Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
suke a jikin mota, gaba d'aya fuskar Adebayo ta canza kala daga fari zuwa ja, zuk'ar sigari kawai yake kamar wanda zai hadi'ye bakinsa saboda b'acin rai.
Dafashi Umar yayi cikin harshen hausa yake fad'in haba abokina kadena damun kanka akan wannan abun, kada kamanta an kawo wad'an da suka fishi tsanani ma amma cikin ruwan sanyi manyan k'asar suka sa aka canza masu wajen aiki, kasan dai wajen aikin mu babba ne, duk wani maiji da kud'i bazai so ace an kawo wanda zai rik'a bincikar kayansa ba, hakan yasa ba'a barin irin su Alhaji su dad'e anan, to ka kwantar da hankalin ka, babu wanda ya isa yazo ya kawo mana wani sabon tsari, yanda muka saba facaka da kud'i taya za'a zo lokaci guda akawo mana wani tsarin banza, kuyi magana da Alhaji Marusa koshi kad'ai ya isa yasa acanza masa wajen aiki.
K'arasa zuk'e sigarinshi yayi kafin ya fara magana cikin harshen turanci"Haba Omar kaima kasan hankalina bazai tab'a kwanciya ba matuk'ar wannan mutumin yana wajen nan, gobe ne kayan Alhaji Marusa zasu iso, kuma kaima kasan akwai abinda za'a sako aciki, gashi wannan Alhajin ya kawo wannan dokar, ya kake tunanin idan ya kama wani abu acikin kayan? Gaskiya akwai matsala, zan kira Alhaji na fad'a masa kada kayan nan su taho gobe, ya jira zuwa nan da kwana biyu kafin su taho.
Jinjina kai Umar yayi yana fad'in haka ne, kawai ka kirashi yanzu. Waya Adebayo ya ciro ya kira Alhaji Marusa, bayan ya d'aga Adebayo yace masa kada kayan nan su taho gobe. Alhaji Marusa yace yanzu nake da niyar kiran ka ai, d'azu muka gama magana da mutanan sunce cikin daren yau kayan zasu iso Lagos, kasan akwai kaya masu muhimmanci da tsada aciki, shiyasa nace zan kiraka naji ko Alhaji Mai Wada yasa hannu a wannan takardar? Adebayo yace akwai matsala fa Alhaji, komai ya b'aci, sabon tsari ya fito, wannan mutumin yazo da sabon tsari, yaki saka hannu a takardar, kuma yace dole a binciki kayan kowa, ina tsoron kada ace ya tsaya da dare idan ya samu labarin kaya zasu iso.
Cike da tashin hankali Alhaji Marusa yace mene? Haba Adebayo, ya zakayi mani haka, kai da nace kayi kok'ari cikin dabara ka shawo mani kansa sai ka fad'a mani bai amince ba, yanzu gashi kaya sun taho, dole nasan abunyi. Umar ne ya amshi wayar yana fad'in Alhaji kawai kayi waya daga can sama kasa ayi kiranshi da dare, idan yaje sai su rik'eshi da magana har kayan su iso idan yaso sai acire abinda ya kamata abar sauran zuwa safiya idan yazo sai yasa hannu a amshi kayan.
Shiru Alhaji Marusa yayi kafin yace maganar ka abun dubawa ce, ka kyaleshi bai isa ya sani cikin tashin hankali ba, zanyi magana da Mr. Kallah.
Kashe wayar yayi yana fad'in ai na fad'a maka Alhaji Marusa bazai bari yayi asara ba. Ajiyar zuciya Adebayo yayi yana fad'in dole ma mutumin nan ya bar wajen nan.
***
Bayan sallar magriba Alhaji Mai Wada ya samu sakon kayan Alhaji Marusa da suka taso. Bayan ya gama aikinsa saiga waya daga Mr. kallah akan yana nemansa k'arfe tara na dare. Cike da girmamawa Alhaji yace zai zo. Yana aje wayar yayi murmushi, tabbas hasashensa yayi dai-dai, dama irin wannan ranar yake jira. Dirowa ya jawo ya d'auko wani abu ya tashi yabar ofis d'in aranshi yana fad'in zanyi maganin ku.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN Card ta wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura a whatsapp ta lambar k'asa, idan kuma bank transfer ne ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar. 08028525263.*
0⃣6⃣
Wata k'aramar kemara ya saka ta yanda zata d'aukar masa komai kafin ya koma ofis ya had'a kayansa ya fito. Da Adebayo yaci karo shima ya fito zai tafi. K'arasowa Adebayo yayi da sauri yana fad'in Sir, tafiya zakayi ne? Alhaji yace e na tashi. Adebayo yace amma ai direban bezo ba. Alhaji yace zan hau mota ne.
Amsar takardun hannunshi Adebayo yayi yana fad'in haba Sir muje na ajeka. Alhaji yace ka barshi ba gida zanje ba Mr. Kallah ne yake nemana. Adebayo yace muje na ajeka kawai. Murmushi kawai Alhaji yayi ya bishi yana fad'in kaima har ka tashi ko? Adebayo yace bana jin dad'i zanje na kwanta.
Mota suka shiga Alhaji yace amma dai ka duba masu aiki yau saboda ance kaya zasu zo. Adebayo yace munyi magana dasu kila cikin dare kayan zasu zo. Alhaji yace da kyau. Shiru sukayi har suka isa ya ajeshi yayi masa sallama.
Sai wajen k'arfe shad'aya Mr. Kallah ya bar Alhaji Mai Wada domin yasan zuwa lokacin bazai iya komawa wajen aiki ba dole ya nufi gida, duk da yawancin firar labarin yanda tsarin aikin yake yake ta fad'a masa, tun Alhaji yana ganewa har ya gaji, sosai yake jin bacci.
Direba Mr. Kallah yasa ya mik'a Alhaji gida, beyi musu ba domin shima baya buk'atar hawan motar haya. Kai tsaye gida yawuce, godiya yayi ma direba hada kud'i ya bashi kafin ya shige ciki.
**** ****
Washe gari da safe Malan Sani ya iso, alokacin har Alhaji ya shirya dan ya k'osa yaje yaga abinda ya faru. Bayan sun gaisa ya tambayi mai jego. Malan Sani yace lafiya lau ya gajiyar aiki? Alhaji yace akwai ta fa.
Kud'i ya bama Madu kafin sukayi masa sallama suka tafi. Lokacin da suka isa Alhaji yace ya tafi da motar idan ya gama zai kirashi. Malan Sani yace Alhaji da ka barni na zauna anan ai. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nima zanso zamanka anan, amma saboda hidimar da take gaban ka gara ka tafi, idan akayi suna sai ka fara zama a wajen aiki.
Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in nagode. Kayansa ya d'auka ya bishi abaya zuwa ofis. Bayan sun gaisa da Malan Bala Alhaji ya gabatar da Malan Sani a wajenshi. Malan Bala yace gaskiya nayi farin ciki da zuwan ka, ya masu jego? Malan Sani yace lafiya lau suke ya aiki? Malan Bala yace gashinan munayi. Malan Sani yace Allah ya taimaka ni zan wuce. Alhaji yace shikenan sai kaji ni.
Bayan da ma'aikata suka gama shigowa suka gaisa da Alhaji sai ga *Peter* wanda shine shugaban masu kula da kayan da ake saukewa. Bayan sun gaisa ya mik'a ma Alhaji takarda yana fad'in jiya wajen k'arfe 2:00 kayan Alhaji Marusa suka iso, na duba abinda ya samu sai muka sallame su kafin kazo ka gama dubawa.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in bara na kammala aiki sai nazo na duba. Risnawa yayi ya juya ya fita. Shiru Alhaji yayi yana nazarin yanda zai b'ulloma Alhaji Marusa idan har ya kamashi da laifi acikin kayansa, domin yasan babban mutum ne, karo dashi bazaiyi kyau ba, amma dole ya tsaya domin ya tabbatar da gaskiya.
Bayan daya gama komai yasa aka kira masa Adebayo, bayan ya iso suka fita tare da wasu ma'aikatan. Tunda suka isa Alhaji yasan an tab'a kayan, haka yasa aka fara bincika kayan, sai dai abun mamaki babu komai na laifi aciki. Adebayo yace ai na fad'a maka Alhaji Marusa baya shigo da kaya masara kyau.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in bazan tabbatar ba sai na gama bincike. Adenayo yace bincike kuma? Na d'auka za agama komai abasu kayan su ai. Alhaji yace ka sani ko akwai haramtattun kaya aciki kafin muzo aka cire? Da sauri ya kalli Alhaji yana had'iyar miyau.
Dafashi Alhaji yayi yana fad'in wasa nake maka, bayan yanzu muka gama dubawa kuma babu komai, amma dai zan sake bincike idan na tabbatar da komai lafiya sai abasu kayansu bayan sun gama biyan komai kamar yanda doka ta tanadar. Adebayo yace ai Alhaji Marusa baya kin biyan kud'in kaya, domin yasan yanda dokar take. Alhaji yace haka akeso ai.
Cikin dabara Alhaji ya ciro abinda yasa kafin ya nufi ofis, mukulli yasa ya kulle ya fad'ama Malan Bala duk wanda yazo yajirashi zai shiga band'aki ne. Malan Bala yace angama Alhaji.
Zaune yayi yana kallon abun mamaki, faskar Adebayo ya gani shida wasu ma'aikata hada Peter da yaran Alhaji Marusa suna ta aikin jidar wasu kwalaye wanda besan meye aciki ba.
Lokaci ya duba yaga k'arfe 3:30 na dare. Mamaki yayi ganin duk saboda su cire wad'an nan kaya ne suke tsaye a cikin dare. Gaskiya duniya ba gaskiya.
Bayan ya gama gani ya kashe dan ya baro (flash) d'insa agida bare ya tura aciki, dirowa ya jawo ya saka kemarar acikin jakarta kafin ya tashi tafiya. Tashi yayi ya bud'e k'ofar yana tambayar Malan Bala ko akwai wad'an da suka zo nemansa? Malan Bala yace Oga Adebayo yazo shida Umar.
Alhaji yace kaje ka kirasu. Bayan sunzo Adebayo yace dama Alhaji Marusa ne yakira waya idan angama duba kayan yana buk'atar su. Alhaji yace bana tunanin bada kayan nan yanzu domin bangama yarda dasu ba. Kallonshi sukayi cike da mamaki.
Alhaji yace akwai fararen kwalaye guda bakwai da akazo dasu wanda nasan da zuwansu sai gashi kuma ban gansu ba, kaga dole mu gano inda suke domin amana Alhaji Marusa ya bamu akan kayansa, yanzu idan yaji acikin kayan babu wasu bayan kuma anzo dasu har nan ai dole yashiga damuwa, kuma tunda naga sun b'ace na tabbatar suna da tsada da muhimmanci shiyasa akayi kokarin sace su, dan haka dole muyi bincike mu gano komai tun kafin Alhaji Marusa yasan da maganar, domin hakan zai iya tab'a aikin mu.
Zufa ce ta fara keto masu jin abinda Alhaji ya fad'a. Adebayo ne yayi kok'arin fad'in gaskiya Sir, babu wasu kaya da suka b'ace, domin Alhaji ya fad'a mani duk abinda yake ciki, kuma na d'auki hoto na tura mashi yace komai haka yake, kila dai ba'a fad'a maka da kyau bane.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in sai da na tabbatar kafin na fad'i haka, dan haka ka fad'ama Alhaji Marusa yayi hak'uri kayansa zasu iso zuwa wani lokaci akwai abinda ba'a gama ba.
Umar yace Alhaji ni ina ganin tunda shi Alhajin yace haka kayansa suke kawai mu bashi, idan ba haka ba zamu jawo ma kan mu wajen son bincike. Alhaji yace tunda nine nace zanyi binciken kawai kuje. Fita sukayi jiki a sanyaye.
Bayan sun koma ofis Adebayo yace ya akayi Sir, yasan da kwalayen da muka cire? Umar yace nima nayi mamaki, kodai wani munafukin ya fad'a masa ko cikin wad'an da mukayi aikin tare akwai wanda ya turo? Adebayo yace bana tunanin haka, dole akwai abinda yayi, domin duk cikin mutanan da mukayi aiki dasu kowa yana da amana, kuma kafin mu fara sai da na tabbatar babu kowa, dole akwai abinda yayi dai.
Umar yace to yanzu ya za'ayi, kada fa ya tona ma Alhaji Marusa asiri ba k'aramun kunya zaiji ba domin kasan kayan da suke cikin kwalin, gashi babban mutum. Adebayo yace Omar bari nashiga tunani dole na gano abinda Sir, yayi, idan yana tunanin zai iya kama mu zamu gani, domin na buga da wanda yafishi.
Dariya Umar yayi yana fad'in dad'ina da kai akwai basira, duk yanda aka k'ulle abu kana iya warwareshi, shikenan bara na barka kayi nazari. Bayan ya fita Adebayo ya kira Alhaji Marusa ya fad'a masa halin da ake ciki.
Sosai hankalinsa ya tashi, nan yace ma Adebayo duk yanda zasuyi kada su bari asirinsa ya tonu, akwai kyauta mai tsoka matuk'ar suka kashe maganar. Adebayo yace angama Alhaji, kasanni akan kud'i bani da wasa, zan iya yin komai.
****
Bayan la'asar Alhaji Mai Wada ya samu kira daga sama, Mr. Kallah ne ya kirashi yana tambayarsa abinda yasa basu sakar ma Alhaji Marusa kaya ba har yanzu? Alhaji yace Mr. Kallah akwai abinda na gani ne shiyasa nakeso ayi bincike kada mu bashi kayan bayan akwai cuta aciki.
Mr. Kallah yace wace irin cuta? Ka ce da kai aka duba kayan kuma babu komai aciki taya yanzu zaka kawo wata magana, tsaya kaji Alhaji Mai Wada, baza kazo ka kawo mana matsala ba, kowa yasan yanda aikin nan yake, matuk'ar aka duba kaya babu matsala, kuma mai kaya ya biya komai abisa k'aida to dole ne abashi kayansa, dan haka na baka nan da awa d'aya ka sakar masa kayansa.
Dafe kai Alhaji yayi yana fad'in Mr. Kallah ka tsaya nayi maka bayani, ana aikata binda bai dace ba, ana shigowa da kaya haramtattu idan bamu tsaya muka gyara ba tofa kan mu cutar zata dawo, domin idan ta tab'a yaran mu kamar ta tab'a mune, Allah kad'ai yasan abinda aka shigo dashi, ina da shedar da zan nuna maka ka tabbatar ina da gaskiya, kuma wallahi kaji na rantse komin girman Alhaji Marusa dole hukuma ta hukuntashi kuma sai tacisa tara, domin ya karya doka.
Ajiyar zuciya Mr. Kallah yayi yana fad'in wace irin sheda kake da ita fad'a mani? Alhaji yace bazan fad'a maka yanzu ba, amma zan kawo maka ka gani da kan ka, kuma ba kai kad'ai zaka gani ba dole sai an had'a taron manya kafin na fito da shedar.
Mr. Kallah yace shikenan Alhaji bazan hanaka aikin ka ba, wannan abun da kayi yana da kyau, nima na d'auka babu wata matsala a kayan shiyasa nashiga maganar bayan da Alhaji Marusa ya fad'a mani, amma tunda kaine shugaba a wajen bazamu hanaka aikin ka ba, domin irin ku k'asa take nema, bakomai Allah ya taimaka kayi aikin ka a natse. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nagode Yallab'ai.
Bayan ya kashe wayar yayi shiru yana tunanin ashe dai Mr. Kallah mutumin kirki ne, ya d'auka shima yana goyan bayan su ne, tunda har ya bashi goyon baya dole a gobe ya mik'a abinda ya d'auka manya su gani kafin a mik'a Alhaji Marusa kotu domin acan ne za'a yanke masa hukunci dai-dai laifinsa, kuma dole ya fito da kayan da aka b'oye domin asan abinda yake ciki.
Haka ya wuni yana aiki sallah kawai take fitar dashi, abinci ma anan Malan Bala ya kawo masa yaci. Har sukayi magriba kafin Malan Sani yazo ya d'aukeshi, sai da ya d'auki komai nashi hada kemarar kafin suka tafi.
****
Washe gari tunda safe ya kira Adebayo akan ya kula da ofis bazai samu zuwa da wuri ba zaije wajen taro. Murmushi Adebayo yayi yace sai ka dawo Sir.
Koda suka isa can babbar hedikwata haka Malan Sani ya koma gefe yana jiran Alhaji, kai tsaye Alhaji ya nufi hanyar shiga, yana dab da shiga wayarsa tayi k'ara. Yana dubawa yaga Mr. Kallah ne, saurin d'auka yayi. Bayan sun gaisa Mr. Kallah yace Alhaji Mai Wada ka sameni a ofis d'ina yanzu, akwai maganar da nakeso muyi dan ban fad'a masu zakazo a zauna ba. Alhaji yace shikenan gani nan zuwa. Mota yashiga suka nufi ofis d'in Mr. Kallah.
Kallonshi Mr. Kallah yayi yana fad'in Alhaji Mai Wada nasan ka dad'e kana wannan aikin, kasan kuma yanda halin k'asar mu take, k'ananan mutane ma ka kalli yanda ake gogawa dasu bare kuma manya, nasan kasan kad'an daga cikin labarin Alhaji Marusa, babban mutum ne shi, bana so kaje kayi abinda zaisa mutuncinka ya ragu, kome zakayi ka tabbatar kana da kwakkwarar sheda kafin kayishi, ko kotu kaje idan baka da sheda kwakkwara kotu tana watsi da k'ara, ajiya ka fad'a mani kana da sheda akan abinda ka fad'a, nace ka fada mani amma kace sai kazo, gashi kuma baka fad'a mani ba amma kake kok'arin kai shedar gaban Manyan mu, wannan dalilin ne yasa ko ajiya daka kirani kace na fad'a masu zaka zo na amsa maka kawai, amma babu wanda na fad'ama wannan maganar, koshi Alhaji Marusan besan kana da wata sheda akanshi ba, shiyasa kaji nace kazo domin mu fara gano komai kafin mu mik'a maganar sama.
Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in wannan gaskiya ne, ya kamata ace mun zauna mun had'a komai kafin afitar da maganar, domin ance idan baka iya kama b'arawo ba shi sai ya kamaka.
Hannu yasa ya ciro kemara yana fad'in ajiya ma naso na tura a (flash) sai kuma bacci ya d'auke ni, da safe kuma na manta kawai na taho da ita. Kunnawa yayi ya mik'a ma Mr. Kallah yana fad'in tun lokacin dana samu labarin kayan zasu iso cikin dare nayi niyar tsayawa ayi komai agabana, sai kawai na samu kira daga wajenka, hakan ya b'ata mani rai, har nayi tunanin wani abu, to da zan tafi sai na mak'ala wannan kemarar domin ina zargin wani abu, washe gari dana zo aka duba kaya babu komai na laifi aciki, bayan dana koma na duba kemarar sai na gano ajiyan an cire wasu kaya kusan kwalaye bakwai wanda bansan abinda yake ciki ba, kuma na tabbata kaya ne marasa kyau aciki, gashinan ka duba zakaga abinda na gani.
Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad'in Alhaji ai banga komai aciki ba, duhu kawai nake gani babu komai aciki. Da sauri Alhaji ya mik'e ya amshi kemarar yana dubawa, ya duba ko ina amma babu abinda ya d'auka aciki sai wata d'auka da akayi ta kusan mintuna talatin amma kuma duhu ne aciki, lokaci ya duba sai yaga k'arfe 1:30 ne lokacin sallar