Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
Da wannan sana'ar sosai yake samu, yana aikinsa kuma yana cigaba da gininshi, ya dad'e beyi aure ba sai daga baya yayi aure inda ya auri matarsa Halima, itama 'yar Katsina, gidansu gidan rufin asiri ne, mahaifinta d'an kasuwa ne, hakan yasa ta taso cikin tarbiya da sanin rayuwa.
Bayan da yayi aure sai ya barta a gidan Mahaifiyarsa shi kuma ya koma Lagos, sai ya samu lokaci yake zuwa wajenta, sai dai duk wata yana yi mata aike.
Da haka Allah ya bashi ikon kammala gininshi, inda yayi d'akuna biyu ciki da falo sai band'aki da kicin sai tsakar gida, daga gefen tsakar gidan kuma an fitar da wani d'aki sai dai bai fara ginashi ba ya fitar dashi ne saboda zuwa gaba idan ya samu hali ya gina d'akinshi sai ya bar ma Halima wancan koda ta haihu.
Bayan daya gama komai yaje ya d'auko matarsa suka dawo nan da zama. Sun dad'e basu samu haihuwa ba har Allah ya taimakeshi kamfanin Fanta suka d'aukeshi aikin direba.
Sosai yayi farin ciki da wannan aikin daya samu musamman daya maido da Iyalinsa Lagos nauyi ya k'aru sai gashi kuma Allah ya taimakeshi da aiki mai kyau. Haka suka cigaba da zaman rufin asirin su yayin da Halima ta fara sana'ar saide-saide a cikin gida har Allah ya basu k'aruwa.
*Wannan shine labarin Malan Sani.*
***** ****
Washe gari bayan sun gama karyawa wajen k'arfe goma Malan Sani ya fita domin ya cika alk'awarin da yayi ma Alhaji Mai Wada. Tafiya yake yana tunanin dalilin da yasa Alhaji yake zaune a wannan unguwar, yasan dai duk wanda aka kawo aiki na Kwastam ana bashi wajen zama bare kuma shi da ya kasance shugaba, sai gashi yazo wannan unguwar ya zauna. Da wannan tunanin ya isa k'ofar gidan Alhaji Mai Wada.
Yana kwankwasawa Maigadi ya bud'e. Bayan sun gaisa ya fad'a masa yazo wajen Alhaji ne. Murmushi Maigadin yayi yana fad'in Malan Sani ko? Kai ya d'aga yana mamakin yanda akayi har Alhaji ya fad'ama Maigadi zuwanshi.
Wajen zama ya nuna mashi yana fad'in ai tun jiya Alhaji ya sanar dani zuwanka, shiyasa kana zuwa nayi tsammanin kaine, domin babu wanda yake ma Alhaji sallama da safe haka musamman irin wannan ranar da baya fita aiki da wuri.
Malan Sani yace Allah sarki, ai da yake yau asabar ma'aikata kowa yana hutawa ba aiki. Maigadi yace gaskiya banda Alhaji, gobe ne kawai nasan baya fita wajen aiki, amma asabar yana fita sai dai bada wuri ba, sannan baya wuce magriba ya dawo gida sai ya wuce masallaci wajen da suke d'aukar karatun asabar da lahadi.
Gyara zama Malan Sani yayi yana fad'in gaskiya ban tab'a ganin mutum irin Alhaji ba, a sanina duk wanda ya kai matsayi irin nashi musamman a aikin Kwastam gidan kud'i da wuya kaga yana rayuwa makamanciyar tashi, unguwar da yake zaune kad'ai abun mamaki ne, sai irin yanda yake rayuwa kuma.
Maigadi yace indai Alhaji ne yanzu ka fara ganin abubuwan mamaki a wajensa, sam be d'auki duniya da zafi ba, mutum ne shi mai saukin kai, ga addini, kana ganin yawancin masu irin aikinsu yanda suke kasancewa musamman idan akace su kad'ai suka zonan ba tare da Iyalin su ba, sai kaga sun aikata abinda suka ga dama.
Ka ganni nan tun farkon zuwan Alhaji garin nan Allah ya had'ani dashi, yazo unguwar nan yana neman gidan haya mai kyau shine naji wasu suna neman damfararsa, ina gefe sai banyi magana ba, asalima sai na tashi nabar wajen dan bana so su fahimci ina wajen kasan yanda rayuwar Lagos take yanzu zasu far maka.
Bayan da suka gama shima kamar ya san mai suke nufi sai yace masu bara yaje ya dawo, ganin basu samu nasara ba sai suka wuce suka kyaleshi. Har yashiga mota yayi hanyar fita na tarbeshi, bayan ya fito na fad'a masa gaskiya abinda wad'an can mutanan suke da niyar yi masa. Murmushi yayi yace mani ai ya fahimcesu shiyasa ya kyalesu.
Anan yake fad'a mani abinda yakeso, an bashi gida acan wajen aikinsu amma yafiso ya shigo cikin mutane ya zauna kafin ya gama gane komai na garin sai ya canza wajen zama. Jin haka yasa nayi masa jagora wajen mai wannan gidan, domin wani ne ya zauna daya tashi kuma bakowa ciki.
Tunda ya samu gidan nine na tsaya aka gyara komai. Bayan da aka gama sai yake tambayata aikin da nakeyi, shine nake fad'a masa ina 'yar buga-buga ne dan bani da iyali, tunda nayi aure mata ta rasu wajen haihuwa acan garin mu shikenan na taho Lagos da zama saboda ban aje kowa ba.
Jin haka yace kawai hankalinsa ya kwanta dani, idan na amince zanyi masa gadi zai rik'a biya na, amma da sharad'in duk ranar daya kamani da cin amanarsa saiyasa an kulle ni. Jin abinda yace jiki na rawa na amince, domin na samu wajen zama mai kyau, da zakaga inda nake rayuwa ada zaka tausaya mani, bacci kawai yake kaini wajen, da nayi asuba zan fice, sai gashi Allah ya kawo mani Alhaji ya taimakeni, shiyasa nake zaune dashi da gaskiya, yana da dad'in zama sosai, sam beda mugunta, yana kyautata mani, kullum sai ya bani kud'in siyen abinci kuma k'arshen wata ya bani albashi, hatta da mukullin cikin gidan ina dashi, domin duk bayan kwana biyu ina shiga ina gyarawa, d'akinshi ne kawai banda mukullinshi, kalli d'akin da nake zaune yanzu.
Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in gaskiya ka godema Allah, kuma kacigaba da rik'e gaskiya arayuwar ka, domin itace tasa ka kawo matsayin da kake ayanzu, shiyasa ake so duk inda mutum yake ya kasance mai gaskiya. Sai dai baka fad'a mani sunanka ba.
Maigadi yace sunana *AMADU* amma anfi kirana da *MADU*. Malan Sani yace sannu Amadu suna mai dad'i. Fitowar Alhaji Mai Wada yasa sukayi saurin tashi.
K'arasowa yayi da sauri yana murmushi. Bayan sun gama gaisawa yace lallai Malan Sani kana da cika alk'awari, shiyasa nace bara na leko naga ko kazo nasan Madu bazai kirani ba zaiyi tunanin ko ban tashi ba. Malan Sani yace ai tunda nace zan zo bazan sab'a alk'awari ba, gashi nazo muna ta fira da Madu ma.
Alhaji yace bismilla kashigo. Kallon Madu yayi yana fad'in ina fatan dai ka karya? Madu yace ai tun d'azu naci k'osai da koko. Alhaji yace haka ake so, Malan Sani kashigo.
Bayan sun sake gaisawa Alhaji ya kawo masa shayi da kyar Malam Sani yasha. Kallonshi Alhaji Mai Wada yayi yana fad'in Malan Sani nasan zakayi mamakin kiran da nake maka, ba wani abu bane yasa nace kazo illa abinda na gani jiya, tunda na ganka kawai naji ka kwanta mani, hakan yasa naji ina so nasan kad'an daga cikin labarin ka, domin ajiya naga wasu mutane sun biyo ka da kyar kasha.
Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in Alhaji wannan labarin ko Mata ta ban fad'amawa ba, domin tana da tsohon ciki, hakika ina cikin damuwa, kuma naji na yarda da kai zan iya fad'a maka koni waye......
Bayan ya gama bashi labarin asalinsa ya d'ora da fad'in, nayi kusan shekara ina aiki da kamfanin yin Fanta, kuma har lokacin nine nake tuk'a motarsu, da farko ban fahimci komai ba, a hankali na fara gano wani abu da suke aikatawa a kamfanin, kuma manajen wajen shine yake da alhakin yin komai, wata rana bayan na tashi daga aiki har nayi masu sallama na tafi sai na manta na sayi biredi na had'a da lemun da ake bamu na aje a mota ban d'auko ba, hakan yasa nayi saurin komawa domin na d'auko.
Kasancewar kullum acan nake barin su Manaja da wasu daga cikin manyan yaranshi, sai su kai sha biyun dare basu tafi ba, ban tsaya bin ta wajen su ba kawai na wuce wajen mota domin na d'auki abinda na manta.
Muryar d'aya daga cikinsu naji yana fad'in akwai kayan da aka kawo masu daga wajen John d'azu, wai daga waje ya shigo dasu kuma lafiya lau aka dubasu a bakin ruwa kuma aka wuto dasu, domin ya saki kud'i sosai shiyasa Kwastam d'in wajen basu binciki kayan ba, yanda naji yana fad'i wasu maganin shaye-shaye ne irin na kwalba kamar dai maganin tari, to irinsu ne ya shigo dasu sai dai kwalinsu na lemu ne irin na waje, idan ba an bud'e ba baza'a tab'a sanin ba lemun bane aciki, yana fad'in zasu samu kud'i sosai da kayan.
Bayan ya gama fad'a masa sai naji Manaja yana fad'in ai sunyi magana da John zasu rik'a siyar da kayan ab'oye tunda kowa yasan harkar lemu sukeyi yan drugs bazasu saka idonsu akan kayan ba, yace zasu rik'a d'ora kayan had'e da katan d'in Fantar da muke d'auka muna kaiwa wajen da ake sara.
Jin wannan abun sai hankalina ya tashi, domin nasan zanyi aiki ne da haramtacciyar abu aciki, alokaci sai na kasa rik'e firgici na har suka jiyo motsi, ganin sun taho zasu duba yasa nayi saurin bud'e mota na d'auko leda ta na fito ina kok'arin b'oye damuwata na fad'a masu mantuwa nayi.
Ganin Manajan ya tsura mani ido yasa na d'an daburce, gashi dama Inyamuri ne, sai kawai ya matso kusa dani yana fad'in tun yaushe nake awajen? Ganin yanda hankalinsa ya tashi yasa nace zuwana kenan. Matsowa d'ayan yayi yana fad'in Manaja nima yanzu naji motsinshi da alama yanzu yazo.
Kallona yayi yana fad'in ka tabbata babu abinda kaji? Kai na d'aga mashi ina fad'in babu abinda naji dan hankalina yana wajen kayana. Kai ya jinjina yace zaka iya tafiya. Bayan tafiya ta bansan abinda suka tattauna ba, ni dai haka na isa gida jikina babu kwari, rayuwata ina tsoron cin dukiyar data fito da haramun acikinta, musamman ace kasan abinda ake kullawa amma kacigaba da aiki a haka, nasan kona je na fad'ama 'yan drugs za'a iya samun masu karb'ar cin hanci a rufe maganar ni kuma na jawo ma kaina, hakan yasa na yanke shawarar barin aikin na nemi wani, duk da Matata tana da tsohon ciki amma naji aikin ya fitar mani, nasan yanda aiki yake da wahalar samu a Lagos, amma ya fiye mani na bar aikin da dai arik'a aikata b'arna dani kuma nasan komai.
A waccan shekaran jiyar ina zuwa wajen aiki na samu takarda daga wajen Manaja ta sallamar aiki wai na manyanta da yawa sunfi son Matasa, gaba d'aya kud'in da suka bani na sallamata dubu talatin ne, ganin haka yasa nayi hamdala ga Allah, ban nuna masu komai ba mukayi sallama dasu, haka naje na siyo komai na abinci, domin nafison na aje abinci da na rike kud'i ahannu na, nasan har Matata ta haihu bamu da matsalar abinci, kud'i ne dai bani dasu a hannu, domin acikin kud'in nayi biyan bashi dan nasan banda aiki bare nace sai na kwashi albashi kafin na biyasu, hakan yasa na biya duk mai bina bashi saura nayi cefanan gida.
Wallahi Alhaji ajiya da muka had'u bana maganin naira biyar a aljihu na, haka na bar gida ko kud'in cefane ban bayar ba, nasan dai akwai abinci shiyasa ban damu ba, sai gashi Allah yasa ka bani wad'an nan kud'in.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in to amma su waye suka biyoka jiya? Malan Sani yace wallahi ban san su ba, kawai ina zaune bayan na gama neman aikin yi na rasa sai na zauna bayan nayi sallar isha'i ina jiran wani Alhaji da naji ance yana neman direba, na dad'e a wajen ina jiranshi amma bai dawo ba, ganin dare yayi nace bara na tafi yau na koma kozan dace.
Kawai na taho sai had'uwa nayi da wasu Matasa suna kok'arin yin Lalata da wata yarinya sai ihu take yi, cikin azama nayi kansu ina kok'arin ceton ta, da kyar na kwaceta daga wajen su nasa ta gudu, ganin ta tafi yasa sukayo kaina d'auke da adduna, shine fa na gudo har Allah yasa muka had'u, sauki na d'aya akwai duhu babu wanda ya sheda fuskata bare naji tsoron sake had'uwa dasu. Kaji dalilin da yasa suka biyo ni.
Jinjina kai Alhaji Mai Wada yayi yana fad'in lallai Malan Sani ka had'u da jarabawa, tabbas kai mutumin kirki ne, ba kowa ne namiji bane zaka samu wanda yake gudun tashin hankalin Iyalinsa ba, kayi kok'ari daka iya b'oye mata halin da kake ciki, kuma wannan abun da kayi shine akeson mutane surik'a aikatawa, matuk'ar ka gano ana aikata haramtaccen abu a wajen da kake samun na abinci abinda zai fi maka kayi kok'arin barin wajen, musamman idan kasan cewar ko ka fad'i gaskiya baza tayi aiki ba.
Ina mai tabbatar maka da ace wad'annan mutanan sun gano cewar kaji su bazasu barka ba, dole su nemi rayuwar ka domin gudun kada ka tona masu asiri, da yawa yanzu ana aikata kasuwanci had'e da haramtacciyar harka, tun zuwana garin nan na gano abubuwan da suke gudana, kasan yanayin aikin mu, duk kayan da za'a shigo dasu hakkin mu ne mu tabbatar da nagartarsu kafin a wuce dasu, kasancewar gaskiya tayi k'aranci yasa mutanan mu suke son karb'ar cin hanci, domin mutane da yawa suna shigo da kaya ba bisa k'aida ba, wannan dalilin ne yasa suke sakin kud'i ga masu matattar zuciya acikin mu domin su samu kayansu su fito lafiya, tabbas k'asar mu bazata cigaba ba matuk'ar muna da irin wad'annan mutanen, nasan ni d'aya bazan iya gyara su ba, amma ga Allah na dogara, kamar yanda nayi rantsuwa zanyi aikina bisa gaskiya da amana to bazan gajiya ba, zanyi kok'ari wajen ganin na kare hakkin aikina, naci ta hanyar halak d'ina, kuma insha Allahu zanyi kok'ari wajen gano b'ara gurbi acikin yankina.
Malan Sani yace hakika Alhaji kai d'in mai gaskiya ne, tun bayan zuwanka na fara jin labarin ka, duk da baka fara aikata komai ba amma naji wasu daga cikin manya sun fara tsoron kada ace kazo da wani abu daban ba kamar wanda ka canza ba, domin sun riga sun saba dashi, sam basu da wata matsala tun alokacin tsohon shugaban kwastam, tun lokacin da na fara jin magana akan ka nake tunanin ko dai Allah ya kawo mai gaskiya ne, duk wanda kaji ana yawan magana akanshi to akwai wani abu na daban agareshi.
Alhaji Mai Wada yace wannan haka yake, hakika ina tsoron kaidin mutane, wannan aikin da nake son tabbatarwa yana da matuk'ar had'ari, domin duk wanda ya fito a zamanin nan yace yana son ya kauda b'arna to yasa aranshi zai iya mutuwa a kowane lokaci, domin su dai masu aikata b'arnar bazasu so wani ya dakatar dasu ba, domin ayanzu mutane sunfi sha'awar aikata haramun akan aikin halak, domin shed'an yariga ya gama da zuciyarsu, ya nuna masu hanyar haramun tafi kawo kud'i, shiyasa zaka iske kowa yanzu wannan hanyar yake bi sai dai fatan shiriya kawai.
Ajiyar zuciya yayi ya kalli Malan Sani yana fad'in, naji labarin ka Malan Sani, kuma na yarda da kai sosai, zuciyata ta aminta da kai har naji dad'i daka fad'a mani mutumin da yake neman direba baka sameshi ba, ina ganin nine wanda Allah yayi ma zab'in ka shiyasa baka sameshi ba.
Murmushi Malan Sani yayi domin yaji dad'in kalaman Alhaji Mai Wada, saboda tunda yaji labarinsa yaji yana son kasancewa dashi. Kamar daga sama yaji Alhaji Mai Wada yana fad'in idan bazaka damu ba Malan Sani inason ka kasance direba na, domin na yarda da kai, na dad'e ina neman wanda zai rik'a tuk'ani amma tsoro yasa na kasa samu har yanzu, kasan yanayin yanzu amana tayi k'aranci, amma samun ka ayanzu yasa zuciyata ta aminta da kai.
Hamdala Malan Sani yayi yana fad'in ina matuk'ar godiya Alhaji, Allah maji rok'on bawansa, cikin rufin asirinsa ya kawo mani mafita tun kafin mai d'akina tasan halin da nake ciki, hakika naji dad'in samun wannan aikin, domin Mai d'akina zata iya haihuwa a kowa ne hali, ko yanzu akace ta haihu baza ayi gardama ba.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in babu komai Malan Sani, abinda nake so kawai shine amana, Allah ya had'ani da maigadi nagari, na roki direba nagari gashi Allah ya bani, babu abinda zanyima Allah sai godiya. Dan haka inaso ranar litinin kazo ka fara aiki, kud'in albashinka ayanzu naira dubu talatin ne awata kafin zuwa gaba muga abinda za'a k'ara maka.
Zaro ido Malan Sani yayi cike da farin ciki yake godiya, kallon Alhaji yayi yana fad'in na rasa bakin magana, ina d'aukar dubu sha biyar ada sai gashi yanzu Allah ya juya mani, ina dab da samun zuri'a sai gashi Allah ya kawo mani cigaba, nagode sosai Allah ya k'ara bud'i ya kuma bamu zaman lafiya.
Alhaji zaiyi magana wayar Malan Sani tayi k'ara. Saurin d'auka yayi ganin sunan makwabcinsa ne. Bayan sun gaisa ya fad'a masa suna asibiti da matarsa tana nakuda shine matarsa tashiga ta fito da ita ya kaisu a motarsa.
Saurin tashi yayi yana fad'in ganinan zuwa. Kallonshi Alhaji yayi yana fad'in ko haihuwar ce? Kai Malan Sani ya d'aga jiki asanyaye. Tashi Alhaji yayi yana fad'in bara na d'auko