Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
dan baya so ya tashi hankalinsu. Jinjina kai yayi yana fad'in nagode Hajiya, muje ki had'a mun ruwan wanka.
*** ***
Ai na d'auka bazai iya yanke ma Fawwaz hukunci ba, domin naga lokacin da Alhaji M. Sanda yazo wajenshi lokacin da aka fito hutun rabin awa, na tabbata alokacin ya shirya masa abinda ya fad'a.
Ra'eez yace ai Abbah shiyasa muka dage sai da aka binciko mana takardar haihuwarsa, domin nasan irin haka zata iya kasancewa, ajiya Yaya yayi magana da Abban Nabeel, shine yayi mana jagora domin samo takardar, duk da ansha wuya saboda shekarun da yawa, amma kasancewar ana adana duk wasu takardu na 'yan makarantar yasa aka sameta.
Alhaji Kamal yace dole a gobe zanje Abuja domin ranar litinin za'a k'aro mutane, kafin nan dole asa masu ido gudun karsu gudu, hatta shi shugaban Kwastam d'in da mataimakinsa duk asa masu ido saboda suma sai an hukuntasu.
Alhaji Mansur yace ai naso ya tsaya yayi shari'ar Naseer da ayau sai dai suyi kwanan takura dan dole a akamasu, amma bakomai Allah ya kaimu litinin d'in.
Alhaji Kamal yace amin. Wato abinda ya bani mamaki da kace mani an samu flash d'in a motar Alhaji Maiwada, abun tambaya nan shin dama Naseer ya kai mashi flash d'in ne ko kuma ya akayi?
Alhaji Mansur yace kasan a labarin da Malan Sani ya bamu, a daren da za'a kashe Naseer da Alhaji Maiwada sun had'u da Naseer yana kokarin shiga wajen aikinsu da gudu har suka kusa tureshi, anan ya tsaidasu yace biyoshi akayi, hakan yasa suka taimaka mashi, dalilin da yasa Malan Sani yace wannan yaron shine Naseer saboda ya fad'a masu sunanshi, kuma da suna maganar kisan Farouk da akayi sai Naseer yace masu abokinsa ne, kaji dalilin da yasa Malan Sani yace wannan yaron shine Naseer, kuma da aka samu flash d'in a motar na fad'ama Malan Sani sai yace tabbas aranar da suka d'auki Naseer a kujerar baya ya zauna saboda Alhaji Maiwada baya zama baya.
Alhaji Kamal yace bara mugani idan zan iya had'a kan labarin..... A hasashe na, bayan da Naseer yaje gidan su Fawwaz sai ya iske su Alhaji Marusa suna tattaunawa akan kashe Alhaji Maiwada, bayan daya gano shugaban kwastam suke nufi shine dalilin da yasa Naseer ya nufi ofishin su domin ya bashi wannan d'auka da yayi, kafin ya kai sai aka tura mashi mutane kamar yanda Adnan ya baku labari yaji ance aje a kashe shi har an anshi hotonshi, ganin an biyoshi sai tsoro ya kamashi, bayan da suka taimaka mashi sai yayi tunanin kada ya bada flash d'in a inda be kamata ba domin kaga ai dare ne bazaiyuwu ya iya gane Alhaji Maiwada ba, bayan da suka ajeshi sai yaga dacewar ya b'oye flash d'in a motarsu saboda ya tsorata kada abiyo bayanshi bayan tafiyarsu, ina ganin wannan shine dalilin samuwar flash a motar Alhaji Maiwada.
Jinjina Alhaji Mansur yayi mashi yana fad'in aiki ga mai k'areka, wani abun sai ku tsofaffin lauyoyi, wannan hasashen naka tamkar kana wajen akayi, domin ya tafi dai-dai, tabbas babu ja hakan ce zata kasance, kuma ba kowa bane yasa hakan ta kasance sai Allah, domin ya riga daya tsara komai, kuma Alhamdulillahi gashi nan yau yayi mana rana.
Alhaji Kamal yace Allah yajik'ansu da rahma, mu kuma yasa mucika da imani kuma yasa a kammala wannn shari'ar lafiya, amma fa Alhaji sai kace ma su Ra'eez su kula, domin ayanzu suna gab'ar rikici domin zasu faraucesu tamkar tsohon zakin daya shekara babu abinci, abinda nake gani kada Ra'eez ya aje wannan flash d'in a wajenshi.
Hannu Alhaji Mansur yasa ya ciroshi yana fad'in Alhaji ina ganin ka tafi dashi wajenka hakan zaifi, duk da mun rarraba shi a wayoyin mu amma nafison a k'ara samun wani awajen ka.
Alhaji Kamal yace shikenan Allah ya bamu ikon tabbatar dashi, ya kuma kare kowa daga sharrinsu. Alhaji Mansur yace amin ya Allah.
*** ***
Daga duba Adnan wajen Ummu suka wuce, ganin yanda jikinta yayi sauki yasa Ra'eez yace abarshi su tafi da ita, Alhaji Mansur ya kira ya fad'a mawa hakan yasa yace su taho da ita. Sosai sukayima matar da take kula da ita alkhairi da godiya, haka sukabi duk 'yan wajen da akhairi, har bakin mota likita ya rakosu suka tafi cike da murna.
Gaba d'aya gidan ya hargitse da murna, Maman Labiba da Mama sun saka Ummu a tsakiya kamar zasu goyata, bayan koke-koke suka zauna akaci abinci, aranar kamar ana biki haka gidan ya kasance.
Madu kasa zaman waje yayi haka yashigo ciki akayi murnar dashi. Suna zaune saiga Ladi dan Madu ya aika yaro ya fad'a mata, zama tayi tana ta farin cikin samun lafiyar Uwar d'akinta.
Gaba d'aya sai abun ya dawo ma Ummu sabo, sosai tayi kuka. Bayan da suka dawo sallar isha'i suka zauna a falo Ummu tayi wanka tasa kaya sai ta fito tamkar ba itace tayi hauka ba, sosai tayi kyau, sai dai har yanzu akwai damuwa a fuskarta, duk ta kosa a fad'a mata abinda ya faru.
Gyara zama Alhaji Mansur yayi yana fad'in Bilkisu inaso ki bani aron hankalinki, na lura idan ba'a sanar dake abubuwan da suka faru ba bazaki tab'a samun nutsuwa ba amma ki dubi girman Allah kada kiyi abinda zai dawo da ciwonki, nasan dai zuwa yanzu kinsan cewar Allah ya amshi Alhaji Maiwada, sai dai bakisan sauran abubuwan ba, dan haka yanzu zan sanar da ke komai......
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
4⃣6️⃣
Kuka kawai Ummu takeyi lokacin da ta gama sauraron labarin abinda ya faru, a hankali Ra'eez ya matso ya rungumeta shima yana kukan, gaba d'aya sai suka bama mutanan wajen tausayi sai mutuwar ta dawo masu farko. Da kyar Alhaji Mansur ya lallashe su kafin sukayi shiru.
Ajiyar zuciya Ummu ta sauke tana fad'in Allah yajik'an ka Alhaji Allah ya kai haske kabarinka, hakika bazan tab'a yafema wad'an da suke dasa hannu a mutuwar ka ba, kuma insha Allahu sai sun wulak'anta.
Alhaji Mansur yace kiyi hakuri komai yazo k'arshe, idan suna tunanin sun rufe sirrinsu Allah zai haskasu kowa ya gansu, ina so kisa jarumta aranki domin kije kiga yanda azzalumai zasuji kunya agaban idonki.
Jinjina kai tayi tana goge ido tace dole nasa jarumta kam, kuma zanje har kotun domin na bada sheda akan zaluncin da akayima Malan Sani, domin duk abinda ya faru alokacin ban mance ba.
Murmushi Ra'eez yayi ya rik'o hannunta yana fad'in Ummu ki kwantar da hankalin ki ina nan babu wanda zai sake saka ki zubar da kwalla, kuma zakiga yanda azzalumai zasu wulak'anta. Kanshi ta shafa tana fad'in Allah yasa Ra'eez.
**** ***
Dan Allah ka cire damuwa aranka, bazan bari kayi zaman gidan yari ba koda ace bani da kud'in da zan biya tarar da aka saka maku wallahi zanje naci bashi, dan haka kadena damun kan ka.
Ummah tace mu godema Allah da abun ya tsaya a haka, yau da ace kana dasa hannu a cikin kisan shikenan kaima rayuwar ka acan zata k'are, babu wanda besan k'addara ba, kuma zuciya bata da k'ashi dan haka kadena saka damuwa aranka kaga likita yace jinin ka ya hau.
Ajiyar zuciya ya sauke yana fad'in dole na damu Nabeel, ka tunafa ko auren farko bakayi ba, kamar yanda wannan abun ya faru ina mai tabbatar maka daga lokacin da ka fara neman aure sai wannan abun ya shafi auren ka, wallahi nayi nadamar abinda na aikata domin nayi maku bakin fenti, taya zan iya fita na kalli mutane, nasan da zaran na fita za'a rik'a nuna ni.
Nabeel yace ni dai bazan damu ba Abbah, damuwata d'aya idan ka kasance acikin damuwa, duk wanda zai nuna mu yaje yayi ta nunawa domin abun kunyar mu mai sauki ne, ina mai tabbatar maka daga nan zuwa litinin za'a mance da labarin ka, domin za'a tono abinda zai girgiza mutane, dan haka kacigaba da neman yafiya awajen Allah, kud'i kuma gobe zanje na kaisu.
Murmushi Abbah yayi yana fad'in nagode Nabeel Allah yayi maka albarka kuma ya baka wad'an da zasuyi maka fiye da haka. Gaba d'aya suka amsa da amin.
*** ***
Washe gari wajen k'arfe goma suka had'u a gidan Alhaji M. Sanda, zaune suke a lambu kowa tashin hankali kwance a fuskarshi.
Mr. Kallah yace hakika muna cikin tashin hankali babba, dama irin wannan ranar nake tsoro, wallahi jiya banyi bacci ba bayan da naji wai an yanke maka hukuncin d'aurin wata ukku agidan yari, sannan Fawwaz d'aurin rai da rai, shiyasa nayi saurin kiran kowa nace mu had'u a nan dan muna da buk'atar tattaunawa kafin litinin saboda shari'ar da za'ayi ta shafemu duka.
Alhaji Barau yace wallahi jiya kwana nayi ina gudawa, banyi baccin kirki ba saboda tashin hankalin da yake gaban mu, gani nake duk kunfini kwanciyar hankali domin nine wanda zan yanke hukunci da zaran an tabbatar da mai laifi.
Alhaji Marusa yace wai an tabbatar da shedar ne? Alhaji Barau yace ai tunda har aka iya samun shedar kisan Fawwaz na tabbata akwai tamu aciki, domin idan baku manta ba alokacin da aka kawo wayar yaron a ciki mukaga duka d'aukar da yayi.
Alhaji Marusa yace muna da sauran lokaci, nasan wannan shedar dole tana hannun Brr. Ra'eez, abinda nake gani mai zai hana mu aika Lucky ya sato mana ita ba shikenan ba.
Mr. Kallah yace kana wasa da wannan lauyen, taya zai bar irin wannan shedar da ta riga ta fito a waje d'aya, kada kamanta yasan abinda yake ciki, idan ma an sace ta wajenshi ina da tabbacin ya tura a wani waje, kawai a samo wata hanyar.
Alhaji Marusa yace bara na kira Lucky naji yanda za'ayi domin ina tsoron yaran can da aka kama idan sukaji duka zasu iya tona komai, kunga idan ma Ra'eez beda wata sheda akan mu sun samu a wajen su.
Waya ya d'auko ya kira Lucky. Bayan sun gaisa yace wai Lucky kasan halin da ake ciki kuwa? Lucky yace na sani mana meye abun damuwa aciki dan kawai an kama Yarana, zuwa anjima zakuji labarin mutuwarsu dan yanzu haka sun kusa shek'awa, maganar shedar da akace an samu ta kisan Fawwaz kuma ina mai tabbatar maku ita kad'ai suka samu a flash d'in, idan kukayi duba da lokacin daya d'auki vedion zakuga be isa ace yaje ya tura a flash ba har ya nufi wajen shugaban kwastam, nafi tunanin tun bayan daya d'auki kisan Fawwaz ya adanashi a flash d'in kuma agidansu ya b'oyeshi, sauran na wayarshi kuma an k'onasu, dan haka kudena damun kanku idan ba haka ba zaku tona kan ku kuma wallahi ba ruwana dan zan iya barin garin gaba d'aya kuma babu wanda zai iya gano inda nake.
Jinjina kai Alhaji Marusa yayi yana fad'in na fahimce ka, mungode sai munyi waya. Kashewa yayi ya kallesu yana fad'in kunji dai abinda yace, dan haka ku kwantar da hankalin ku yaran ma zai gama dasu, ai nasan Lucky beda wasa, kuma nima na aminta da bayaninsa.
Gyara zama Alhaji M. Sanda yayi dan tun d'azu beyi magana ba, kallonsu yayi yana fad'in hankalina ba zai tab'a kwanciya ba matuk'ar ba gani nayi an gama da shari'ar litinin ba, wai meyasa ma acikin mu babu wanda yake hud'd'a da malan tsubbun nan.
Alhaji Barau yace haba dai 'Yallab'ai kai da kan ka, ai wannan sai mutane marasa ilimin boko sune suke irin wannan harkar, dama can ban yarda da irin wannan abubuwan na Iyaye da Kakanni ba, nafi gane nasa majiya k'arfi suyi mani aiki, amma ka tsaya a wajen wani tsugunnan nan mutum kace shine zai maka aiki, idan Kura na maganin zawo tama kanta mana, kai tunda kake ka tab'a ganin Malamun tsubbu cikin kyakkyawan yanayi, shegu kullum suna zaune a bukka ko arami kamar mujiya, kawai ka barshi Lucky ma ya ishe mu da sauran basirar da muke da ita.
Alhaji Marusa yace baka had'u da manya bane shiyasa, idan kana buk'atar aiki babu b'ata lokaci kaje wajen manyan arna a cikin tsaunuka anan sai abinda kaso.
Mr. Kallah yace kudena wannan maganar ta wasu masu tsafi bamu da lokacin yin wannan, kamar yanda Alkali Barau yace aiki ne na marasa ilimin boko nima na goyi bayanshi, muyi amfani da ilimin mu da basirar mu kawai.
Alhaji M. Sanda yace shikenan Allah ya kaimu litinin d'in muga da abinda zasuje, amma fa asanar dasu Adebayo domin suma acikin mu suke. Alhaji Barau yace wannan ba matsala bace duk za'a fad'a masu, kuma nasan ma dole suji hukuncin dana yanke a kotu tunda akwai sunan ka, abinda yafi kawai bakin mu ya zamo d'aya. Gaba d'aya suka ce badamuwa.
Alhaji Marusa yace ni yanzu babban abinda yake damuna rashin kud'in da yake so ya sameni, domin jarina yayi k'asa sosai, a yanzu haka bani da jarin da zan iya shigo da kaya masu yawa dole sai dai na fara da kad'an-kad'an, gashi dama ni ba gwanin sayen kadara bane duka gidajena basu wuce ukku ba agarin nan, biyu haya ake aciki, gaskiya duk b'arayin da suka mani satar nan ban yafe masu ba wallahi kuma sai Allah ya saka mani.
Kauda kai Alhaji Barau yayi yana murmushi a b'oye. Alhaji M. Sanda yace ka kwantar da hankalin ka a kammala wannan matsalar sai asan abunyi. Alhaji Marusa yace shikenan nagode maku.
*****
Bayan sun tafi Alhaji M. Sanda yashigo gida, zaune ya iske Ammi tayi tagumi tana tunani. Zama yayi yana fad'in wannan tunanin babu inda zai kai ki, idan zakije ganin Fawwaz kitashi muje.
Ajiyar zuciya ta sauke tana fad'in yanzu Alhaji hankalin ka har akwance yake da zakace na bar tunani, gudan jinina fa aka yanke ma hukuncin kisa shine zakace na bar damuwa.
Gyara zama yayi yana fad'in kinsan dai baki fini sonshi ba ko? To tunda kika ga na saka hakuri araina kema kisa, domin Fawwaz bazai tab'a wulak'anta ba, da ace yau ratayeshi za'ayi shine hankalina zai tashi, amma zan ganshi a duk lokacin da naso, kuma ni nasan yanda zanyi domin a sama masa kwanciyar hankali a gidan yari domin ina da mutane acan, kuma kinsan babu abinda kud'i basayi, dan haka kitashi muje idan zaki.
**** ***
Ya isa haka Fawwaz kadena kuka babu abinda za'ayi maka, yanzu daga nan zanje naga shugaban gidan Yarin zamuyi magana dashi har wajen kwana dole asake maka, ina zaka iya kwanciya da manyan katti wad'an da suka gawurta awajen aikata laifuka, ko aiki ma bazan bari kayi ba, sannan abinci zansa arika baka wanda kake so kaji.
Kai ya d'aga yana goge idonshi. Ammi tace Fawwaz ka godema Allah da yasa ba kisan lokaci guda za'ayi maka ba, yanzu lokacin da zaka koma ma Allah ne, kaga dai har abada bazaka fita anan ba sai dai a fitar da gawar ka, abinda nakeso da kai ka zama nagari, domin duk wanda yazo gidan yari zai had'u da wad'an da suka fishi komai arashin ji, haka kuma zai had'u da wad'an da yafi, dan haka ina so ka natsu ka koyi darasin rayuwa, kada kace zaka biyema wasu ka lalata rayuwar ka, duk inda aka tara jama'a akwai na banza dana kirki, abinda nakeso da kai kayi kokarin nemo na kirki kayi tarayya dasu, ni dai na yafe maka duk abinda kamun kuma zan cigaba da nema maka shiriya.
Shiru tayi tana goge hawayen da suka zubo mata. Matsawa Fawwaz yayi ya rungumeta yana kuka, kasa daurewa Alhaji yayi shima ya juya yana goge kwalla, soyayya tasa ya jefa d'ansa cikin matsala.
Wani daga cikin ma'aikatan yazo yana fad'in Alhaji lokaci yayi. Kallonshi Alhaji yayi sai yaga da alamu sabon d'auka ne dan duk ma'aikatan wajen girmamashi sukeyi. Kai ya jinjina yana fad'in naji, wucesu yayi yana fad'in kai ka taso kaje ku faskara wancan iccen.
Kuka Fawwaz ya fashe dashi yana fad'in Dady kaji ko, dan Allah kayi wani abu wallahi bazan iya wahala ba, ni gara ma asake mani hukunci arataye ni zaifin mu sauki, kwana d'aya bakaji yanda nakeji ba. Saurin tashi Ammi tayi ta bar wajen tana kuka.
Tashi Alhaji yayi yana fad'in kada ka damu zanyi magana yanzu. Kud'i yasa mashi aljihu yana bin kayan da suke jikinsa na gidan yari da kallo, wai yau 'Dansa ne yake sanye a cikin kayan nan, shida yayi shekara da shekaru yana aiko mutane gidan nan, da masu laifi da marasa laifi yau gashi shima an kawo nashi.
Juyawa yayi yana fad'in sai mun sake dawowa... Barka dai Alhaji Muhammad Sanda. Saurin jiyowa yayi yana kallon dattijon da yake tsaye kusa da Fawwaz. Ido ya tsura mashi sai dai ya kasa gane waye.
Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in dama ai bazaka sheda ni ba, domin ka yanke ma mutane da yawa hukunci zuwa gidan nan ba lallai bane ka iya gane kowa musamman wad'an da sukayi shekaru