Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
yayi saurin barin ofis d'in yana jin wani b'acin rai. Sosai jikin Jabeer yayi sanyi akan abinda ya faru, bai tab'a ganin Ra'eez a irin wannan yanayin ba,daga wannan maganar har zai iya fushi haka, ya d'auka yana son Raheena amma yau ya tabbatar da zahiri, sai dai dole akwai dalili. Ajiyar zuciya ya saki tare da barin ofis d'in.
***
Bayan an tashi ya fito ya hangi Jabeer a jikin motarsa yana kok'arin shiga, da sauri ya k'arasa wajensa. Dafashi yayi yana fad'in yau guduwa zakayi babu sallama.
Murmushi Jabeer yayi yana fad'in haba Ra'eez, meyasa har yanzu baka d'auke ni kamar yanda na d'auke ka ba? Kasan kuwa yanda na d'auke ka? Wallahi kamar d'an uwana da muka fito ciki d'aya haka nake jinka, amma na lura akwai abubuwan da kake b'oye mani naka, ban gama tabbatarwa ba amma ka sani duk ranar dana tabbatar da hakan aranar zan san matsayina awajenka, domin ni ban b'oye maka komai nawa ba, tun ranar had'uwar mu na sanar da kai komai nawa, amma babu komai bance dole sai ka sanar dani labarin ka ba.
Ajiyar zuciya Ra'eez ya saki idanuwansa suka ciko da kwalla, tabbas ya aminta da Jabeer, amma alk'awarin Abbah ne bazai fad'ama kowa labarinsa ba yanzu.
Jin motsin Jabeer yashiga mota yasashi saurin shiga yana goge idonshi. Da kallon mamaki Jabeer ya bishi. Hannunsa Ra'eez ya kamo yana fad'in kayi hakuri Jabeer, zanje kano cikin satin nan nayi maka alk'awarin zan sanar da kai labarina idan na dawo.
Murmushi Jabeer yayi ya rik'o hannunsa yana fad'in kada kadamu abokina, bana son kana zubar da kwalla, na dad'e da sanin kana da ciwo aranka sai dai bansan komeye ba, amma nasha ganin ka cikin damuwa wani lokacin, dan haka kayi hak'uri da abinda nace maka bazan sake tada maka maganar ba.
Murmushi yayi yana fad'in nagode da ka fahimce ni. Jabeer yace bakomai zo mu tafi. Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in ka gaishe da Mamy. Jabeer yace zataji agaida Rumaisa.
**** ***
A ranar alhamis ya lek'a gidan su Raheena saboda damunshi da tayi yazo siyi sallama zasuji Dubai ranar asabar.
Bayan sun gaisa da Momy Raheena ta shige kicin domin d'auko masa kayan motsa baki. Kallonshi Momy tayi tana fad'in yau dai Raheena hankali zai kwanta kazo, kullum cikin damuwana take kaki zuwa, nace mata ai aikin ku haka yake, shine yau tace zaka zo kuyi sallama.
Kai a duk'e Ra'eez yace wallahi kuwa. Momy tace ai gara muje a fara rago siyayyar kayan d'aki dan Alhaji yace baya son bikin yawuce wata guda, shine zamuje Dubai jibi musiyo kayan d'aki, naji tace kaima zaka je kano ko? Kai Ra'eez ya d'aga yana mamakin wannan lamari.
Momy tace idan kaje ka gaishe su, ai gara kaje a kammala komai, muma kwana biyu zamuyo kada suzo bamu dawo ba. K'ara duk'ar da kai Ra'eez yayi yana sakin murmushi.
Tashi Momy tayi tana fad'in Raheena kuje falon baki nan kada ayita gitta maku. Raheena tace to Momy. Kallon Ra'eez tayi tana fad'in D muje can.
Kallonta yayi yana sakin murmushi mai kama da dariya yace ai wucewa zanyi akwai abinda zanyi. Zama tayi tana fad'in kai D zamuyi sallama bazaka tsaya muyi fira ba kuma.
Hannu ya mik'a mata alamun ta zuba mashi ruwa. Saurin zuba masa tayi ta mik'a masa tana fad'in yi hakuri ina wuni. Lafiya lau sarkin mantuwa, ya amsa. Murmushi tayi tana rufe fuska.
Tashi yayi yana fad'in Allah ya kiyaye hanya zance ko? Murmushi tayi tace nagode kaima ka dawo lafiya, me kake so nasiyo maka? Ra'eez yace dama tambaya akeyi? Girgiza kai tayi tana fad'in shikenan zan kawo maka zab'ina.
Kai ya jinjina yana fad'in ki gaida Momy zan wuce. Biyoshi tayi tana fad'in wallahi kamar kada ka tafi. Ra'eez yace dole ko na tafi. Har bakin mota ta rakasa, sai da ya tafi kana ta wuce gida.
Daga wajenta wajen Kawu ya wuce, sun dad'e suna tattaunawa kuma ya sanar masa duk kok'arin da yakeyi kana ya fad'a masa zaije kano gobe. Kawu yace agaishe mani da Alhajin kuma insha Allahu zan cigaba da addu'a Allah yashige mana gaba. Ra'eez yace amin, zasuji.
Sai da ya fara biyawa wajen Ummunsa kafin yawuce gidansu Rumaisa, daga can bayan ya gama yawuce gida dan yagaji sosai.
*** ***
Washe gari be tsaya aka tashi dashi wajen aiki ba, bayan yayi ma Alhaji Barau sallama Jabeer ya kaishi filin jirgi dan ta jirgi zai bi. Sun dad'e suna fira kafin lokacin tafiyarsu yayi, haka sukayi sallama ya tafi.
***
Jinjina kai kawai Abbah Mansur yake yana kallon takardar da Ra'eez ya kawo mashi hawaye suna fita a idonshi. 'Dago kai yayi yana kallon Ra'eez wanda shima kukan yakeyi bayan ya gama fad'a masa abinda ya faru da kuma wanda ya gani awajen Rafeek da Sameer wanda suka fad'a masa.
Hannu Abbah yasa ya goge idonshi yana fad'in tabbas a wannan karon Ra'eez kaine zakayi nasara a kotu, hakika Malan Datti yana da matuk'ar mutunci, sannan na amince maka daka fad'ama Jabeer da Rafeek sirrinka, domin inaji ajikina sune bangon da zaka jingina dasu, sune tsaninka wanda zaka taka zuwa matakin da nakeso kaje, domin na fahimci Jabeer aboki ne nagari, dan haka ka sanar dashi komai saboda duk lokacin daya fahimta da kanshi abotar ku zata iya samun matsala.
Ra'eez yace shikenan Abbah zan fad'a masu, dama umarninka nazo nema dan bana so nayi abinda ya kaucema umarnin ka. Murmushi Abbah yayi yana fad'in na sani Ra'eez, nasan bazaka tab'a tsallake umarni na ba, Allah yayi maka albarka.
Ra'eez yace amin Abbah. Murmushi yayi yana fad'in zuwa gobe sai ka lek'a wajen Labiba ku gaisa dama tana korafin rashin zuwanka. Ra'eez yace tunda nazo dole naje mu wuni muyi fira.
Abbah yace maganar motar fa? Sosa kai Ra'eez yayi yana fad'in Abbah kaga gobe zanje gidan Mamyn Sultan bansan lokacin da zan dawo ba, kuma jibi da wuri nake son tafiya inaga abar motar zan dawo ko nan da wata d'aya sai na kaita gyara.
Abbah yace da alamu nakusa sayar da motar nan. Zaro ido Ra'eez yayi yana fad'in kai Abbah, shikenan ko ina can sai ka bama mai gyaranka sai ya duba mani ita kaga ina dawowa sai na tafi da abuna.
Murmushi Abbah yayi yana fad'in shikenan zan bashi ya duba maka ita amma yanzu yayi tafiya ni kuma nafi aminta dashi idan ya dawo zan kirashi yazo ya tafi da ita, amma ka sani bazaka je Lagos da ita ba, ko an gyara ta anan za'a barta domin ana kammala wannan shari'ar Kano zaku dawo gaba d'aya sai kacigaba da aikin ka anan.
Ra'eez yace haka ne Abbah, nima bani da buk'atar zama a Lagos, muna kammala shari'ar har gidan zan sayar domin nasan Ummu bazata iya komawa gidan nan ba. Abbah yace to Allah yashige mana gaba. Ra'eez yace amin.
**** ***
Yaji dad'in zuwanshi Kano har yaji kamar kada ya tafi, haka Abbah ya kaishi ya hau jirgi ya tafi cike da kewar juna.
Tun kafin ya taso ya sanar ma Jabeer, aikuwa suna sauka ya iskeshi yana jiranshi. Rungume juna sukayi kafin suka shiga mota suka tafi.
Jabeer yace wallahi abokina ka canza kwana biyu. Ra'eez yace ba dole ba ina can ana shagwab'ani. Dariya Jabeer yayi yana fad'in naga alama ai.
Waya Ra'eez ya ciro ya kira Rafeek. Bayan sun gaisa Ra'eez yace Yaya ko kana wani abu zuwa dare? E dama inaso kazo gida akwai maganar da zamuyi ne. Toshikenan sai kazo nagode.
Jabeer yace ina ka samu Yaya kuma? Murmushi Ra'eez yayi yace wannan d'an jaridar da nake fad'a maka ne. Jabeer yace lallai kayi Yaya kuwa. Ra'eez yace idan yazo zan fad'a maku wata magana, dan haka yau muna tare. Jinjina kai Jabeer yayi yace Allah ya kaimu.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣3⃣
Lokacin da Ra'eez ya kammala basu labarinshi babu abinda akeji sai sautin kuka, gaba d'ayansu an rasa mai lallashin wani. A hankali Ra'eez ya zame ya kwanta yana jin wani iri a zuciyarsa, kasancewar shine aka bama labarin da farko shiyasa beji abinda yakeji yanzu ba, dan ayanzu da yake bada labarin abinda ya faru da kanshi sai yakejin wani irin d'aci a ranshi.
Sun dad'e a haka kafin Rafeek ya kamo hannun Ra'eez yana fad'in tabbas Yaron da Abbunka ya rage ma hanya Naseer ne k'anina, domin a ranar shima aka tsinci gawarsa, duk da bani da masaniyar haka amma zuciyata ta bani hakan, domin kace Kawunka ya fad'a maka yaron da suka d'auko yace abokinsa ne yaron da suke magana alokacin an kashe a kings college, tabbas ina zargin mutane iri d'aya ne suka aikata kisan Abbunka da Naseer, banbancin shi Abbunka bayan an kashe shi anyi amfani da allura, amma da wuya idan allurar aka fara masa, domin ance akwai sahun hannu na shaka, haka shima Naseer shakeshi akayi har ya rasu.
Ajiyar zuciya yayi yana fad'in dole akwai abinda Naseer ya sani agame da mutuwar abokinsu wanda Sameer yace Fawwaz ne ya kashe shi, tabbas wannan yaron da Adanan k'anin Sameer yace ya gansu shima ankashe shi Naseer ne, amma zamu zauna mu zana yanda komai yakasance, dole akwai abinda yake faruwa,
Abbunka - Naseer
⬇
*Fawwaz, - tsohon Alkali mahaifin Fawwaz,- Alhaji Barau,- Alhaji Marusa, - Mr. Kallah*.
Wad'annan mutanan suna da alak'a da mutuwar Abbunka, idan ko haka ne Alhaji Barau shine abokin tsohon Alkali a wancan lokacin, kunga Fawwaz yaron Alkali yayi kisa dole su san yanda suka shafe maganar, domin wannan dalilin ne yasa aka tura Fawwaz waje karatu.
Saurin gyara zama Jabeer yayi yana fad'in, amma ya akayi Naseer yaje wajen aikin Abbun Ra'eez? Domin a cikin labarin Kawu yace sunzo fitowa suka had'u dashi hakan yasa suka taimaka masa, bayan kuma kace aranar yace ma Hajiyar ku zaije wajen abokinsa Mannir, kuma kace ba wajen unguwarsu bane, to meya kaishi wajen aikinsu Abbunka?
Rafeek yace yes! Wannan maganar taka tana kan hanya, a yanzu muna cikin damuwa dan haka mu bari bayan kwana biyu muzo anan domin mu bama kanmu tambaya kuma mu nemo amsa, kafin nan dole sai Sameer yashigo, domin ya had'amu da K'aninsa, sai dai bazamu fad'a masu case d'in Abbunka ba, iya abinda ya shafesu kawai zamu sani, case d'in Abbunka ya tsaya iya mu har zuwa lokacin da komai zai kammala, sannan bayan mun fara wannan aikin dole muna buk'atar ganin Uncle d'in ka Jabeer, domin shine lauyen daya tsaya ma Kawu a wancan lokacin, kaga yanzu yana abuja babbar kotu komai zai zo mana da sauki.
Jabeer yace babu damuwa, naji Dady yana maganar zasuyi wani taro k'arshen satin nan na family ne kuma maza kad'ai ne zasu zauna, nasan dole Uncle zaizo dan irin wannan taron baya wuceshi, abinda nake gani mu bari yazo zanyi masa maganar, idan yana buk'atar ganin ku sai muje gaba d'aya.
Rafeek yace yauwa komai ma zaizo da sauki, insha Allahu wannan shari'ar da zafi zamu d'auketa, a wannan karon zasu gane kuskurensu, domin zasu had'u da 'yan zamani, kamar yanda sukayi amfani da basira haka zamuyi muma, kuma a hankali zan nemo duk mutanan da suka bada gudummuwa wajen aikata laifi, zan amshi sunayen likitocin da suka kula da gawar Abbu, hatta da wanda ya duba Ummunka inaso na ganshi, sai kuma 'yan sandan da suka kula da case d'in dan nasan yanzu duk sun zama manya, amma komin girman mutum bazai ja da shari'a ba, insha Allahu zamu gudanar da komai, Ra'eez kasa aranka tare zamuyi wannan yaki, kuma insha Allahu zamuyi nasara, sai Kawu ya fito kuma sai an d'aure duk wani mai hannu a cikin wannan laifin.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana hawaye dan ya kasa magana saboda wani sanyi da yakeji. Kamoshi Jabeer yayi sai yaji jikinsa yayi zafi ga rawar sanyi da yakeyi. Saurin kallon Rafeek yayi yana fad'in Yaya Ra'eez fa beda lafiya.
Tasowa Rafeek yayi yana fad'in damuwace ta haifar masa da hakan, ai yana ma kok'ari, akwai ciwo arayuwarshi amma haka yake daurewa domin ya sa burin d'aukar fansa aranshi, dole muje asibiti a aunashi saboda asan irin maganin da za'a bashi dan damuwa tayi masa yawa.
Jabeer yace Ra'eez tashi muje asibiti. Girgiza kai yayi yana hawaye. Rafeek yace wallahi sai munje, matuk'ar kana son kammala wannan shari'ar to ka bari a duba lafiyar ka, sannan kasa jarumta aranka kamar yanda Kawu yayi, idan ba haka ba ciwo zai kwantar da kai.
Jinjina kai yayi yana kok'arin tashi, kamoshi Jabeer yayi tare da gyara masa rigarsa suka fita waje, rufe gidan sukayi suka wuce asibiti.
***
Cire glass likitan yayi yana fad'in Rafeek ya akayi Brr, yake barin damuwa aranshi har haka? Jininsa fa ya hau ga zuciyarsa tana samun damuwa saboda yana yauwan tunani, gaskiya dole akula dashi idan ba haka ba zai iya kamuwa da ciwon zuciya.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in insha Allahu za'a kiyaye likita, kasan yanayin aikinsu, ga rashin hutu gashi dole sai mutum yana zurfafa tunani, amma duk da haka za'a kula insha Allah.
Likita yace dama kana da alak'a da hazikin lauyan nan? Murmushi Rafeek yayi yana fad'in cousin d'ina ne a Kano suke da zama. Likita yace lallai kunyi dace da samun hazikin lauya, dan haka ku kula dashi kada al'umma ta rasa mutum mai gaskiya.
Murmushi Rafeek yayi yana fad'in zamu kula insha Allah. Likita yace ba sai mun kwantar dashi ba zaku iya maidashi gida tunda nasan zaku kula dashi acan. Rafeek yace likita inaso ka bashi gado ko na kwana biyu ne, domin Ra'eez yana da buk'atar hutu sosai, idan ya koma gida bazai iya hak'ura beje aiki ba, koda munce kada yaje acan wajen aikin bazasu gane beda lafiya ba, amma idan suka san yana kwance a asibiti dole zasu d'aga masa k'afa.
Jinjina kai likita yayi yana fad'in shikenan bara a bashi VIP room domin babban mutum ne. Dariya Rafeek yayi yana fad'in lallai kanaji da Ra'eez, ko dai ya tab'a tsaya maka ne? Murmushi likita yayi yana fad'in ko d'aya, ban tab'a zuwa kallon shari'arsa ba ma, kawai dai yanayin aikinsa ne yake burgeni, domin an bani labarin shari'arsa ta farko, sannan an bani labarin wadda yayi wancan satin, tun daga lokacin kawai nake sonshi.
Rafeek yace to mungode, akwai magungunan da za'a siyo ne? Likita yace yanzu kam tunda a nan za'a barshi zamuyi masa komai, kuma nine zan biya domin gwarzo na ne.
Tashi Rafeek yayi yana fad'in nagode abokina. Likita yace haba bakomai, muje akaishi d'akin saboda akwai allurar da zan saka masa a ruwa wadda zata sashi bacci mai k'arfi.
***
Sai da aka gama masa komai kana Rafeek yace ma Jabeer yaje gida ya fad'ama su Momynsa tunda yace anan zai kwana, amma kada ya fad'a ma Maman Rumaisa tunda dare yayi abarsu zuwa gobe.
Jabeer yace ai ba sai naje ba sai nayi masu waya kawai. Rafeek yace baza'ayi haka ba, kwanciya asibiti tana buk'atar shiri, kaje ka fad'a masu nasan kaima bazaka rasa abinda zaka d'auko ba. Jabeer yace shikenan bara naje ai kana nan ko? Rafeek yace ina nan har sai ka dawo zan tafi.
***
Bayan mintuna Jabeer ya dawo. Haka Rafeek yayi mashi sallama yace zuwa safe zaizo ya kawo masu kayan kari. Godiya Jabeer yayi masa, har bakin mota ya rakashi sannan ya dawo.
*** ***
Washe gari wajen k'arfe bakwai da rabi Rafeek ya iso asibiti ya kawo masu kayan kari, alokacin Ra'eez ya fito daga wanka yana zaune ya idar da sallah, dan Jabeer be tashe shi da asuba ba ganin yanda baccinsa yayi nauyi.
Tashi yayi jiki a sanyaye dan har lokacin baya jin kwarin jikinsa, zama yayi yana gaishe da Rafeek. Matsowa yayi yana fad'in Ra'eez ya jikin? Ra'eez yace da sauki nagode Yaya.
Zama yayi yana fad'in kadena gode mani domin duk abinda zanyi maka dan Allah ne nayi, dan haka bana son godiyar ka, kallon Jabeer yayi yana fad'in kaci abinci kaje gida ka shirya sai ka sanar ma su Mama bayan ka shiryo ka taho da ita sai ta zauna dashi kafin mu taso.
Tashi Jabeer yayi yana fad'in ka had'a masa abincin idan naje gida zanci ni. Rafeek yace shikenan amma ka biya ka fad'a masu kaga kafin ka shiryo itama ta gama shiryawa. Jabeer yace to. Sallama yayi masu yana fad'in Ra'eez sai na dawo.
****
Cike da damuwa Mama ta kalli Jabeer tana fad'in shiyasa nace ya dawo nan da zama yana ganin mu bazai rik'a damuwa ba, amma ya je ya zauna acan dole yarika damuwa, a d'akin Abbunsa fa yake kwana a saman gadonshi, taya bazai d'aura aure da damuwa ba, amma ka barni dashi dole ya dawo nan duk da yafi sabawa da can amma bazan bari wani abu ya sameshi ba.
Jabeer yace haka ne Mama, nima tunda wannan abun ya faru