganin Malan Sani d'auke da bak'ar jaka ta kamfutar Alhaji. Batayi magana ba ta shiga ciki tana fad'in shigo mana.


Shiga yayi ba tare daya rufe k'ofar ba. Zama Ummu tayi tana fad'in Malan Sani Abbun Ra'eez ko aiki ya rik'esa ne? Duk'ar da kai yayi hawaye suna cika masa ido yace shine ya aiko ni na d'auke ki mu tafi can gidana gobe kuma zamu wuce kano.


Zatayi magana kenan sukaji alamun motsin shigowa, dama zaman jiran Malan Sani sukeyi kuma aka ci sa'a be rufe k'ofar ba.


Saurin mik'ewa sukayi ganin manyan mutane a cikin gidan. Hannu Ummu tasa ta dafe cikinta tana fad'in Malan Sani kace mun sun kashe Alhaji kawai, gashinan kaima kuka kakeyi, meyasa zasuyi mani haka, ina gawarsa take dan Allah? Kuka Malan Sani yasa yana kallon su yace narok'e ku da girman Allah kada ku kashe ta, ku kasheni amma kubarta ita da abinda yake cikinta.


Zuciya ce ta ciyo Ummun Ra'eez ta rarumi flask d'in ruwan zafi da yake kusa da ita ta wurga ma Lucky, saurin kaucewa yayi cikin zafin nama ya kwad'a mata sandar da take hannunsa akai.


K'ara Ummu ta saki ta fad'i da k'arfi saman cikinta, nan take jini ya b'alle mata. Salati Malan Sani yasa yayi kanta da sauri, kamota yayi yana jijjigata amma babu alamun rai ajikinta, ga kanta yana fitar da jini k'asanta ma jini na fita.


Kuka yake yana fad'in baku da imani, me wannan matar tayi maku. Tsaki Lucky yayi danshi baya b'ata lokaci a aikinsa. Wata hoda ya fesama Malan Sani nan take yaji kanshi yayi nauyi, hannu yasa ya dafe kanshi yana jin yanda falon yake juya masa.


Duk'awa Lucky yayi ya kama hannun Malan Sani ya kamo na Ummun Ra'eez, Malan Sani yana kallonsa amma jikinsa ba kwari, hannun Ummun Ra'eez yasa a wuyan Malan Sani ya karceshi da faratan ta da bata yanke ba, nan take sahu ya fito harda jini.


D'aukar jakar kamfutar sukayi suka kamo Malan Sani suka fito dashi sai layi yake dan sam baya cikin hankalinsa. Turashi sukayi hanyar gate, sai da sukaga ya kama hanya yana tafiya yana layi kafin suka fice ta bayan gidan.


Saurin tasowa Madu yayi ganin Malan Sani yana tangad'i, kamoshi yayi yana fad'in lafi... Tsayawa maganar tayi ganin jini a jikinsa, zeyi magana Malan Sani ya tureshi har sai da ya faad'i yayi tafiyarsa ya fice daga gidan.


Yana fita su Lucky suna jiransa bakin k'ofa, saurin kamashi sukayi sukasa a mota suka tafi. Koda Madu ya lek'a sai kurar motar ya iske.


Mamaki ne ya kamashi, me yasamu Malan Sani haka? Me ya aikata acikin gida tunda yasan Ladi bata nan? Ga jini ajikinsa, ko dai wani abu yayima Hajiya? Ai kuma yaso yaji ihu, Saurin komawa Madu yayi, cikin gidan ya nufa jikinsa sai rawa yakeyi.


Yana shiga falo yayi mutuwar tsaye, da sauri ya fito yana gudu yayi wajen gidan yana neman taimako. Makwabcin su ya gani shida abokinsa, da sauri ya k'arasa wajensu jikinsa na kyarma.


Tsayawa sukayi ganin Madu. Makwabcinsu mai suna *Alhaji Musa* yace Madu lafiya kuwa? Kuka Madu yasa yana nuna masu cikin gidan. Mamaki ne ya kamasu sukace meya faru? Madu yace ya kasheta wallahi gata can a kwance cikin jini Alhaji.


Wanda aka kira da Alhaji yace waye ya kashe ta kuma wa aka kashe? Madu yace Hajiya ce, Malan Sani ne yashigo kuma shi kad'ai ya dawo ba tare da Alhaji ba, hannunsa d'auke da jaka kamar ta kud'i, yana shiga cikin gidan sai ihun Hajiya naji, band'au ka wani abu bane ina zaune sai gashi ya fito jikinsa duk jini, dana rik'esa saiya tureni ya fito, kafin na fito wata b'akar mota ta d'aukeshi sun bar wajen.


Abokin Alhaji yace tabbas naga bak'ar mota har nake maka magana nace mai motar can yana tukin hauka ashe da abinda suke ma sauri.


Ajiyar zuciya Alhaji yayi yana fad'in lallai duniya babu gaskiya, yanzu bazamu shiga gidan ba, bara nayi waya a turo 'yan sanda idan suka zo sai mushiga saboda tsaro.


***

Sai da suka d'auki yaron daya gano masu gidan Malan Sani sannan suka wuce unguwarsu, har k'ofar gida suka kaishi, kuma sukaci sa'a ba mutane a wajen, ajeshi sukayi suka kama gabansu.


Cikin layi Malan Sani ya k'arasa cikin gidansa yana rik'e da kanshi. Halima da Rumaisa suna zaune tsakar gida suka ga Malan Sani yashigo ko sallama babu. Da sauri Halima ta tashi tana fad'in Malan lafiya kuwa? Hannu ya d'aga mata, beyi magana ba yayi hanyar d'akinsa, bayansa tabi cike da damuwa ga jini ajikinsa duk sai hankalinta ya sake tashi. Yana shiga ya rufe k'ofar yasa mukulli, zubewa yayi saman gadonsa nan take nannauyen bacci ya d'aukeshi.


Kamo Rumaisa Halima tayi suka zauna nan take hawaye suka wanke mata fuska, gaba d'aya jikinta yayi sanyi ganin Malan Sani a cikin wani yanayi wanda betab'a shiga ciki ba.


***

Bayan 'yan sanda sun gama bincike motar asibiti ta d'auketa aka nufi asibiti da ita dan sunce ba mutuwa tayi ba. Gaba d'aya unguwar hankalinsu atashe yake saboda abinda ya faru. Madu kuwa kamar wanda aka watsama ruwan zafi, gashi yakira Alhaji wayar bata shiga.


Ana shirin rufe gidan sai ga wata motar 'yan sandan sunzo. Bayan sun shigo suka tambayi maigadin gidan. Madu ya taso yana fad'in gani nan. Tambayarsa sukayi nan ne gidan Alhaji Maiwada shugaban kwastam? Jiki a sanyaye Madu yace nan ne.



Hannu babban cikinsu ya mik'ama d'an sandan da suka samu, Alhaji Musa makwabcin su Alhaji ya matso yana tambayar lafiya? 'Dan sandan yace mun samu gawar Alhaji Maiwada ne a motarsa shine akayi mana kwatancen gidansa, yanzu haka gawarsa tana asibiti an wuce da ita domin ayi bincike, tare ma muka kaita data wani yaro da muka tsinta itama anjefar, gaba d'aya de suna asibiti kafin mu samu Iyayen yaron.



Wani irin kuka Madu yasa yana fad'in shikenan shima ya kashe shi, kai Malan Sani ina zaka kai alhakin wad'an nan mutanan? Mutum ya d'auko ka cikin talauci ya taimake ka amma kazo kayi masa butulci.


Alhaji Musa ne ya kamo Madu yana fad'in ya isa haka, tunda hukuma tashigo ciki za'ayi bincike. 'Dan Sandan yace kasan gidan Malan Sanin? Kai Madu ya d'aga yana fad'in sosai ma.


Kallon Alhaji Musa yayi yana fad'in Alhaji zamuje can gidan domin mutafi da Malan Sanin, idan akwai wani d'an uwan Alhaji Maiwada asanar masa domin dole a rufe gidan nan kafin su zo.


Alhaji Musa yace gaskiya danginsa ba anan suke ba, kuma bani da lambar kowa. Madu yace ina da lambar Alhaji Mansur a kano yake. Alhaji Musa yace kawo lambar asanar masa idan yaso sai arufe gidan ku tafi da mukullin wajen ku kafin yazo.


Bugu biyu Alhaji Mansur ya d'auka, ganin bak'uwar lamba yasa gabanshi ya sake fad'uwa. Bayan sun gaisa Alhaji Musa ya fad'a masa halin da ake ciki. Salati kawai Alhaji Mansur yakeyi jikinsa yana rawa, ya dad'e kafin yace gobe zai taho da wuri, sannan ya roki alfarmar Alhaji Musa ya kula da Ummun Ra'eez kafin yazo da matarsa. Alhaji Musa yace bakomai sai kazo.



Haka aka kulle cikin gidan Madu yace zai cigaba da zama kafin ya tafi dan shima bazai iya cigaba da zama ba. Haka ya kulle gate d'in yashiga motar 'yan sanda suka nufi gidan Malan Sani, sauran 'yan unguwa sai jimamin abinda ya faru sukeyi.


***

Har sun rufe gida taja Rumaisa d'akinta sun kwanta dan Rumaisa har tayi bacci, ita ko ta kasa baccin, tunanin halin da Malan Sani yake ciki kawai takeyi.


Jin k'arar buga gida yasa tayi saurin tashi tana lallubar fitila, hijabi tasa kafin ta nufi waje jiki a sanyaye. Tsayawa tayi tana tambayar waye? Daga waje akace 'yan sanda ne ki bud'e.


Jikinta ne ya tsananta rawa, da kyar ta iya bud'e k'ofar. Madu ta fara gani hakan yasa taji sanyi, kallonshi tayi duk idanuwanshi sunyi ja. 'Daya daga cikinsu ne yace ina maigidan ki? Halima tace yana ciki ina jin beda lafiya dan ya kule k'ofar d'akinsa kuma ya dawo cikin wani yanayi.


'Dan sandan yace muje ki nuna mana d'akin munzo tafiya dashi ne. Gabanta ne ya faad'i ta kalli Madu tana fad'in wai meye yake faruwa dan Allah? Matsawa Madu yayi gefe yana goge kwalla ya kasa magana.


Kuka Halima tasa tare da komawa ciki ta fara bubbuga d'akin Malan Sani. Shiru babu alamun motsi hakan yasan d'an sandan yace zamu b'alle k'ofar tunda bai bud'e ba.


Abun buge k'ofa suka samo haka suka bud'eta da k'arfi. Mamaki ne ya kamasu ganinshi kwance kamar gawa, da sauri Halima tayi ciki tana fad'in Malan na shiga ukku me yasame ka haka? Ciki suka shiga suna tsoron kada dai ace shima ya mutu shirin da Brr. Barau yayi ya rushe.


Komawa baya d'aya daga cikinsu yayi ya d'ebo ruwa, yana zuwa ya watsa mashi, a firgice ya tashi sai dai jikinsa babu kwari. Rungumoshi Halima tayi tana kuka tace Malan me yasame ka? Kallonta yayi idanuwansa suna rufewa amma ya kasa magana.


'Dan Sandan yace Malama ki matsa muyi aikin mu kina b'ata mana lokaci, idan kina son sanin abinda ya aikata zaki iya zuwa ofis d'in mu gobe da safe amma yanzu dashi zamu tafi.


Kuka Halima tasa tana fad'in wallahi mijina ba me laifi bane, dan Allah kada ku tafi dashi. Murmushi d'an sandan yayi yana fad'in idan baki sani ba to mijinki makashi ne, domin ya kashe uban gidansa kuma ya nemi matarsa da alfasha yanzu haka tana asibiti.


A zabure Halima tayi baya tana binsu da wani irin kallo, hannu tasa ta rik'e cikinta jin yanda ya murd'a mata, ganin halin da take ciki yasa wani daga cikin 'yan sandan yaji tausayinta, duk'awa yayi yana fad'in ki kwantar da hankalin ki, idan akayi bincike beda laifi babu abinda za'ayi masa.


Ajiyar zuciya Halima ta saki tare da sakin wani irin kuka. Tana ji tana gani suka rik'e Malan Sani dan bema iya tafiya saboda mutuwar jiki, sai kallonta yakeyi, yana so yayi magana amma ya kasa, hawaye ne suka zubo mashi, haka sukayi waje Halima tana zaune ta kasa tashi.


Jin k'arar motarsu yasa tayi saurin tashi, mararta ce ta murd'a hakan yasa ta duk'e tana cije baki, ta jima ahaka kafin ta dafa bango har ta kai k'ofa, tsayawa tayi tana kallon kurar motarsu hawaye suna wanke mata fuska. A hankali ta maida k'ofar ta rufe kafin ta koma d'aki ta fashe da kuka.


***

Wai Baffan Naseer har yanzu baka samu wayar tashi ba? Ajiyar zuciya Baffa yayi yana fad'in duk kiran da nakeyi wayarsa akashe take, gaba d'aya hankalina ya tashi domin Naseer baya kai dare awaje.


Mama tace kuma fa gidansu Mannir yace zaije a masallacin unguwar nan ma yayi sallar magriba. Baffa yace ba agida nayi sallah ba da bazan barsa yaje ba, idan ma yace dole yaje sai dai na kaishi da kaina, kinsani sarai bana son yawon dare.


Mama tace kayi hakuri gani nayi yace littafinsa zai amso. Baffa yace wai baki da lambar shi Mannir d'in? Mama tace ina da ita dan Naseer ne ma ya ajeta saboda wata rana yana kiransa da wayata.


Baffa yace bani lambar. Bugu biyu Mannir ya d'auka, bayan sun gaisa suka tambayeshi Naseer. Shiru Mannir yayi yana mamakin Naseer baya gida, yace masa zaizo da yaga shiru ya d'auka ko agida aka hanashi.... Labarin yanda sukayi da Naseer ya fad'a masu.


Jiki asanyaye suka masa godiya. Hawaye ne suka zuboma Mama tana fad'in kada dai ace saceshi akayi. Baffa yace banga ta zama ba bara na kira DPO gara mushigar da k'ara da wuri.


Suna gama waya da DPO yace yajirashi zaisa yaranshi suje su duba. Zama sukayi gaba dayansu jiki amace.


Can wajen sha biyun dare DPO yakira Baffa, yana d'auka yace masa ya tura yaranshi zasuyi bincike, amma wani yace an kai wasu gawawwaki guda biyu d'azu asibiti data babban mutum data yaro, ko zasuje su duba? A zabure Baffa ya tashi yana fad'in yanzu zan fito DPO mu had'u a asibtin. Da sauri DPO ya amsa saboda Baffa babban mutum ne akwai naira.


Tare suka tafi hada Mama sai kuka takeyi domin Naseer shine autan ta, yaranta biyu babban yana can abuja yana karatu.


***

Kuka kawai sukeyi asaman gawar Naseer, Mama tana fad'in su waye ne suka maka haka Naseer? Ya Allah ka saka ma bawanka. DPO yace Alhaji kuyi hak'uri insha Allahu zamuyi bincike, idan muka gano wad'an da suka aikata haka dole ashigar da k'ara kotu.


Jinjina kai Baffa yayai kafin suka wuce domin su amshi gawar. Likita yace zasuyi bincike dole su bari zuwa safiya tunda ba yau za'a rufeta ba. Baffa yace ayanzu zakayi binciken ka bani gawar Yarona, gara naje na kwana ina masa karatu daya kwana anan. Jikin likita yana rawa yace angama.


Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*



1⃣6⃣


Washe gari ko da Malan Sani ya farka sai ya dawo cikin hankalinsa, tashi yayi yana dafe kanshi da yake masa ciwo, a hankali abubuwan da suka faru jiya suka fara dawo masa, tun daga shigarsa gidan Alhaji har abinda ya faru ya fito ya shiga mota har zuwanshi gida, iya nan kawai ya iya tunawa sai kuma yau daya tashi.


Da sauri ya d'aga kai yana sake kallon inda yake, mamaki abun ya bashi,

17 / 54