Advertisements
Chapter 4 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   4 / 54

9K to 12K   out of 160.3K words

MTN card ta wannan lambar.. 08147669770, kayi screen shoot ka turo a whatsapp ta lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi ka tuntub'e ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263*


0⃣3⃣


*ALHAJI HAMZA MAI WADA* shine cikekken sunansa, asalinsa d'an *MAIDUGURI* ne, aiki ne ya fito dashi daga garinsu, ma'aikacin *KWASTAM* ne, yayi aiki a garuruwa da yawa, tun yana a k'aramin matsayi har Allah ya d'agashi, mutum ne mai gaskiya da amana, kowa yasan yanda halin masu irin aikinsu yake a wannan zamani, duk wanda aka ce maka yana aikin Kwastam da wuya ka sameshi mai gaskiya, zaka sameshi mai dukiyar gaske musamman idan akace ya kai babban matsayi, kafin ka samu mutane masu irin wannan aikin da gaskiya a wannan zamani zaka sha wahala, akwaisu sai dai basu da yawa.



Alhaji Mai Wada ya kasance acikin mutane masu riko da gaskiya da amana, wanda hakan ya jawo masa bakin jini a wajen manyansa da kuma manya a najeriya, yayin da ya jawo masa farin jini a wajen masu k'aramin k'arfi musamman masu shigo da kayansu ta hanya mai kyau.


Saboda halinsa yasa ake yawan canza masa wajen aiki, wannan dalilin ne yasa yayi zama garuruwa da yawa, hakan ne ya jawo masa rashin yin aure da wuri, domin yana ganin akwai zalinci yayi aure ya bar matar ya tafi wajen aikinsa.



Sai da 'yan uwansa suka matsa masa kafin ya amince su zab'a masa wata daga cikin danginsa dan baya son yaje wani waje ya samo mata. Kasancewar zuri'arsu akwai had'in kai, dan zaune suke a waje d'aya, katafaren gida ne mai b'angarori da yawa hakan yasa duk 'yan uwan suke zaune awaje d'aya, dama basu da wani yawa a zuri'arsu.


Cikin lokaci k'ank'ani aka sama masa mata mai suna *BILKISU*, mace ce mai hakuri da juriya, masaniya ce a karatun addini, iya karta diploma a fannin girke-girke, lokacin da aka mata maganar anyi mata miji babu b'ata lokaci ta amince dan dama yana burgeta.



Bayan anyi bikinsu da wata d'aya aka sake masa canjin wajen aiki zuwa Kano. Haka ya tafi ya kwashi kusan wata biyu kafin ya dawo, da zai koma Mahaifinsa yace daga yanzu duk inda aka maidashi ya d'auki matarsa su tafi, be amince masa yarik'a barinta ba, da ace tare suka tafi kila da yanzu ta samu rabonta, amma ya tafi har wata ukku taya zai tara zuri'a a haka.


Haka ya d'auki matarsa sukayi sallama da 'yan uwa sai kuka Bilkisu take kamar kada ta bishi. Haka suka tafi cike da kewar gida. A wannan karon ya dad'e a Kano ba'ayi masa canjin wajen aiki ba.


Har Bilkisu ta haifi d'anta namiji suka koma gida domin ayi suna acan. 'Yan uwa sunyi matuk'ar farin ciki, domin Alhaji Mai Wada shine babban 'Dah a zuri'arsu, kuma gashi Allah ya bashi magaji. Anyi taron suna na gani na fad'a, anyi hotuna kowa yayi farin ciki, inda aka sama yaron *RA'EEZ*.


Bayan suna haka ya tafi ya barta anan sai bayan tayi arba'in kafin ta koma. Kwanan su talatin da biyar Mahaifinsa yayi masa waya akan yazo ya d'auki matarsa.



A washe gari ya taho. Bilkisu kuka tasa da taji zasu tafi dan asonta tayi kwana hamsin, sauran matan ma hakuri suka bama Mahaifin Alhaji Mai Wada amma yace sai sun tafi baiga amfanin zamanta ba ta bar mijinta shi kad'ai.


Haka suka tafi sai kuka takeyi. Tafiya suke Alhaji Mai Wada yana tunanin maganganun da sukayi da Mahaifinsa adaren da zasu taho, haka kawai yake jin jikinsa yana sanyi.


Bayan komawarsu da sati biyu fad'a ya kaure a Maiduguri, gaba d'aya babu wanda ya tsira a gidansu. Lokacin da suka samu labari sumewa Alhaji Mai Wada yayi, kwanansa biyu a asibiti kafin ya farfad'o.


Bilkisu ma duk ta fita hayyacinta. Babban aminin Alhaji Mai Wada wato *ALHAJI MANSUR*, shine wanda yake tsaye akansu, shima d'an Kano ne babban d'an kasuwa ne, tunda Alhaji Mai Wada ya dawo Kano ya tab'a taimakonsa akan wasu kayansa da wasu suka so dannewa, tun daga lokacin suka kulla abota, sun zama tamkar 'yan uwa, matarsa *AISHA* suna zumunci da Bilkisu sosai, dan halinsu yazo d'aya.


Bayan da aka sallamesu Alhaji Mai Wada yaso su tafi can garinsu amma Alhaji Mansur ya hanashi dan garin a hargitse yake. Sai da aka rik'a had'a masu da rokon Allah kafin suka samu natsuwa.



Sai da akayi watanni da faruwar abun kafin suka je domin su duba ko akwai wad'an da suka rayu. Haka sukaje ofishin 'yan sanda anan suka samu labarin yanda abun ya kasance. Lokacin da sukaje unguwar su sunsha kuka, dan kamar ba'a tab'a gini a wajen ba. Sun sha kuka haka akayita basu hakuri.


Kasa zama agarin sukayi aranar suka koma Kano. Tun daga lokacin Maiduguri ta fitar masa arai, bai sake tunanin zuwanta ba, domin babu abinda zeyi bayan zuri'arsu sun mutu babu kowa, be tab'a tunanin yaje ko Allah zaisa wasu sun tsira ba, dan har lokacin ance ba'aga gawar wasu ba kuma ba'aji labarinsu ba kawai yacigaba da rayuwarsa da matarsa da d'ansa.



Lokacin da Ra'eez ya isa sawa makaranta haka aka sashi tare da d'iyar Alhaji Mansur *LABIBA*, tare ake kaisu a maidosu tare. A lokacin ne kuma Alhaji Mai Wada ya samu k'arin matsayi inda aka maidashi Lagos aka bashi matsayin shugaban Kwastam acan.


Alhaji Mansur yafi kowa shiga damuwa shida matarsa, domin sun shaku dasu Alhaji Mai Wada, Bilkisu hada kukanta, duk da ta rasa danginta sai Allah ya had'ata da Aisha, tana jinta tamkar 'yar uwarta, sai gashi kuma yanzu zasu rabu.


Ganin halin da suka shiga ita da Aisha har ma da Alhaji Mansur sai Alhaji Mai Wada ya yanke shawarar barin Bilkisu anan domin Ra'eez ya k'arasa makarantarsa. Lokacin da sukaji haka sosai sukayi farin ciki, duk da Alhaji Mansur yaji dad'i amma kuma zaiyi rashin amini nagari.



Haka Alhaji Mai Wada ya tafi cike da fatan nasara, duk lokacin da akayi masa canjin wajen aiki yana sawa ayi masa sauka da addu'oi saboda neman tsari daga mahassada.



Tun farkon zuwanshi Lagos ya fara gano ta'asar da akeyi a wajen aikinsu, baiyi yunkurin hanawa ba duk da ya kasance shugaba, domin abinda ya sani shine ba'a saurin nuna ma mai laifi kuskurensa musamman idan kana bakon waje, ba kamar gari irin Lagos, domin ya dad'e da sanin garin, babu labarin da bai sani ba a hukumar Kwastam ta Lagos, tun kafin yazo garin yake da labari hakan yasa yayi masu kwanciyar b'auna domin ya gano komai cikin sauki ta yanda zai san yanda zai b'ullo masu.



Kowa yasan yanda aikin Kwastam yake, kowa baya da buri wanda ya wuce ya tara abin duniya. Haka ya kasance a wajen da Alhaji Mai Wada yake, akwai mataimakinsa mai suna *ADEBAYO*, d'an *kudu* ne, Allah yayi masa son kud'i ga karb'ar cin hanci kamar me, yana harka da manyan mutane na garin Lagos har ma dana waje, duk wani wanda ake shigo masa da kaya yasan da zaman Adebayo, kafin a canza ma shugabansu wajen aiki shima jirgi d'aya ne ya kwaso su, shiyasa alokacin masu kaya basa jin dad'in abinda ake masu, domin ana karb'ar kud'i awajensu sosai, idan bakaci sa'a ba wani lokacin a kama kayan ka, sai ka saki kud'i masu yawa kafin a sakar maka su.


Da yawa ma'aikatan da suke aiki ak'ansan su basa jin dad'insu, domin idan suka samu sai abinda sukaga damar yaga masu, wasu suna fatan a kawo masu canji yayin da wasu sunfi buk'atar abar masu su kodan samun na cefane da sukeyi.


Tun bayan zuwan Alhaji Mai Wada ya amshi komai a rubuce daga wajen Adebayo, sai rawar jiki yake dan yana so ya samu shiga awajenshi.


Bayan da Alhaji Mai Wada yayi wata guda a wajen sai ya canza wanda yake kula da karb'ar haraji domin ya gano ta wajenshi ana babbar b'arna, haka ya canza wanda yake kula da shigowar kaya da saukesu, haka duk ya tarwatsa kowa Adebayo kuma yace ya tsaya a matsayinsa baya so yana shiga abinda ba aikinsa ba.


Tun daga wannan rana daya tarwatsa kowa mutane da dama sunji zafinsa, yayin da wasu sukaji dad'i, wasu daga cikin wad'an da ake shigo masu da kayansu sunyi farin ciki da zuwan Alhaji Mai Wada, yayin da wasu suke bakin ciki.



Hatta da direban da ya iske wanda yake tuk'ashi sai da ya canza, domin Alhaji Mai Wada bashi da saurin yarda da mutane, tunda ya lura direban yana da kusanci sosai da Adebayo yaji bai kwanta masa ba, domin yasan wasu daga cikin halayyar Adebayo.


Ya dad'e yana tuk'a kanshi kafin ya samu direba mai suna *MALAN SANI*. Ya had'u da Malan Sani wata rana bayan ya dawo daga ofis da dare wajen k'arfe goma da rabi, ya tsaya domin ya sayi biredi sai kawai ya hango Malan Sani ya fito daga wani lungu da gudu sai waige -waige yakeyi, yana tsaye har yazo ya wuceshi sai yaga ya b'oye a bayan motarsa yana lekowa yana kallon hanyar daya fito.


Bayan daya gama siyen biredin sai ya zagayo domin yashiga mota, sam baiji tsoron komai ba ya dafa Malan Sani, a firgice ya jiyo jikinsa yana rawa. Alhaji Mai Wada yace kwantar da hankalin ka babu abinda zanyi maka, zan tafi ne kuma naganka ajikin mota ta shine na tab'o ka.


Hannu Malan Sani yasa ya goge zufar data keto mashi kafin yace na rokeka da Allah ka taimaka mani na fita daga wajen nan, wallahi kashe ni zasuyi. Cike da mamaki Alhaji Mai Wada ya kalleshi, har zai masa tambaya sai kuma yayi saurin bud'e bayan motarsa yana fad'in shiga amma ka duk'e kada aganka.


Yana shiga yaja motar suka bar wajen, babu wanda yayi magana har sai da suka iso unguwar da Alhaji Mai Wada yake kafin ya tsaya agefen hanya ya juyo yana fad'in Malan anan nake da zama kai ina zakaje? Tashi Malan Sani yayi yana kallon inda suke, ajiyar zuciya ya saki yana fad'in ai nazo gida Alhaji, nima anan unguwar nake gidana yana can layin baya.


Alhaji Mai Wada yace nima ga gidana can idan bazaka damu ba mu k'arasa akwai abinda nake son na tambayeka. Malan Sani yace Alhaji yanzu dare yayi, kaga har goma ta wuce, nasan Iyalina suna can cikin damuwa dan bana wuce goma awaje, amma muje ka nuna mani gidan ka ni kuma nayi maka alk'awarin gobe da safe zanzo na sameka.


Kallon Malan Sani Alhaji Mai Wada yayi na wani lokaci, tabbas haka kawai yake jin ya yarda dashi, domin beyi kala da macuci ba, magidanci ne sosai yana da fuskar kamala. Ajiyar zuciya yayi yana fad'in kana da gaskiya, nima bani da iyali shiyasa banyi tunanin dare yayi ba, badamuwa muje kaga gidan nawa.



Har bakin gate suka isa kafin suka fito. Kallon Malan Sani yayi yana fad'in sunana Alhaji Hamza Mai Wada, kuma ni mutumin Maiduguri ne, sai dai Iyalina suna zaune akano, banfi wata d'aya dana dawo nan ba dan anyi mani canjin wajen aiki nine shugaban Kwastam na wannan garin.


Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in ikon Allah, dama kaine naji ana ta magana a wajen aikin mu? Wallahi ko d'azu naji ana maganar sabon shugaban da aka kawo a wajen da naje. Ni sunana Malan Sani, d'an Katsina ne ni, neman kud'i ya kawo ni Lagos nafi shekara goma sha biyu anan, tun ina k'aramun aiki har Allah ya bud'a mani na samu aikin tuki a kamfanin Fanta, da buga-buga har Allah yasa nayi gidan kaina.



Murmushi Alhaji Mai Wada yayi yana fad'in lallai Malan Sani ka zama d'an Lagos, bara na barka kada ashiga hakkin Iyali, tunda gobe asabar babu inda zanje zanyi jiranka dan akwai abinda nake son ji daga gareka.


Malan Sani yace insha Allahu wajen k'arfe goma zanzo nasan zuwa lokacin ka tashi. Dubu biyu Alhaji Mai Wada ya mik'a mashi yana fad'in ga wannan kayi cefane. Malan Sani yace haba Alhaji ka bar su nagode da wannan taimakon ma da kayi mani. Alhaji Mai Wada yace bafa roko na kayi ba, dan haka ka amsa dan Allah. Amsa yayi yana fad'in nagode sosai Allah ya k'ara bud'i.


Sallama yayi masa ya tafi cike da farin ciki, har sai da kwallar farin ciki ta fito masa. Allah mai jink'ai kenan, ko sisi be tashi dasu ba yau, haka ya fita domin neman aiki har dare be samo komai ba sai rayuwarsa da akaso illatawa, gashi yayima matarsa laifi, ya b'oye mata sallamarsa da akayi daga aiki kusan kwana ukku kenan, a nufinsa idan Allah yasa ya samu aiki yau sai kawai ya fad'a mata ya canza wajen aiki, sai gashi bai samu ba kuma ko kud'in abincin safe bedasu, sai gashi Allah ya kawo masa wannan Alhajin ya bashi har dubu biyu bayan taimakonsa da yayi. Lallai mutanan kirki basa k'arewa duniya.


Haka ya nufi gida cike da farin ciki, yaji dad'in samun kud'in nan domin yana tausayin matarsa saboda tana da tsohon ciki.



Ur's.
Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN card ta wannan lambar.. 08147669770 kayi screen shoot ka tura a whatsapp ta lambar k'asa, idan kuma bank transfer ne ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263*


0⃣4⃣


Da sallama Malan Sani ya shiga gidanshi fuskarsa d'auke da fara'a. Matarsa tana zaune a tsakar gida tana hutawa bayan ta gama shan fatan tsakin da tayi, amsa masa sallamar tayi tana kok'arin tashi tana fad'in sannu da zuwa Malan.


Saurin k'arasowa yayi ya kamata suka zauna yana fad'in haba *HALIMA* kada ki wahalar da kanki kina fama da jikin ki. Murmushi tayi tana fad'in ai bana jin komai. Malan Sani yace ai dai kinyi nauyi kidena yunkurin tashi da sauri haka.



Halima tace Malan hankalina yau ya tashi ganin ka dad'e a waje na d'auka ma ko kunyi tafiya waje mai nisa ne. Murmushi yayi yana fad'in wallahi nima hankalina yana wajenki musamman da nasan ke d'aya ce agidan, yau nayi wani aiki ne shiyasa ban dawo da wuri ba, a hanyar dawowa ta kuma na had'u da wani Alhaji har ya rago mani hanya, layin gaban mu yake da zama shine sabon shugaban Kwastam d'in da aka kawo, to shine fa na tsaya dashi mukayi fira kamar mun san juna.


Halima tace Allah sarki, wallahi har hankalina ya kwanta na d'auka wani abun ne ya faru da kai, musamman da naga yanayin daka fita da safe, baka tab'a barina babu kud'in cefane ba sai yau, acikin kwanakin nan sai nake gani kamar akwai abinda yake damun ka.


Murmushi yayi yana fad'in babu abinda yake damuna kawai kicigaba dayi mani addu'a ina so na canza wannan aikin da nakeyi. Da sauri ta kalleshi tana fad'in ba dai korarka sukayi ba? Murmushi yayi yana fad'in basu kore ni ba kawai nagaji dayi masu aiki ne saboda basu da lokacin tashi, kina ganin kullum idan na fita sai dare nake dawowa, gashi yanzu kinyi nauyi bana son ki haihu ace ina barin ki ke kad'ai, gara na canza aiki kema kirik'a samun kulawa keda abinda zaki haifa.


Halima mun dad'e da aure Allah be babu haihuwa ba, yau gashi Allah ya amshi addu'ar mu kinga dole na tsaya na rik'a kula daku, duk da kince d'iyar yayarki zata zo cikin sati mai kamawa amma nafison ace nima ina kusa da ke.


Murmushi tayi tana fad'in to Allah ya zab'a maka wanda yafi wancan alkhairi, Allah ya kareka daga sharrin ko wane aiki da zaka samu. Hannunta ya kamo yana fad'in amin Halimatus Sa'adiya.


Tashi tayi tana fad'in bara na kawo maka abinci yau dai faten tsaki nayi da wake sai nasa alaiyahu. Malan Sani yace baiwar Allah, ubangiji Allah ya biyaki da aljanna, nasan dai akwai abinci agidan, amma ban bar na cefane ba ashe kin samu kinyi? Halima tace d'azu ne *JAMILA* ta aiko mani da d'ari biyun dana ara mata shine nayo mana cefane dasu.


Malan Sani yace Allah yayi maki albarka, kinga nima wannan Alhajin ya bani dubu biyu yace nayi cefane, kuma gobe da safe yana nemana. Halima tace amma mungode masa Allah ya biyashi da alkhairi. Malan Sani yace amin.


Wucewa ciki tayi ya bita da kallon tausayi, baya so ya fad'a mata halin da yake ciki yasan halinta da damuwa, ga tsohon ciki tana dashi idan taji an koresa a aiki zata shiga damuwa, haka idan ya fad'a mata wasu sun biyoshi d'azu hankalinta bazai kwanta ba. Gara ya cigaba da b'oye mata har Allah yasa ya samu wani aikin.

*WAYE MALAN SANI?*


*MALAN SANI HASSAN*, shine cikekken sunanshi, d'an asalin garin Katsina ne, neman kud'i ne ya kawosa Lagos, tun yana kwana a k'asan gada har ya koma kwana a shago, yasha wahala sosai arayuwarsa kafin ya samu na kanshi, kasancewarsa mutum mai gaskiya da amana yasa duk inda yayi aiki ake sonshi, a hankali yarik'a tara kud'i har Allah ya bashi ikon siyen fili a unguwar *AGEGE*. Da kad'an -kad'an ya fara gini, da a kasuwa yake aiki sai kuma ya fara aiki da masu had'a buhun da ake rufe saman babbar mota dashi (TAMPOL) .

4 / 54