Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
ya natsu yana kallon su.
Ra'eez... Kotu zata so taji sunan ku.
Sunana Gali Haruna... Ni kuma sunana Zubairu Garba.
Ra'eez... Gali ko zaka iya fad'ama kotu dalilin dayasa kuka kamasu Adnan da Alhaji?
Gali... Hakanan muka kamasu domin muna so a bamu kud'i amma babu wanda yasa mu.
Ra'eez... Ai ban tambayeka waya saka ba, kawai dalilin sace su na tambayeka, kenan kaine shugaban ku ko?
Gali gaskiya ba nine shugaba ba bansan inda yake ba dan babu wanda yasan gidanshi a cikin mu iya abinda na sani kenan.
Ra'eez... Zubairu zaka iya fad'ama kotu wanda kuke ma aiki?
Zubairu... Babu wanda muke ma aiki kawai muna neman kud'i ne.
Ra'eez... Shikenan zaku iya tafiya. Ina so kotu ta bani dama domin na gabatar da sheda ta k'arshe.... Kotu ta baka dama.
Jabeer ne ya tashi ya fara had'a kayan da zasu haska domin kowa ya gani. Tunda Alkali ya fahimci abinda suke shirinyi hankalinsa ya tashi, kafin su gama yasha ruwa kusan kofi ukku, sai goge zufa yake yayin da cikinsa yake buk'atar agajin zuwan band'aki, haka ya daure gudun kada ya tona kanshi.
Shiru kotun tayi yayin da kowa ya zuba ido yana jiran a kunna. Hannu Ra'eez yasa ya kunna nan take aka hasko fuskar Fawwaz alokacin da suke fad'a da Farouk. A zabure Fawwaz ya mik'e yana shirin barin kotun, da sauri jami'an tsaro suka cafkoshi, ladabtar dashi sukayi kafin yayi shiru.
Dede lokacin da ya yanki Farouk da wuka da zuwan su Adnan har suka bar wajen. Hannu Ra'eez yasa ya kashe kallon.
Salati akasa gaba d'aya kotun. Wani babban mutum da yake zaune a baya yasa hannu ya goge hawayen da suka zubo masa, tun ranar Talata da yaronshi yaje masa da labarin shari'ar su Farouk yayi alkawarin zuwa domin yaji yanda shari'ar zata kasance danshi ya cire rai da neman adalci a mutuwar Farouk saboda afarko ma beyi niyar neman hakkinsa ba bare kuma yanzu, kawai yazo ne domin yaga wad'an suka tado da wannan shari'ar, sai gashi zuwanshi yayi amfani domin Allah ya nuna mashi wanda ya kashe mashi babban 'Danshi da idonshi.
Bayan kowa yayi shiru Ra'eez yace ya mai shari'a iyakar abinda zan gabatar kenan, ba sai nace wani abu ba, domin nasan adalcin wannan kotun ne, saboda duk abinda zan fad'a idanuwan kowa sun gani, ina fatan wannan kotu zata bima Farouk hakkinsa, sai magana ta gaba akan shari'ar Naseer Sambo Jarmai. Nagode.
Duk yanda Alkali yaso ya daure kasawa yayi domin jikinsa ya jik'e da zufa, gashi cikinsa yariga ya kad'a bazai iya daurewa ba dole sai yaje band'aki.
Cije baki yayi cikin dauriya yace kotu zataje hutun rabin awa, kafin nan kotu tana buk'atar da a killace Fawwaz da sauran masu laifi. Kottt!!!
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
4⃣5️⃣
A sanyaye mutumin yabi bayan d'ansa suka fita, kai tsaye wajen Ra'eez wanda yake tare dasu Alhaji Mansur suna magana ya nufa.
Sallama yayi tare da mik'a ma Alhaji Mansur hannu suka gaisa. Kallonshi sukayi dan basu fahimceshi ba. Kallon Ra'eez yayi yana fad'in barka dai Brr, nasan baka sanni ba, sunana Alhaji Ahmad Ringim, Asalina d'an kano ne, kuma nine mahaifin marigayi Farouk, agaskiya nayi farin ciki da wannan shari'a, na dad'e da fidda ran nemawa Farouk adalci, sai gashi ranar talata Yaro na yazo mani da maganar shari'ar hakan yasa nace zanzo wajenka domin naji wanda yayi silar tado da shari'ar.
Alhaji Mansur yace Allah sarki, ashe dai wad'an da aka zalunta suna da yawa, sannu Alhaji insha Allahu komai yazo k'arshe, kuma ayau zakaga yanda za'a yanke ma azzalumai hukunci, muje can mu zauna na fad'a maka yanda akayi.
****
K'arar burkin mota yasa mutane suka maida hankalinsu inda ya fito, tsayawa sukayi suna kallon Alhaji M. Sanda ganin ya fito daga mota tamkar wanda aka wurgo, ganin yanda mutane suke kallonshi yasa yayi kok'arin dai-daita kanshi.
'Yan jarida ne sukayo kanshi hakan yasa yayi saurin shigewa kafin su k'araso, dole tasa suka hakura kowa yana jiran d'aukar rahoto.
Alhaji Barau ne ya fito yana sharce zufa yana kok'arin d'aure wandonshi. Cak ya tsaya yana kallon Alhaji M. Sanda yayin da gabanshi yayi wani irin fad'uwa.
Jiki a sanyaye ya samu waje ya zauna yana kokarin shan ruwa, sai da ya gama sha kafin ya goge fuskarshi yana fad'in Alhaji sannu da zuwa.
Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in Alhaji Barau me nake shirin ji haka? Brr. Bajinta ya kirani ya fad'a mani halin da ake ciki, duk yanda naso abun ya kasance amma naji ana niyar kai bango, a jiya na shiryama Brr. Bajinta duk yanda zaiyi sai gashi yana fad'a mani wai an kawo irin shedar da muka k'ona a wayar wannan yaron, Alhaji Barau lokacin mu fa yayi, inaji ajikina bamu da sauran mafita matuk'ar aka samu d'ayar shedar da yaron ya d'auka.
Ajiyar zuciya Alhaji Barau ya sauke yana fad'in wallahi Alhaji kaina ya d'aure, yanzu haka saura mintuna a koma kowa yana jiran ayanke hukunci, babban abinda yafi d'aga mani hankali ganin Alhaji Kamal tare da wasu mutane wad'an da nake kyautata zaton daga chamber suke, kasan kuwa abinda yasa Alhaji Kamal ya iya baro ofishinsa kasan babban dalili ne.
Gyara zama Alhaji M. Sanda yayi hankali tashe yace ba dai an kai maganar sama ba? Alhaji Barau yace wallahi bansani ba, amma idan zaka tuna Alhaji Kamal shine Baristan Alhaji Maiwada, sannan acikin wannan vedion da muka kona ta wayar Naseer akwai maganar da mukayi ta yanda za'a kashe Alhaji Maiwada, gaskiya jikina yayi sanyi.
Ajiyar zuciya Alhaji M. Sanda ya sauke yana fad'in su Alhaji Marusa sun san da wannan maganar? Alhaji Barau yace babu wanda na fad'amawa, sun san dai maganar shari'ar Fawwaz kuma na fad'a masu komai zaiyi dai-dai tunda an kama su Alhaji Sulaiman.
Kallon agogo yayi yana fad'in yanzu dai lokaci ya tafi, abinda nakeso da kai kada ka yanke ma Fawwaz hukuncin kisa. Saurin kallo shi yayi. Kai ya jinjina yana fad'in nasan lokacin da yayi kisan shekarunsa sun kai ya amshi hukunci saboda alokacin zeyi shekara 18, kaga kuwa hukunci ya hau kanshi, amma za'a iya juya abun, kace shekarunsa 14 kawai ya shiga makaranta ne da wuri, kaga hukuncinsa bazaiyi dede dana baligin mutum ba, idan kayi mani haka zanji dad'i.
Alhaji Barau yace abu d'aya zakayi, sai dai ka b'oye takardar shedar haihuwarsa hakan ne zesa kowa ya yarda. Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in babu damuwa dan bazasu tab'a gano inda take ba, kawai kayi yanda nace, su Alhaji Marusa kuma ka barsu a kammala wannan shari'ar sannan.
Kai ya jinjina yana fad'in bara na koma lokaci yayi. Alhaji M. Sanda yace zan zauna anan bazan iya fita ba, kome kenan idan kowa yashige zan fice dan bana son had'uwa da 'yan jarida.
***
Hannu Alhaji Ahmad yasa ya goge hawayen da suka zubo masa, sosai ya jinjina rashin imani irin nasu Alhaji Barau. Kallon su yayi yana fad'in wannan shi ake cema Allura ta tono galma, lallai wannan shari'ar abun so ce, domin d'aya bayan d'aya za'a warware komai, nagode sosai Alhaji Allah ya biyaku da alkhairinsa.
Alhaji Mansur yace amin, ku tashi mu koma gashi can ana shiga. Tashi sukayi suka wuce. Rafeek ne ya fito daga mota, Jabeer yace yauwa gashinan ma ya dawo. Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in kasan abinda nake tunani kenan hakan yasa kaji nayi shiru tun d'azu. Jabeer yace ai tunda Abban Nabeel yace za'a samu nasan za'a samu.
Mik'a mashi takardar Rafeek yayi yana fad'in sai da naje na tayasu kafin Allah yasa aka binciko file d'in, ai gaskiya Allah na sammu. Amsa yayi yana fad'in sannu Yaya. Murmushi yayi yace yauwa.
Sameer ne da Nabeel suka k'araso wajensu, gaisawa sukayi suna tambayarsu Adnan da jiki. Sameer yace da sauki dan ya farfad'o, muna ta sauri kada a kammala ashema yanzu za'a koma. Jabeer yace muje gashi can Babban Alkali ya shiga. Dariya sukasa kafin suka wuce.
***
Tsit kotun tayi kowa yana jiran hukuncin Alkali. Bayan daya gama rubuce-rubucenshi ya d'ago yana fad'in kotu taji duka bayanin da aka gabatar mata, bisa manyan hujjojin da aka gabatar ma wannan kotu ta gamsu da cewa Fawwaz Muhammad Sanda shine ya kashe Farouk Ahmad, wanda yayi amfani da wuk'a wajen kashe shi.
Sai dai anan kotu zatayi duba da abubuwa guda biyu, na farko kotu zatayi duba da yanayin shekarun Fawwaz alokacin da yayi kisan kafin ta yanke masa hukunci, na biyu kotu zata kalli yanayin yanda akayi kisan, domin kisa kala-kala ne, akwai kisan da akeyinsa da niya, akwai kuma kisan tsautsayi.
Idan akayi duba da yanayin yanda Fawwaz yayi wannan kisan zamuga cewar zuciya ce ta d'ebeshi, domin ba daga zuwanshi ya yankeshi da wuk'a ba, sai da suka fara kokowa kafin tsautsayi ya ratsa har ya yankeshi da wuk'a, sai na biyu, wannan kisan anyishi a shekarar 2008, alokacin Fawwaz yana da shekara 14, idan akayi duba da yanayin shekarunsa zamu ga cewar be kai shekarun girma ba, domin Mahaifinsa ya tabbatar ma kotu an sakashi makaranta da wuri shiyasa ya kammala ta a k'ananun shekaru, dan gaka kotu zata zartar da hukunci.
Saurin tashi Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a ina neman alfarma, inaso kotu ta bani dama domin akwai abinda zan gabatar ma kotu. Langwab'ar da kai Alkali yayi alamun k'osawa da maganganun Ra'eez, ganin kallon da ake masa yasa yayi saurin amincewa.
Murmushi Ra'eez yayi ya fito yana fad'in ya mai shari'a wannan takarda ce ta haihuwar Fawwaz wadda aka samo a cikin file d'insa na makarantar daya kammala secondary d'insa, idan akayi duba da wannan takardar haihuwar za'aga cewar alokacin da Fawwaz yake aji shidda yana da shekaru 18 ne, hakan kuma yayi dai-dai da lokacin daya kashe Farouk, abisa tsarin addinin musulunci duk namiji mai wannan shekarun ya isa ya d'auki hukunci domin yashiga shekarun baligi, sannan kuma ba a wajen da sukayi fad'an ya samu wuk'ar ba, dama can yazo da ita, kunga kenan dama yazo da niyar kashe shi, zamu iya cewa wannan kisa bana ganganci bane, kisa ne da aka shiryashi kafin ayi, bisa wannan hujjar nake so kotu tayi amfani da ita wajen yanke ma Fawwaz hukunci dai-dai da laifinsa. Nagode.
Mik'ama Magatakarda yayi shi kuma ya mik'ama Alkali. Jiki a sanyaye ya amshi takardar yana dubawa. Tabbas takardar haihuwar Fawwaz ce, kuma duk wanda ya ganta zai tabbatar cewar bata k'arya bace.
Ajiyar zuciya ya sauke, shikenan babu sauran wata hanya domin duk wasu shedu sun tabbata dole ayanke ma Fawwaz hukunci. Kallon gefen dasu Alhaji Kamal suke zaune yayi, ganin shi kad'ai suke kallo dole tasa yayi gyaran murya yana fad'in kotu ta gamsu da wannan shedar, dan haka zata yanke hukunci.
Abisa hujjojin da aka gabatar ma kotu kwarara, wanda suka tabbatar da Fawwaz shine wanda ya kashe Farouk, abisa kundin tsarin mulki na k'asa, sashen kisa, amfani da makami ko wani abu, wannan kotu mai albarka ta yanke ma Fawwaz M. Sanda hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari, sannan Iyayen shi zasu biya diyyar Farouk ga mahaifansa idan sun buk'aci hakan.
Sannan kotu ta yanke ma Alhaji Sulaiman da Alhaji M. Sanda hukuncin d'aurin wata ukku a gidan yari ko kuma tarar naira dubu d'ari biyu saboda an kamasu da laifin taimakawa wajen b'oye gaskiya.
Mutanan da aka gabatar ma kotu cewar sun kama su Alhaji Sulaiman kotu bata gamsu da hujjar da aka gabatar mata akansu ba, dan haka take umartar da a koma a sake bincikensu a tabbatar da hujja kafin a sake kawo su.
Annan kotu ta kawo k'arshen wannan hukunci, zaku iya d'aukaka k'ara nan da wata ukku idan kuna buk'atar hakan.
Ihu Fawwaz yasa yana kuka yana kiran Dady, saurin rik'eshi akayi aka fita dashi. Tashi Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a sai shari'a ta gaba akan Naseer Sambo Jarmai.
Runtse ido Alkali yayi ya bud'e yana fad'in kotu ta d'age sauraron wannan shari'ar zuwa ranar litinin idan Allah ya kaimu. Kottt!!!
Gaba d'aya mutane suka tashi kowa yana fad'in shari'a tayi, haka kowa ya jinjina ma Ra'eez, sannan sun k'ara jinjina adalci irin na Alkali.
Alhaji Barau kuwa ta kofar kotun yayi saurin ficewa dan yasan 'yan jarida zasu iya rutsashi.
Suna fita Nabeel yaja Abbansa zuwa mota dan yasan 'yan jarida suna iya rufeshi da tambaya, ayanda yaga jikinsa yayi sanyi yasan dole yana buk'atar hutu, hakan yasa yasashi mota suka bar kotun, ko su Ra'eez sai dai yayi masu waya.
Brr. Ra'eez wane irin farin ciki kake ciki da Allah ya baka sa'a kayi nasara a wannan shari'ar? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in ina mai cike da farin ciki domin yau Allah yasa Iyayen Farouk sunga yanda aka yankema wanda yayi silar mutuwar d'ansu hukunci, duk da shari'a ce tsohuwa amma yau Allah yasa an kammala ta, har Allah yasa a cikinta an samo wata hanya da zata kaimu ga samo gaskiyar wata shari'ar.
Brr. Ra'eez ya kake gani akan shari'ar da za'ayi ranar litinin? Insha Allahu itama muna saran nasara. Nagode. Saurin wucewa yayi dan a matuk'ar gajiye yake.
****
Wai Alhaji wane hali ake ciki naga tunda ka dawo kotu wajen Alhaji Barau kake kwance anan baka sake cewa komai ba. Ajiyar zuciya Alhaji M. Sanda ya sauke yana fad'in ko dai muyi nasara ko kuma suyi nasara, yanzu haka an tabbatar cewa Fawwaz shine ya kashe Farouk.
A zabure Ammi ta mik'e tana dafe kirji idanuwanta awaje, kallon Alhaji tayi tana fad'in amma ba haka kuka fad'a mani ba. Runtse idanuwanshi yayi ya bud'e, sosai sukayi ja. Kallonta yayi yana fad'in ban d'auka abun zai kai haka ba shiyasa na b'oye maki, amma yanzu dole kiji komai.....
Kuka kawai Ammi takeyi da tagama jin abinda ya faru, kallon Alhaji tayi tana fad'in yanzu shima kashe shi zasuyi? Garinya saboda b'oye laifin Fawwaz zaku kashe wani, haba Alhaji.
Saurin tashi zaune yayi yana fad'in saboda irin haka yasa na b'oye maki, ki sani zan iya yin komai domin farin cikin Fawwaz, dan haka ban fad'a maki dan kiyi mani wa'azi ba, na fad'a maki ne dan naga babu amfanin b'oyewar. Tashi yayi ya shige d'aki.
Zubewa Ammi tayi hawayen bakin ciki yana zubo mata, ashe dama Alhaji zai iya kisan kai akan son da yake ma Fawwaz? Lallai biri yayi kama da mutum, gashinan Fawwaz yayi kisa an kamashi, idan bincike ya tsananta shima dole akamashi, lallai wannan shine abun kunya Uba da 'Dah sunyi kisan kai.
Yana shiga d'aki wayarsa tayi k'ara, saurin d'auka yayi ganin Brr. Bajinta........
Salati kawai Alhaji M. Sanda yake bayan da ya gama jin yanda shari'ar ta kasance, zubewa yayi saman gado jikinsa yana rawa, a sanyaye yace yanzu shikenan an tafi dashi? Brr. Bajinta yace wallahi dole ne tasa Alkali ya yanke wannan hukuncin, domin idon mutane suna kanshi, ga bak'i da nagani a kotun, Alhaji sai dai hakuri kawai, idan kuma zaka d'aukaka k'ara shikenan.
Jinjina kai yayi yana fad'in shikenan, amma bazan iya zaman gidan yari kona wuni d'aya bane bare har wata ukku, kawai zan biya tara nagode. Kashe wayar yayi ya fara neman Alhaji Barau, tsaki yayi jin wayar a kashe. Hannu yasa ya dafe kanshi yana jin d'akin yana juya masa, tabbas idan har suka bari aka gabatar da shari'ar Naseer asirin su zai tonu, tunda har suka iya gabatar da wannan vedion dole suna tare da d'ayar. Kwanciya yayi hawayen bakin ciki suka zubo mashi.
**** ***
Sannu da zuwa Alhaji bansan ka dawo ba sai da Raheena take fad'a mun kana kwance a falo taga kamar baka jin dad'i. Tashi zaune yayi yana fad'in Hajiya ina cikin tashin hankali kawai kitayani da addu'a.
Zama tayi tana fad'in menene ya faru kuma? Hukuncin kisa ya tabbata akan Fawwaz, domin an tabbatar da shine yayi kisan da nake fad'a maki, yanzu haka na yanke masa hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari, wallahi kunyar Alhaji M. Sanda nakeyi shiyasa ma na kashe wayata domin shima hukunci ya hau kanshi.
Jinjina kai Momy tayi tana fad'in gaskiya akwai tausayi, amma kadena damuwa, shima fa tsohon Alkali ne, waya san yawan mutanan daya yanke ma hukuncin kisa, wasu ma ratayesu akeyi wasu a jefesu wasu kuma a harbesu, damme zaka damu kanka kamar ka aikata wani babban laifi, abune a fili, dole sai da kowa yaga hujja kafin ka yanke hukunci, kuma ma wannan hukuncin arabuce yake, kana tunanin da ace shine a matsayinka akace d'anka yayi kisa zaice kai abokinsa ne bazai yanke masa hukunci ba? Kada kamanta nasan awajen hada 'Yan Jarida, da ace baka yanke hukuncin daya dace ba ina mai tabbatar maka da yanzu ka amsa kira daga sama, dan haka ka kwantar da hankalin ka bana so wani abu ya same ka, Allah ya basu hak'urin rashinsa.
Murmushin takaici yayi yana kallon Momy, batasan sirrin da yake k'asa ba da bata fad'i haka ba, amma zai bita ahakan