Advertisements
Chapter 41 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   41 / 54

120K to 123K   out of 160.3K words

tawa yasa na kawo wannan matsayin.


Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in duk da lokaci ya fara hararar mu amma zanso ka fad'ama masu sauraron mu a shekarun baya lokacin kana aiki a k'aramin ma'aikaci wane case ne yafi baka wahala kuma ya baka tsoro.


E to, gaskiya nayi cases da yawa wad'an da bazan iya tunawa da wasu ba, amma ina ganin akwai wani case da na tab'ayi wanda yayi matuk'ar bani wahala da tsoro, idan ban manta ba yau kusan shekaru goma kenan, case ne wanda yake a cukurkud'e hakan yasa nasha wahala kafin na kammala lashi, zan iya cewa a wannan case d'in bayan kammalashi har k'arin matsayi na samu.


To 'Yallab'ai tambayata ta k'arshe a wannan shirin ko zaka fad'a mana dalilin zuwanka wannan matakin?


Gyara zama yayi kafin ya d'auki ruwa yasha yana gyara glass d'in idonshi. Kofin ya aje yana fad'in E to, gaskiya wannan matsayi dana zo zan iya cewa dalilin taimako ne yasa nazoshi, nasan kuma mutanan da suka taimaka mani nazo wannan matsayin har yanzu suna alfahari dani, bazan iya fad'arsu ba domin ba'a son ka fad'i wanda yayi maka alkhairi tunda dan Allah yayi, amma gaskiya har in mutu bazan iya mantawa dasu ba.


Murmushi Rafeek yayi yana fad'in 'Yallab'ai kayi mana halin ku na 'yan sanda, domin baka fito fili ka fad'a mana silar zuwanka wannan matsayin ba.


Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in wannan kuma sirri ne. Dariya sukasa gaba d'aya. Rafeek yace daga k'arshe wata shawara zaka bama sauran 'yan sanda.


E to inaso nayi amfani da wannan damar na k'ara bama sauran yan sanda shawara akan surike gaskiya, dan duk wanda ya rike gaskiya baya tab'ewa, kuma su sani wannan aikin da sukeyi a ciki zasu nemi duniyarsu da lahirar su, Allah yasa mudace amin.


Juyowa Rafeek yayi yana fad'in to masu sauraron mu anan muka kawo k'arshen wannan shiri na fira da mukayi da Kwamishnan 'Yan sanda, sai muce mungode Allah yasa aje gida lafiya.


Kwamishna yace madallah nima nagode, masu saurare ina maku fatan Alkhairi.


****

Bayan da Rafeek ya koma gida duk da dare yayi sai da ya tace shirin da ya gabatar ya adanashi dan yasan zeyi masa amfani kafin ya kwanta.


**** ****

Alhaji ya jikin Alhaji Marusan? Jiki da sauki za'ace, amma fa yana can yana jin jiki. Momy tace bawan Allah, gaskiya asara bata da dad'i dole yashiga wannan halin, amma ai zaku taimaka masa da wani abun ko zai rage asara ko? Murmushi yayi yana fad'in Hajiya Binta kenan, baki san waye Alhaji Marusa ba, shine fa silar arzikin mu, taya kike tunanin dukiyarsa zata girgiza dan kawai yayi wannan 'yar asarar, kawai shegen son kud'i gareshi shiyasa yashiga wannan halin, amma babu abinda zamu taimaka masa dashi sai kulawa.


Jinjina kai tayi tana fad'in to Allah ya kyauta ya kuma tsayar akanshi. Yace amin. Kallonta yayi yana fad'in wai Ra'eez yana zuwa gidan nan kuwa? Girgiza kai tayi tana fad'in rabonsa da gidan nan tunda yazo sukayi sallama da zamuje Dubai, amma tace aiki ne yayi masa yawa shiyasa.


Murmushi yayi yana fad'in wallahi na kosa naga Raheena a gidan miji nima ko na samu jika. Momy tace lokacin zai zo, ai anyi mewuyar tunda ta samu mijin aure, Allah dai ya bashi ikon kammala wannan aikin lafiya. Alhaji Barau yace amin ya Allah. 🤣


**** ****


Wajen k'arfe goma na safe Ra'eez ya kwankwasa k'ofar ofis d'in Alhaji Barau dan yaga lokacin da yazo, amsa mashi yayi tare da bashi izini hakan yasa ya tura k'ofar bakinsa d'auke da sallama.


Amsawa yayi yana fad'in wai Ra'eez kaine shine ka tsaya kwankwasawa? Gaisheshi yayi yana fad'in wallahi kuwa. Kujera ya nuna masa yana tambayarsa k'arfin jiki.


Ra'eez yace jiki yayi sauki babu abinda yake damuna yanzu. Alhaji Barau yace nima asibiti na biya shiyasa ban shigo da wuri ba, abokina Alhaji Marusa ne beda lafiya wata asara ce ta sameshi tunda yaji hankalinsa ya tashi ya zube shikenan sai ya samu shanyewar b'arin jiki.


A zabure Ra'eez ya kalleshi yana fad'in Alhaji Marusan? Ido ya tsura mashi kafin ya furta kasanshi ne? Duk'ar da kai Ra'eez yayi yana fad'in a wajenka nasanshi shiyasa naji tausayinsa.



Murmushi ya saki yana fad'in ai da sauki tunda likita yace jininsa ya sauka saboda har yanzu basu bari ya farka ba, sunfi so sai ya samu hutu zuciyarsa ta natsu sannan, a wajenshi ma na d'an jima saboda babu kowa a gunshi, kasan yaran zamani, akwai babban d'anshi amma saboda be damu dashi ba ko kuma ince shi Alhajin be jawosu ajikinshi suka saba ba shiyasa basu damu dashi ba, ga matarsa taje Dubai sai gobe zata dawo.


Ra'eez yace Allah ya kyauta. Alhaji Barau yace amin. Kallonshi yayi yana fad'in kamar akwai magana a bakin ka ko? Jinjina kai Ra'eez yayi yana fad'in dama jiya bayan mun tashi daga aiki wani yazo ya shigar da k'ara, to case d'in kisa ne, kuma nine suka d'auka amatsayin wanda zai tsaya masu, shine nazo inji ko an kawo maka takardar?


Gyara zama Alhaji Barau yayi yana fad'in yanzu na shigo gaskiya ban iske takardar komai ba, kila dai ko zuwa anjima, amma case d'in waye? Ra'eez yace e to, gaskiya tsohon case ne, dan abun ya dad'e za'ayi kusan shekaru sha biyu da faruwar abun, to alokacin basu da shedar da zasu gabatar ma kotu shiyasa sukayi hak'uri, amma ayanzu sun samu duk wata sheda shiyasa suke so ayi shari'ar.



Tsaki Alhaji Barau yayi yana fad'in kaji wani shirme, ko sababbin cases nawa muke dasu duk basu ishemu ba sai an koma shekarun baya an d'auko mana wata tsohuwar shari'a saboda kawai an maida kotu wajen wasan yara, yanzu haka ko anyi shari'ar bance shedarsu zata wadatar ba, saboda na tabbata da wuya a samu wanda yayi kisan araye, idan ko an sameshi to wasu shedun basa nan, gaskiya banji dad'i daka amshi wannan case d'in ba, kawai ka turasu k'aramar kotu.


Gyara zama Ra'eez yayi yana fad'in Alhaji a taimaka masu, kasan kowa yana alfahari da wannan kotun, ba kowa bane kuma yake jawo mata farin jini sai kai, yau idan babu kai a wajennan nasan ba kowa ne zaiso ya kawo shari'arsa nan ba, domin kaine hasken da yake haske kotun, duk wasu mutane da suke zarya nan saboda kai suke zuwa, idan sukaji kayi fatali da case d'insu zaka sare masu sa ran da suke dashi, domin idan basu samu adalci a wajen ka ba sun san babu inda zasuje a amshe su.


Murmushi Alhaji Barau yayi yana gyara zaman glass d'inshi yace wannan haka yake, nagode daka tunatar dani, shiyasa nake jin dad'in kasancewar ka akusa dani, domin wani lokacin nakan so na kwafsa amma sai ka maidoni hanya, gaskiya Ra'eez kai d'in na daban ne, shikenan kashirya tsaya masu zuwa litinin za'a fara shari'ar, kuma insha Allahu zan sama masu adalci kodan ta silarka.


Turo k'ofar ofis d'in akayi had'e da sallama, amsawa sukayi kafin ya shigo. Alhaji Barau yace Malan Jamilu yau ka makara ko? Wanda aka kira da Malan Jamilu yace wallahi iyalina ne basuji dad'i ba sai da mukaje asibiti amma da sauki.


Alhaji Barau yace Allah ya basu lafiya, ai bazaka zauna ba dama yau juma'a sa hannu kawai ka tafi. Mik'a masa takarda yayi yana fad'in jiya aka kawota lokacin ka tafi shiyasa na ajeta, takardar... Katseshi yayi yana fad'in Ra'eez yayi mani bayani, amsa yayi yana fad'in zaka iya tafiya.


Godiya yayi mashi Ra'eez ya gaishe shi yana masa ya mai jiki. Kud'i Alhaji Barau ya bashi yana fad'in ga wannan ka siya mata magani. Godiya yayi mashi ya fita yana mamakin yau Alhaji Barau yayi masa kyauta. (Niko nace agaban suriki ai dole yayi gwaninta😉)


Tashi Ra'eez yayi yana fad'in zan koma nagode Alhaji. Murmushi yayi yana fad'in babu damuwa Allah ya bada sa'a, idan kana da wata matsala kazo ka fad'a mani, domin bazan bari ka fad'i ba. Godiya yayi masa ya fice.


****


Dariya sosai Jabeer yayi jin yanda Ra'eez yayi da Alhaji Barau. Tsaki Ra'eez yayi yana fad'in wallahi wannan mutumin beda kunya, amma ka kyaleshi na kusa koya masa yanda akejin kunya.


Jabeer yace gashi kuwa hada maka addu'ar neman sa'a besan akanshi zata k'are ba. Ra'eez yace ai d'azu munyi waya da Yaya yace ayau zai sanar da shari'ar dan yana so tayi mutane.


Jabeer yace kasan kuwa duk wanda yaji za'ayi shari'ar shekaru da yawa dole yazo yaji yanda zata kaya, ni kaina ina so litinin tayi kawai naji yanda za'a fafata.


Ra'eez yace wallahi ni kaina nakosa akammala komai kona samu natsuwa, gaba d'aya bani da lokacin kaina, Pretty hak'uri kawai take dani damma muna d'an waya.


Jabeer yace ai komai ya kusa zuwa k'arshe da izinin Allah. Waya Ra'eez ya d'auka yana fad'in bara naji muryarta ko naji kwarin yin aikin dan gaskiya yau dole na tsaya fira.


Murmushi Jabeer yayi ya mik'e yana fad'in nayi nan kada naji kayan haushi. Ra'eez yace idan kaji haushi gobe na ganka da budurwa. Jabeer yace kai dai kasa ido Allah ya kusa kawota.



Maganar da yaji yasa ya maida hankalinsa ga wayar. Jabeer kuwa ficewa yayi yana masu dariya. Bayan ta gaishe shi yace Prettyna ki k'ara hakuri kinji, ni kaina ina kewar ki da yawa.


Murmushi tayi tana fad'in haba bakomai, ai wannan aikin da kakeyi mu kake mawa, dan haka ina nan ina jiranka kuma ina maka addu'a nasan zakayi nasara. Ra'eez yace nagode sosai ina so yau kimun kwalliya kamar zakije party dan yau fira zamuyi.


Murmushi tayi tace shikenan yanda kace, sai kazo. Ra'eez yace me zan taho maki dashi? Duk abinda yayi maka ta fad'a cike da farin ciki dan tayi kewarsa, kwana biyu koya zo baya dad'ewa shima da Mama kawai suke gaisawa.


Ra'eez yace shikenan sai nazo ki gaishe da Abdallah da Mama. Zasuji ta fad'a. Kiss yayi mata yana fad'in miss u, da sauri ta kashe wayar. Dariya yayi yana fad'in zan kamaki ne.


**** ***


Tsaki Fawwaz yaja a karo na ba adadi, zaune yake a cikin lambun gidansu, yau kwana biyu kenan ya kasa samun nutsuwa, tunda Adnan yayi masa maganar Farouk shikenan hankalinsa yaki kwanciya, duk yanda yaso ya cire abun aranshi ya kasa, gashi baya so ya fad'ama Dad d'insa hankalinshi ya tashi, gara kawai yayi shiru ya magance matsalar da kanshi.


Kashe sigarin daya gama sha yayi yana kurb'ar giyar da ya zuba a kofi, a 'yan kwanakin nan ko wajen abokansa baya zuwa saboda damuwa, shaye-shayenshi ya k'aru ko zai samu sauki amma abanza.


Waya ya d'auka ya kira babban abokinsa, yana d'agawa yace *Milo* mu had'u a gidan shakatawa ta akwai maganar da zamuyi, amma kazo kai d'aya. Shikenan sai kazo




Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*



4⃣0⃣


What? Dude kasan abinda kake fad'a kuwa? Kai Fawwaz ya jinjina yana zuk'ar sigari. Gyara zama Milo yayi yana fad'in lallai kai babba ne Dude, haba shiyasa baka da tsoro ashe tuni tsoron ya bar zuciyar ka, ai duk mutumin da zai iya aikata kisan kai bana tunanin yana da tsoro a ranshi, ka ganni nan ko fad'a bana so saboda nasan yanda halin maza yake akwai bak'ar zuciya, da an fara fad'a yanzu zakaji an yanki wani ko an fitar masa da jini, wannan dalilin ne yasa bana son zama a club.



Tsaki Fawwaz yayi yana fad'in kada ka bani kunya mana Milo, ina tunanin na kawo kuka gidan mutuwa sai kazo mani da wannan banzar maganar.


Gaskiya na fad'a maka ai, Milo ya fad'a yana kunna sigari. Ajiyar zuciya Fawwaz yayi yana fad'in wallahi tsoro nakeji kada Adnan ya tona abinda ya faru.



Murmushi Milo yayi yana fad'in haba kada ka bani kunya, kada kamanta Dadyn ka shine tsohon Alkalin babbar kotu, duk da ya aje aiki har yanzu yana fad'a kuma anaji, sannan kace abun ya faru tun kuna secondary banga dalilin da zaisa ka damu kan ka ba, shima Adnan d'in cewa yayi kawai ya tuna maka ne bawai zai tona asiri yake nufi ba, kaga idan har zaka saka damuwa aranka ina tabbatar maka kaine zaka tona kan ka, kawai ka share kacigaba da chilling.


Dariya Fawwaz yasa yana fad'in shiyasa nake sonka abokina, amma wallahi kwana biyu bana baccin kirki. Hannu Milo yasa aljihu yana fad'in ina zuwa, ai nine mai bada maganin bacci, ina tabbatar maka daga yau ka dena rashin bacci.


Mik'a masa yayi yana fad'in kaga wannan kwayar ita ake kira da 'yar hutu, nima wani abokina ne ya bani ita d'an gidan Alhaji Marusa.


Fawwaz yace ba dai Marwan ba? Shifa, ai kasan Gayen yasan ta kan kayan hutu, shiyasa fa kaga muna d'asawa dashi dan baya harka da kayan Nija dan basu da inganci, jiya mukayi waya dashi yake fad'a mani ranar monday zai koma india kasan baya son zama a Nija.


Amsa Fawwaz yayi yana fad'in ai gaskiya Marwan babba ne, shiyasa nima banso su Dad sukace na dawo ba, acan hankalin mu kwance sai abinda mutum yaga damaryi.


Milo yace tashi muje Beb d'ina tana jirana d'azu tazo mani week end. Fawwaz yace ai kai kaji dad'inka tunda an ware maka gidanka, ni kuwa basa bari na kwana a wani waje duk da an mallaka mani gida.


Tashi Milo yayi yana fad'in ba sai karik'a wuni anan ba wayasan abinda kakeyi, iyaka sai lokacin bacci yayi ka koma. Fawwaz yace ka kawo shawara haka za'ayi, nagode abokina.


**** ****


Wai Marwan ba magana nake maka ba. Baki ya turo yana fad'in wai meyasa kike son takura mani Mom, ko dan kinga ina zuwa ganin ku, shi *Khalil* da baya zuwa ai bakiyi masa haka.



Hannunshi ta kamo tana fad'in yi hakuri ba takura maka nakeyi ba, naji kace mun Alhaji beda lafiya kuma kana maganar zaka tafi bayan kasan yanzu ne Alhaji yake da buk'atar ka tunda kaga halin da yake ciki, ni dai mace ce bazan iya jinyarsa ba, gashi ba wani d'an uwa gareshi ba da an kirashi, dole kaine babba kai zaka tsaya ka kula dashi.


Saurin kallonta yayi yana fad'in wallahi Mom bazai yuwu ba, shikenan abubuwan da nake dasu acan sai na hakura dasu, Dad fa yana da kud'i, idan kana da kud'i babu abinda zai gagareka, shi kanshi likitan yace zasu kula dashi tunda akwai kud'inshi da yawa a account d'insu, dan haka ni bazan iya jinya ba.


Kai ta jinjina tana fad'in shikenan dena fushin, tunda akwai kud'in za'a samu masu kula dashi, nima ba zama zanje inyi ba saboda kasuwancina, amma zan rik'a lek'awa, kaga yanzu asara ta sameshi idan ban tsaya na kula da tawa dukiyar ba sai nima nabi sahunsa dan shi tsufa ya taho masa ga mutuwar b'arin jiki ai kaga beda sauran amfanuwa matuk'ar be warke ba, yanzu haka kayan dana saro suna hanya jiransu ma nakeyi kafin na lek'a asibitin tunda kace allurar bacci sukayi masa.


Tashi yayi yana fad'in zan fita ni. Kallonshi tayi tana fad'in amma Marwan akwatin da naga ka d'auko a d'akin Alhaji na meye? Fuska ya d'aure yana fad'in amma ai ina da gadonshi ko? Kai ta d'aga, kauda kai yayi yana fad'in amfani zanyi dasu to.


Be jira amsarta ba yayi waje. Murmushi tayi tana fad'in Marwan manya, da Alhajin yana nan zai baka wad'an da sukafi haka ma. Wayarta ce tayi k'ara hakan yasa tayi saurin d'auka ganin wanda ya kira.


A zabure ta mik'e tana fad'in ban gane ba, ka bincinka jirgin da akace ya nutse kuwa? Shiru tayi tana sauraronshi. Salati tasa hawaye suka fara wanke mata fuska, hakuri ya bata ya kashe wayar.


Zaman 'yan bori tayi tana kwara ihu, da sauri masu aikin gidan suka fito jin Hajiya na ihu. Kuka suka isketa tanayi kamar k'aramar yarinya, nan suka shiga bata hakuri amma kamar izata sukeyi.


**** ****


Ido kawai Alhaji Marusa ya tsura ma Matarsa da take zaune a gefenshi tana share hawaye, Alhaji Barau da Mr. Kallah sai hakuri suke bata jin asarar data sameta.


Alhaji Barau yace Hajiya hakuri zakiyi, kinga yanayin da yake ciki be kamata arik'a tada masa hankali ba, addu'a zakiyi Allah ya maido maki da wasu kud'in. Goge idonta tayi tana fad'in dole nayi kuka, wannan bala'i kamar wad'anda aka sama hannu, so akeyi asirin mu ya tonu.


Mr. Kallah yace Hajiya sai hakuri, yanzu Alhaji kulawa yake buk'ata dole ki daure ki kula dashi hakan zaisa ya samu k'arfin jikinshi tunda likita yace abun beyi yawa ba za'a iya shawo kan matsalar dan yanzu haka zasu fara mashi gashi kinga idan kina kwantar masa da hankali zaifi saurin warkewa.


Alhaji Barau yace to Allah ya kyauta, Mr. Kallah muje ko. Tashi sukayi suna fad'in Alhaji Allah ya k'ara sauki. Kai ya jinjina masu yana binsu da kallo har suka fita.



Zaune suke a mota suna kwasar dariya. Mr. Kallah yace gaskiya na tausaya masu, ga Hajiya itama asara ta sameta,

41 / 54