Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
gashi a kwance ko magana baya iyawa, gaskiya da munsan haka zata faru dashi da bamu aikata masa haka ba.
Alhaji Barau yace bamuda laifi, son kud'inshi ne ya jawo masa haka, ita kuma Hajiya kila zakkace aka fitar mata, itama son kud'in gareta ai, kasan kuwa yanda take cin kud'in Alhaji ita da 'Ya'Yanta, ga satar da suke masa, ai alhakinsa ne ya kamata.
Mr. Kallah yace duk da haka ya kamata mu tausaya mashi a fitar dashi waje sai kaga cikin kwana ukku ya tashi amma zafin zeyi masa yawa, gaskiya ko bazaka taimaka ba ni zansa afitar dashi. Ganin yanda Mr. Kallah ya dage yasa Alhaji Barau ya amince.
Fita sukayi zuwa ofis d'in likita, anan suka masa bayani, nan take ya kira wani abokinsa a America, babu b'ata lokaci suka gama komai, inda za'a tafi dashi gobe saboda litinin a fara masa magani.
Sallama sukayi masa suka wuce domin nema masa Visa, dole da Mr. Kallah zasu tafi tunda Marwan yace bazeyi jinya ba. Kasancewarsu manya nan take suka samu jirgin safe na gobe, haka suka rabu.
**** ****
Washe gari tunda safe jirginsu ya d'aga, Hajiya taso ta bisu dan bata jin dad'in zaman gidan, wayar data samu daga Yaronta zai zo yasa ta fasa binsu asalima taji dad'in tafiyar tunda zata sake wannan karon a gida zasuyi sha'aninsu ba sai taje gidanta da suka saba had'uwa ba tunda Marwan ma yau ya tafi.
**** ***
Duk wani shirin shiga kotu sun kammalashi, duk inda kaje zakaji ana maganar shari'ar da za'ayi gobe, mutane da yawa suna son suje suji wace irin shari'ace haka bayan shekaru masu yawa kuma za'a maidota baya.
Wajen k'arfe sha biyu su Alhaji Mansur da Matarsa suka sauka lagos, Ra'eez da Jabeer suka d'aukosu, kai tsaye gidan Mama suka kaisu inda Alhaji Mansur zai zauna a gidan Ra'eez.
Sosai Mama tayi farin ciki da zuwan su, Rumaisa ta kawo masu abincin da zob'o. Zama sukayi aka gama gaisawa kafin suka ci abinci, haka suka cigaba da tattaunawa.
Da yamma Alhaji Mansur da su Ra'eez suka nufi wajen Kawu tare dasu Jabeer. Sosai Kawu yayi farin cikin ganinsu. Haka suka zauna suna ta fira. Alhaji Mansur yace sunyi waya da Abubakar yace da zaran za'a fara gabatar da shari'ar su Malan Sani zai zo.
Murmushi Kawu yayi yana fad'in wallahi jinake kamar mafarki, bani da abun roko daya wuce Allah ya nuna mani ranar da zan fita daga wajen nan, ranar da zanga lokacin da za'a tona asirin munafukai.
Ra'eez yace ai Alhaji Marusa da Mr. Kallah suna America. Alhaji Mansur yace akan ciwon Alhaji Marusan ne? Ra'eez yace wallahi kuwa, nima d'azu Alhaji Barau yake fad'a mani.
Alhaji Mansur yace ina rokon Allah ya bashi lafiya domin ya amshi hukuncinsa, bakomai nasan bazasu dad'e ba tunda kace jikin da sauki, kafin a kammala wannan shari'ar zasu dawo da izinin Allah.
Wayar Ra'eez ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Dr. Saddek ne, d'agawa yayi, bayan sun gaisa Dr,
yace masa yazo yana son ganinshi. Ra'eez yace gani nan zuwa.
Kashe wayar yayi yana fad'a masu abinda Dr, yace. Alhaji Mansur yace ai sai kutashi muje kila wani abunne. Kawu yace aduba mani Hajiyar.
**** ***
Zaune suke a ofis d'in Dr. Saddek, bayan sun gama gaisawa Dr, yace dama akan maganar shari'ar da naji za'a gabatar gobe ne, tunda har shari'ar zata kai zuwa gano abinda ya shafi abinda yayi silar jefa Hajiya wannan halin ina ganin zaku tafi da ita, ina so na gwada wani abu ko Allah zaisa a dace, shiyasa nace bara nakira ka.
Alhaji Mansur yace likita kana ganin babu matsala atafi da ita? Bana so fa Alhaji Barau ya gano wani abu, sannan kada aje garin gyara ayi b'arna, kana gani kwanaki daga fad'in sunanshi yanda tayi, inaga ace ta ganshi kuma ta san shine Brr. Barau d'in.
Likita yace Alhaji jikina yana bani wani abu shiyasa kaji nace aje da ita, kasanfa da yawa irin wannan haukan yana warkewa ne ta silar faruwar wani abu, musamman idan mutum yaga abinda ya tsaya masa arai, ina rokon ka amince aje da ita, idan Allah besa zata warke ba shikenan sai adawo da ita.
Hawaye ne suka zubo ma Ra'eez, kallon likitan yayi yana fad'in koda ace Ummu bazata warke ba ana kammala wannan shari'ar zan tafi da ita, tunda dai haukarta bata duka bace ni zan cigaba da zama da ita ahaka.
Dafashi Alhaji Mansur yayi yana fad'in insha Allahu Ummunka zata warke, bakomai likita zamuyi yanda kace, amma akwai maganin da zaka bata ko? Kai likita ya jinjina yana fad'in zan bata magani, kuma nima zan halarci wajen tare da wasu daga cikin ma'aikatan mu, kuma zamu kula babu abinda zai faru.
Godiya sukayi masa. Sallama sukayi mashi akan gobe zasu taho da ita, sai dai bazasu bari kowa ya gane daga asibiti suka fito ba. Alhaji Mansur yace shikenan mungode, akwai Maman Rumaisa da Hajiya sai su kula da ita goben.
**** ****
Zaune suke su biyar sai Alhaji Mansur na shida a gidan Ra'eez. Rafeek ne ya kalli Adnan yana fad'in ina fatan ka shirya ma shiga kotu gobe? Jinjina kai Adnan yayi yana fad'in sosai kuwa, domin a wannan karon bazan bari a sake aikata zalunci ba.
Rafeek yace Nabeel fa? Nabeel yace ashirye nake Yaya, domin nashirya duk yanda zan shawo kan Abbana, dalilin da yasa banyi masa maganar ba bana so yaje masu Alhaji Barau da maganar shiyasa nace sai yau da dare zanje na rokesa akan ya fad'i gaskiya.
Ra'eez yace lallai da ka kwafsa, ai gara da baka fad'a masa ba, kabarshi idan yaje zaiji komai da kunnansa, abinda nakeso kawai kayi kok'arin sashi yazo kotun domin nasan za'a buk'aci ganinsa.
Nabeel yace shikenan dana koma gida zansan yanda zan fad'a masa. Rafeek yace insha Allahu babu abinda zai gagara, domin kowa yasan yanda komai ya kasance, shikuwa Fawwaz ku barshi Alkali da kanshi zai bada umarnin a kawoshi.
Alhaji Mansur yace ni narasa ma bakin magana, agaskiya nayi farin ciki da wannan had'in kan naku, domin taimako ne zakuyi kuma Allah ne kad'ai zai iya biyanku, dan haka idan kowa ya samu dama kafin ya kwanta yayi nafila ta neman nasara, sai kuga Allah ya taimake mu, Allah yayi mana jagora. Gaba d'aya suka amsa da amin.
**** ****
Abbah ka kalli labaran jiya na Liberty radio kuwa? Abbah yace labaran da yawa ai, wanne a ciki? Gyara zama Nabeel yayi yana fad'in aikuwa agari naji ana ta maganar shari'ar da akace za'ayi gobe a babbar kotu kuma tsohuwar shari'a ce, naji mutane suna fad'in zasuje suyi kallo.
Abbah yace wai wace irin shari'ace haka bayan shekaru kuma za'a maidota? Nabeel yace gaskiya ban sani ba, amma koma menene nasan babbar shari'arce tunda gashi an maido ta.
Abbah yace aikuwa nima zanje kodan naji wace shari'ace haka, kasan ina son zuwa saurarar shari'a. Murmushi Nabeel yayi yana fad'in nima nace zanje ai. Abbah yace dama ku ai ba'a barin ku abaya. Murmushi Nabeel yayi yana fad'in ai bana son naga anyi zalunci Abbah. Abbah yace to Allah ya bama masu gaskiya sa'a. Nabeel yace amin.
***** *****
*Safiyar litinin a Kotu*
Cike babbar kotu take da mutane, yayin da su Mama da Maman Labiba, Rumaisa sai Ummun Ra'eez da matar da take kula da ita suke zaune a cikin kotun, saboda dawuri sukazo dan kada su rasa wajen zama, sannan basa son sai an shiga su shiga gudun kada Ummu tayi wani abun, duk da jikinta amace yake tun maganin data sha.
A hankali mutane suka shige ciki kowa ya zauna ana jiran zuwan Alkali. Shigowar Alkali yasa kowa ya mik'e, bayan ya zauna kowa ya zauna.
Shiru kotun tayi ana jiran a fara. Bayan ya kammala abinda yake Magatakarda ya tashi domin ya karanto shari'ar da za'a gabatar.
*A yau litinin biyar ga watan december shekera ta dubu biyu da shatara wannan kotu zata saurari k'arar da Iyalan Alhaji Sambo Jarmai suka shigar akan kissan gillan da akayima 'Dansu a shekarar dubu biyu da takwas, wanda aka tsinci gawarsa a ranar juma'a da misalin k'arfe tara da rabi na dare, suna rokon wannan kotu mai albarka data kwato masu hakkinsu.*
Mika takardar yayi ya koma ya zauna. Gyara zama Alkali yayi yana fad'in ina lauyoyin da zasu fabatar da shari'ar? Tashi Ra'eez yayi yana fad'in ya mai shari'a nine lauyen da zai k'are wad'anda suke k'ara.
Jinjina kai Alkali yayi yana fad'in zaka iya farawa.
Fitowa Ra'eez yayi yana fad'in Iyalan Alhaji Sambo Jarmai sun shigar da wannan k'ara ne saboda suna da yakinin a wannan kotun ne kad'ai za'a iya kwato masu hakkin su, duk da wannan case ya dad'e amma dalilin rashin kwakkwarar sheda yasa basu shigar da k'ara ba, haka zalika basu shigar da k'ara a ofishin 'yan sanda ba, sai dai kuma alokacin da abun ya faru akwai shedar sa hannu ta 'yansanda a wancan lokacin, wannan shine rahoton da muka samu a ofishin 'yan sandan da suka kula dashi a wancan lokacin.
Amsar takardar Magatakarda yayi ya mik'a ma Alkali. Ra'eez yace a shekarun baya an tsinci gawar Naseer Sambo Jarmai a wajen gari da misalin k'arfe tara da rabi na dare, kuma 'yan sanda ne suka d'auki gawarshi suka mik'ata asibiti, a lokacin inspector Musa shine wanda ya kula da wannan gawa harya d'auketa zuwa asibiti inda ya mik'a case d'in ga abokin aikinsa Inspector Bello Kabir wato Kwamishnan 'yan sanda na yanzu, inaso kotu ta bani dama na kira Alhaji Musa domin muji bayani daga bakinsa. Kotu tana buk'atar Alhaji Musa.
Ra'eez.... Kotu zata so taji sunanka da kuma aikin ka.
Sunana Alhaji Musa Adam, nayi aikin d'ansanda a shekarun baya, amma ayanzu na aje aiki tun shekaru biyar da suka wuce, ayanzu haka ina kasuwanci ne.
Ra'eez... Alhaji Musa ko zaka iya tuna abinda ya faru a shekarar dubu biyu da takwas akan gawar da kuka tsinta ta Naseer Sambo Jarmai? Muna so kayima kotu cikekken bayani.
Alhaji Musa.... Kwarai kuwa zan iya tuna wannan case d'in, domin bashi kad'ai muka samu a wannan dare ba, kuma wannan lokacin yana d'aya daga cikin abinda bazan iya mantawa ba, domin a wannan shekarar a wannan kotun anyi zazzafar shari'a, wanda d'aya daga cikin gawar da muka tsinta had'e data Naseer ce akayi shari'a akanta, sai dai ita ta Naseer Iyayenshi basu buk'aci yin shari'a ba, saboda babu wata sheda da muka samu a lokacin da muka tsinceshi.
A wannan dare na juma'a mun samu waya cewar an samu gawar tsohon shugaban kwastam wato Alhaji Maiwada, bayan da 'Yallab'ai Bello ya tura mu wajen, da muka d'auko gawarsa mun taho muka sake samun labarin gawar da wasu suka gani, haka muka wuce muka d'auko gawar Naseer, kai tsaye asibiti muka nufa dasu, daga can kuma case d'in ya koma hannun Ogana wato 'Yallab'ai Bello Kabir, iya abinda na sani kenan akan gawar Naseer, sai rahoton dana baka wanda nine na rubutashi da hannuna.
Ra'eez... Mungode Alhaji Musa zaka iya tafiya. Ya mai shari'a wannan shine d'an sandan daya d'auki gawar Naseer, ga rahoton mutuwarsa nan, sai dai a binciken da mukayi mungano Naseer yana aji shidda ne a makarantar Kings college a wancan lokacin, kafin mutuwarsa akwai abinda ya faru a makarantar su wanda akan idonshi abun ya faru, yayi kok'arin ya tabbatar da gaskiya sai dai silar wannan abun ya jawo mashi mutuwar wulakanci.
A binciken da mukayi akwai abokinshi *Fawwaz Muhammad Sanda* wanda shima d'alibi ne a makarantarsu, bincike ya nuna mana akwai rigima da akayi tsakanin Fawwaz da d'an ajinsu mai suna Farouk, wanda Adnan da Sufwan duk sun san da wannan rigima domin su ukku suke tare abokai ne sosai, kuma bincike ya nuna cewar bayan rigimar Farouk da Fawwaz a ranar aka tsinci gawar Farouk a wajen gari, komenene ya faru alokacin Fawwaz ne zai fad'a mana saboda yasan Naseer, ina neman alfarmar wannan kotu data bada umarnin a kawo Fawwaz Muhammad Sanda domin muji komai daga bakinsa. Nagode.
Tashin hankali wanda ba'a samasa rana. Gaba d'aya zufa ce ta lullube Alkali da Abban Nabeel, da wani zaije kusa da Alhaji Barau zaiji yanda zuciyarsa take bugawa, jarumta ya tattaro ya kalli Ra'eez, cikin k'arfin hali yace an d'age wannan shari'ar zuwa gobe, kafin nan kotu tana umartar akawo mata Fawwaz Muhammad Sanda zuwa gobe. Kotttt!!!
Gaba d'aya kotun ta d'auki hayaniya, Abban Nabeel kuwa kasa tashi yayi daga inda yake, gaba d'aya hankalinsa ya tashi, abinda ya guda shekarun baya gashi zai faru, Allah ya sani tun bayan daya aikata wannan laifin yayi nadama, bayan da Nabeel yazo masa da maganar kuma be sake samun kwanciyar hankali ba, haka kawai yake jin kamar wani abu zai faru ashe kuwa lokacin jin kunyarsu ne yazo.
Cira ido kawai Ummu takeyi saboda gaba d'aya hayaniyar tayi mata yawa, jin kanta tayi yana sara mata. Wasu mutane da suke bayansu taji suna fad'in.... Ai wannan shari'ar da akayi ta shugaban kwastam Alhaji Maiwada a wancan lokacin Brr. Barau ne yayita, gashi kuma yanzu shine Alkali, amma kuma Fawwaz da ake magana ai d'an gidan tsohon Alkali ne, lallai wannan shari'ar akwai lauje cikin nad'i, ga mutuwar Farouk ana magana kuma duk 'yan makaranta d'aya ne, tabbas za'ayi tone-tone a yanda na fuskanci wannan shari'ar babban al'mari ne.
Zumbur sukaga Ummu ta mik'e, saurin tashi Mama tayi tana kok'arin kamota amma ina tuni Ummu ta zube k'asa yayin da kanta ya bugu da kujera.
Da sauri ma'aikatan da sukazo tare sukayo kanta, hankali tashe Ra'eez ya nufo wajenta, sai dai kafin ya iso Alhaji Mansur yayi saurin rik'eshi yana girgiza mashi kai, dole ya tsaya. Jabeer ne ya jashi sukayi waje.
Haka hankalin mutane yayo kanta, sai dai kafin a taru tuni anyi waje da ita ansata mota sun wuce. Da sauri su Alhaji Mansur sukabi bayansu shida Rafeek.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
4⃣1⃣
A gado aka turota zuwa d'akinta bayan an gama mata dressing goshinta daya fashe sanadiyar buguwar da tayi da kujera.
Hannunta Ra'eez ya rik'e yana kuka. Dafashi Jabeer yayi yana bashi hak'uri. Ra'eez yace dole nayi kuka Jabeer, sai da Abbah yace kada aje da ita gashinan abinda ya faru, yanzu idan ciwonta ya tsananta mai zaice mana.
Alhaji Mansur yace Ra'eez kadena fad'ar haka, ni na hango alkhairin da yasa Likita yace aje da ita, kuma insha Allahu hakan ne silar samun saukinta, dan haka mujira farkawarta zamuji alkhairi, yanzu shari'ar da take gabanka zaka fuskanta kuka ba naka bane.
Jinjina kai Ra'eez yayi yana goge ido yace shikenan Abbah Allah ya bata lafiya. Abbah yace amin, dan haka kutashi mutafi dan tana buk'atar hutu. Tashi sukayi suka wuce.
*** ****
Zagaye kawai Alhaji Barau yake a ofis yayin da zufa take zubo masa, duk da ya kure masanyar ofis d'in amma duk da haka zufa yake, shigowarshi ya sha ruwa yafi roba biyu.
Jin k'arar wayarsa yasashi saurin nufar inda take dama jiran kiran yake dan ya kira ba'a d'aga ba. Sunan Alhaji M. Sanda ya gani hakan yasa ya zauna yana amsa wayar.
Lafiya Babban Alkali nazo na iske kira kusan so goma shine nace babu lafiya. Ajiyar zuciya Alhaji Barau ya saki yana fad'in Alhaji babu lafiya, wani tashin hankali ne yake tunkaromu, wallahi da nasan abinda shari'ar da zan gabatar kenan yau da duk juyin da za'ayi bazan amsheta ba, kuma bazan bari hazikin lauya kamar Ra'eez ya tsaya masu ba.
Alhaji M. Sanda yace dakata Alkali, ka fito fili kayi mani bayani yanda zan fahimceka, nasan kace mun kana da shari'a yau wadda naga ana tallar ta a gidan radio amma bansan meta kunsa ba, dan haka kayi mani bayani yanda zan fahimta.
Gyara zama yayi yana fad'in Alhaji ina Fawwaz yake? Alhaji M. Sanda yace yana nan lafiya dai? Alhaji Barau yace zaka iya tuna abokansa Naseer Sambo Jarmai da Farouk d'an ajinsu na makarantar kings college?
Alhaji M. Sanda yace taya zan iya tuna abokan Fawwaz kuma na secondary ma. Alhaji Barau yace zaka iya tunawa mana, a shekararsu ta k'arshe, fad'an Fawwaz da Farouk wanda yayi sanadin yankarsa da Fawwaz yayi da wuk'a ajali na kusa ya mutu, Naseer shine wanda ya d'auki lokacin da akayi kisan, silar haka muka had'u mu hud'u muka yanke hukunci akanshi, yayin da aka tsinci gawarsa a bayan gari, wanda aka kashe shi tare da Alhaji Maiwada. Wannan shari'ar da ba'ayita ba a shekarar dubu biyu da takwas, itace aka gabatar da ita a kotun mu yau.
A zabure Alhaji M. Sanda ya mik'e yayin da zufa tayi masa sallama, ya d'auki mintuna kafin ya furta Alhaji Barau garinya aka tado da wannan shari'ar? To waye ma ya tadota bayan lokacin da akayita shi kanshi lauyen da ya tsaya masu yana k'arami dan nasan dai beda wasu shekaru masu yawa.