Advertisements
Chapter 16 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   16 / 54

45K to 48K   out of 160.3K words

da wani abokinsa akan mace shine fa ya yankeshi da wuk'a a wuya ajali yana kusa yaron ya mutu, 'Yallab'ai yace agaban mutum biyu akayi abun yanzu haka sun wurgar da gawar a wani waje, to sauran mutum biyun manyan abokansa ne nasan bazasu tab'a tona masa asiri ba, to amma d'aya daga cikinsu yace yaga wani d'an ajinsu kamar yana d'aukarsu alokacin da akayi abun, domin yaga lokacin daya fito ya ruga, shine hankalin 'Yallab'ai ya tashi, domin idan wannan maganar ta fito zai rasa kimarsa, toshine yace naje yana nemana.



Jinjina kai Mr. Kallah yayi yana fad'in lallai wannan babbar magana ce, abinda ya sameshi ai ya same mu ne, dan haka kutashi muje yanzu sai mu gama komai kawai.


**** ***


*Naseer* ne ya fito daga gidansu hankali atashe, ya rasa wanda zai nuna ma wannan abun daya d'auka, haka Allah yayishi da tsoro gashi yaje ya gano abinda yafi k'arfinsa har ya d'auko saboda ya nuna sheda, domin yaron da aka kashe abokinsa ne suna gaisawa.


Kallon wayarsa yayi yana tunanin wanda ya kamata ya nuna ma wannan abun, ko a gidansu babu wanda yasani, shiyasa ya fito kada Mamansa ta ganoshi. Tunani yayi ko dai ya kaima Baban Fawwaz tunda babban mutum ne yasan dole ya d'auki mataki akanshi.



Jinjina kai yayi cike da gamsuwa, wayarsa yasa aljihu yana fad'in bara yayi sallah yaje ya kaimasa shima ya huta. (Allah sarki Naseer yarinta ta hana ka gane tsakanin Uba da 'Dahsai Allah🤦🏻‍♀) .



***

Lokacin da yaje gidansu Fawwaz Maigadin gidan ya samu, bayan sun gaisa ya fad'a masa d'an makarantar su Fawwaz ne malaminsu ya aikoshi wajen Babansu. Murmushi maigadi yayi yace aikuwa Alhajin yayi baki suna lambu suna ganawa, amma tunda sako zaka bayar kaje ka fad'a masa kada na tsaida ka bansan lokacin da zasu gama ba.


Godiya Naseer yayi masa yashiga, babu wanda ya ganshi har ya d'auki hanyar lambu, yana dab da zai isa wajensu yaji muryar Brr. Barau yana fad'in 'Yallab'ai ba ance sunan yaron daya d'auki kisan Naseer ba? Abinda zaifi anemoshi a daren yau a kashe shi kawai.


Hannu Naseer yasa ya dafe kirjinsa jin abinda aka fad'a, har ya juya zai gudu sai kuma jarumta tazo masa, wayarsa ya d'auko ya kamo wajen ya matsa kusa dasu yanda zai d'auka da kyau ya b'oye yana d'aukar su.


Mr. Kallah yace wai Brr. Barau meyasa fad'in kisa baya maka wahala ne, kace akashe Alhaji Maiwada, sannan kuma k'aramin yaro kace akashe shi Allah fa zai kama ka.


Alhaji Marusa yace Mr. Kallah yanzu idan yaron ka ne aka ce ya aikata haka zaka bari a yanke masa hukuncin kisa bayan be gama more rayuwarsa ba? Brr. Barau yace Fawwaz shekararsa 19 ya isa ya d'auki kowane hukunci, tunda aji shidda yake yanzu gab suke da gamawa domin jarabawa suke zanawa, Mr. Kallah kayi tunani mana, mu da 'Yallab'ai mun saba tonawa mu rufe domin zaman lafiyar mu, idan asirin wani ya tonu acikin mu gaba d'ayan mu ya shafa.


Jinjina kai Mr. Kallah yayi yana fad'in haka ne, yanzu ya kuke gani za'ayi? Alhaji Marusa yace ayau za'a kashe su duka, Abubakar da Moses na tura su Lucky tun d'azu ina da tabbacin sun kamasu yanzu, zanyi magana da Peter 'Yallab'ai ka tambayar mana kwatancen gidan su Naseer zaije ya d'aukoshi za'a shafe babinsa, shi kuma Alhaji Maiwada su Lucky zasu kaddamar masa anjima bayan ya taso daga wajen aiki.


Dariya Brr. Barau yasa yana fad'in shugaban kwastam ake fad'a maka, daga yau bamu da sauran tashin hankali, Alhaji zaka cigaba da tafiyar da kasuwancinka yanda kakeso, muma zamu k'ara hannun jari domin ya bunk'asa.


'Yallab'ai yace wannan haka yake, dama dole kasa rigar mutunci ka b'oye zahirin ka idan kana so ka zauna lafiya da mutane, domin yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba, nafi son mutuncina so dubu.


Mr. Kallah yace amma akwai abokan Fawwaz da kace sun san komai, baka tunanin yanayi yasa su tona? Brr. Barau yace bazasu iya tona komai ba, kawai zanyi magana dasu akan su manta da komai, 'Yallab'ai dole a fitar da Fawwaz waje yayi karatu hakan zaisa hankalinsa ya kwanta.


Jinjina kai 'Yallab'ai yayi yana fad'in nagode sosai, kuma zanyi hakan, abinda nakeso mu k'ara rik'e sirrin junan mu, Brr. Barau kayi mani alkhairi da yawa arayuwa, abu d'aya zanyi maka wanda zan saka maka, kaine zaka zamto *ALKALIN GOBE* na babbar kotun ku. Murmushi Brr. Barau yayi yana fad'in nagode Allah ya saka, ashe zan kai wannan matsayin.



Jiki na rawa Naseer ya baro wajen, gaba d'aya zufa ta gama rufeshi, ko takan Maigadi bebi ba yayi hanyar waje, Maigadi yana tambayarsa ya bada sakon amma be saurareshi ba yayi waje da gudu.



Kai tsaye d'akinsa ya shige ya saki kuka, ya dad'e yana kuka kafin ya d'auko Flash ya jona da wayarsa, gaba d'aya abinda ya d'auka ya tura, kayan jikinsa ya canza ya b'oye Flash d'in a aljihu ya fito.


Mamansa ce ta kalleshi tana fad'in Naseer wai yau lafiyar ka kuwa? Murmushi yayi yana fad'in lafiya lau Mama. Dama zanje gidansu Mannir na amso littafina saboda muna da jarabawa da safe ranar litinin a makaranta na mantoshi a ajakarsa.


Jinjina kai tayi tana fad'in yanzu za'ayi kiran sallar magriba ka biya masallaci kayi sallah kafin ka wuce, kuma kasan yanda unguwarsu take da ka bari ma sai da safe. Naseer yace bazan dad'e ba Mama. Murmushi tayi tace shikenan kaje kayi sallah. Naseer yace to Mama yanzu zanyi. Har ya kai bakin k'ofa Mamansa ta kirashi, dawowa yayi yana fad'in gani.


Ido ta tsura masa kafin tace Naseer kamar akwai abinda kake b'oye mani ko? Saurin girgiza kai yayi yana fad'in bakomai Mama. Murmushi tayi tana fad'in shikenan ai nasan baka mani k'arya, Allah ya tsare ka gaishe da Mannir d'in.


***

Risnawa Maigadi yayi yana fad'in barkan ku da fitowa, hannu Alhaji Marusa yasa aljihu ya ciro kud'i yana fad'in ga wannan anci goro ko. Amsa yayi yana masa godiya. Har sun kai bakin k'ofa Maigadi yace 'Yallab'ai wannan yaron ya samu ganin ka kuwa? Cak suka tsaya jin abinda yace.


'Yallab'ai yace wane yaro kenan? Maigadi yace d'azu wani yaro yazo yace yana nemanka shine nace kana da baki, sai yace sako zai baka inji malaminsu, shine nace kuna lambu yaje ya sameka, to bayan wani lokaci ina zaune sai kawai naga yaron ya fito a firgice, yanayin yanda naganshi yasa na taso ina tambayarsa ya ganka, amma be tsaya saurarata ba yayi waje a guje, to da yake bansan yanda kukayi ba shiyasa na kyaleshi na zauna.


Gaba d'ayansu hankalinsu ne ya tashi jin binda Maigadi ya fad'a. Brr. Barau ne yace a ina Yaron yace maka yake? Maigadi yace ni dai yace mun d'an ajinsu Fawwaz ne. Dam... Gabansu ya sake fad'uwa.


Da sauri suka fita waje hankali tashe. Da kallon mamaki Maigadi ya bisu ganin yanda hankalinsu ya tashi.


Dafe kai 'Yallab'ai yayi yana fad'in duk yanda akayi wannan yaron turoshi akayi. Brr. Barau yace ba lallai turosa akayi ba, nafi tunanin yazo wajenka domin ya fad'a maka abinda ya faru, sai kuma yaci sa'ar sauraron abinda muke tattaunawa wanda ya tada hankalinsa ya kasa ganinka ya fita da sauri, abin tambayar anan shine, ya d'auki abinda muke tattaunawa akai ko kuwa saurara kawai yayi? Alhaji Marusa yace koma menene bazamu barshi ba, dole anemoshi kuma a amso wannan shedar daya d'auka.


Waya ya ciro yana fad'in bara nakira Lucky. Bayan ya d'auka Alhaji Marusa ya bashi umarnin su nemo Naseer a duk inda yake, su kashe shi kuma su amso wayarsa.


Peter ya kira anan yake fad'a masa ya baza yaranshi su jiran Alhaji Maiwada ya fito su k'addamar masa. Godiya yayi masu ya kashe wayar.


Fawwaz ne yazo wucewa shida abokansa, risnawa sukayi suka gayar dasu Alhaji, duk sai Fawwaz ya tsargu ganin fuskokinsu d'auke da damuwa. Dadynsa ne yayi kiransa, bayan yazo ya tambayesa unguwar su Naseer. Fad'a masa yayi, Brr. Barau yace baka da hotonsa? Fawwaz yace akwai, wayarsa ya d'auko ya nuna masu, amsa Alhaji Marusa yayi nan take ya tura awayarsa, bayan sun shiga Alhaji Marusa ya turama Lucky had'e da kwatancen unguwar.


Brr. Barau yace zamu wuce 'Yallab'ai ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru, anjima zan dawo domin in gana da abokan Fawwaz hada shima. Godiya yayi masu yana fad'in ab'atar da duk wata sheda. Alhaji Marusa yace wannan ba matsala bane nasan yarana.


****


Bayan an gama sallar magriba kafin Naseer ya fito yaji ana sanarwar mutuwar abokinsa wanda aka tsinci gawarsa a cikin daji saboda unguwarsu d'aya. Runtse ido Naseer yayi hawaye suka zubo masa, da sauri yazo fita sai yaji an dafashi, yana juyowa yaga wani abokinsa ne makwafcinsu.


Hannu yasa ya goge idonshi yana fad'in Saddik ya gidan? Saddik yace lafiya lau Naseer, naji wanda aka fad'a ya rasu a makarantar ku yake ko? Kai Naseer ya jinjina masa. Saddik yace Allah yajik'ansa, cike da k'osawa Naseer yace amin kafin ya fice.


Wayarsa ya d'auka ya kirawo abokinsa Mannir, yana d'auka Naseer yace Mannir kana gida? Mannir yace ina gida lafiya naji muryarka wani iri? Naseer yace akwai wata magana da nakeso na fad'a maka akan mutuwar abokin mu amma ka jirani agida yanzu zanzo. Mannir yace shikenan sai kazo.


Mota ya tare ya hau yana fad'in dan Allah Malan ofis d'in shugaban kwastam zaka kaini, jiyowa mai motar yayi yana fad'in sai dai na ajeka bakin titi domin bana son harka da kwastam. Naseer yace bakomai muje.


Tafiya suke sai mai motar yaga kamar ana binsu, kallon Naseer yayi yana fad'in nifa jikina yana bani wani abu, sai nake ganin kamar ana binka, kodai ka d'auko wasu kud'i ne? Naseer yace ba wasu kud'i kawai ka tsargu ne.



Lucky ne ya kira Alhaji Marusa ya fad'a masa sun samu yaron mma sunga kamar ya d'auki hanyar ofis d'in Kwastam. Alhaji Marusa yace kuyi a hankali kunga dai dare beyi ba sosai, bana so kuzo ba tare da kungama komai ba.


Tsayawa direban yayi yana fad'in iya nan zan tsaya sai ka k'arasa. Kud'i Naseer ya bashi yana fad'in nagode. Tafiya ya fara gabanshi yana fad'uwa, yanaso yaje ya tambaya a nuna masa shugaban Kwastam dan shine yaji su Alhaji suna maganar za'a kashe, gara yaje ya fad'a masa yasan kila shima ya samu kariya, gashi ko ganinshi bai tab'ayi ba ballantana ya ganeshi, dole sai yayi tambaya.


***

Alhaji Maiwada bayan ya gama aikinsa ya fito, sallama sukayi da Malan Bala yana fad'in gobe bazan shigo aiki ba sai litinin, a gyara ofis d'in da kyau. Malan Bala yace insha Allahu. Kud'i Alhaji ya ciro ya mik'a masa yana fad'in gashi kayi kud'in mota kayi cefane naga wata ya raba tsakiya. Godiya sosai Malan Bala yayi masa, har bakin mota ya rakoshi.


Ganin su Abubakar da Moses yasa ya tsaya, k'arasowa sukayi suna fad'in har yanzu basu samu wayar Malan Hassan ba, kuma agidanshi ance bai koma ba. Moses yace ina tunanin wani abu, ko dai sun kamashi ne suka kulle? Alhaji yace insha Allahu babu abinda zasuyi masa, gobe zamuje can gidanshi muji. Godiya saukayi tare da masu sallama yashiga mota Malan Sani yaja suka tafi.


Su Moses suna barin wajen kasancewar a motar Abubakar suke, bayan sunyi nisa yaran Peter suka tare su, nan take suka shiga motar suka bar wajen dasu bayan sun watsa masu wata hoda.


**

A hanya Alhaji yana gyara wasu aiyuka a cikin kamfutarsa yake fad'ama Malan Sani yanda sukayi da Alhaji Mansur. Malan Sani yace Alhaji ni har wannan kamfutar ma da kadena fitowa da ita kasan akwai abu mai muhimmanci aciki. Alhaji yace ai babu wanda yasan yanda ake bud'eta, kuma natura shedar a Flash saboda tsaro. Malan Sani yace hakan dai yafi.


***

Jikin Naseer ne ya fara rawa ganin kamar ana binsa, nan take tsoro ya kamashi sai ya baza da gudu yana tunanin ya koma gida kada garin neman shugaban kwastam akamashi, haka kawai ma yaje garin tambaya wani yace shine sai ya fad'a masa gaskiya a kamashi tunda duniyar babu gaskiya, gudu yake aranshi yana fad'in babu wanda zan tambaya gara naje na fara saninshi a hoto kafin naje wajensa.


***


Birki Malan Sani ya taka da sauri ganin mutum ya faad'o masa. Alhaji yace lafiya dai Malan Sani? Bud'e motar Naseer yayi ya shige sai haki yake yana fad'in dan Allah ku taimaka mani wasu ne suka biyo ni.


Alhaji yace ikon Allah! Kai ko yaro meya had'aka dasu? Naseer yace kawai 'yan iskan gari ne. Malan Sani yace ka tabbata abinda ka fad'a gaskiya ne? Naseer yace wallahi da gaske nakeyi. Alhaji yace tuk'a muje.



Malan Sani yace Alhaji... Hannu ya d'aga mashi hakan yasa yaja suka tafi. Naseer yayi masu kwatancen unguwar su Mannir, kasancewar hanyar gidansu bata da kyau Malan Sani yace sai dai mu ajeka bakin hanya dan yasan unguwar bata da kyau. Naseer yace hakan ma yayi nagode.


***

Waya Lucky yakira Alhaji Marusa yana fad'a masa yaron yashiga motar su Alhaji Maiwada. A firgice Alhaji Marusa ya mik'e yana fad'in mene? Wallahi idan kuka bari ya sha sai na kashe ku, inaso kushiga gabansu yaron yana fita ku gama dashi, shima Alhaji bazai sha ba yana barin wajen su Peter zasu k'addamar masa.



**

Malan Sani ne yace Alhaji kaji labarin wani yaro da aka kashe ko? Alhaji yace wallahi d'azu nakejin labari, kai zamanin nan ran mutum ba abakin komai yake ba. Naseer yace ai abokin mu ne makarantar mu d'aya. Alhaji yace Allah sarki, Allah yajikansa ya tona asirin wad'an da suka kashe shi. Naseer yace amin. Yana so ya fad'a masu gaskiya yana jin tsoro hakan yasa yaja bakinsa yayi shiru.


Suna zuwa bakin hanya Malan Sani ya tsaya yana fad'in kayi sauri ka wuce kasan dai wannan hanyar bata da kyau. Godiya Naseer yayi masu, jiyowa yayi yana fad'in Abba nagode. Murmushi Alhaji yayi masa yace bakomai ka kiyaye ka daina kaiwa dare a waje kaji. Kud'i ya bashi yana fad'in ga wannan kasa kati.


Godiya Naseer yayi masa, haka kawai yaji ya yarda da mutumin, sai yayi tunanin ya b'oye Flash d'in amotarsa yasan zai gani, idan ya gani zai taimaka. Hannu yasa ya zaro Flash d'in, a hankali ya turashi k'asan kujerar baya ya fita.


Kan motar Malan Sani ya juya yana fad'in wallahi shiyasa nake jin dad'i da Ra'eez baya zama agarin nan, kallifa ko isha'i ba'ayi ba amma an fara bin mutane. Alhaji yace kai dai sai addu'a, shiyasa nace maka muna gama wannan shari'ar zan aje aikina na bar garin nan. Malan Sani yace ai k'afarka k'afata Alhaji, domin bazanji dad'in zaman garin nan ba idan bakanan.


Alhaji zaiyi magana kenan sukaji motarsu tana rawa alamun taya ta samu matsala. Malan Sani yace kila kuwa mun taka k'usa, Alhaji yace tsaya mugani. Malan Sani yace gara mu tuk'ata ahaka wajen nan beda kyau kuma babu mutane. Alhaji yace Malan Sani kaci ka tsoro, dare fa beyi ba gara mu canza wata tayar zaifi.


***

Taku ukku Naseer yayi yaji an damkoshi, baki ya bud'e zeyi ihu aka rufe bakin, d'aukarshi sukayi zuwa cikin motarsu. Kasancewar motar bakin gilashi ne yasa ba'aganin na ciki.


Mari Lucky ya d'auke Naseer dashi yana fad'in mai ka fad'ama Alhaji Maiwada? Cikin firgici Naseer ya kallesu yana fad'in waye haka kuma? Lucky yace motar data ajeka yanzu ai shugaban kwastam ne aciki meya had'a ka dashi? Farin ciki ne ya kama Naseer jin ya aje shedarsa a inda ta dace, kuma ko zasu kashe shi bazai fad'a masu abinda ya aje ba.


Dukan da akayi masa yasa ya dawo daga tunanin da yakeyi. Cikin wahala yace wallahi babu abinda na fad'a masa ni bamma sanshi ba kawai ragemun hanya sukayi dama wajen shugaban kwastam zanje sai kuma tsoro ya hanani k'arasawa shine na dawo sai muka had'u suka d'aukoni.


Amsar wayarsa Lucky yayi, yana dubawa yaga abinda ya d'auka duka suna nan, waya ya kira Alhaji Marusa ya fad'a mashi, murmushi yayi yace ku gama dashi kuma ku jefar da gawarsa, banaso ku rifeta ku barta domin Iyayensa su masa sallah.



Duk magiyar da Naseer yake masu haka suka kashe shi suka ja motar zuwa inda zasu yarda shi sukayi tafiyarsu da wayarsa bayan sun cire layin sun yona rami sun rufe.


***


Cike da tsoro Alhaji yake kallon mutanan da suke tun karosu, Malan Sani yace Alhaji kana ganin abinda nake gani kuwa? Alhaji yace dama tunda su Moses sukace Malan Hassan ya b'ace jikina ya bani kamashi akayi, sun gano komai shine suka turo akashe mu. Abinda nakeso da kai Malan Sano ka fita da gudu kai ka tsira.


Malan Sani yace ka daina fad'ar haka, bazan barka anan ba. Alhaji yace dole wani ya tsira acikin mu, Bilkisu da Ra'eez basu da kowa sai ni, idan suka kasheni zasu iya zuwa su kashe ta, Ra'eez zai taso cikin maraici, inaso kaje ka fitar da ita daga gidan nan, inaso ka kula mani dasu domin rayuwata suke nema ba taka ba, idan ka tsaya zasu had'a da kai.


Kuka Malan Sani yasa yana mai rik'e da hannun Alhaji.Kamfutarsa

16 / 54