Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
lokaci guda a wuce wajen cin abinci hada matan, ana gamawa amaren kusa akaisu gidajensu, na nesa kuma washe gari atafi dasu.
Dariya suka sa kowa yace wannan yayi ba sai an tsaya yin wani dogon biki wanda za'a fara tun daga laraba sai lahadi a gama. Bayan sun kammala suka kulle taron da addu'a.
Kowa wajen budurwarsa yawuce domin suyi fira. Jabeer da Husnah tamkar masoyan da suka dad'e, dan Husnah ta iya soyayya, tasan yanda zata sa namiji ya mace akanta ya kuma saba da ita cikin kankanin lokaci, abunka da sabon shiga tuni Jabeer ya zurma har yakusa fin Ra'eez kwarewa.
Kallon juna kawai suke fuskarsu d'auke da murmushi. Rumaisa ce ta fara d'auke idonta tana murmushi. Ra'eez yace komai yayi farko zaiyi k'arshe, kinga yanzu sai muje musha biki babu sauran damuwa ko tunanin shiga kotu. Dariya Rumaisa tasa tana fad'in ai wannan kotu taci mana lokaci.
Ra'eez yace shiyasa ai na zab'i wannan aikin domin nasamu damar kula dake, kinga kema sai kishiga makarantar ki anatse, ko har yanzu kina akan bakarki na bakison karatu? Murmushi tayi tana fad'in yanzu kam nake da sha'awar karatu koda bazanyi aiki ba, dan haka ashirye nake dana fara karatun aikin lafiya.
Tafi yayi mata yana fad'in haka nake son ji, ina matuk'ar son na ganki kina taimakon al'umma, duk da nasan zan baki kulawa amma inaso kema kiyi aiki domin kishiga cikin al'umma kirika sanin rayuwa, Allah ya baki sa'a kuma ya barmu tare. Kallonshi tayi tana fad'in Amin Annur.
***
Tsaye suke a tashar jirgin sama suna jiran akirasu, gaba d'ayansu fuskokinsu d'auke suke da farin ciki, acikin matafiyan hada Madu dan shima yace binsu zeyi, duk wanda yaga wannan zuri'a sai sun burgeshi saboda yanda fuskarsu take d'auke da annashuwa.
Ra'eez kuwa mutane sai zuwa suke suna gaisawa wasu kuma suna d'aukar hoto. Kiran sunaye da aka fara yasa mutane suka barshi.
Murmushi Jabeer yayi yana fad'in kaga angon Rumaisa. Ra'eez yace ga kuma angon Husnah ba, wai ya akayima bata zo rakiya ba? Jabeer yace nine na hanata dan bana so ta sani kuka.
Dariya sukasa gaba d'aya hada su Rafeek, Sameer, Adnan da Nabeel. Rafeek yace ai dama fa ance farin shiga sunfi saurin iya abu, yanzu ko kunyar Yayunta bakaji kake fad'in haka.
Rufe fuska Jabeer yayi yabar wajen yana fad'in na d'auka bakowa ai. Dariya sukasa Adnan yace gara ka fad'a sai dai kuma baka canka dai-dai ba ka ganta can a baya dan kuka tasa mana sai ta biyo mu hakan yasa Yaya yace ta taho.
Jabeer yace Yaya Sameer kai da kan ka? Gira Sameer ya d'aga yana fad'in bana son k'anwata tayi kuka shiyasa na taho da ita, kaje ku k'ara sallama kafin azo kan ka. Ra'eez yace ba sai yaje ba kamar naji an kira sunanshi fa.
Da gudu Jabeer yayi wajenta yana fad'in d'an bakin ciki saboda kasan da Rumaisa za'a tafi ai dole ka fad'i haka, to sai naje. Dariya suka sa. ajiyar zuciya Rafeek ya sauke yana fad'in gaskiya zamuyi kewa, amma bakomai ai Kano da Lagos babu nisa musamman da sauki yazo yanzu, insha Allahu zumuncin mu bazai lalace ba zai d'ore a haka.
Sameer yace Allah yasa. Haka sukayi ta fira har aka kirasu. Sallama sukayi cike da kewa dan Ra'eez sarkin kuka sai da yayishi, suma duk jikinsu yayi sanyi haka suka rabu cike da kewar juna.
Sai da kowa ya gama shiga jirgin kafin jirgi ya d'aga. Hannun Jabeer Ra'eez ya rik'e yana fad'in aiki ya kammala gashi yayi riba tunda ya sama mani babban aboki kuma d'an uwa. Jabeer yace sosai kuwa domin gashi na samu K'ani daga sama.
Harara Ra'eez ya watsa mashi yana fad'in kamanta, ai kasan dai na girmeka. Juyawa Jabeer yayi yana fad'in dan Allah Ummu nida Ra'eez waye babba? Murmushi Ummu tayi tana kok'arin maida kwallar idonta ta kewar mijinta kafin tace kaine babba.
Dariya sukasa hada mutanan da suke kusa dasu. Gwalo Jabeer yayi ma Ra'eez. Murmushi Ra'eez yayi ya rik'e hannun Jabeer, runtse ido yayi yana fad'in daga k'arshe Allah ya bani Yaya nima. Hawaye ne suka sauko masa. Hannu Jabeer yasa ya jawo kanshi ya kwantar a kafad'arsa yana shafa bayansa.
Murmushin farin ciki Alhaji Mansur yayi yana fad'in Allah ya k'ara had'a kanku baki d'aya. Malan Sani da yake gefe yace amin.
*ALHAMDULILLAH*
Nima anan jirgina ya d'aga zuwa Zango daga Lagos😉. Ina mik'a godiyata ga Allah daya bani ikon kammala wannan littafi nawa mai suna *ALKALI NE,* ina rokon Allah ya yafe mani kuskuren da yake ciki, ya kuma bada ikon d'aukar darasin da yake ciki.
Ina mik'a godiyata ga dukkanin masoyana, hakika kun nuna mani soyayya, wad'an da suka karanta da wad'an da basu samu damar biyan kud'in littafin ba da wad'an da suka karanta asama duk ina mik'a godiyata agareku, domin masoyin tsuntsu shike binsa da jifa, sai ana sonka ake iya kallon kayan ka, ina matuk'ar farin ciki dana samu ana yad'a labarina domin soyayyace ta jawo hakan, Allah ya gafarta mana baki d'aya, dama kuma ban kullaci duk wanda ya karanta be biya ba. Nagode nagode sosai da addu'ar ku agare ni Allah yabar zumunci.
*ALKALI NE FANS GROUP,*... Jinjinar ku ta dabance, Allah ya biya maku buk'atun ku na alkhairi amin.
Sai kunjini asabon littafina mai zuwa insha Allah... *NA SHIGA BAN 'DAUKA BA.*
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
Ur's.
Nabeelert Lady🖋