Advertisements
Chapter 35 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   35 / 54

102K to 105K   out of 160.3K words

nake wani tunani, amma mujira asallamosa sai musan abunyi. Mama tace shikenan kaje ka shiryo zan k'arasa aiki kafin ka dawo, abinci ma Rumaisa zata tsaya tayi idan ta gama sai ta same ni can ai tasan asibitin.


Jabeer yace shikenan sai na dawo. Kallon k'ofar d'akin Rumaisa yayi yana murmushi dan tunda ya shigo ya fara magana ya ganta tsaye tana hawaye. Suna had'a ido tayi saurin sakin labulen. Murmushi yayi yana ma Mama sallama ya fice.


**

Ko da sukaje alokacin Ra'eez ya koma bacci anyi masa allura bayan yaci abinci yasha magani. A tare da Rafeek suka fito zasu wuce aiki, Mama sai godiya take masu. Bayan sun tafi ta zauna cike da tausayin Ra'eez.

***

K'arfe 12:00 Rumaisa ta iso asibitin, waya tayima Mama ta fito suka shiga ciki, a bakin k'ofar shiga suka had'u da likita tare da Alhaji Barau da Brr. Bajinta.


A jingine da filo suka iskeshi yana shan lemun da Mama ta bashi kafin ta fita. Da sallama suka shiga. Kallonsu yayi da idanuwanshi da suka fad'a a dare guda.


Murmushi yayi yana masu sannu da zuwa. Shigowa sukayi Alhaji Barau yana fad'in kaga ikon Allah ko Brr. Bajinta, jiya fa mukayi waya yace mun ya dawo lafiya ashe a asibiti ma zai kwana.


Brr. Bajinta yace aishi ciwo beda lokaci, idan mutuwa ce ma haka zamu jita daga sama. Hannu ya mik'ama Ra'eez yana fad'in sannu ya k'arfin jikin? Ra'eez yace da sauki.


Gaishe da Alhaji Barau yayi. Alhaji Barau yace lafiya lau ya jikin? Ra'eez yace da sauki sosai. Su Mama suna gefe tashiga gaishe su. Kallonta Alhaji Barau yayi yana fad'in lafiya lau ya mai jiki? Mama tace da sauki.


Tashi sukayi Alhaji Barau ya aje kud'i masu yawa a gefen Ra'eez yana fad'in ban siyo komai ba ga wannan an saya masa lemu Allah ya k'ara lafiya, zuwa anjima da dare zamuzo tare da Hajiya, amma nasan Raheena tanaji zata taho nan.



Godiya Ra'eez yayi mashi fuskarsa a d'aure. Brr. Bajinta yace to Allah ya k'ara lafiya. Sallama sukayi ma su Mama suka fice. Tsaki Ra'eez yayi yana jin wani bakin ciki, hannu yasa ya ture kud'in daya aje suka fad'i k'asa.


Matsowa Mama tayi tana fad'in munafikin Allah, da yardar Allah k'arshensa bazeyi kyau ba, zezo ya kawo ma mutane kud'in haram.


A hankali Ra'eez yace Mama d'auke su nadena ganin su, ki ajesu idan kika fita ki badasu sadaka. Mama tace sai dai sadakar, amma wallahi ko da yunwa nake kwana bazan iya cin kwandalar munafuki ba.


Kwashe su tayi ta nemi bak'ar leda tasa sannan tasasu ajaka. Matsowa Rumaisa tayi idanuwanta cike da kwalla, tsaye tayi a gefen gadon tana wasa da yatsunta.


Tashi Mama tayi tana fad'in bara naje waje kila na samu mabarata. Har ta fita Rumaisa bata d'ago kai ba sai hawayen da suke sakko mata.


Tsura mata ido Ra'eez yayi shima idanuwanshi cike da kwalla, a hankali yasa hannu ya jawota ta fad'o jikinshi, kamar jira take ta kifa kanta tare da sakin kuka.

Lumshe ido yayi hawaye masu zafi suka sakko mashi, tabbas daga jiya zuwa yau yana jin wani irin ciwo a rayuwarshi, amma dole yasa jarumta aranshi matuk'ar yana so yabar asibitin nan gobe.


Sun dad'e a haka yana bubbuga mata baya, a hankali tayi shiru tana ajiyar zuciya. Duko da kanshi yayi yana fad'in Pretty kinaso ciwo na ya tashi ne, kinsan dai kukan ki yana d'aga mani hankali sosai, gashi jinina ya hau idan kina kuka zai k'ara hawa.


Saurin tashi zaune tayi tana goge idonta. Murmushi yayi yana fad'in ashe dai ba'aso na mutu? Turo baki tayi tana fad'in dan Allah Yaya na kadena maganar mutuwa.


Waro ido yayi yana fad'in yau kuma na koma Yaya? Kai ta girgiza tana murmushi. Ra'eez yace to afad'amun sunan. Murmushi tayi tace kai Annur! Dariya yasa yana fad'in yanzu naji.


Tashi tayi ta zuba masa abinci, gyara masa filo tayi ya gyara zamansa kafin ta mik'a masa filet d'in. Ido ya tsura mata be amsa ba, jin shiru yasa ta kalleshi. Turo baki yayi yana mak'ale hannu a baya.


Murmushi tayi ta zauna gefen gadon ta fara bashi abaki. Haka yarik'a amsa idan yaci d'aya sai yace dole sai taci dan yasan bataci komai ba saboda rashin lafiyarsa. Haka suka cinye hada k'ari, abincin da sukaci sunyi mamaki dan basu san sunci ba.


Wajen k'arfe 3:00 Jabeer ya iso, a d'akin waje ya iske Mama tana jan carbi Abdallah yana gefenta wanda Rumaisa taje ta d'aukosa a makaranta.


Duk'awa yayi suka gaisa yayi mata ya mai jiki. Mama tace yaji sauki sosai suna ciki kashiga. Tashi yayi yana fad'in Allah ya k'ara sauki.



Yana tura k'ofar Rumaisa tana kok'arin bama Ra'eez aiba a baki. Cak ta tsaya tare da duk'ar da kai tana murmushi. Da sallama yashigo yana murmushi.


Harara Ra'eez ya aika masa yana gyara zamanshi. Zama Jabeer yayi yana fad'in ae dole a tura Mama waje ashe ana nan ana.... Da sauri Rumaisa tayi waje cike da kunya.


Dukan wasa Ra'eez ya kaima Jabeer yana fad'in wannan ai wulakanci ne mutum yana jin dad'i da iyalinsa azo a takura masa.


Jabeer yace lallai kam Yaro ka samu, banda wukalanci a asibiti zaku zo kuna soyayya saboda rashin kunya kayi wani kwance ana baka abinci abaki.


Ra'eez yace wani ma ya samu hakan, kaga malan bana son sa ido. Dariya Jabeer yayi ya bashi hannu suka gaisa yana tambayarsa jiki.


Ra'eez yace da sauki sosai, ai Pretty tana zuwa naji na warke gabad'aya. Jabeer yace da alama yau ita zamu bari ta kwana kaga kafin gobe sai ka koma dai-dai.


Dariya Ra'eez yasa yana fad'in wallahi baka da kirki, mutumin ka fa yazo shida d'an kazaginsa. Jabeer yace ina zuwa na fad'a mashi shine yace dole yazo ya dubaka.


Ra'eez zeyi magana aka turo k'ofa, Raheena ce tashigo bakinta d'auke da sallama. Jabeer ne ya amsa yana mata sannu da zuwa. Wani b'acin rai ne ya ziyarci Ra'eez, shikenan zatasa Pretty cikin damuwa.


Cikin sauri ta k'ara so idanuwanta suna kawo ruwa, gefen gadon tazo zama da sauri Ra'eez yasa k'afarsa a wajen yana mata nuni da kujera. Jiki a sanyaye taja kujera ta zauna ta fara gaishe su.


Tashi Jabeer yayi yana fad'in matso da kujerar jikin gadon keda kika zo jinya. Murmushi tayi ta matso tana tambayar Ra'eez jiki. Zamewa yayi ya kwanta yana amsawa.


Kallonshi tayi tana fad'in sannu Dear, wallahi bakaji yanda hankalina ya tashi da Dady ya fad'a mun ba, tare muke da Momy tana wajen wasu anan da alamu 'yan uwanka ne shine ta tsaya suna gaisawa.


Kai Ra'eez ya jinjina yana fad'in nagode. Momy ce tashigo bakinta d'auke da sallama. Jabeer ne ya amsa mata yana mata sannu. Bayan ta zauna suka gaisheta tayima Ra'eez sannu.


Kallon Raheena tayi tana fad'in to ke haka ake zuwa jinyar bazaki zuba abinci ki bashi ba? Murmushi Raheena tayi tana fad'in Momy yanzu zan zuba mashi ai.


Momy tace yauwa, matsa ki zauna gefen gadon ki bashi ba sai ya wahalar da hannunsa ba. Saurin juyawa Jabeer yayi ya fita saboda dariyar da ta taho mashi. Da sauri Ra'eez yace akoshe nake yanzu naci abinci.


Raheena zatayi magana sai ga Rumaisa ta shigo da sauri, tunda taga Raheena hankalinta ya kasa kwanciya musamman da Momy ta fad'a masu daga inda suke.


Ganin Raheena akusa da gadon Ra'eez yasa tayi saurin k'arasawa, bata san lokacin data zauna gefen gadon ta kamo hannun Ra'eez tana fad'in Annur baka buk'atar komai ko? Runtse ido Ra'eez yayi ganin Rumaisa zata rusa masa shiri.


A firgice Raheena ta kalli Rumaisa jin abinda tace. Ganin Ra'eez ya runtse ido yasa Rumaisa tayi saurin sakin hannunsa tana fad'in Yaya dama fa Mama tace nazo na tambayeka idan akwai abinda kake buk'ata tunda taga surikarta tazo jinya.


Murmushi ne ya sauka a fuskar Raheena da Momy wad'an da sukayi zuru suna jiran k'arin bayani. Da sauri Ra'eez ya bud'e idonshi jin abinda Rumaisa tace, a cikin idanuwanta ya sauke nashi, sai dai ganin yanda idanuwanta suka canza yasashi gano tsananin kishi a ciki.


Da sauri Raheena tace lallai wannan k'anwar tamu tana ji da Yayanta, kada ki damu ina nan zan bashi duk abinda yake buk'ata, idan kina son zuwa gida ki huta zaki iya tafiya dan sai dare zan bar nan shima dan bazeyuwu na kwana anan ba da zan kwana dashi.


Momy tace sosai kuwa, tunda kinzo zasu iya tafiya su huta dan nasan tun safe suke nan. Kai Rumaisa ta jinjina dan bazata iya magana ba tayi saurin barin d'akin.


Runtse ido Ra'eez yayi cike da jin haushin Raheena da Momynta, yasan Rumaisa zata shiga damuwa, ko abinda tayi ganin ya rufe ido ne yasa ta fad'i haka kuma ya gano da biyu ta fad'a.


Tashi Momy tayi tana fad'in Ra'eez Allah ya k'ara sauki, zan tafi na barku kuyi firar ku, Raheena idan direba ya maidani zai maido maki motar sai ya koma gida saboda idan kin tashi komawa sai kiyi amfani da ita.


A hankali Ra'eez yace nagode. Raheena tace Momy sai na dawo. Momy tace ki kula dashi sosai fa. Raheena tace to Momy.


Sallama tayi masu Mama ta wuce. Jabeer da yake kok'arin shiga yaji abinda ya faru dan tunda yaga Rumaisa ta fito idanuwanta jawur yasan akwai abinda ta gani.


Yana shiga Ra'eez yayi saurin tashi yana fad'in Jabeer kayana akwai matsala fa, kaje ka gyara komai bana so asamu matsala suyi kura. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in da alamu ajiyar tayi kura sosai, bara naje na kakkab'e kada k'ura tayi mata illa.


Kwanciya Ra'eez yayi yana fad'in kayi sauri dan Allah. Raheena tace Dear meyasa zaka aje kaya baka rufe ba ai dole k'ura ta b'ata su, Allah yasa ba fararen kaya bane nasan dole a sake wanke su🤣.


Kasa rik'e dariya Jabeer yayi da sauri ya fita yana fad'in farare ne tass sosai Raheena yanzu zanje na gyara komai. Raheena tace sai ka dawo. Murmushi kawai Ra'eez yayi yana lumshe ido jin abinda Jabeer ya fad'a.



Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*



3⃣4⃣


Saurin b'oye fuska Rumaisa tayi tana kok'arin goge hawayen da suke fuskarta jin labarin da Jabeer ya bata. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in a mana afuwa matar lauya, laifin mu ne da bamu fad'a maki shirin mu ba, amma yanzu ina fatan kin fahimci labarin dana baki, sam Ra'eez baya son Raheena, yana so shima ya rama abinda akayi ma Abbunsa ne.


Jinjina kai Rumaisa tayi tana fad'in Allah ya so ban kwafsa ba, ai da farko kansu ya d'aure da na kirashi Annur, amma jin na ambaceta amatsayin surikar Mama sai hankalinsu ya kwanta, nima haka kawai naji na fad'i surikar Mama dan naga yanayin fuskar Yaya kamar beji dad'in abinda nayi ba.



Jabeer yace ai kin kyauta, ina fatan kuma zaki taya Ra'eez yakin da yake gabansa, ki d'auka Raheena namiji ce kawai, kuma kirik'a kokarin kaucema had'uwar ku waje d'aya hakan zesa zuciyarki ta natsu.



Rumaisa tace wallahi bakomai, ni mai iya sadaukar da farin cikina ne matuk'ar Yaya zai cika burinsa, yau ko cewa akayi saiya aureta zan iya amincewa idan har hakan zaisa ya cika burinsa.


Jabeer yace hakan ma bazata faru ba, domin yanzu ne zamu fara aiwatar da komai, kinga ana kammala shari'ar sai musha biki. Murmushi tayi ta rufe fuska.



Jabeer yace muje na ajeku gida tunda nazo. Rumaisa tace bara nayima Mama magana. Jabeer yace shikenan.


Tare da Mama suka shiga d'akin, mamaki Rumaisa tayi ganin Ra'eez a kwance ya rufe ido kamar me bacci ga Raheena a kusa dashi sai kallonshi takeyi. Saurin amsa sallamarsu Raheena tayi tana matsawa hada duk'ar da kai.



Bud'e ido Ra'eez yayi jin muryar Mama. Gyara kwanciyarshi yayi yana fad'in sannu Mama. Murmushi tayi tana fad'in kai ne da sannu, ya jikin naka? Da sauki Ra'eez ya amsa.


Kallon Rumaisa yayi suna had'a ido ya kashe mata ido d'aya, murmushi tayi itama ta rama. Mama tace zamu koma sai gobe idan Allah ya kaimu tunda ga Jabeer nan yazo.



Ra'eez yace kai Mama, ku bari zuwa dare bana son ku tafi. Da sauri Raheena tace haba ka barsu suje su huta ai akwai gajiya, tunda gashi nazo zan zauna da kai har wajen tara sai na tafi.


Murmushi Mama tayi tana fad'in sannu da kokari angode. Turo baki Ra'eez yayi yana fad'in to Rumaisa ta zauna sai ya kaiki ke da Abdallah anjima zai maidata.


Mama zatayi magana Raheena tace gaskiya baza'a wahalar mun da K'anwa ba, da ganinta ta gaji taya zaka ce ta zauna bayan ko ta zauna sai dai ta koma wancan falon tunda bazata iya zama anan ba dan a takure take.


Murmushi Rumaisa tayi tana fad'in maganar ki gaskiya babbar Yaya, nima bazan zauna ba kada na shiga hakkin ki. Raheena tace to ka gani, Mama kawai kuje ku huta zan kula dashi.


'Daure fuska Ra'eez yayi ya koma ya kwanta, jiyake kamar ya kwad'a mata mari saboda haushi, shi sam beso zuwanta ba yaso ace Pretty d'insa ce akusa dashi yau su sha soyayya amma wannan anacin tazo ta zauna.



Muryar Mama yaji tana fad'in to sai da safe kaci abinci sosai kafin kasha magani. Kai ya d'aga yana hararar Rumaisa. Dariya tayi ta wuce tana fad'in Yayana Allah ya baka lafiya kaji.


Suna fita Raheena ta matso tana fad'in D ashe ba bacci kake ba kawai ka rufe ido ka barni shiru,. Kauda kai yayi bece komai ba. Hannunshi ta kamo tana fad'in idan ina tare da kai tamkar ahalinka ne a kusa da kai, domin zan d'auke maka abinda bazasu iya d'auke maka ba ma.



Saurin zare hannunshi yayi yana mata wani kallo. Baki ta rik'e tana fad'in yi hak'uri wallahi mantawa nayi, zamana akusa da kai sai nake ganin kamar agidan mu muke shiyasa na iya rik'e ka amma ba halina bane.



Zeyi magana Rafeek ya shigo. Murmushi ya saki yana fad'in Hajiya Raheena kece mai jinyar kenan? Murmushi ta saki tana gaishe shi, sosai taji dad'i, duk da bata sanshi ba amma tasan abokin Ra'eez ne, lallai Ra'eez yana sonta, gashi har abokanshi sun santa.



Zama Rafeek yayi yana fad'in Ra'eez ya jikin? Ra'eez yace da sauki Yaya ya aikin? Rafeek yace akwai wahala, sai yanzu fa na tashi, abinci kawai na biya naci agida.


Ra'eez yace sannu da aiki. Shigowar Jabeer yasa Ra'eez ya kalli Raheena yana fad'in ki tashi ki wuce gida magriba ta kusa. 'Bata fuska tayi tana fad'in ka barni sai zuwa anjima bazan iya barin ka a..... Kallon da yayi mata yasa tayi saurin tashi tana turo baki.


Murmushi Jabeer yayi yana fad'in wai a ina aka tab'a korar d'an jinya? Rafeek yace ai mace ce ga magriba ta kusa kaga babu dad'i ta zauna nan, da ace babu kowa dan ta zauna ba wani abu bane, amma bana son ina ganin mace a waje da dare domin ba mutuncinta bane.



Murmushi Raheena ta saki jin abinda Rafeek ya fad'a, sai yanzu ta gane Ra'eez baya son tayi dare a waje, sannan ga abokansa duk maza yana kishi ta zauna a cikinsu.


Jaka ta d'auka tana fad'in D kana da gaskiya, tunda akwai maza a d'akin be kamata na zauna acikinsu ba, wasu ma zasu iya zuwa kaga babu dad'i a kalle maka ni, shikenan zan tafi sai zuwa goben.


Dariya Jabeer yayi yana fad'in ai kinsan abokina akwai kishi. Harara kawai Ra'eez yake aiko masa, be kulashi ba yacigaba da fad'in nan gaba kila bazai barmu shiga gidansa ba.


Raheena tace ai jin dad'i ne ka samu mai kishinka. Jabeer yace sosai kuwa, ai Allah ya nuna ranar biki. Raheena tace amin.



Juyawa tayi tana fad'in D kaci abinci da yawa dan Allah. Rafeek yace zaici, ki gaida gida. Fita tayi tana murmushi.


Tsaki Ra'eez yaja yana fad'in wallahi Jabeer kashiga hankalin ka. Jabeer yace daga fad'in gaskiya. Ra'eez yace shikenan, insha Allahu kaine zaka aureta.


Dariya Jabeer yasa hada rike ciki yana fad'in amma baka ta kirki, yanzu ka rasa da wadda zaka had'ani sai Raheena, haba ai koda bani da budurwa bazan iya aurenta ba.


Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in me yasa kake shiga maganarta to? Jabeer yace kawai ina tausayinta ne, duk da bansan zafin so ba amma ina tausaya mata domin ta kamu da sonka, kuma ma ni bazan iya auren wacce take son wani ba, to na aureta nace na auri wa? Ka auri mace, Ra'eez ya fad'a.


Dariya Rafeek yayi yana fad'in wallahi idan mutum yana kusa da ku sai kusashi ciwon ciki saboda dariya, yanzu kai Jabeer ai taimakon ka Ra'eez yayi daya baka ita, domin naga ko 'yar tsana baka da ita.



Dariya Ra'eez yasa yana fad'in wallahi kuwa Yaya, kaganshi nan kullum yana gida, lokacin bacci haka yake kwanciya babu mai sashi farin ciki, dan na bashi Raheena ai banyi laifi ba.



Jabeer yace sai dai ka bani Rumai.... Kamar walkiya Ra'eez ya diro daga gado, dariya Jabeer yasa yayi bayan Rafeek. Nufoshi Ra'eez yayi sai ga likita ya turo k'ofa.


Dariya Rafeek yasa yana fad'in likita kaga marar lafiyar

35 / 54