Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
yayi yana fad'in nizan tafi, Sameer sai munyi waya kila ko zuwa goben ne sai muje can. Tashi Sameer yayi yana fad'in nagode sosai.
Mamy tace ka gaida gida dan Allah karik'a zagayowa muna gaisawa. Ra'eez yace insha Allahu. Sallama yayi mata suka fita shida Sameer.
Sai da ya shiga mota kafin Sameer ya rufe masa k'ofar yana masa godiya. Sai da ya b'acema ganinsa kafin ya koma gida cike da farin ciki.
*** ***
Sai yamma sosai ya isa asibiti, bayan sun gama shiriritar su da Ummunsa ya wuce ofis d'in likita dan Dr. Saddek ma yazo yana jiranshi.
Bayan sun gama gaisawa Dr. Saddek yace gaskiya Ra'eez jikin Ummunka yayi sauki sosai, domin a hoton da mukayi mata akwai cigaba sosai, matuk'ar zata cigaba da tunawa da abubuwan da suka faru abaya to zata dawo hankalinta, shiyasa yanzu an canza mata magani kuma akwai cigaba.
Ra'eez yace nagode sosai likita Allah ya saka da alkhairi, bansan da abinda zan saka maku ba. Dr. Sadeek yace haba ai babu komai, Allah dai ya bata lafiya. Ra'eez yace amin. Sallama yayi masu yawuce gidan su Rumaisa.
Tun a hanya Jabeer ya kirashi akan zaije gidansa sai Ra'eez yace ya sameshi gidan su Rumaisa. Dariya Jabeer yasa ya fara zolayarsa, be kulashi ba ya kashe wayar yana dariya.
Yana zaune bayan sun gama gaisawa da Mama tana masa murnar nasarar da yayi Jabeer ya kirashi. Tashi yayi yaje ya shigo dashi.
Bayan sun gaisa da Mama tasa Rumaisa ta kawo masu abinci. Ra'eez yace Mama ki barshi an kusa kiran sallah idan mukayi sai muci. Mama tace ai shikenan.
Jabeer yace Rumaisa bazaki fito mu gaisa ba? Murmushi Mama tayi tace ai tana jinka. Ra'eez yace ya akayi yau bata je islamiya ba ma? Mama tace kanta ne yake ciwo harta shirya zataje naga yanda jijiyoyin kanta suka tashi shiyasa nace tasha magani ta kwanta sai Abdallah ne kawai yaje nasan shima yanzu yana hanya.
Cike da damuwa Ra'eez ya kalli d'akin Rumaisa, badan yana kunyar Mama ba sai yaje ya ganta. Jabeer yace Allah ya bata lafiya ciwon kai beda dad'i. Mama tace amin.
Mama tace ya shari'ar taku ta kasance kuma? Zunguro Ra'eez Jabeer yayi yana fad'in ana magana fa. Harara ya buga mashi yana kallon Mama.
Murmushi tayi tana fad'in kaje ka duba jikin Rumaisar kafi jin dad'in bamu labarin. Rufe fuska Ra'eez yayi yana fad'in kai Mama! Dariya tasa Jabeer yace Mama ashe dai kin harboshi? Murmushi Mama tayi tana fad'in bara nashiga ciki na kira maka ita.
Da sauri Ra'eez yace dan Allah Mama ki zauna dama labarin nazo baki. Dariya Jabeer yasa yana fad'in haka ne Mama kizauna nima labarin zai bani sai ja mani aji yake.
Zama tayi tana fad'in ina jinka...... Labarin yanda shari'ar ta kasance ya bata har da zuwanshi gidansu Sameer.
Jabeer yace saura bayani akan hoton Sameer da yanda ya amsa laifinsa. Ra'eez yace wallahi idan maye ne kai ka kama mutum sai ka cinyeshi duka.
Jabeer yace naji kawai ka fad'a mana. Dariya Ra'eez yayi yana fad'in d'azu ma sai da Sameer ya tambayeni amma naki fad'a masa.
A cikin week end da na fad'a maka zan had'a komai, duk iya bincike na na rasa yanda zan samo shedar da zata nuna Sameer ne ya aikata laifin, Baba na kira nake tambayarsa basu da wani abu da zai nuna Sameer ne ya aikata laifin.
Sai yake fad'a mani alokacin daya d'aukota zasuje asibiti yana kok'arin gyara mata hijabinta yaji wani abu a akanta, yana dubawa yaga zobe shine ya cireshi ya aje, gashi nan ma zaije ya kaima Brr. Bajinta dan yana tunanin na Sameer ne.
Cikin sauri nace masa ya dakata zanje na amsa dan nasan ko ya bama Brr. Bajinta bazaiyi amfani dashi ba, bayan na amso nazo ina tunanin yanda zanyi dashi.
Komawa nayi unguwar su Sameer cikin sa'a na samo lambar wayarsa. Bayan na ajeta sai na shiga Whatsapp ina dubawa ko zan ganshi, cikin sa'a sai gashi, ina dubawa naga babu hoto a Dp d'inshi, har zan fita sai kuma na hau status ina cikin dubawa kawai naga ya d'ora wasu hotunanshi, yan dubawa sai naga hannunsa sanye da irin zoben da aka bani, saurin d'aukar hoton nayi.
Ban b'ata lokaci ba naje aka wanke mani hoton, sosai naji dad'in wannan hujja, ana gobe za'a shiga kotu nayi wani tunani, sai kawai na daure na kira Sameer, har ya kwanta bacci amma ina fad'a masa nine yayi saurin tashi.
Nan nake tambayarsa ya tabbata be bar wata sheda da zata tonashi ba? Sai yace mani yana da wata azurfa kuma tun bayan da abun ya faru be ganta ba, yasan kuma baya rabuwa da ita.
Anan na fad'a masa zanyi kok'arin nemota abinda nake so dashi ya fad'a mani gaskiya. Sai yace mun be aikata komai ba. Sai nace masa amma yace mun bayan abun ya faru bega zobensa ba.
Ganin na ganoshi babu b'ata lokaci ya tabbatar mani shine ya aikata laifin amma na rufa masa asiri, nan nayi masa nasiha na kuma ce masa ga zoben a hannuna, idan har ya iya fad'in gaskiya a kotu zan taimaka masa, kuma na tabbatar masa baza'a d'aureshi ba dole zab'i biyu za'a bashi nasan kuma Iyayensa bazasu bari a d'aureshi ba.
Anan ya amince zeyi abinda nace, amma nace masa kada ya fad'i gaskiya har sai na nuna zoben sannan. Kaji yanda mukayi dashi.
Jinjina Jabeer yayi masa yana fad'in gaskiya kai d'an baiwa ne Ra'eez, Allah kad'ai yasan irin baiwar da yayi maka amma ka gode masa.
Mama tace gaskiya kayi kok'ari, kaga ka fita daga zargin kowa, Allah dai ya k'ara tsare ka kuma ya baka sa'a akan shari'ar da za.... Saurin tashi Ra'eez yayi dan yasan abinda Mama zata fad'a shi kuma baya son Jabeer yasan komai yanzu.
Kallonshi tayi suna had'a ido yayi mata alama, nan take ta gane abinda yake nufi. Murmushi tayi tana fad'in duk son ganin Rumaisar ne baza'a tsaya na k'arasa addu'ar ba.
Jabeer yace idan ba ya ganta ba hankalinsa ba zai kwanta ba, ni Allah ma yasa ka bamu labarin dai-dai. Duka Ra'eez ya kai mashi da sauri ya mik'e yana dariya.
Tashi Mama tayi tana fad'in ai bakayi kokowa kana yaro ba gara kayi k'ari. Turo baki Ra'eez yayi yana hararar Jabeer da yake masa dariya.
Bayan Mama ta tashi ta turo Rumaisa. Fitowa tayi sanye da hijabi dan kanta yayi sauki. Zama tayi tana gaishe su kanta ak'asa. Saurin matsawa Ra'eez yayi yana fad'in Pretty na ya kan naki? Murmushi tayi tana fad'in ya warke ai.
Ra'eez yace bana son wasa da lafiyar ki kizo muje asibiti. Jabeer yace kaji mani mutumi, tace ta warke zaka jajibo mata wani asibiti.
Ra'eez yace malan ba ruwanka, kai da ko tsuntsu baka kiwo taya zakasan yanda ake kula da mutum ma, dan Allah idan ana maganar Iyali kadena tsoma baki.
Baki Jabeer ya rik'e yana kallon Ra'eez. Gwalo yayi masa ya zauna gaban Rumaisa ya juya ma Jabeer baya yana dariya k'asa-k'asa.
Tashi Jabeer yayi yana zungurinshi da k'afa yana fad'in ni zan wuce bazan iya tsayawa kallon kayan haushi ba. Dariya Ra'eez yasa yana fad'in kaje kayi fira da Baba Madu yanzu zan fito muje masallaci.
Wucewa Jabeer yayi yana murmushi, sai da ya kai k'ofa sannan yace daga masallaci wajen Raheenar ka zamuce ko dan nasan shine dalilin da yasa kace nazo nasan baka iya zuwa kai kad'ai.
A zabure Ra'eez yayi kanshi jin Bom d'in da yake had'a masa. Da gudu Jabeer yayi waje yana dariya. Kwafa Ra'eez yayi ya dawo wajen Rumaisa kada ta yarda da abinda yace.
**** ****
Kai amma Alhaji ka tsallake rijiya da baya, gaskiya Ra'eez d'an albarka ne, shiyasa nace maka gara azo ayi maganar auren su da Raheena tun kafin wata ta kwace matashi.
Gyara zama Alhaji Barau yayi yana fad'in abinda nake tunani kenan, jira nake yazo nasa Raheena tayi masa magana na fad'a masa ya turo iyayenshi ayi magana dan bana son aja bikin tunda mu duka kowa yana da halinsa.
Momy tace yauwa Alhaji dan Allah kada yawuce wata d'aya, kaga sai ka bani kud'i muje Dubai nida Raheena mu zab'o kayan da take so, idan so samune a cikin sati mai zuwa muje.
Alhaji yace haka ne, bakomai ku fara shiri zansa a nema maku Visa zuwa asabar sai ku tafi, dama bani da matsala akan kud'i dan akwai su a account kawai tura maki zanyi.
Murmushi Momy tayi tana fad'in dole ayi bikin da zai girgiza mutane, naji dad'i da muka tara yanda kowa zaizo ya dangwali arziki.
Alhaji yace ai da wuri zan bugo kati saboda kowa ya samu dan wannan babban biki ne. Momy tace Allah ya k'ara girma. Yace amin.
**** ****
Washe gari tunda wuri Ra'eez yaje wajen aiki, yana zuwa kai tsaye d'akin ajiyar tsofaffin kundi ya nufa yana addu'ar Allah yasa mai kula da wajen yazo.
Cikin sa'a ya sameshi, da sauri ya k'arasa ya fara gaishe shi kasancewar babban mutum ne. Murmushi mutumin yayi yana fad'in Malan Ra'eez ya gajiyar shari'ar jiya kuma? Ra'eez yace lafiya lau gajiya tawuce *Kawu Datti*.
Murmushi yayi cikin jin dad'in abinda Ra'eez ya kirashi dashi. Kallonshi Ra'eez yayi yana fad'in dama Kawu Datti akwai wata alfarma da nake son na nema awajenka idan babu damuwa.
Kawu Datti yace haba bakomai fad'i koma menene kaji Ra'eez. Cike da fatan nasara Ra'eez yace dama akwai wani kundi da nake son dubawa ne domin jiya Iyalan mutumin suka sameni ganin mun kammala wannan shari'ar suka kawo mani wata magana data girgiza ni, duk da nasan abun akwai wuya amma sun roke ni na tausaya masu kuma na masu alk'awarin zanzo na duba kundin ko bazan iya yin komai akai ba, shine nake son ka taimaka na duba kuma inason abun ya zama sirri dan Allah.
Murmushi Kawu Datti yayi yana fad'in kada kaji komai Ra'eez, kasa aranka tamkar da kurma kayi magana, domin bazan iya fidda sirrin makiyina ba bare kuma kai, wallahi Ra'eez tun shari'ar da kayi akan 'Yar uwata nake jinka araina, nasan baka san Amina 'yar uwata bace, idan baka manta ba shari'ar ka ta farko wata Amina daka tsaya mawa, to ita d'in tamkar 'Ya take awajena, kuma mijinta shine silar zamana anan gashi har yanzu ina cin gajiyar aikin, dan haka ka d'auke ni tamkar d'an uwanka bazan tab'a cin amanar ka ba.
Jinjina kai Ra'eez yayi cike da farin ciki yace nagode Kawu Datti, shari'ar anyita ne shekarar 2008, kila kana nan lokacin da akayi ta ma.
Jinjina kai Kawu Datti yayi yana fad'in tabbas ina nan, domin na fara aiki anan a shekarar 2005, duk wata shari'a da akayi a bayan wannan shekara babu wadda ban sani ba sai dai na manta, matuk'ar na zauna na saurareta kuwa to nasanta, kuma duk wasu kundi suna cikin d'akin nan nida abokin aikina muke kula dasu dan yau ma na amshe shi aiki.
Ra'eez yace amma naji dad'i nasan kila kasan shari'ar, dama ina so na samu wanda yasan shari'ar saboda ban tsaya na fahimci abinda suke nufi ba, sunce nayi kok'ari na duba kundin zan fahimci komai.
Kawu Datti yace akan me akayi shari'ar? Ra'eez yace akan tsohon shugaban Kwastam Alhaji Hamza Maiwada wadda aka mik'a direbansa Malan Sani gidan yari akan laifin shine ya kashe shi kuma yayi yunkurin yima matar Alhajin fyad'e silar haka ta samu tab'in hankali.
Girgiza kai Kawu Datti yayi yana fad'in kace azzalumar shari'a, ai bazan tab'a mantawa da wannan shari'ar ba, domin tunda na fara aiki ban tab'a cin karo da shari'ar da na zubar ma kwalla kamar k'aramin yaro ba irin wannan, kai Ra'eez wata shari'ar sai a lahira, amma Allah bazai bar azzalumai ba, domin wallahi tun a lokacin kawai naji ban yarda da shari'ar ba, dan dai an gabatar da shedu masu kyau, amma tabbas nasan akwai munakisa a shari'ar.
Kwalla ne ya ciko ma Ra'eez yayi saurin kauda kai yana kok'arin maidasu. Kawu Datti yace kayi hak'uri yanzu mutane sun fara zuwa, bana son kowa yasan abinda zakayi, domin naji ajikina zaka taimake su, ka bani lambarka zanyi kok'arin nemo maka kundin na kawo maka shi a b'oye ba tare da kowa ya sani ba, idan yaso sai ka kwafeshi ka maido amayar gudun matsala.
Murmushin jin dad'i Ra'eez yayi yana masa godiya. Lambarsa ya bashi shima ya bashi kafin yayi masa sallama ya tafi, sosai yaji dad'i da Allah yasa Kawu Datti ya iske dan yafi Malan Salisu fuskar kamala.
Wajen k'arfe da'ya Sameer yazo ofis d'in su Ra'eez, waya yayi masa ya fita suka had'u, shine yayi masa jagora ya gama cike komai na shedar biyan kud'in tarar da kotu tayi masa, bayan sun gama yace ma Ra'eez maganar zuwa gidan su Halima.
Kallon agogo Ra'eez yayi yana fad'in yanzu lokacin cin abinci ne, ina ganin muyi amfani da wannan damar muje mu dawo. Murmushi Sameer yayi yace nagode Ra'eez, Allah yasa Halima ta yafe mani. Ra'eez yace amin. Jabeer yayima magana yazo suka wuce.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣1⃣
Jinjina kai Baba Haruna yayi yana goge idonshi yayin da Sameer yake tsugunne akusa dashi shima kukan yake da alamu neman gafara yakeyi.
Kallonshi Baba Haruna yayi yana fad'in shikenan Sameer, k'addara ta riga fata, haka Allah ya tsaro ma Halimatu dole sai ta faru kuma, tabbas nasan da ace alokacin da abun ya faru nazo gidan ku na sanar maku bazaku saurare ni ba, da ace kamar yanda kazo ka rok'i yafiya irin hakan ne zai kasance alokacin da zanje gidan ku da farko wallahi bazan tab'a fitar da maganar duniya ta sani ba, amma sanin halin masu kud'i yasa dole sai da kowa yaji wannan maganar, a hakan ma badan wannan bawan Allah Ra'eez ya tsaya mana ba da shikenan ahaka zamu shigar da k'ara amma a tozar tamu kuma a sake b'atama Halima suna, amma duk da haka mungode ma Allah, bakomai, Allah ma muna masa laifi murokesa yafiya kuma ya gafarta mana, ni kama na yafe maka, bara na kira Mahaifiyarta da ita kuyi magana.
Bayan sunzo Sameer ya d'ora guiwarsa k'asa ya had'e hannuwansa biyu yana rokon su yafiya. Cikin kuka Maman Halima tace ta yafe masa. Kallon Halima yayi yana sake rok'onta.
Jinjina kai tayi tana share hawayen idonta tace na yafe maka, koba komai ta silata Allah ya ganar da kai gaskiya, kuma bazan bijirema Allah ba naki yafe maka ba, ina fatan kamar yanda ka cutar dani kuma ka rokeni yafiya na yafe maka Allah ya d'aukaka rayuwata, yasa ko nan gaba kada na wulak'anta daga ni har zuri'ata.
Gaba d'aya suka amsa da amin. Ra'eez yace gaskiya Halima kinyi matuk'ar burge ni, domin kalamanki masu tsada ne sai mai zurfin ilimi ne zai iya amfani dasu, gasu sun fito daga bakin mai k'ananun shekaru, ubangiji Allah ya amsa addu'ar ki amin.
Jabeer yace Allah ya k'ara tsare gaba, ga wannan check d'in kud'in ki ne da kotu tace abaki, Baba idan kana da asusu a banki sai muje a ciresu asaka aciki domin zasuyi mata amfani wajen karatun ta.
Baba yace gaskiya banda wani asusu a banki, amma inaso aje a bud'e da sunan Halima sai azuba su ciki, hakika badan hakkinta bane babu abinda zaisa na amshi kud'in nan, amma sune zasu taimaka ma rayuwarta wajen inganta, domin burin ta ne karatu musamman a fannin lafiya.
Kallonshi Sameer yayi yana fad'in ta kammala makaranta ne Baba? Kai ya d'aga masa yana fad'in sakamakonta ma yayi kyau.
Jinjina kai yayi yana fad'in zaka iya barinta taje waje tayi karatun fanin lafiya kamar a Madina? Shiru Baba yayi yana tunani. Ra'eez yace Baba ka barta ta tafi, domin Madina k'asa ce mai kyau, kuma zatayi karatu hankalinta a kwance, sannan zata koyo abubuwa da yawa na addini, a ganina Halima tana da natsuwar da zatayi karatu a waje.
Kai Baba ya jinjina ya kalli Halima yana fad'in zaki iya Halimatu? Saurin d'aga kai tayi tana sakin murmushi. Baba yace shikenan na amince, nasan wad'an nan kud'in zasu isheta ta kammala karatun ta.
Sameer yace Baba zan bayar da naira million biyar nasan zasu isheta ta kammala karatunta, sannan nine zan sama mata makarantar, wannan itace babbar kyautar da zan bata bisa yafiyarta agare ni, fatana Allah yasa kada mu samu rabo a tsakanin mu.
Baba yace nagode sosai, kuma insha Allahu babu rabon da za'a samu, domin tun a asibiti wannan malamar ta kawo mana wani magani tace abata tasha insha Allahu ciki bazai shiga jikinta ba.
Sameer yace amma naji dad'i sosai, kuma zanje nayima sister Asabe kyauta domin ta taka rawar gani akan wannan matsala, Allah ya k'ara tsare gaba. Gaba d'aya suka amsa da amin.
Ra'eez yace gobe idan Allah ya kaimu ko daga ofis ne zan zo na d'auki Halima muje a bud'e mata asusu a banki. Sameer yace muje na rubuta mata kud'in sai a had'a dasu.
Godiya sukayi masu kafin suka masu sallama suka tafi.
Bayan sun koma Sameer yace nagode sosai