Advertisements
Chapter 46 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   46 / 54

135K to 138K   out of 160.3K words

sun samu kama b'arayin da suka sace Adnan da Abban Nabeel, yanzu haka Adnan da Abban suna gidanshi ana bama Adnan taimako dan yaji jiki.


Gaba d'ayan su sukayi hamdala. Alhaji Mansur yace Jabeer kira Nabeel ka fad'a mashi dan hankalinsu ya kwanta, kai ma kira Sameer ka fad'a masa.


Bayan sun kirasu Rafeek yace d'auko flash d'in mu duba. Lek'awa Ra'eez yayi sai yaga ya shige ciki, tasowa yayi yana fad'in sai kazo ka d'aga katifar a d'auko. Murmushi Jabeer yayi yana fad'in Ra go kawai.


Alhaji Mansur yace Rafeek kama masu naga yau shiriritar tasu ta motsa. Tashi Rafeek yayi yana murmushi ya kama mashi suka d'age katifar.


Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*



4⃣4⃣



Bayan ya d'auko flash d'in har za'a maida katifar Ra'eez yace wallahi Abbah mutanan Da akwai su da dabara, tun kwanaki dana d'aga katifar nan naga wata loka a jiki amma ban bud'eta ba.


Da sauri Alhaji Mansur ya taso yana fad'in ina lokar take? Ra'eez yace gata nan ajikin gadon hada mukullinta ajiki da gani babu komai ciki tunda ba'a cire makullin ba.


Saurin lek'awa Alhaji Mansur yayi yana fad'in ku k'ara d'age katifar. Hannu yasa ya bud'e, jawowa yayi saiga ajiyar da Abbu yayi ta flash daya adana sirrikanshi.


Da sauri ya d'auko yana fad'in ikon Allah, lallai yau muna da sa'a, garinya da ka ga lokar baka d'aga ba? Ra'eez yace wallahi lokacin sauri nakeyi shiyasa ban bud'e ba, tun daga lokacin kuma ban sake tunawa da ita ba.


Sakin katifar sukayi gaba d'aya suka zo domin ganin abinda yake ciki. Jabeer yace wanne za'a fara sawa? Alhaji Mansur yace ku fara saka mana wanda aka samu yanzu kamar zamufi samun abinda muke so. Sakawa sukayi gaba d'aya suka natsu.


***


Ajiyar zuciya suka saki lokacin da ya k'are. Hawaye ne suka saukoma Ra'eez a lokacin daya gama jin bayanin Abbunsa, dan daga k'arshe Abbu ya d'auki kanshi yana fad'in wannan sheda ce ta haramtattun kaya da Alhaji Marusa yake shigowa dasu, ko da bana raye ina fatan wannan sheda zata riski adalin Alkali domin a yanke ma masu laifi hukunci dai-dai da abinda sukayi.


Jinjina kai Alhaji Mansur yayi yana fad'in wato wannan shine abinda ya jawo suka kashe Alhaji Maiwada, domin Abubakar ya fad'a mani sun gano abinda Malan Hassan yasa a gidan Alhaji Marusa shine suka kashe shi, jin yace Alhaji Maiwada yaga komai shine dalilin da yasa suka kashe shi suka d'auke kamfutarsa atunaninsu sun b'atar da kowace sheda basu san Allah yafisu ba.


Rafeek yace su hud'u ne manyan cikinsu kuma manyan masu laifi, Adebayo da Umar sune k'ananan masu laifi, sai sauran 'yan dabarsu.


Jabeer yace wato sun had'a kai an kashe Abbu sai suka d'ora Adebayo amatsayinsa, shi kuma Alhaji Barau bayan tsohon Alkali ya sauka sai ya d'orashi amatsayinsa, shi kuma Umar ya hau matsayin Adebayo, haba shiyasa yanzu ake shigo da abinda akaga dama saboda sune keda abun.


Alhaji Mansur yace kunna d'ayan mu gani.......


Bayan ya k'are suka kashe, mayar da flash d'in sukayi cikin jaka. Hamdala sukayi Alhaji Mansur yace shari'a tazo k'arshe, wannan karon mune masu matsayi domin mune masu abun nunawa, Allah sarki Naseer, Allah yaji k'ansa ya kyautata makwancinsa, domin yayi abinda akeso, dan wannan shedar tashi tafi komai muhimmanci, ko ita kad'ai muke da ita basu da hanyar da zasu iya k'aryata zargin da ake masu, ko da kotun da tafi kowace kotu shiririta da rashin iya aiki za'a kai shari'arsu ina mai tabbatar maku dole a yanke masu hukunci, haka zalika ko akwai shugaban k'asa acikinsu k'arewar kud'i da matsayi dole hukunci ya hau kansu, dan haka dole muyi magana da Alhaji Kamal a daren nan kafin gobe.


Rafeek yace gaskiya Naseer yayi jarumta, amma Abbah a shawarata a fara gabatar da shedar Naseer, bayan da kowa yasan masu laifi idan za'ayi shari'ar su sai agabatar data Abbu.


Alhaji Mansur yace wannan haka yake, Ra'eez wannan aikin ka ne, dole ka saka wad'annan shedun a mizanin da kowa zai k'ayatu da shari'ar, dan haka kasa tunani irin naku na lauyoyi ka tafiyar da shari'ar yanda zata k'awatu.


Ra'eez yace insha Allahu Abbah. Tashi yayi yana fad'in Malan Sani komai yazo k'arshe, domin daga gobe ya gama kwanan gidan yari insha Allah, zan kwanta Rafeek ka gaishe da mutanan gidan.


Tashi Rafeek yayi yana fad'in zasuji Abbah, nima tafiya zanyi ina so naje wajen Hamza kafin nawuce. Alhaji Mansur yace ka masa godiya. Sallama yayi masu ya wuce d'akin da yake kwana.


Tashi sukayi suka raka Rafeek, bayan ya tafi suka kulle gidan suka dawo ciki. Wanka Ra'eez yayi kafin ya kwanta, bayan Jabeer ya fito ya kwanta yana kallon Ra'eez da yake waya k'asa-k'asa.


Murmushi yayi ya juya baya yana fad'in gulmamme wayar ma baza'ayi da k'arfi ba. Kyaleshi Ra'eez yayi yana fad'in Pretty kikace Raheena tazo? Rumaisa tace ai naji dad'i da kace bazaka zo cin abincin rana ba Yaya Jabeer yazo ya kai maku asibiti kai da Ummu zakuci, bakaga yanda ta b'ata rai ba, abincin ma kasa ci tayi dole ta tafi.


Murmushi yayi tana fad'in daga gobe ai zata gane dalilin da yasa naki karb'ar soyayyar ta, idan tana da hankali bazata sake nemana ba. Rumaisa tace wallahi na kosa a gama wannan shari'ar mubar garin nan.


Ra'eez yace kinsan gobe Kawu a gida zai kwana fa. Rumaisa tace da gaske? Ra'eez yace insha Allahu, domin a gobe zamu nemi ayi shari'arsa dasu Alhaji Barau.


Rumaisa tace Allah ya tabbatar, aikuwa gobe azumi zanyi. Ra'eez yace muna tare kenan, nima azumin zanyi, kinga zamuyi shan ruwa mai dad'i. Murmushi tayi suka cigaba da firar su.


Bayan daya kashe wayar ya lek'a fuskar Jabeer yana fad'in kayi hak'uri na hanaka bacci abokina. Tsaki Jabeer yayi ya tureshi yana fad'in dalla matsamun marar kunya.


Dariya Ra'eez yasa yana fad'i. Haushi kakeji kai baka da abokiyar fira. Jabeer yace Allah tausayin Raheena nake, ina tunanin yanda zataji idan tasan asalin kalar Mahaifinta. Ra'eez yace hakuri zatayi, shiyasa nace ka aureta hakan zai rage mata zafi, kaga.... Saurin juya masa baya Jabeer yayi ya rufe kunnuwanshi yana fad'in sai da safe. Dariya Ra'eez yasa yana fad'in Allah ya kaimu.


***** *****


*Safiyar alhamis a kotu*


Duk da kasancewar shari'ar ta bama mutane haushi amma hakan be hana suka dawo ba domin suji yanda za'a k'are. A sannu kowa ya shiga kotun suna jiran zuwan Alkali.


Bayan da Alkali yazo kowa ya samu nutsuwa, sai dai Alkali sam baya cikin natsuwarsa, tunda Lucky ya fad'a masa an kama yaranshi kuma an tafi dasu Adnan hankalinsa yake tashe, gashi Lucky yace bazai zauna ba shima guduwa zaiyi, hakan ne yayi masifar tada mashi hankali, dan ko sauran abokansa bai fad'amawa ba dan yasan suna iya barinshi tunda shine ya zamar ma dole yazo kotu.


Magatakarda ne ya tashi ya sake karanto shari'ar da za'a gabatar. Bayan ya zauna Alkali ya d'ago kai yana fad'in Brr. Ra'eez muna jiranka, da fatan wannan karon kazo da cikakkar sheda.


Fitowa Ra'eez yayi yana fad'in nazo dasu ya mai shari'a, kamar yanda kowa ya sani a ranar talata an buk'aci kotu da ta kawo Fawwaz M. Sanda domin ya amsa wasu tambayoyi wad'an da suka shafi wannan shari'ar da akeyi, sai dai bayan da aka je kiransa sai akace baya k'asar wanda na ja da hakan sai aka buk'aci dana tabbatar da shedar yana cikin k'asar nan, alokacin bani da wannan shedar, amma ayanzu ina so kotu ta bani dama domin na gabatar da ita.... Kotu ta baka dama.


Hamza ne yayi ma su Hassan alamu hakan yasa suka fita, ba'a jima ba sai ga Fawwaz sun taso shi agaba duk ya fita hankalinsa, duk da babu wanda ya tab'ashi amma tashin hankali ya hanashi sakat.


Gyara zama Alkali yayi kirjinsa yana dukan ukku-ukku, gaba d'aya zufa ce take zubo masa, amma duk wanda ya kalleshi sai ya d'auka yayi murna da hakan, saboda ba'a gane komai ta fuskarshi.


Bayan da Fawwaz ya shiga ya tsaya sai Ra'eez ya tako kusa dashi.


Ra'eez... Kotu zata so taji cikekken sunan ka.


Sunana Fawwaz Muhammad Sanda.


Ra'eez... Malan Fawwaz ko zaka fad'a mana yaushe ka dawo k'asar nan.

Fawwaz... Zanyi wata d'aya dana dawo.


Ra'eez.... kenan dai baka sake komawa ba? Kai Fawwaz ya d'aga yana fad'in E.


Ra'eez... Malan Fawwaz ko zaka iya fad'a mana sunan makarantar da kayi wato secondary da shekarar da ka gama, da kuma abokan ka wad'an da bazaka iya mantawa ba.


Fawwaz... Kings college nayi, na kammalata a 2008, manyan abokaina kuma guda biyu ne, Sufwan da Adnan, sai dai Sufwan ya rasu.


Ra'eez... A cikin 'yan ajinku ko zaka iya tuna *Farouk Ahmad Ringim*?


Fawwaz... Shiru yayi yana mazurai, can kuma yace gaskiya na mantashi domin shekarun da yawa.


Ra'eez... Naseer Sambo Jarmai fa?


Fawwaz... Nifa mutane biyu kad'ai na iya rik'ewa saboda sune manyan abokai na, sauran kawai ana gaisawa wasu ma ko magana bamayi.


Ra'eez... Murmushi yayi yana fad'in shikenan bara na tuna maka su, Farouk shine abokin fad'an ka lokacin kuna aji shidda, a binciken da nayi hakan ta faru ne silar wata yarinya mai suna Minal wacce ta kasance budurwa a wajen Farouk, bayan ka ganta kaji kana sonta hakan yasa ka nemi daya bar maka ita, shi kuma ya nuna besan haka ba, wannan shine silar rikicin ku dashi, shin ko zaka fad'ama kotu abinda ya faru a ranar da kukayi fad'a na k'arshe wanda Adnan ne ya raba ku?


Fawwaz... Zufa ce ta fara keto mashi, kallon mutanan kotun ya farayi ko zaiga Dadynsa. Runtse ido yayi yana tuna maganar da sukayi da Dady ana gobe za'a saceshi.


*Fawwaz abinda nakeso da kai ka sani, koda Allah yasa dole sai kaje kotu ina so ka tsaya akan maganar da zan fad'a maka, duk yanda za'ayi kada ka sake ka amsa laifinka, domin ita kotu da hujja ukku take amfani, na farko idan aka samu shedu mutum ukku, na biyu idan aka sami hujjar zahiri kamar ace hujja ta vedio, na ukku idan wanda ake zargi ya amsa laifinsa. Ina so ka sani ayanzu Adnan da Alhaji Sulaiman ne kawai suka. san abinda ya faru kaga kuwa su biyu ne, sannan basu da shedar da zasu iya nunawa saboda mun konata, kai ka d'ai ne zaka iya bada k'ofar a kamaka da laifi, dan haka ina so duk yanda Brr. zai maka tambaya ka nuna baka san komai ba.*


Ajiyar zuciya Fawwaz ya saki yana kokarin tattaro jarumta, kallon Ra'eez yayi yana fad'in gaskiya ni bani da wani abokin fad'a a makaranta, duk wanda yasan mu yasan mu ukku ne, bama shiga harkar kowa bare har muyi fad'a da wani, kuma ni bana soyayya a makaranta.


Ra'eez... Jinjina kai yayi yana fad'in shikenan zaka iya tafiya. Ajiyar zuciya Fawwaz ya saki shida Alkali kafin ya koma ya zauna.


Ra'eez... Ya mai shari'ar ina so kotu ta bani dama domin nayima Alhaji Sulaiman tsohon shugaban makarantar kings college tambaya.... Kotu ta baka dama.


Ra'eez.... Kotu zata so taji sunan ka da kuma bayani akan tsohuwar makarantar ka.


Sunana Alhaji Sulaiman, na rik'e matsayin shugaba amakarantar kings college wanda tuni na aje aiki.


Ra'eez... A shekarar 2008 an samu gawar d'aya daga cikin d'alibanka a bayan gari, shin ko zaka iya fad'a ma kotu abinda ka sani.


Alhaji Sulaiman.... Ajiyar zuciya yayi yana jin wata irin kunya, kallon yawan mutanan kotun yayi kafin ya duk'ar da kai yana fad'in da farko ina so na fara neman yafiyar Iyayen Farouk Ahmad, domin na aikata masu laifi mai girma, duk da bani da hannu cikin kisan da akayi masa amma ina da sa hannu a wajen lullub'e gaskiya.


A shekarar 2008 a ranar alhamis da misalin k'arfe 5:15 na yamma, a ranar ina zaune a ofis na samu waya daga Alhaji Muhammad Sanda wato tsohon Alkalin kotun nan wanda ya kasance Mahaifin Fawwaz, bayan mun gaisa yake fad'a mani yana so nayi masa alfarma, idan har nayi masa haka zai bani mak'udan kud'i, to alokacin kunsan zuciya da kwad'ai, jin yawan kud'in da za'a bani yasa na amince da abinda ya fad'a.


Anan yake fad'a mani Yaronshi Fawwaz yayi fad'a da Farouk tsautsayi yasa ya yankeshi da wuk'a har hakan ya jawo ajalinsa, ayanzu haka yana bayan makarantar wajen band'akuna yana so nayi kok'ari kafin kowa yaga gawar a fitar da ita, hakan ne zaisa babu wanda zai zargi komai tunda ba'a makarantar aka ga gawar ba, kuma lokacin tashi yayi.


Duk da na jinjina abun amma tuna yawan kud'in yasa banyi tunanin komai ba kawai na amince, haka naje da mota ta dan bana so nasa wani ya tayani aje a tona asiri, koda aka ganni nayi cikin makaranta babu wanda ya damu acikin masu aiki saboda sun san nine sunyi tunani zagaye nakeyi.


Haka naje na d'auki gawar nasata a mota na bar makarantar, sai da gari yayi duhu kafin naje na wurgar da ita na bar wajen, tabbas zuciyata taji babu dad'i domin na aikata babban laifi, amma tunda na amshi kud'i a hannu sai na manta da komai, tabbas nayi nadamar abinda na aikata, kuma ina neman alfarmar wannan kotu data sassauta mani akan hukuncina.



Ina da ja ya mai shari'a. Brr. Bajinta ne yayi saurin tashi, risnawa yayi yana fad'in ya mai shari'a nine lauyan Alhaji M. Sanda, ina so kotu ta bani dama domin na kareshi abisa sharrin da Alhaji Sulaiman yake son yayi masa.


Ajiyar zuciya Alkali ya saki dan besan Alhaji M. Sanda yayi magana da Brr. Bajinta ba. kai ya jin jina yana fad'in kotu ta baka dama, amma zaka iya jira Brr. Ra'eez ya kammala tambayoyinsa.


Komawa yayi ya zauna yana fatan nasara. Gaba d'aya kotun ta d'auki hayaniya. Bubbuga tebur Alkali yayi kafin akayi shiru. Hannu yasa yana gyara glass d'insa ganin abinda yake faruwa a cikin kotu. Alhaji Kamal ne ya shigo shida wasu mutane guda biyu, hakan yasa wasu daga cikin kotun suka tashi domin su basu wajen zama.


Ajiyar zuciya ya saki yayin da cikinsa ya fara kad'awa, meya kawo Alhaji Kamal kotu kuma bayan shima Alkali ne? Hannu yasa ya d'auki kofin ruwan da yake kusa dashi yasha, gyara zama yayi yana fad'in Brr. Ra'eez kacigaba.


Ra'eez... Murmushi yayi yana fad'in Alhaji ko zaka iya fad'ama kotu dalilin da ya hanaka halartar kotu a ranar talata bayan kuma kace zaka zo?


Alhaji Sulaiman... Tabbas nayi niyar zuwa kotu domin nazo na fad'i gaskiya, kuma aranar na shirya na fito daga gida domin halartar kotu, sai dai ina barin gida wasu mutane suka tare ni, tunda na tsaya suka fiddo ni ban sake sanin abinda yake faruwa ba sai da na farka na ganni a d'aure ni da wani yaro wanda shima yana da alak'a da wannan shari'ar domin shine abokin Fawwaz da yake magana wato Adnan, tun alokacin na gane dalilin kamo mu, an azabtar da Adnan yanzu haka yana can ana masa magani dan cikin ikon Allah 'Yan sanda suka ceto mu yayin da suka samu sa'ar cafke mutane biyu daga cikin b'arayin.


Ra'eez... Mungode Alhaji zaka iya tafiya, ya mai.... Saurin tashi Brr. Bajinta yayi yana fad'in ya mai shari'a ina so kotu ta bani dama domin nayi magana akan abinda Alhaji Sulaiman ya fad'a. Da sauri Alkali yace kotu ta baka dama.


Mamaki ne ya kama mutane, gashi dai Brr. Ra'eez be kammala tambayoyinsa ba amma an bama wani dama. Ra'eez kuwa murmushi yayi ya koma gefe yana kallonshi.


Matsowa Brr. Bajinta yayi yana fad'in Alhaji Sulaiman naji bayanin ka, sai dai kada ka manta kotu tana amfani ne da hujjar zahiri ba ta baki ba, shin ko zaka iya nuna ma kotu hujja akan cewa Alhaji M. Sanda ne ya saka aikata abinda ka fad'a.


Alhaki Sulaiman... Gaskiya bani da wata hujja domin lokaci ne mai tsawo, kuma banyi tunanin d'aukar wata sheda ba saboda nasan bazata mun amfani ba, amma tabbas shine yasani wannan aikin.


Brr. Bajinta... Baka da hujja Alhaji Sulaiman, domin duk wanda yake cikin kotun nan da wanda yasan tsohon Alkali da wanda besanshi ba kowa yasan irin adalcinsa, kuma wannan abun daka fad'a zai iya yuwuwa wasu ne suka biyaka domin kazo ka b'ata masa suna tunda gashi ka kasa gabatar da hujjar abinda ka fad'a, ina rokon wannan kotun da kada tayi amfani da abinda Alhaji Sulaiman ya fad'a. Nagode.


Matsowa Ra'eez yayi yana fad'in Alhaji zaka iya tafiya, ya mai shari'a ina so kotu ta bani dama domin na gabatar da mutanan da suka sace Adnan da Alhaji domin nayi masu tambayoyi.


Dammm gaban Alkali ya fad'i, hannu yasa ya sake d'aukar ruwa yasha, abun goge fuska ya ciro ya goge zufar data sauko masa, da kyar ya sauke ajiyar zuciya yace kotu ta baka dama.


Zuwa yanzu mutane sun fara mamakin Alkali, domin gaba d'aya ya fara rasa nutsuwarshi sai gyaren zama yake ga ruwa da yake yawan sha yana goge fuska.


Bayan da suka tsaya agaban kotu kowa

46 / 54