Advertisements
Chapter 3 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 54

6K to 9K   out of 160.3K words

ta katse su, amsawa sukayi. Da sauri ta k'araso tana fad'in Yayana sannu da zuwa. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Rumaisa ya gidan? Tace lafiya lau, an gama shari'a lafiya? Ra'eez yace lafiya lau nayi nasara.


Tashi tayi tana murmushi tace naji dad'i Allah ya k'ara d'oraka akan makiya. Ra'eez yace amin 'Yar K'anwata. Mama tace an samo komai ko? Rumaisa tace an samo.


Tashi Mama tayi tana fad'in bara na tayaki naga lokaci ya kure. Da sauri Ra'eez yace aa Mama kinyi aikin ki, yanzu mune zamu shiga ofis. Dariya sukasa, Mama tace ai shikenan ayi aiki lafiya bara naje na gyara cikin kafin Abdallah ya dawo makaranta.


Ra'eez yace ina ruwan Autan Mama, ina fatan dai yana karatun sosai? Rumaisa tace ai Abdallah ba wasa, dana fad'a masa zaka zo sai kaga ya dage. Ra'eez yace saura ke, tunda kin gama makaranta.


Turo baki Rumaisa tayi tana fad'in Yaya kaima dai ka san ra'ayina ai. Harara ya wurga mata yana fad'in wannan tsohuwar magana ce, dan haka dole kiyi karatu.


Duk'awa tayi tana hawaye tace dan Allah Yaya bana son karatu. Murmushi yayi yana fad'in Rumaisa kina nan da ra'ayinki, da ace baki da kok'ari da bazan takura maki ba, kada ki manta kece zakara a makarantar ku fa, tun kafin kishiga makaranta fa kike da kok'ari, meyasa baza kiyi amfani da iliminki ba? Kece babba agidan nan, kina ganin halin da Mahaifinki yake ciki, ga Abdallah k'aninki yana makaranta, baki so yayi koyi da ke? Idan yaga baki karatu shima sai abun ya fice masa arai ai.


Hawaye ne suka zubo ma Rumaisa. Ra'eez yace ba kuka nasa kimun ba, gaskiya nake fad'a maki, a zamanin nan kowa yana son auren mace mai ilimi, ko ba dan kanki ba zaki taimaki yaranki, Rumaisa duk kok'arin ki matuk'ar baki wuce karatu ba wata rana zaki nemi ma'anar kalma d'aya ki rasa, domin shi ilimi sai ana tilawarsa yake zama, duk da kinayin islamiya amma zakisha wahala matukar bakiyi karatun boko ba, bance dole kiyi aiki ba, amma idan kikayi karatun wata rana kwalin zaiyi maki amfani, kin ganni nan bazan iya auren macen da iyakarta sakandire ba.


Da sauri Rumaisa ta d'ago tana kallonshi. Jinjina kai yayi yana fad'in da gaske nake, nafison na auri mai ilimi kodan saboda yaran mu, idan kuma auren kike so badamuwa ki fito da wanda kike so ni zan maki aure.


Mama ce ta fito tana fad'in gara dai kayi mata fad'a, kullum maganar da nake mata kenan amma ta toshe kunnanta, tunda Rumaisa ta taso take fad'in baza tayi karatu ba bayan ta gama sakandire, ada na d'auka yarinta ce ashe har zuciyarta abun yake, ko auren da kake magana ai bata kula kowa, na rasa inda tasa gaba.


Ra'eez yace barni da ita Mama, kada ki sake mata maganar karatu, nima bazan sake mata ba, kuma dole tayi aure. Murmushi Mama tayi ta shige tana fad'in aiko zan fara shirin biki.


Da sauri Rumaisa ta tashi tana dire-dire ta nufi kicin tana gungunai. Dariya Ra'eez yasa yana rufe baki. Tashi yayi yana fad'in bani alaiyahun na yanka maki. Baki ta murgud'a tana fad'in bana so. Dariyar da yake b'oyewa ce ta kwace masa, sosai yake dariya. Kayan miyar ta d'auka ta cigaba da aikinta tayi banza dashi.


Tashi yayi yana fad'in bara na d'auko maki tsarabar ki amota na manta. Bata kulashi ba yayi waje. Bayanshi tabi da kallo hawaye suna zubo mata, dole ma ta amince tayi karatu matuk'ar tana son Yayanta, da sauri ta d'auko wayarta ta rubuta mashi ya samo mata makarantar aikin lafiya ta unguwar zoma (Mid-Wife) zatayi karatun.


Tun a zaure Ra'eez yake dariya, sai da yasha dariyarsa kafin yashigo ciki, dama yasan idan ba haka yayi mata ba baza tayi karatun ba, yana matuk'ar son Rumaisa amma yafi so ya auri mai ilimi, kamar tasan yana son mace tayi aikin asibiti ta zab'i haka. Ciki yashiga ya fara taya ta aiki be nuna mata yaga sakon ta ba.


**** ****


Kwankwasa k'ofar ofis d'in Alkali yayi kusan sau biyu kafin daga ciki aka bashi izinin shiga. Tare da Brr. Bajinta ya iske Alkali. Murmushi Alkali yayi yana fad'in kaga d'an halak d'in ma, yanzu muke maganar ka ashe kana hanya.


Hannu Ra'eez ya mika masu suka gaisa cike da girmamawa. Kujera Brr. Bajinta ya nuna mashi yana fad'in bismillah. Zama yayi Alkali yace ba dai yanzu kashigo ba? Ra'eez yace tun d'azu nazo nasan baka shigo ba shiyasa na zauna a ofis.


Alkali yace ya gajiyar aikin jiya kuma? Ra'eez yace Alhamdulillahi. Brr. Bajinta yace ai jiya Brr. Ra'eez ya caza mana kwakwalwa, na rasa yanda akayi ya iya had'a wannan aikin acikin sati d'aya.


Alkali yace shiyasa nace ya sameni domin naji yanda akayi yayi wannan kok'arin, gaskiya ban tab'a samun mutum irinka mai hazaka ba, shiyasa tun ajiyan nayi masa jinjina. Brr. Ra'eez ko zaka fad'a mana yanda akayi kayi wannan aikin haka? Kada ka damu nasan ba hurumi na bane nayi maka wannan tambayar, kawai dai naga kok'arin ka ne shiyasa zan so naji daga gareka.


Murmushi Ra'eez yayi ya kauda kai bece komai ba. Tashi Brr. Bajinta yayi yana fad'in Yallab'ai zanje ana jira na a ofis. Alkali yace to badamuwa nagode.



Bayan ya fita Ra'eez ya d'ago kai, dama saboda Brr. Bajinta yaki yin magana, taya Alkali zai tambayeshi agaban abokin aikinsa bayan yasan tare suka kara.


Alkali yace yi hak'uri nayi maka tambayar da bata dace ba. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in haba ba komai. Alkali yace kawai ina so naji yanda akayi ka iya gano gaskiya ne dan gaskiya ka burgeni, zan so ka saki jiki dani, ka d'auke ni tamkar d'an uwanka dan gaskiya ka burge ni, da alama ba'a garin nan kake ba ko? Kai Ra'eez ya girgiza yana fad'in a garin nan nake, sai dai ba anan nayi karatu ba shiyasa, nayi aiki a babbar kotu da take kano na kusa shekara d'aya kafin na nemi canjin wajen aiki aka maido ni nan.


Alkali yace zuwanka alkhairi ne a kotu ta, domin ina da buk'atar mutane irin ku, domin tunda na saurari bayaninka na gano kana da gaskiya, dan haka kacigaba da rik'e gaskiya dan ita ce cikar darajar mutum.


Ra'eez yace nagode da wannan karamcin daga gare ka, kuma insha Allahu ba zaka sameni da rashin gaskiya ba. Hakika lokacin da nazo wannan kotun na kawo takardar canjin aikin da akayi mani aranar na iske wannan shari'ar, zaman da nayi ina jiranka alokacin na tsinci kad'an daga cikin shari'ar, alokacin Lauyen da yake kare Amina naji yana fad'in bazai iya cigaba da shari'ar ba, domin yayi iya bincikensa ya kasa gano komai, gashi Brr. Bajinta ya fishi sanin makamar aiki bazai iya gogawa dashi ba, yaso ya taimaka ma Amina amma dole ya hakura har ya fad'a mata ta samu wani lauyen kafin lokaci ya kure mata.



Bayan dana gama jin firarsu bayan da kazo nashiga muka gama komai kasa a nuna mani ofis d'in mu shine naje nayi masa sallama na gabatar masa da kaina na nuna masa naji firarshi ko zai iya bani dama na amshi shari'ar da yakeyi? A lokacin da nayi masa magana sosai farin ciki ya bayyana a fuskarshi, babu b'ata lokaci yashiga warware mani komai akan shari'ar.


Aranar bayan na koma gida banyi bacci ba, yanda ya bani labarin na zauna na fitar da komai, washe gari na nufi gidan marigayi nida lauyen, bayan munje muka samu Amina ya fad'a mata nine zan karb'esa.


Sosai tayi farin ciki anan tashiga bani labarin gaskiyar abinda ta sani, bayan nayi mata tambayoyi anan na gano mai aikinsu bata gidan da dad'ewa, shine nace mata ina so ta fad'a mani inda zan samu Iya, shine ta fad'a mani 'yar asalin 'Danja ce, sai dai bata san gidanta ba, amma ta tab'a fad'a mata gidanta yana bayan kasuwa wata rana da suke fira.


Bayan na gama jin labarin Iya sai na nemi da ta fad'a mani aminin Alhaji data sani, shine ta fad'a mani sunan Alhaji Kabeer, nan nace mata zan tafi tunda babu lokaci, ina so naje can garin su Iya. Haka mukayi sallama da ita muka tafi.


A ranar nabi jirgi zuwa kano, washe gari na nufi funtua sai da na huta daga can naje garin su Iya, cikin ikon Allah bansha wata wahala ba na gano gidanta, alokacin da naje mata da bayanin daga Lagos nake nasan tayi aiki agidan Alhaji k'ark'ashin Hajiya Binta.


Fad'ar sunan Hajiya Binta yasa Iya ta fara kuka tana fad'in ba laifinta bane, tun anan na gano akwai wata ak'asa, hakan yasa na lallab'ata nace ta bani labarin abinda ta sani domin Alhajin ya rasu.


Haka ta warware mani komai tana kuka, na tausaya mata domin naga nadama a idanuwanta, nan na roketa akan ta biyoni idan har ta yarda tayi nadama kuma tana so ayi mata hukunci a duniya.


Babu b'ata lokaci ta amince, domin ta fad'a mani gara a yanke mata hukunci akan rayuwar da takeyi agarinsu, duniyar tayi mata zafi koda banje ba ta yanke shawarar barin garin ta koma wani gari ko zata samu sauki. Naji dad'in maganarta, aranar muka nufi Funtua da ita, dole ta mota muka dawo saboda naga zamu b'ata lokaci.


Bayan da muka dawo naje na samu 'Dan sanda yayi mani jagora zuwa gidan Alhaji domin a bayanin Iya ta fad'a mani ta aika masa da takarda, bayan munje na tambayi Amina ko an samu wata takarda a d'akin Alhajin wadda aka fad'a masa tana da ciki? Sai tace gaskiya bata sani ba, ganin haka yasa muka nemi izinin Hajiya Binta muka shiga d'akin, cikin sa'a na samu wannan takardar dana gabatar.


Haka muka tafi na nuna masu ban samu komai ba. Bayan nan naje na samu Alhaji Kabeer, shima mun dad'e muna tattaunawa dashi kafin muka rabu, ana saura kwana d'aya a koma kotu na kammala had'a shedu na, cikin ikon Allah nazo na gabatar dasu kuma nayi nasara. Kaji yanda akayi na gano komai cikin lokaci.


Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in gaskiya Brr. Ra'eez kai na daban ne, basirar ka daga Allah take, kayi aiki da ilimi, sai kwararren lauye ne zai iya abinda kayi, sai gashi baka dad'e da aikin ba amma ka tafiyar da wannan shari'ar mai rikitarwa, gaskiya dole na yaba maka, kayi abinda ya kamata, kuma daga yau ka zama babban lauya a wajena, insha Allahu zan rik'a aiki da kai, domin ra'ayin mu iri d'aya ne, ina son mutum mai son zakulo gaskiya a duk inda take.


Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in nagode Yallab'ai. Alkali yace karik'a kirana da Abba kamar yanda Yarana suke kirana zanfi jin dad'in hakan domin nasan zakayi sa'an 'Dana na biyu, duk da banyi aure da wuri ba da nasan sai dai kazo ana ukku ma.


Ra'eez yace to Abba nagode. Alkali yace a ina kake da zama ne? Yace a Apapa nake. Alkali yace kayi aure ne ko kana zaune da Iyayen ka? Murmushi yayi yana fad'in banyi aure ba ni kad'ai nake zaune. Alkali yace Allah sarki, Iyayenka ba anan suke ba ne? Baki Ra'eez ya bud'e zai bashi labarinsa sai kuma ya tuna da maganar Kawu ( *Ra'eez ka koyi b'oye sirrin ka, a ciki hada labarin zuri'ar ka, kasan dai yanda kake kok'arin gano wad'an da suka aikata ma Iyayenka wannan abun, kuma nasan dole asan Mahaifinka agarin nan tunda babban mutum ne, kuma ana da tabbacin akwai sa hannun manyan mutane a kisanshi, a ciki hada lauyen da nake zargi domin Mahaifinka ne ya hanasu sakewa hakan yasa suke kokarin ganin bayansa, bani da sheda a hannu amma ina zarginsu domin sune abokan fad'an mahaifinka, dole ka b'oye labarinka har sai komai ya kammala domin gujema matsala, bana son kowa yasan ko kai waye, dan haka bana son ka fad'ama kowa labarin ka.*)



Gyara zama yayi yana fad'in Iyaye na suna Gombe ni kad'ai ne anan. Alkali yace Allah sarki, lallai kayi nisa da gida, bakomai ka d'auke ni tamkar Mahaifinka, idan ka tashi kajira ni sai muje na gabatar da kai a wajen Iyalina domin karik'a zuwa kuna gaisawa, ina zaune a *SURELERE*.


Ra'eez yace bakomai zan jira ka. Alkali yace nagode zaka iya tafiya. Wayar Alkali ce tayi k'ara, sallama Ra'eez yayi masa ya fita. Bayan ya d'auka suka gaisa, alamu sun nuna abokinsa ne ya kira. Shiru yayi yana jin bayanin da yake masa. Kai ya jinjina yana fad'in haba *Alhaji Marusa* wannan ai ba abun tada hankali bane, shikenan na gane bayanin ka, insha Allahu bamu da sauran matsala, na kammala shari'ar da nake fad'a maka kuma an gano gaskiya, sabon lauya ne ma ya gano komai, ai ina fad'a maka yanzu ya bar ofis d'ina, gaskiya yaron yana da hazak'a, dan haka abinda ya kamata zan rik'a bashi, sauran kuma sai aba Brr. Bajinta saboda kasan shine namu bazamuyi saurin nuna fuskar mu a wajen sabon zuwa ba. To shikenan sai kazo. Wayar ya aje yana murmushi.


Tunda Ra'eez ya shiga ofis ya gama duba takardun da suke akan teburinsa ya janwo hoton da sukayi shida Iyayenshi, alokacin bai wuce shekara takwas ba, yana tsakiyarsu suna dariya aka d'auki hoton. Koda yaushe yana tare da wannan hoto dan shine yake d'ebe masa kewar Mahaifinsa.


Zaroshi yayi daga cikin jakar da yake ajeshi (wallet) aranshi yana fad'in dole ya maidashi gida ko dan gudun b'acin rana, tunda Kawu yace ya kikaye barin duk wata alama da zata nuna koshi waye har sai ranar da burinshi ya cika.


A hankali yasa hannu cikin dabara ya goge hawayen da suka kusa gangaro masa ta gefen gilashinsa, tashi yayi yasa hoton a aljihu ya d'auki mukullin mota domin yaje ya aje hoton agida dan hankalinsa yaki kwanciya akan ya kara ko mintuna biyu a wajenshi, hakan yasa ya fita domin yaje gida ya adana hoton.


A waje suka had'u da Brr. Bajinta ya rako wasu manyan mutane, da ganinsu ba sai an fad'a maka naira ta zauna masu ba, har sun gaji da kud'i a yanayin jikinsu, motar da suke tsaye ajiki kad'ai abun kallo ce bare kuma suturar da take jikinsu. Yanda yaga Brr. Bajinta yana wani risna masu ya k'ara tabbatar masa da su d'in wasu ne.


Kai tsaye wajen daya aje motarsa ya nufa ba tare daya sake kallon su ba, maganar Kawu ce take masa yawo akan tsohon ma'aikacin wannan kotu mai suna *Brr. Barau*, akoda yaushe yafi tsayama masu hannu da shuni akan talakawa, hakan ya nuna masa yana danne gaskiya akan k'arya, tunda ya kasance shine ya tsaya har aka yanke ma Kawu hukunci amatsayin ya kare hakkin Mahaifinsa wannan ya nuna akwai wata ak'asa, duk da hakkin mahaifinsa ya kare amma kuma ai ba Kawu bane ya aikata laifin meyasa ya tsaya har sai da yaga an yanke masa hukunci? Gaskiya dole ya fara bincikensa akan Brr. Barau, to wai ma yana ina? Yasan dai zuwa yanzu kila ya aje aiki ko kuma ya zama shugaba, gashi kuma Kawu bai fad'a masa komai akansa ba, ko hotonsa bai sani ba bare idan ya ganshi ya ganeshi, amma zai tambayi Kawu inda yake.



Haka ya isa gida da wannan tunanin. Bayan ya adana hoton ya zauna yana tunanin hanyar da zai fara bibiyar Brr. Barau domin ya gano hakikanin gaskiya, dole ta kanshi ne zai fara aiki hakan zaisa ya gano komai, domin lokacin da aka kashe mahaifinsa bai bari kowa ya kai k'ara kotu ba yayi saurin amsar shari'ar Mahaifinsa yayi tsaye har sai da yaga an gama komai cikin k'ank'anin lokaci.


Saurin tashi yayi ya d'auko wani k'aramin littafinsa, sunan Brr. Barau ya fara rubutawa aciki kafin ya b'oye littafin ya kwanta yana kallon sama. Dole ya gano masu hannu akisan Mahaifinsa kodan ya sama ma Mahaifiyarsa lafiya domin ta silar mutuwarsa ta samu kanta acikin wannan hali. Ta ina ya kamata ya fara kenan? Dole yaje wajen aikin Mahaifinsa yasan zai samu wani abu, sannan lokaci yayi da Kawu zai bashi labarin Mahaifinsa, saboda Abba Mansur ya fad'a masa Kawu ne kawai zai iya bashi labarin komai. A zabure ya tashi ya d'auki mukullin motarsa ya nufi gidan Yari, bazai iya jira a k'ara kwana ba tare da yasan labarin Iyayensa ba.



Yaci sa'a alokacin da yaje suna hutawa, hakan yasa akayi kiran Kawu suka samu waje suka zauna. Kawu ya kalleshi cike da mamaki yana fad'in Ra'eez lafiya? Wannan zuwan fa? Kuka Ra'eez yasa yana fad'in daga wajen Alkali nake, yace mani yana son yarika aiki dani, gashi na gama duba sunayen ma'aikatan wajen banga sunan Brr. Barau ba, dan Allah Kawu ka bani labarin komai.


Murmushi Kawu yayi yana fad'in wannan Alkalin ai shine Brr. Barau, na fad'a maka ne saboda kasan ta yanda zaka cigaba da tarayya dashi, kuma tunda yanzu ka kawo girma dole na baka labarin komai saboda ka fara shiryama doguwar shari'a, yanzu zakaji komai......



*ASALIN LABARIN*



Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal,

3 / 54