Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
ko kuma nace nagode ma Ra'eez domin nasan wannan sabon canjin daga garesa ne. Dariya Raheena tasa tayi kicin tana fad'in kai Momy.
****
Tunda suka tafi Jabeer yake damun Ra'eez da tambaya akan yanda zaiyi da Raheena. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in yanda kowane namiji yakeyi da 'yan matansa nima haka zanyi da ita. Jabeer yace amma dai kai bakayi kama da mayaudara ba.
Ra'eez yace ka sani ko zan fara daga yau. Dukansa Jabeer yayi yana fad'in dan Allah muyi maganar gaskiya. Ra'eez yace amma dai a gabanka kaji tace tana sona ko? Kaga kuwa bazaka kirani da mayaudari ba, bata tsaya tayi binciken akwai wacce nake so ba ko babu kawai kanta ta sani, kaga kuwa idan taga na auri wata bazata zargeni ba.
Jabeer yace duk da haka, ya kamata ka fad'a mata akwai wacce kake so idan zata iya rayuwa da kai ahaka shikenan, idan kuma bazata iya ba kaga sai ta hakura.
Ra'eez yace bazan iyaba, ka sani ma wai ko ina sonta. Dariya Jabeer yasa yana fad'in ai har mata hud'u ma zaka iya aure, to Allah ya bada sa'a, amma wallahi duk ranar da aka rutsa ka kada ka nemeni. Ra'eez yace insha Allahu.
Sai da ya fara aje Jabeer gida kana yawuce gidansu Rumaisa, tana jin k'arar motarsa tayi saurin shigewa d'aki ta gyara fuskarta hada fesa turare.
Muryarsa tajiyo a tsakar gida shida Mama, kwala mata kira Mama tayi tana fad'in ki d'auko littafin ga Yayan naki nan yazo. Ciki ta shige ta barshi a saman tabarma.
Kai ak'asa Rumaisa ta fito, bakinta d'auke da sallama ta k'araso wajenshi. Tunda ta fito yaji k'amshin turarenta, dama shine yake shiya mata saboda yana matuk'ar son k'amshinsa saboda na mata ne.
Idanuwa ya tsura mata ganin yanda tayi kwalliya kamar mai shirin fita wani waje hada shafa janbaki ita da bata sonshi. Amsa mata sallamar yayi yana sakin murmushi.
Tana zama ta gaisheshi. Amsawa yayi yana fad'in Rumaisa ko dai bako zakiyi ne? Saurin kallonsa tayi tana zaro ido. Murmushi ya saki yana kallonta yanda ta zaro idanuwanta masu matuk'ar burgesa.
Maida kanta k'asa tayi tana wasa da hannunta tace ni babu wani bakon da zanyi, waye ma yake zuwa wajena. Ra'eez yace to wannan kwalliya wa akayi mawa? Rufe fuska tayi tana fad'in haka kawai naji ina buk'atar nayi.
Ra'eez yace Uhmm! Ke dai ki fad'i gaskiya. Rumaisa tace da gaske mana, yauwa wai Yaya ina kukaje? Ra'eez yace naje fira ne. Saurin kallonsa tayi idanuwanta tuni suka canza, a hankali ta mik'e tana shirin komawa d'aki.
Da sauri ya tashi yana fad'in ina zaki ba'ayi k'arin ba? Murya na rawa tace na iya ai. Ra'eez yace dawo ki zauna. Kasa dawowa tayi kawai tashige d'aki da gudu saboda kukan da taji ya taho mata, ashe dama ita kad'ai take haukanta, ta d'auka kulawar da yake bata soyayyace ashe ba haka bane a zuciyarsa, lallai ta cutar da kanta data bari ta girma da soyayyarsa a ranta.
Ra'eez kuwa jiyayi jikinsa yayi sanyi, tabbas yasan Rumaisa tana sonshi, meyasa zai fad'a mata haka? Kada garin neman ruwa kwad'o yayi masa k'afa. Lek'awa yayi wajen Mama yayi mata sallama.
A mota ya zauna yana tunanin abunyi. Kasa daurewa yayi kawai ya jawo wayarsa ya fara rubuta sako.... *Haba pretty na taya zaki tafi kibar Yayanki bayan kinsan ke kad'ai yake gani yaji dad'i, ina da kamar ki ina zan iya zuwa fira, wasa nake maki fa, Rumaisa ina matuk'ar sonki bazan iya had'a kowa da ke ba, kece rayuwata, da sonki na girma bana jin zan iya rayuwa babu ke, na dad'e ina son na fad'a maki wannan maganar amma ina tsoron kada ki kasa amincewa dani, ina sonki Rumaisa, kuma kisa aranki kece Uwar 'Ya'Yana da yardar Allah, ina so ki maido mani da amsa idan ba haka ba bazan iya bacci ba.*
Ya mai-maita sakon daya rubuta yafi so biyar kafin ya tura fuskarsa d'auke da murmushi, yana turawa yayi saurin barin k'ofar gidan.
Rumaisa da Mama take tama fad'a akan k'uncin da ta sameta tanayi taji k'arar wayarta, amma saboda Mama tana wajen sai ta share taki dubawa. Mama tace idan kin gama k'uncin ki fito ki kai Abdallah yayi fitsari ya kwanta tunda bazaki fad'a mani abinda yake damunki ba, bansan lokacin da kika fara b'oye mani abu ba Rumaisa.
Tashi Rumaisa tayi tana turo baki tace bakomai fa Mama Yaya ne yace dole sai na bashi hadda gobe ko mu b'ata. Murmushi Mama tayi tana fad'in ai gara ku b'ata tunda kina son wasa da karatu.
Bayan ta kwantar da Abdallah taje tayi shirin kwanciya ranta a dagule, saman gadonta ta kwanta sai tsaki takeyi, wayarta ta jawo domin ta kunna karatu ko zataji sauki sai taci karo da sakon Ra'eez.
Da sauri ta bud'e, tana fara karantawa tayi saurin tashi zaune tana mutstsike ido, bata san lokacin da murmushi ya bayyana a fuskarta ba, filo ta jawo tana sakin dariya. Ta karanta sakon daya turo yafi akirga.
Kwanciya tayi tana fad'in ashe ma yana sona shine yake ja mani aji, nima bazan maida amsar ba sai gobe nima sai naja aji. Kwanciya tayi da anjima sai ta jawo wayar ta sake karanta abinda ya rubuta.
Can dai ta kasa daurewa, tashi tayi domin ta maida masa amsa... *Yayana nagode da soyayyarka agare ni, insha Allahu zaka sameni amatsayin Uwa tagari a wajen 'Ya'yan mu, amma dan Allah kadena mani wasa da wata mace zuciyata bazata iya d'auka ba. Kayi bacci lafiya nagode.*
Tana turawa tayi saurin kashe wayar gaba d'aya tana murmushi.
***
Ra'eez daya kasa bacci yana rokon Allah yasa ta amince dashi, k'arar wayarsa yaji alamun shigowar sako, jiki na rawa ya jawota yana fatan Allah yasa yayi farin gani.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:39 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
2⃣5⃣
Ra'eez besan lokacin daya tashi zaune ba, filo ya jawo ya rungume yana sakin murmushi, ya dad'e yana jiran irin wannan ranar domin shima yashiga sahun masoya amma sai yau Allah yasa zai shiga.
Komawa yayi ya kwanta yana kok'arin kiran Rumaisa, sai dai kiran farko yaji wayar akashe. Murmushi yayi yana fad'in sarkin kunya, dama nasan bazan sameki ba.
Lumshe ido yayi yana tunanin ya kamata ya sama mata gurbin shiga makaranta kafin ayi bikinsu. Saurin girgiza kai yayi yana fad'in bana son ta fara karatu garin nan saboda ba lallai zaman mu ya d'ore anan ba, daga ranar da aka gano gaskiya dole zasu koma kano, gara ma ya bari bayan anyi biki a hankali sai tayi karatun ta.
Cike da gamsuwa ya jinjina kai. Shiru yayi yana tunanin Raheena. Murmushi yayi yana fad'in kiyi hakuri Mahaifinki ne ya jaza maki, amma dole su d'and'ana illar yaudara da zalunci, koba komai nima zakici moriyata.
Haka ya kwanta cike da tunanin masoyiyarsa har bacci ya d'aukesa.
*** ***
Kiran wayar Raheena ne ya tashesa a bacci da ya makara, saurin tashi yayi ya d'auka. Murmushi Raheena tayi tana fad'in lokacin sallah yayi. Ra'eez yace amma nagode maki, badan ke ba da na makara, amma nasan kema bakya tashi sallar asuba ya akayi har kika tashe ni? Raheena tace wallahi ada ne bana tashi sai da safe nake sallah, amma tun daga ranar da kace kaji dad'i dana tasheka kuma kana son mai sallah da wuri yasa nake tashi, saboda kai har alarm nasa wallahi.
Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Allah yasa ki dawwama a haka, kuma ina so ki rik'a yin komai saboda Allah ba danni ba, hakan zai sa abun ya bi maki jiki ko dani ko bani kicigaba.
Raheena tace insha Allahu. Ra'eez yace nagode bara naje masallaci. Raheena tace ka sani cikin addu'ar ka. Murmushi yayi yana fad'in insha Allah. Sauka yayi ya nufi band'aki yana murmushi yayin da k'asan zuciyarsa ya fara tausayin Raheena danshi mutum ne mai tausayi.
***
Bayan ya kammala shirinsa na fita aiki ya tsaya yana duba wayarsa, yasan bayan ya fito wanka Jabeer ya kirasa, bayan sun gama waya ya ajeta saman gado yacigaba da shiri.
Kugu ya rik'e yana mamakin ina ta shige? K'aranta ya faraji alamun ana kiransa, dubawa ya farayi har ya gano daga k'ark'ashin gado k'aran yake fitowa. Murmushi yayi yana fad'in ashe kina nan.
Hannu yasa ta k'asan gadon sai dai tayi ciki hakan yasa ya tashi ya fara d'aga katifar, sai da yasa k'afarsa ya tokare katifar kafin ya duk'a ya d'auko wayar.
Bayan ya d'auko wayar har ya d'ago ya koma yana duba jikin gadon ganin kamar wata durowa a jiki, mamaki ne ya kamashi yana tunanin dama anama gado durowa? Murmushi yayi yana fad'in mutanan Da akwai dabara. Hannu ya kai zai bud'e wayarsa tayi k'ara, yana dubawa yaga Mama ce, saurin sakin katifar yayi ya tsinke kiran kafin ya kirata.
Tana d'agawa ta fara tambayarsa lafiya be fito ba har yanzu? Ra'eez yace na shirya wayata na tsaya nema amma gani nan. Kashe wayar tayi. Juyawa yayi yana kallon gadon kafin ya d'auki jakarsa da mukulli yayi waje yana tunanin abinda yake cikin durowar.
Yana tuki ya kira Alhaji Mansur, bayan sun gama gaisawa yake tambayarsa jikin Ummunsa? Ra'eez yace kamar koda yaushe Abba, kwana biyu banje ba saboda wani aiki da nakeyi amma yau daga ofis zan je na ganta.
Alhaji Mansur yace baka kyauta ba gaskiya, kasan dai yanda take jin dad'i idan kaje shine zaka kwana biyu ba tare daka lek'a ba. Ra'eez yace ayi hakuri Abbah zanje yau.
Alhaji Mansur yace shikenan, yasu Mamar taku da Rumaisa fa? Ra'eez yace duk suna lafiya ina hanyar zuwa gidan ma. Alhaji Mansur yace ina Kawun ka fa? Ra'eez yace duk yau zan lek'a insha Allahu.
Alhaji Mansur yace idan kaje wajensa ka had'amu ina so mugaisa, kaima idan ka samu lokaci akwai maganar da zamuyi, ina fatan kana kula a wajen aikin ka ko? Ra'eez yace sosai ma Abbah.
Alhaji Mansur yace haka ake so, da fatan kana kula da yanayin Alkalin ku? Ra'eez yace Abbah shekaran jiya har gidansa ya gayyace ni cin abinci wai yana sona, ashe d'iyarsa yake so ya had'amu, sai da mukaje gidan na samu ashe tsohon gidan Abbu ne.
Alhaji Mansur yace ka kula fa, duk yanda zai jaka jikinsa kada ka saki jiki dashi har ya gano wani abu daga gareka, bana so kowa yasan kana da alak'a da Mahaifinka, nasan waye Brr. Barau, yana da matuk'ar wayau, dan haka ka kula sosai.
Ra'eez yace insha Allahu. Alhaji Mansur yace ina fatan ba son yarinyar tasa kake ba ko? Zaro ido Ra'eez yayi yana fad'in haba dai Abbah, ai ko d'aura mani ita akayi na kwanceta na gudu.
Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in ai dole na tambaya kasan ita zuciya ba ruwanta da kiyayyar wasu. Ra'eez yace babu komai a zuciyata Abbah, ni yanzu ma ta Rumaisa nake dan jiya na fad'a mata abinda yake raina.
Murmushi Alhaji Mansur yayi yana fad'in ja'iri, ai na d'auka zaka cigaba da b'oyewa ne, ko jiya Ummanku tamun maganar nace ta barka idan ka gaji da ajiyar abunka zaka furta ne, ashema har ka shigar da kan ka.
Shafa kai Ra'eez yayi yana fad'in wallahi kuwa Abbah. Alhaji Mansur yace haka akeso, Allah ya tabbatar da alkhairi. Kasa amsawa Ra'eez yayi yana fad'in ina Labiba? Alhaji Mansur yace jiya ma tazo gida da yaranta.
Ra'eez yace zan kirata. Alhaji Mansur yace bara na barka gashi ma ka kusa makara, ka gaishe dasu Maman ta ku. Ra'eez yace nagode agaishe da Ummah.
****
Koda yaje gidan su Rumaisa bai isketa a tsakar gida ba, tana jinsa tayi saurin shiga band'aki. Bayan sun gaisa da Mama ta kawo masa abinci.
Yana ci suna fira yana fad'a mata Abbah yana gaisheta. Mama tace Allah sarki ko jiya munyi waya da Umman ka ai. Ra'eez yace anjima idan na taso zan biya wajen Kawu da Ummu.
Mama tace wallahi nima ina son naje na ganshi, Abdallah yana yawan tambayarsa. Ra'eez yace kushirya idan na dawo sai na biyo mutafi gaba d'aya, amma sai dai Abdallah ya hakura da islamiya tunda dawuri zan dawo.
Mama tace shikenan. Rumaisa ta kwalama kira amma taji shiru. Tsaki tayi tana fad'in bansan me kike a band'aki ba idan ki kashiga kamar wacce zata canza fata.
Ra'eez yace Mama kibarta tayi wankanta atsanake. Rik'e baki Mama tayi tana fad'in goya mata baya zakayi? Dama saboda kai nake kiranta tazo ku gaisa.
Tashi yayi yana murmushi yace zamu gaisa a waya ai, idan Abdallah ya dawo agaishe mani dashi sai na dawo.
Mama tace to Allah ya bada sa'a ya kare ka daga sharrin mahassada. Ra'eez yace amin. Kud'i ya aje mata yayi waje da sauri dan yasan halinta. Tana tambayarsa abinda zaici amma yayi waje.
Madu ne ya taso yana fad'in Ra'eez har ka fito? Ra'eez yace nafito Baba Madu ya kasuwar? Madu yace gatanan Alhamdulillahi sai godiya. Kud'i Ra'eez ya ciro ya mik'a masa yana fad'in ga wannan, anjima idan na dawo ka shirya zamu kaima Kawu da Ummu ziyara.
Madu yace gaskiya daka kyauta, angode sosai Allah yayi albarka sai ka dawo. Ra'eez yace amin na tafi.
Yana shiga mota ya latso wayar Rumaisa, bugu biyu ta d'auka bakinta d'auke da sallama. Lumshe ido yayi yana amsawa tare da fad'in kin gama gudun? Murmushi tayi mai sauti ta fara gaishe shi.
Ra'eez yace bana cin mike, wallahi idan kina mani rowar ganin ki zakisa na rik'a kula wasu. Da sauri Rumaisa tace kayi hak'uri to. Ra'eez yace bazanyi ba, aikinsan bazan iya aikin kirki ba idan ban ganki ba ko.
Saurin tashi tayi tayo waje tana bashi hak'uri, kamar ance ya d'aga idonshi sai ganinta yayi a k'ofar gida ta langwab'ar da kai tana kallonshi hannunta rik'e da waya tana murmushi.
Da sauri ya kashe wayar ya fito. Yana zuwa tayi saurin duk'ar da kanta k'asa tana sake gaisheshi. Tsura mata ido yayi yana fad'in ashe dai ana tsoron kishiya? Turo baki tayi tana fad'in ni bana tsoro.
Dariya yayi yana fad'in gashi daga fad'in magana kin fito, ai dama nasan ba wani abinda kikeyi aband'aki saboda kada Mama ta kira ki kawo mani abinci yasa kika shige band'aki, to daga yau bazan sake cin abinci ba matuk'ar ba kece kika kawo mani ba.
Kallonshi tayi tana fad'in shikenan bazan sake ba. Murmushi yayi yana fad'in yauwa Pretty na, ina fatan dai jiya kinyi bacci mai dad'i? Kai ta d'aga a hankali tace sosai ma.
Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in bara na tafi aiki na kusa makara, idan na dawo zamuje wajen Kawu da Ummu. Murmushi ta saki tana fad'in sai ka dawo ka kular.... Shiru tayi tana sunne kai.
Murmushi yayi mai sauti yana fad'in zan kular maki da kaina sosai. Da sauri tashige ciki tana murmushi. Girgiza kai yayi ya juya zuwa mota ya tafi.
Da Mama taci karo a tsakar gida. Saurin duk'ar da kai tayi kamar marar gaskiya. Murmushi Mama tayi tana fad'in zaku k'araci gulmar ku dai. Turo baki Rumaisa tayi tace kai Mama me nayi kuma? Mama tace ina zan sani, idan tayi wari dai naji.
Dariya Rumaisa tayi tashige ciki. Murmushi Mama tayi tana fad'in Allah ka tabbatar da alkhairi. Idanuwanta ne suka ciko da kwalla tana fad'in Allah ka kawo mana k'arshen wannan masifa da muke ciki, Allah ka fiddo bawanka haka nan, ka bama Hajiya lafiya kuma ka tona asirin munafukai.
**** ****
Zaune suke a ofis suna ta aiki Ra'eez yana kok'arin had'a aikin da Alhaji Barau ya bashi akan wani case wanda za'ayi da Yaron abokin kasuwancinsu, Alhaji Marusa shine yayi mashi jagora domin yasan matuk'ar akazo kotun su case d'in zai mutu cikin ruwan sanyi.
Bayan da aka kawo ma Alhaji Barau sai yace Ra'eez zai bamawa. Alhaji Marusa yace abama Brr. Bajinta domin shine namu, shine yasan yanda muke tafiyar da komai, bana so azo a samu matsala.
Murmushi Alhaji Barau yayi yana fad'in ina da dalilin da yasa na bama Ra'eez, domin idan muka bama Brr. Bajinta aikin su wad'an can zasu iya d'aukar Ra'eez ya tsaya masu, na tsora ta da yaron domin yana da wata baiwa, koni da nayi gogayya alokacin ina Barrister bazan nuna masa komai ba, kaga dan ya goga da Brr. Bajinta tuni zai kadashi, wannan dalilin ne yasa na bashi case d'in, domin zamu bashi shedar bogi kuma kaga dole da ita zaiyi amfani, nasan zasu iya d'aukar Brr. Bajinta domin sun san yana kada mutane, kaga shikuma sai yaki zaluko kwararen hujjoji, kaga kuma kotu da kwararen shedu take aiki, shikenan case ya mutu.
Tafi Alhaji Marusa yayi yana fad'in Alhaji Barau har yanzu kana nan yanda na sanka, shiyasa akoda yaushe hankalina yake kwance, domin nasan kowace katob'ara nayi ina da mai tsaya mani.
Alhaji Barau yace ai baku da matsala, wani abun ma sai ya zama surikina. Dariya sukasa, Alhaji Marusa yace amma duk da haka Brr. Bajinta ya tarbi wad'an da suka kawo k'arar yace zai tsaya masu kada suje su bama wani lauyan. Alhaji Barau yace kaima ka kawo shawara,