Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
ka ko? Murmushi likita yayi yana fad'in da alama yau zan baku sallama. Zama Ra'eez yayi yana fad'in wallahi da yafi.
Dariya suka sa Jabeer yace aikuwa sai jibi. Rafeek yace tunda dai ya warke ai shikenan. Matsawa Likita yayi yana fad'in bara na duba na gani.
Har likita ya gama dubashi yana hararar Jabeer. Kallon Rafeek likita yayi yana fad'in gaskiya jikin lauya da sauki, ko yanzu zaku iya tafiya gida.
Rafeek yace nima naga alamun sauki gara asallameshi mu koma gida. Likita yace shikenan bara ayi sallah. Jabeer yace mungode.
Sai da sukayi sallah kafin suka had'a kaya suka wuce. Kai tsaye gidan Ra'eez suka wuce dan Rafeek yace Jabeer ya kwana acan zuwa gobe sai suje wajen Mama aji abinda ta yanke akan zaman Ra'eez.
**** ****
Washe gari tare da Jabeer suka nufi gidan su Rumaisa, Mama tayi mamakin ganin su dan sauri take ta had'a kayan abinci Rumaisa ta kai masu.
Bayan sun gaisa suka fad'a mata sallamar da akayi masu. Murmushi tayi tana fad'in to Allah ya k'ara sauki, kaga yanzu sai kuje a kwaso kayanshi ga d'aki can ya zauna aciki.
Jabeer yace Mama ina ganin abar Ra'eez a gidanshi zaifi, domin a ayanzu akwai shirin da zamu fara kuma yana buk'atar natsuwa, tun bayan da ya bani labarinshi na fara tunanin yanda zan taimakeshi, rashin lafiyarsa da sanin abinda yake damunshi yasa na yanke shawarar komawa kusa dashi kafin Allah ya bama Ummu lafiya, hakan yasa na samu Iyaye na nayi masu bayanin zan koma gidanshi mu zauna, kuma sun amince mun.
Jinjina kai Mama tayi tana fad'in gaskiya mungode, dama haka Allah yake, idan ka rasa wani jigo sai ya baka madadinsa, hakika kai aboki ne nagari, Allah ya saka maka da mafificin alkhairin sa.
Jabeer yace amin. Rungume Jabeer Ra'eez yayi yana hawaye. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in meye na kuka kuma, yanzu ka zama d'an uwana.
Bayan sun karya Jabeer ya bar Ra'eez anan yawuce gidansu saboda zaije wajen aiki. Shimfid'a Mama tayi masa a falo ya kwanta dan bacci yake ji saboda maganin da yasha.
Sai da Rumaisa ta kammala aikinta kafin taje ta zauna a kusa dashi, duk da bacci yake amma haka ta zauna tana gadinshi.
Wayarsa ce tayi k'ara, tana dubawa taga ansa Raheena. Tsaki tayi ta maida wayar silent. Ganin an cigaba da kira yasa ta d'auka.
Cikin sauri tace bacci yakeyi. Raheena tace Rumaisa ce? Kai ta d'aga tana fad'in itace. Raheena tace dama naje asibiti akace an sallameshi shine nake son naji inda yake nazo.
Rumaisa tace ai bacci yakeyi ki bari zuwa anjima da rana sai amaki kwatance kizo. Ba haka Raheena taso ba amma haka ta daure tayi mata godiya tare da kashe wayar.
Murgud'a baki tayi tana fad'in jarababbiya kawai, hakanan kin takuwara ma mijina, wallahi badan shiri bane da na nuna maki iya karki dan bazan lamunci had'a Annur da kowa ba.
Haka tayi ta masifa tamkar agaban Raheena take. Ra'eez da tun farkon wayar ya tashi ido ya tsura mata sai murmushi yakeyi ganin yanda ta dage tana masifa ita kad'ai.
Kamar ance ta juyo, waro ido tayi ganin Ra'eez ya tashi yana kallonta, da sauri ta yunkura zata gudu yayi saurin jawota ta fad'o jikinshi. Tusa kanta tayi tana mashi shagwaba.
Dariya yayi ya tashi tare da cire hannunshi ajikinta yana fad'in babu inda zaki sai kin mai-maita abinda kika fad'a.
Rufe fuska tayi ta zame gefe tana fad'in nifa bance komai ba. Ra'eez yace shikenan, amma ki sani ina binki bashi. Saurin d'aga kai tayi tana fad'in naji.
Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Raheena, kallon Rumaisa yayi yana kallon wayar. Tsam ta tashi tayi waje da sauri. Murmushi yayi kafin ya d'aga.
D ina kwana ya jikin? Lafiya lau, ya amsa cike da yanga kamar mace. Wayyo D d'azu na kira Rumaisa ta d'auka wai kana bacci, dama ina so nazo na dubaka tunda ance an sallameka.
Yatsina fuska yayi yana fad'in ki barshi bana son kina zuwa kunyar Mama nakeji. Murmushi tayi tana fad'in nikam bazanji dad'i ba idan banzo ba, kasan fa har yanzu gajiyar Dubai bata sakeni ba amma tunda naji baka lafiya naji bazan iya zama ba, muma ranar lahadi muka dawo cikin dare, naso na kira alokacin amma naga dare yayi, da safe kawai Dady ya fad'a mana kana asibiti nan take naji gajiyar ta tafi.
Murmushi yayi yana fad'in kun dawo lafiya ko? Raheena tace lafiya lau, kayan suna hanya sai zuwa jibi zasu iso, D bakaga zab'en da nayi mana ba, tsarabar ka tana nan idan kazo zan baka.
Girgiza kai yayi yana fad'in ki adana mun ita sai nan gaba zan amsa. Kai ta jinjina kamar yana ganinta tace angama Angona, fatana Allah ya baka lafiya.
Ra'eez yace ina so na kwanta. Murmushi tayi tana fad'in ka huta lafiya idan ka tashi ka kirani kada na kira kuma baka tashi ba na katse maka bacci.
Ra'eez yace angama. Kashe wayar yayi yana sakin murmushi. Hannu yasa yana shafa wuyansa, ta wani gefen yana tausayin Raheena, bayaso Allah ya kamashi da laifin yaudara, Raheena batayi masa komai ba, asalima lokacin da abun ya faru batasan komai ba, mahaifinta ne me laifin shi yakamata ya amshi hukunci ba ita ba, amma dole ya dakatar da komai koda hakan zai ruguza amintakar da Alhaji Barau yayi masa, domin ko yanzu suka b'ata bazai damu ba, domin lokacin fafatawa yayi.
Ajiyar zuciya ya saki yana tunanin hanyar da zaibi dan kada ya cutar da zuciyar Raheena, yasan koya rabu da ita yayi mata gata, domin ta silar shi ta canza rayuwar ta wacce duk wanda ya aureta zaiji dad'in hakan. Lumshe ido yayi yana tunani.
***
Har la'asar suna tare da Jabeer, tashi sukayi domin suje gidan su Jabeer daga can su wuce gida. A tare suka fito. Mama tace ina kuma zakuje? Jabeer yace ai gara mu fita hakan zeyi masa dad'i, zamuje gidan mu daga can mu wuce.
Mama tace to abincin daren fa? Ra'eez yace Mama kinsan bana cin abu mai nauyi da dare. Mama tace to Jabeer fa? Jabeer yace nima hakan take mama.
Murmushi tayi tana fad'in haka kawai kun maida kan ku turawa, ai shikenan sai Allah ya kaimu, amma kasha maganin ka. Ra'eez yace to Mama.
*** ***
Kamar ya saba da 'yan gidan su Jabeer haka sukayi ta fira, har isha'i suna tare, anan suke jin Kawun Jabeer zaizo gobe. Jabeer yace yauwa idan yazo zanyi masa maganar ka, kaga sai muzo musameshi muji yanda zaice. Ra'eez yace Allah ya kaimu.
Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Yaya Rafeek, bayan sun gaisa yace yana jiransu a gidanshi tare suke da Adnan k'anin Sameer zasuyi magana akan mutuwar Naseer.
Ra'eez yace gamu nan zuwa. Tashi sukayi suna masu sallama suka nufi gida cike da farin ciki, koba komai zasu fara samun hujjar shiga kotu.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣5️⃣
Kamar yanda nace maku mu ukku ne abokai a kings college, tun farkon had'uwar mu muka kulla abota, duk wanda yazo makarantar atare ya sammu, domin kusan arana d'aya mukaje, hakan yasa wasu suke tunanin 'yan uwa ne mu.
Duk cikin mu Fawwaz ya fimu wayewa, domin Mahaifinshi yafi namu kud'i, sannan gatan da ake masa ba'ayi mana, sai Sufwan, shima d'an gata ne, a cikin mu ni kad'ai ne nake shakkar Mahaifiyata, duk da Abban mu yana mana gata kuma baya hana mu abinda muke so, amma gaskiya Mamy tana kula da mu sosai.
A hankali muka zama manya amakarantar, ajin mu d'aya da Naseer, ganin yana da kok'ari yasa muke kulashi, munso mu jawoshi cikin mu amma yaki amincewa domin yanayin mu da nashi ba d'aya bane, abokinsa d'aya Munnir. Ganin yaki bamu had'in kai yasa muka kyaleshi amma duk da haka muna gaisawa.
Zuwan mu aji shidda Fawwaz ya k'ara zama tantiri, wani abun ma muna tsawatar masa amma duk da haka sai abinda yaga dama, akwai wata yarinya *Minal* aji biyar take alokacin, Fawwaz yana matuk'ar sonta, sai dai ita bashi take so ba, wani d'an ajin mu take so *Farouk*, Fawwaz ya dad'e yana jama Farouk kunne akan ya rabu da Minal amma yayi banza dashi, saboda shima akwai zuciya.
Ganin abun ya fara koma masu fad'a yasa muka fara bama Fawwaz hakuri akan ya rabu da ita ya nemi wata, amma yace bazai hakura ba.
Wata rana da yamma zamu tafi gida yaga Minal da Farouk suna zaune suna shan lemu, takawa yayi har inda suke, yana zuwa ya kwashe Farouk da mari, cikin zafin nama Farouk ya rama, yana marinsa Minal ta k'ara masa hada juye masa lemu a jiki.
Saurin rik'e Fawwaz mukayi gudun kada abun yayi tsamari, duk yanda yaso mu sakeshi kiyawa mukayi, haka muka turashi mota naja muka tafi gida.
Washe gari koda mukazo makaranta muna zaune sai dai mukaga Fawwaz yana murmushi yana sakin kwafa, da muka tambayeshi lafiya yace bakomai.
Aranar mun tsaya lesson har yamma, bayan mun tashi mukaga Fawwaz ya mik'e ya fita da sauri, juyawar da mukayi sai mukaga ashe Farouk ne ya fita zuwa bayan aji da alama band'aki zaije, har mun zauna sai kuma muka tashi muka bi bayansu.
Kafin mu k'arasa muka hangosu suna fad'a, kasancewar wajen babu mutane yasa babu wanda yagansu, da sauri muka nufesu, sai dai kafin mu isa Fawwaz ya zaro wuk'a ya yankar masa wuya nan take ya zube.
Cike da firgici muka isa tare da rik'e Fawwaz, muna dubawa mukaga Farouk baya numfashi, cike da tashin hankali na fige wuk'ar naje na sata cikin wani k'aton rami da ake kona bola, dawowa nayi mukaja Fawwaz muka wuce, sai dai alokacin naga Naseer ya juya baya da gudu ya bar wajen yana kok'arin maida wayarsa aljihu, tabbas ko ba'a fad'a ba nasan ya d'auki abinda ya faru.
Sai alokacin shima hankalinsa ya tashi. Kuka yasa yana fad'in shima kashe shi za'ayi, lallashinsa muka farayi muna fad'in bazamu bari kowa yasan shine ya kashe shi ba, saboda muna son junan mu.
Kai tsaye gidansu muka nufa, wajen Dadynshi mukaje, bayan daya gama jin abinda ya faru na d'auka zai shiga tashin hankali ko kuma yayi ma Fawwaz fad'a amma sai naga cikin ko in kula ya kamo kafad'ar Fawwaz yana shafa kanshi yana fad'in Auta ka kwantar da hankalin ka, meye zaka tashi hankalin ka dan d'an wannan abun, ka d'auka kwananshi ne ya k'are, dan haka ba kaine ka kashe shi ba tsautsayi ne ya kai wuk'ar hannunka wuyanshi, amma babu mai kashe wani sai Allah, dan haka ka kwantar da hankalin ka kacigaba da hidimar ka tamkar yau aka haife ka, bana so ka nuna damuwa, ina fatan babu wanda ya ganku? Suka amsa mashi da babu. Saurin kallonshi nayi nace masa naga wani abokin mu Naseer ina tunanin ya d'auki abinda ya faru kuma ya gani da idonshi dan naganshi yana maida waya aljihu.
Jinjina kai yayi yana fad'in nine Alkalin babbar kotu, kome na fad'a ya zauna, ko case d'in yaron baza'a kaishi kotu ba bare aje afara bincike, zakuce na fad'a maku babu wanda zai tada maganar kawai gawar yaron za'a d'auka a rufe Iyayenshi suyi hakuri, dan haka kuje kawai, shima waccan yaron zansan yanda zanyi dashi.
Kud'i ya bamu masu yawa yana fad'in kuje kusayi wani abu. Anan take Fawwaz ya warware, ni kuwa jikina ne yayi sanyi sosai, ba dan ina son Fawwaz ba babu abinda zai hana na rabu dashi, amma amintakar mu daban take. Haka na wuce gida jiki a sanyaye, aranar da zazzab'i na kwana.
Washe gari haka mukaje makaranta abun mamaki babu wanda yaje da sunan bincike, sai nake jin labarin wai an tsinci gawar Farouk a bayan gari an yankashi, koda na tambaya a ina nayi tunanin za'ace a makaranta amma babu wanda yace haka, abun ya bani mamaki, nan Fawwaz yake rad'a mana ai Dadynshi ne yayi komai, muna tafiya yayi magana da shugaban makarantar akaje inda gawar take aka fita da ita ba tare da kowa ya sani ba, wannan dalilin ne yasa babu wanda yasan a cikin makarantar aka kashe shi, sai dai aka buga ajarida amma Iyayenshi basu tada maganar ba saboda basu san wanda zasu tuhuma ba.
A ranar mun dawo daga yawo mukazo gidansu Fawwaz kawai muka iske Dadyn Fawwaz yayi bak'i, anan aka kiramu, Brr. Barau shine wanda ya tambaye mu kwatancen gidan su Naseer tare da hotonshi, bayan mun bashi ya sake ja mana kunne akan kada mu fadama kowa, nan muka jaddada masu babu wanda zamu fad'amawa.
Kafin mu wuce naji yana waya da wasu yana fad'a masu kada su bar Naseer, su amso abinda ya d'auka kuma su kashe shi. A lokacin nashiga firgici jin za'a kashe Naseer, tun daga lokacin naji Fawwaz ya fice mun arai, nayi danasanin tarayyar mu, haka na wuce gida.
Washe gari sai labarin mutuwar Naseer naji, tun daga lokacin zuciyata ta tsinke, haka kuma tarayyata da Fawwaz tayi baya, Allah yaso zamu fara jarabawa babu sauran zama amakaranta, hakan yasa ban cika shiga cikinsu ba, bayan mun kammala jarabawa aka fitar da Fawwaz waje, tun daga nan muka rabu sai dai waya.
Shigata makaranta a hankali halayyata ta canza, a hankali na rika shiga damuwa saboda abubuwan da suka faru sun kasa barin zuciyata, shiyasa har yanzu ban mance abinda ya faru ba, duk da an d'auki shekaru na kasa manta koda kalma d'aya ce, wani lokacin inajin kamar ina da laifi, domin nayi tarayya wajen b'oye mai laifi, kuma nine silar tona Naseer, domin nine na fad'a ya gammu.
Abinda ya faru da Yaya Sameer da kammala komai har zuwanshi wajena ya fad'a mun Fawwaz ya dawo da abinda yakeso nayi yasa hankalina ya sake tashi, kuma nayi alk'awarin a wannan karon zan tsaya na bada kowace irin sheda ake buk'ata domin a tabbatar da gaskiya, duk abinda ya faru yana nan a zuciyata be goge ba, dan haka ashirye nake domin bada sheda.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in tabbas wannan 'Yallab'ai d'in da muke nema ina kyautata zaton tsohon Alkali ne wato mahaifin Fawwaz, domin alokacin da sukaje gidansu Fawwaz su ukku sun had'u, kunga kenan shine na hud'unsu.
Rafeek yace babu tantama shine na cikon hud'unsu, kuma dole zamu tabbatar da abinda zai tona asirinsu, ayanzu mu kad'ai ne mukasan gaskiya, kuma mu dukan mu babu wanda yake da tsinken da zai iya rik'ewa a matsayin hujja, kotu bata amfani da hujjar baki, ko shari'ar muka dawo da ita baya sune zasu sake nasara domin sune masu hujja mai kwari, dan haka ba yanzu zamu tado da maganar ba.
Jabeer yace wannan haka yake, gobe zan samu Kawu da maganar abinda yace zakuji, Yaya dole mu fara bincike a b'oye, sai mun had'a komai kafin mu fara aiki.
Ra'eez yace ina ganin shari'ar su Naseer zamu fara, itace zata tono waccan shari'ar. Rafeek yace haka ne, domin muna da d'an wani abu akan shari'ar Naseer, duk da itama ba mai kwari bace, domin d'ayan abokinsu ya mutu, ko yana nan su biyu bazasu bada sheda ba, ko sun bada baza tayi amfani ba saboda abaki take, kunga anan ma sai mun zurfafa bincike.
Jabeer yace Adnan kana da hoton ku alokacin kuna makaranta? Adnan yace ina da su sosai ma. Jabeer yace Fawwaz bazai iya k'aryata abotar ku ba, kana da labarin shugaban makarantar ku? Adnan yace e amma yanzu baya makarantar ya aje aiki, sai dai nasan gidanshi dan d'anshi abokina ne.
Rafeek yace turk'ashi, yanzu ya za'ayi musamu ganawa dashi bana so abokin ka yayi tunanin kayi masa rashin mutunci idan yaji kana dasa hannu wajen saka Babanshi cikin masu laifi.
Adnan yace a wannan gab'ar babu batun abotaka, tunda har na amince zan tsaya a yanke ma babban aminina na da hukunci babu wanda zan iya rufa ma asiri, domin shi Nabeel jami'a mukayi dashi, shikuwa Fawwaz akwai shakuwa atsakanin mu, dan haka ku bani lokaci insha Allahu Nabeel zai bamu goyon baya, duk da Babanshi ya aikata laifi amma dole a hukuntashi.
Rafeek yace mungode sosai, kuma zamu tafiyar da komai yanda ya kamata, idan komai ya kammala zasu san gata mukayi masu domin sun huta amsar hukunci a lahira.
Tashi Adnan yayi yana fad'in zan wuce gida dare yayi. Rafeek yace muje na aje ka zamuyi waya. Hannu ya bama su Jabeer suna ta masa godiya. Rafeek yace zuwa gobe zan fara binciken mutanan da sukayi tarayya a waccan shari'ar.
Jabeer yace nima a goben zan samu Kawu da maganar. Ra'eez yace Allah ya kaimu, nima gobe zan koma aiki. Tashi sukayi suka rakasu kafin suka dawo.
Bayan sun kwanta wayar Ra'eez tayi k'ara, yana dubawa