Advertisements
Chapter 38 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   38 / 54

111K to 114K   out of 160.3K words

shin-shino karayar arziki kaga dole ya dawo k'asan mu.



Mr. Kallah yace shikenan yanda kace babban Alkali. Dariya sukasa Alhaji Barau yace zaka iya tafiya Lucky sai munji daga gareka. Lucky yace nagode Alhaji.



Yana fita Mr. Kallah yace yanzu kai ka yarda dashi? Alhaji Barau yace shiyasa ai na zab'eshi saboda nasan yana da haushin Alhaji Marusa akan kisan abokinsa, kaga kuwa bazai tab'a komawa bayanshi ba.



Mr. Kallah yace zaiji idan cin amana tana da dad'i, kuma zamu nuna mashi munshiga tashin hankali. Alhaji Barau yace da masu ilimi fa yake tare wad'an da suka goga da mutane, duka nawa iliminshi yake, meya sani a harkar duniya, kabarshi zamu nuna mashi muma munyi asara. Mr. Kallah yace Alhaji Barau a kiyaye ka. Dariya sukasa.


**** ***


Wai Adnan kayi shiru bayan kuma akwai magana abakin ka. Murmushi Adnan yayi yana fad'in bakomai kawai wani abu na gani d'azu daya tada mani wani tsohon ciwo da yake zuciyata shekaru masu yawa da suka wuce.



Nabeel yace lallai agaisheka, taya zan iya aje abu araina har na wasu shekaru masu yawa, kaganni nan ko b'ata mani rai akayi baya wuce kwana biyu yawuce, amma kuma bansan wane irin ciwo bane aranka, kasan wani ciwon sai mutum ya mutu dashi be manta ba.



Adnan yace d'azu muka had'u da Yayan wani abokin mu da aka kashe lokacin muna aji shidda a secondary, rabona dashi tunda mukaje masu gaisuwa, saboda yasan nine babban abokinsa yasa da muka had'u d'azu muka zauna muna ta fira hada firar abokina mukayi bakaji yanda jikina ya mutu ba, gaba d'aya sai mutuwar ta dawo mani sabuwa musamman da naga yana kuka, kuma yake fad'a mani har yanzu Mahaifiyarsu bata warke ba akan ciwon daya sameta alokacin da aka kawo mata gawar d'anta, wannan abun shine ya tada mani hankali sosai.



Nabeel yace Allah sarki, amma basu shigar da k'ara ba ne? Adnan yace basu shigar ba. Nabeel yace da sun sani sun shigar da k'ara, kasan wani lokacin idan aka kashe maka naka matuk'ar an yanke ma wanda yayi kisan hukunci kana jin sauki a zuciyarka domin ka rage wani abun.



Adnan yace taya zasu shigar da k'ara bayan an juyar da abun, kasan fa ita shari'a sai da shedu take amfani, domin kisan a makarantar mu akayi ta amma sai aka gano gawar abokina a wajen gari, alokacin ma Abban ka ne shugaban makarantar.


Nabeel yace a kings college ko? Adnan yace nan fa. Nabeel yace tabbas acan Abbah yayi aiki ashe kayi karatu ak'asanshi? Adnan yace sosai kuwa, ai Abbanka beda wasa, nayi mamaki alokacin da aka kashe Farouk da aka fita da gawarsa kuma be tsananta bincike ba. Nabeel yace dan Allah bani labarin abinda ya faru.


Adnan yace abinda na sani ance a makaranta aka kashe shi, domin akwai wanda yaga lokacin da akayi kisan kuma har d'auka yayi, sai dai kuma daga baya aka samu gawarsa a wajen gari sannan yaron daya d'auki shedar shima aka kashe shi, kuma shedar ta b'ace, mamakin da nayi duk zafin Abbanka da iya aikinsa amma beyi komai ba, daga baya kuma nayi tunanin kila besan a makaranta aka kashe shi ba.


Girgiza kai Nabeel yayi yana fad'in duk da haka Adnan ya kamata ace anyi bincike koda da gaske ba'a makarantar aka kashe shi ba amatsayin Abbah na shugaban makaranta ya kamata ace yayi ruwa da tsaki wajen nemawa Farouk hakkinsa.


Murmushi Adnan yayi yana fad'in Nabeel kenan, kaida kayi wannan tunanin zaka fad'i haka, ka rabu da duniya idan akace akwai azzaluman shuwagabanni, talaka beda ikon aiwatar da komai matuk'ar ta had'oshi da mai kud'i, ko d'azu Yayan Farouk ya fad'a mani da zai samu sheda koya take saiya maido da shari'ar Farouk kotu, sai anyi bincike koda wanda ya kashe shi baya duniya.


Jinjina kai Nabeel yayi yana fad'in amma Abbah bazai iya taimakawa ba? Adnan yace a wajen me kenan? Gyara zama Nabeel yayi yana fad'in dole yasan duk wasu masu gadi da sukayi aiki dashi a waccan shekarar, ina zargin kamar an had'a baki da masu gadi wajen fitar da gawar Farouk, kaga idan aka tabbatar da haka dole za'a gano wanda yasa suka aikata haka, daga nan kuma zai kai agano wanda yayi kisan, danni ina tunanin kamar a cikin yaran makarantar ne aka samu wani ya kashe shi, kaga makarantar yaran masu kud'i ce dole asan yanda za'a rufe maganar.



Adnan yace abu ne me wuya Abbanka ya saurari wannan maganar, domin shekarun da yawa, idan aka tado mashi da maganar zaiga kamar anaso asashi wani babban aiki ne, tunda ya jima da aje aiki kaga abu ne mai wuya ya koma binciken abinda ya faru abaya.



Nabeel yace wallahi duk naji jikina yayi sanyi, kasanni Adnan bana son zalunci, haka Allah yayi ni, matukar naga anyi zalunci bana kyalewa, shiyasa a secondary d'in mu nine Ameer dan gaskiya bana goyon bayan zalunci, shiyasa fa ban zab'i makarantar ku ba dan bana son irin makarantun yaran masu kud'i, dan haka ka barni da Abbah zanyi magana dashi cikin sanyi, kuma zamuyi nasara.



Adnan yace Nabeel sai kayi ahankali kaga Mahaifinka ne. Nabeel yace koda shine ya aikata laifin bazanji kunyar tonashi ba, domin Allah ya hana zalunci.


Ajiyar zuciya Adnan yayi cike da farin ciki, yana masa godiya. Shiru Nabeel yayi can ya kalli Adnan yana fad'in akwai abinda ka b'oye mani Adnan.


Saurin kallonshi Adnan yayi yana fad'in kamar mefa? Murmushi Nabeel yayi yana fad'in wasa nake, kome kenan zamuyi magana. Adnan yace nagode sosai abokina. Nabeel yace bakomai.



Sallama yayi mashi ya rakoshi. Sai da ya tafi kafin ya nufi d'akin Mahaifinshi cike da fatan dacewa dan yasan yanzu yana kallon news.


****


Sai da Adnan ya tsaya wata super market yayi siyayya kafin ya fito zai wuce gida. Adnan Abdurrazak Matawalle! Saurin juyowa yayi jin ankirashi da cikekken sunanshi.


Gabanshi ne ya faad'i ganin wanda yake gabanshi. Matsowa Fawwaz yayi yana ware hannu ya rungume Adnan yana dariya. Jiki a sanyaye Adnan ya rungumeshi zuciyarsa tana tsinkewa.


Kallonshi Fawwaz yayi yana dariya yace shegen kaya, kaganka kuwa? Lallai na yarda ka zama Baba. Murmushi Adnan yayi yana fad'in Fawwaz dama da gaske ka dawo, Yaya Sameer yake fad'a mani shine ko kaneme ni.


Fawwaz yace taya zanki nemanka kawai abubuwa ne sukayi mani yawa, yanzu haka sauri nake zamuje wani party na abokin mu.


Adnan yace lallai dole bazaka nemeni ba saboda kazama d'an gayu ga sababbin abokai kayi. Fawwaz yace No ba haka bane, kasan yanzu kai ka girma, kana da Iyali bekamata narik'a sako ka cikin mu ba, gashi gaba d'aya ma naga kacanza daga yanda nasanka, duk da tun kafin mu rabu naga sabon canji daga gare ka.


Murmushi Adnan yayi yana fad'in dole nake canzawa, domin mun aikata babban laifin da har mu mutu yana bin mu, naga kamar kai kamanta, duk da ba nine na aikata laifin ba kullum cikin nadama nake da istigfari, amma kai gashinan kana morewar ka yanzu ma party zakaje.



Canza fuska Fawwaz yayi yana fad'in bangane ka aikata laifi ba? Adnan yace ka aikata dai, mu kam ai taimaka maka kawai mukayi nida marigayi.



Ja da baya Fawwaz yayi yana k'ank'ance idanu yana kallon Adnan. Murmushi Adnan yayi yana fad'in kada ka damu kawai na tuna maka ne saboda inaso ka fara neman yafiyar Allah, amma tabbas har yanzu ina kallon lokacin da ka yanki Farouk da wuk'a.



Sosai Fawwaz ya canza fuska tamkar wanda be tab'a dariya ba, jijiyoyin kanshi suka tashi idanuwanshi sukayi ja, hannu yasa aljihu ya ciro kwalin sigari, abaki yasa kafin ya bata wuta, sai da yayi mata kyakkyawar zuk'a ya fesar kafin ya kalli Adnan yana fad'in ban d'auka zaka iya tuna wannan abun ba, kamar yanda kasa ma bakin ka kwad'o a wancan karon to inaso kacigaba da zama ahaka, bazan d'auki wannan maganar ba, idan kuma ka san zaka rik'a mani ita to ka d'auka bamu tab'a sanin juna ba.


Jinjina kai Adnan yayi yana murmushi yace haba abokina, kada ka manta da amintakar mu, ada ma banyi magana ba bare yanzu, kawai shawara na baka tunda baka so baza'a sake ba.



Murmushi Fawwaz yayi yana fad'in nasanka ai bazaka iya tona asiri na ba, nagode ka gaishe da Yaranka. Adnan yace zasuji tunda babu kara. Fawwaz yace zan wuce.



Mota Adnan ya shige ranshi fess, koba komai ya tado mashi da abinda yawuce, idan yana da hankali maganar bazata bar zuciyarshi ba.



Fawaaz har ya shiga mota ya d'auki hanyar wajen Partyn yayi saurin canza hanya, tsaki yayi yana zuk'ar sigari ranshi ab'ace, gaba d'aya Adnan ya b'ata masa shirinshi, ya tuno masa abinda ya dad'e da mantawa.



Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga abokinsa ne, d'auka yayi yana fad'in Guy bazan samu zuwa ba gida zanje kaina yana ciwo. Shiru yayi kafin ya kashe wayar, gudun motar ya k'ara zuwa gida.


Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*



3⃣7️⃣



Fawwaz lafiyar ka kuwa? Kauda kai yayi yana fad'in Ammi normal. Zama tayi tana fad'in kace mun zakaje wajen Party amma kuma kadawo kana b'ata fuska ko partyn beyi maka ba? Ammi kawai b'ata mun rai akayi shiyasa.


Murmushi tayi tana fad'in Fawwaz nasha fad'a maka ka girma, yakamata karage wannan shirmen da kakeyi, zuwa yanzu yaci ace ka aje Iya.... Ammi dan Allah kada ki k'arasa, duka me nayi a duniyar da zan cutar da kaina ta hanyar aure har da tara wasu Iyali can, kina ganin Dady sai da ya more rayuwarsa kafin yayi aure, bayan aurensa ma sai da kuka dad'e kafin ya yarda kika haihu gashinan yanzu kowa yaganki bazaiyi tunanin kin haifeni ba, da ace kin haihu da yawa ko kinyi aure da wuri da yanzu kila hak'oranki sun fara fita.


Duka ta kaimashi yayi saurin kaucewa yana dariya. Dadynshi da yake jinsu ya shigo yana fad'in kada ki dokar mani yaro kinsan tunda ya taso besan me ake kira zafin duka ba.


Ammi tace ai duk kaine ka sangartashi, ba damar yaro yayi laifi a tab'ashi sai ka fara fad'a, idan bam manta ba har rabuwa mun tab'ayi akan zan dokeshi.


Dady yace sa'a kikaci baki kai ga dukansa ba shiyasa hukuncin ya tsaya a haka kikaje gida kikayo kwana biyu, da ace kin dokesa kila sai nayi babban hukunci.



Tab'e baki tayi tana fad'in dad'ina da gobe saurin zuwa, shima gashinan ya girma damma ka hanashi aure ai da yanzu shima ya fara jin yanda naji akan Yara.


Zama Dady yayi yana fad'in My Son wai kana son aure yanzu? Saurin girgiza kai yayi yana fad'in bana so Dady, gara abari na k'ara girma.


Ammi tace lallai kam zamu mutu bamuga auren ka ba. Dady yace aikuwa da ran mu zaiyi aure, kana ji na, kada ka damu da ita ka kwantar da hankalin ka babu me takura maka akan aure, duk lokacin daka shirya sai kayi abunka.


Gyara zama Fawwaz yayi yana fad'in Yawwa Dady d'azu daka aike ni gidan Abbah Barau na ga wata yarinya d'iyarsa ce? Dady yace Raheena kenan, itama waje tayi karatu lafiya? Ya mutsa fuska yayi yana fad'in ko gaishe ni batayi ba tana zaune a wajen lambu duk da taji shigowar mota kuma taji masu aiki suna gaishe ni.


Ammi tace dan me zata gaishe ka bayan ba kusa kuke ba, ina ma ruwanka da ita dan batayi maka magana ba? Kika sani ko Yaron nawa ya k'yasa. Dady ya fad'a.


Murmushi Ammi tayi tana fad'in to wannan dai anyi mata miji dan Hajiya Binta ta fad'a mani sunje Dubai siyo kayan aurenta kila ma bikin bazai wuce wata d'aya ba.


Kallonta Fawwaz yayi yana fad'in d'an bani lambarta mugaisa to. Harara Ammi ta banka masa tana fad'in bana son sakarci, meye zaka amshi wayarta bayan kaji aure zatayi.


Dady yace bana son haka fa, da Raheena da Fawwaz duk d'aya ne a wajena, domin Alhaji Barau na hannun dama ta ne, kuma Fawwaz kamar Yaya yake agareta, ko kinji yace maki yana sonta? Girgiza kai Ammi tayi tana fad'in kasan halin zuciya.


Dady yace to ki bashi suyi zumunci, yace maki ba aure zeyi yanzu ba damme zakisa zargi akanshi. Murmushi Ammi tayi tace ayi hak'uri baza'a sake ba.



Kamo hannun Fawwaz Dady yayi yana fad'in akwai abinda yake damunka dan nasan baka saba dawowa kamar haka ba. Yamutsa fuska Fawwaz yayi yana fad'in Dad babu komai kawai gajiya nayi zan kwanta.


Tashi Dadyn yayi yana fad'in shikenan ka kwanta, Ammi muje kada mu hanasa bacci. Tashi tayi tana fad'in Allah ya tashemu lafiya. Fawwaz yace amin.



Kwanciya yayi sai dai daya juya maganganun Adnan ne suke dawo masa, tsaki yayi yana fad'in wallahi Adnan ka b'atamun rai, banda jahilci taya zaka tado abinda yawuce shekaru kusan sha biyu, gashi nan nima abun ya dawo mani.


Tashi yayi ya d'auko wata kwalba a cikin durowarsa, bud'ewa yayi ya shanye abinda yake ciki duka, wurgar da ita yayi ya haye gado yana jin jikinsa yana saki, a hankali idanuwansa suka fara rufewa tamkar wanda ake yawo dashi asama, da haka bacci yayi gaba dashi.


****


Washe gari har wajen k'arfe goma be fito ba, Dady ne ya kalli Ammi yana fad'in wai yau lafiyar Fawwaz kuwa, nasan baya tashi da wuri amma kuma yana fita motsa jiki idan ya gama ya sake kwanciya yau banji motsinshi ba? Ammi tace nima abinda nake tunani kenan. Dady yace muje mu dubashi.



Da mamaki Dady yake kallon kwalbar da take hannunshi, kallon Ammi yayi yana fad'in dama Fawwaz yana shan syrup ne? Ammi tace wallahi nima sai yau na gani.



Girgiza kai Dady yayi yana fad'in wannan syrup d'in mai k'arfin ne, shiyasa be tashi ba har yanzu, da alama kuma be had'ashi da komai ba haka kawai ya sha dan banga robar lemu ba.



Hannu Ammi tasa ta fara tadashi, girgizashi tayi kafin ya farka a firgice yana kiran sunan Farouk. Da mamaki suka bishi da kallo. Zama Dady yayi yana fad'in Fawwaz waye kuma Farouk? Hannu yasa ya dafe kanshi yana goge zufar datake goshinsa.


Sake tambayarsa yayi kafin ya kallesu yana fad'in bakowa. Ammi tace banyarda ba, taya zaka farka da sunan mutum abakin ka da alamu mafarkinsa kayi, kuma da tunaninshi ka kwanta.



'Bata fuska yayi yana kokarin sauka yace Ammi nace bakowa wani abokina ne. Dady yace shikenan tashi kaje kayi wanka kayi sallah kazo ina da magana da kai.


**** ****


Wai Nabeel lafiya kake kuwa? Jiya da dare ina kallo kazo ka zauna kayi shiru kamar da magana abakin ka, na tambayeka kace bakomai ka tafi, yauma gashi kazo mun gaisa kuma kazauna kamar zaka fad'i wata magana amma kayi shiru.


Gyara zama Nabeel yayi yana fad'in Abbah dama wata tambaya zanyi maka to jiya naga hankalin ka yana wajen kallon news shiyasa na tafi.


Kofin shayin Abbah ya aje yana fad'in ina jinka. Duk'ar da kai Nabeel yayi yana fad'in d'azu ne da ana gyara wancan tsohon d'akin na kaya shine naga wata tsohuwar jarida, har na barta sai kuma naga sunan makarantar da kayi aiki a jiki ga hoton wani yaro a kwance da kayan makarantar jikinsa duk jini, hakan ne yaja hankalina na karanta shafin, kuma hada hotonka na gani a kasan shafin a matsayin ka na shugaban makarantar, to shine labarin yaja hankalina nakeso naji yanda abun ya faru.


Saurin zare glass d'in idonshi yayi yana kallon Nabeel, ido Nabeel ya d'ago yana karantar mahaifinsa. Kayi hak'uri Abbah idan maganar ta b'ata maka rai.


Ajiyar zuciya Abbah yayi yana fad'in waye ya baka wannan labarin? Nabeel yace a jarida na gani. Jinjina kai Abbah yayi yana fad'in dama ba'a kone duk wasu jaridun d'akin ba? To yaushe ma aka fiddo da kayan d'akin tunda nasan babu abinda za'ayi a d'akin, ko dai kaine kaje kayi mani bincike? Saurin girgiza kai Nabeel yayi yana fad'in da gaske gyaran d'akin nasa ayi, gashi can ma suna k'arasawa.



Ina jaridar take? Abbah ya fad'a jiki a sanyaye. Hannu Nabeel yasa a aljihu ya cirota ya mik'a masa. Shiru Abbah yayi yana kallon hoton Farouk da yake kwance cikin jini ga wuyansa da shatin wuka.


Wasu hawaye ne suka taho masa, da sauri ya maida glass d'inshi ya aje jaridar. Kallon Nabeel yayi cikin dakiya yana fad'in wannan ai tsohon abu ne, kanaga tun 2008 fa, ni harna manta da abun ma, muma haka muka samu labari dan abun ya faru ne bayan an tashi daga makaranta.


Nabeel yace to Abbah bakuyi bincike ba? Girgiza kai yayi yana fad'in duk abinda ya faru bayan makaranta to bamu da hakki akansa, sannan kuma abun ba'a makaranta ya faru ba, kaga bamu da ikon yin wani abu, kayan makarantar da suke jikinsa ne yasa kaga ansa hotona saboda 'Dalibina ne, da ace Iyayenshi sun nuna zasu shigar da k'ara da amatsayin mu na shuwagabannin makarantar Yaron mun taimaka wajen

38 / 54