Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
mijina mai tawakkali ne, kuma nasan zaka amshi duk abinda yazo maka da hannu biyu, dan haka kada ka damu da kiran da suke maka, idan su basa tare da kai ni da Ra'eez muna tare da kai har abada.
Murmushi ya saki wanda har hak'oransa sai da suka fito, sake matseta yayi yana fad'in nagode Uwar gidana, ina mai tabbatar maki matuk'ar suka barni akan aikina sai na zaluko gaskiya, ko bayan raina sai duniya tasan cewar bani da laifi, sai Allah ya haska su kowa ya gansu.
Ummu tace amma kayi komai a hankali kada su sake maka wani sharrin. Alhaji yace kada ki damu, wannan abun da ya faru alkhairi ne a wajena, domin ya k'ara haska mani duhun da nake ciki, ayanzu zasu gane basu da wayau, domin zanyi aiki ta k'ark'ashin k'asa. Murmushi tayi tana fad'in nasan zakayi fiye da haka.
**** ****
Cike babban d'akin taron yake da manyan mutane masu babban matsayi, bayan da aka gama tattaunawa kowa ya fad'i ra'ayinsa akan Alhaji Maiwada, wasu suna ganin ayi masa canjin wajen aiki tare da rage masa matsayi, wasu suna ganin takardar sallama ce ta dace dashi domin yaci amanar aikinsa, idan aka barshi hakan zai bama wasu dama su aikata irin abinda yayi ko fiye da haka, wasu suna ganin a bashi takardar jan kunne.
Bayan da kowa ya gama kawo tasa shawarar Mr. Kallah ya mik'e yana fad'in naji duk abinda kuka fad'a, kuma a dokar tsarin aiki idan aka kama mutum da laifi abu na farko da akeyi ana duba file d'insa, idan har ba'a tab'a samunsa da wani laifi ba to ana masa uzuri, acikin mu nan babu wanda bai san irin tsarin aiki na Alhaji Maiwada ba, tun yana k'aramin ma'aikaci ake yabon iya aikinsa, yarik'e matsayi kala-kala ba'a tab'a samunsa da karb'ar cin hanci ko so d'aya ba, har kawo warsa wannan matsayin ba'a tab'a kamasa da wani laifi daya sab'a ma doka ba, kuma wannan abu daya faru ina ganin kamar akwai lauje cikin nad'i, koma menene Allah ne yasan gaskiya, be kamata ace mun rufe ido munyi masa haka ba, idan mutum yayi ba dai-dai ba sai ajuya a kalli aikin kwarai nashi sai ayi masa hukunci dashi, dan haka ni dai a tawa shawarar ina ganin aja masa kunne a bashi dama ta biyu, kuma ya tsaya a aikinsa, kada yarik'a shiga aikin wasu, idan ya kiyaye shikenan, idan kuma aka sake kamashi sai ayi masa hukuncin daya dace.
Bayanin Mr. Kallah yayi ma mutane da dama dad'i, kuma sun gamsu da bayaninsa, nan take aka amince da shawararsa. Bayan sun gama rubutu aka rufe taro.
Alokacin Alhaji Maiwada yana zaune a inda aka tanadar ma baki dan ba dashi akayi taron ba, bayan sun fito Mr. Kallah yayi kiransa suka shiga ofis, su ukku ne a ofis d'in. Bayan ya gama karanto masa abinda suka yanke anan kowa yayi masa tashi nasihar.
Bayan sun fita ya rage su biyu Mr. Kallah ya dubeshi yana fad'in kayi hak'uri haka aikin kwastam ya gada, kafin nazo wannan matsayin nasha wahala sosai, matuk'ar kace zakayi gaskiya dole karik'a had'uwa da sharrin mutane, shawarar da zan baka ka tsaya akan aikin ka, kuma duk abinda zakayi karika tanadar kwakkwarar sheda, sannan ka rage shiga harkar Alhaji Marusa dan zai iya b'atar da kai. Alhaji Maiwada yace bakomai zan kiyaye, nagose sosai. Mr. Kallah yace bakomai.
Kud'i ya d'auko dubu d'ari biyar ya mik'a masa yana fad'in ga tawa gudummuwar. Alhaji yace kabarshi Mr. Kallah nagode. Murmushi Mr. Kallah yayi yana fad'in sunyi kad'an ko? Girgiza kai Alhaji yayi. Mr. Kallah yace to ka amsa. Amsa yayi yana masa godiya, haka sukayi sallama ya fito yana jinjina kirki irin na Mr. Kallah.
Mr. Kallah kuwa yana fita yayi murmushi, ya rasa ya akayi duk cikin ma'aikatansa yake jin nauyin Alhaji Maiwada, sosai yake masa kwarjini, duk da abinda yayi masa yayi ne dan ya k'arama kansa yarda awajen mutane amma ya rasa dalilin da yasa baya so Alhaji Marusa ya cutar dashi. Wayarsa ce tayi k'ara hakan yasa ya dawo daga tunanin da ya keyi.
**** ***
Haka Alhaji Maiwada ya koma bakin aikinsa, sosai ya canza daga yanda suka sanshi, babu ruwansa da kowa, abinda ya kamata shi yakeyi, kowa ya raba masa wajen aikinsa, kuma idan kayi aiki dole ka kawo rahoto ya duba, duk abinda ya faru sai anzo an sanar dashi, haka duk wad'an da zasu duba kaya dole su duba su da kyau, kuma dokar amsar cin hanci tana nan, sai dai ba ruwansa da kayan Alhaji Marusa, idan sunzo ma ba shine yake dubasu ba, amma duk da haka ana bincikasu yanda ya kamata, idan akwai abinda aka samu ana cirewa, shima Alhaji Marusan ya rage shigo da miyagun kwayoyi ta bodar Lagos, yace sai abun ya lafa.
Adebayo da Umar kowa yaga sun canza, domin hada sabbin motoci suka sake, sosai suke fantamawa, saboda suna cikin kud'i yasa basu damuwa da dokar ansar cin hanci ba.
A b'oye Alhaji yasa Abubakar da Moses suna bincika masa abinda yake faruwa, dan wannan abun daya faru yasa Moses yaji tausayin Alhaji, domin yasan wani abun daga cikin abinda su Adebayo sukayi, kawai yayi shiru ne saboda beda sheda, kuma yasan halin Alhaji Marusa matuk'ar ya ganoshi zai iya kashe shi, hakan yasa yaja bakinsa yayi shiru, amma yayi alk'awarin sai ya taya Alhaji sun gano gaskiya koma me zai faru, hakan yasa ya had'e da Abubakar.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣3⃣
*Bayan dogon lokaci*
Wajen wani abokinsa mai suna *Tayo* Moses yaje domin ya taimaka masa, dan wannan hanyar ita kad'ai zasubi domin su gano gaskiyar komai, dan Moses yayi alk'awarin sai ya taimaki Alhaji saboda yasan abubuwa da yawa a wajen su Adebayo kawai beda sheda a hannu ne.
Tayo gurun kamfuta ne, kuma abinda ya karanta kenan. Babu b'ata lokaci ya bama Moses abinda zaiyi amfani dashi, wasu na'urori ya bashi sai yayi masa saitin da wayarsa hada kamfutarsa ta hannu duk ya had'a masa ya nuna masa yanda zaiyi amfani dasu. Godiya Moses yayi masa ya tafi.
A ofis d'in Adebayo ya fara zuwa yasa d'aya daga cikin na'urorin da aka bashi, sai yayi kok'ari yasa a cikin motarsa, daga nan yaje wajen da ake duba kaya nan ma yasa guda d'aya, saura d'aya ta rage kuma yana so ya sata a gidan Alhaji Marusa musamman inda yaga yana ganawa da mutane, duk da yana zuwa gidanshi ada yanzu ya rasa ta yanda zaije yasa wannan na'urar, kuma duk tafi sauran muhimmanci saboda yasan a wajen Alhaji Marusa za'afi sanin komai.
Shiru yayi yana tunanin abunyi sai ga Abubakar yazo, nan yayi masa bayanin abinda yake kok'arinyi. Abubakar yace gaskiya Moses ka kyauta, tun jiya nake tunanin hanyar da zamubi mu taimaki Alhaji, ashe har ka rigani.
Moses yace abinda nakeso shine yanda zan had'a wannan abun agidan Alhaji Marusa. Shiru Abubakar yayi kafin yace akwai maigadin gidansa nasanshi, mai zai hana mu je masa da maganar kila ya amince.
Moses yace kasan halin mutane da son kud'i, kada muje muna tunanin yasa yaki sakawa yaje ya fad'ama Alaji kasan dai bazai barmu ba.
Abubakar yace kai dai muje, inaji yau ba shine keda aikin kwana ba, idan mun tashi daga nan mu biya ta wajen da yake zama insha Allahu zai amince. Moses yace shikenan.
***
Bayan da suka tashi suka nufi wajen da Maigadin Alhaji Marusa yake zama. Yana ganin Abubakar ya saki murmushi yana fad'in kaga kwastam masu gidan kud'i, murmushi Abubakar yayi yana fad'in *Malan Hassan* bazaka dena fad'a mani wannan abun ba ko, ai ma'aikatan banki sune masu gidan kud'i.
Malan Hassan yace ai dole na fad'a, kowa yasan kwastam kuna morewar ku domin kunfi masu banki 'yanci. Murmushi yayi anan suka gaishe shi. Malan Hassan yace wannan abokin aikin ka ne? Abubakar yace aikuwa dai Malan Hassan.
Zama sukayi Malan Hassan yana fad'in ina shugaban ku bawan Allah? Abubakar yace yanzu muka rabu ya wuce gida, ashe kaima kana tausaya masa? Malan Hassan yace ai dole na tausaya masa domin kowa yasan sharri akayi masa.
Moses yace Baba kaima kasan sharri akayi masa kenan? Malan Hassan yace ni ganau ne ba jiyau ba. Dariya Moses yayi yana fad'in Baba me kake nufi haka? Shima dariya yayi yana fad'in Abubakar ya fahimci abinda nake nufi ai.
Murmushi Abubakar yayi yana ma Moses bayani. Dariya Moses yayi yana fad'in Baba nima na fahimta yanzu. Abubakar yace wallahi Malan Hassan Alhaji mutumin kirki ne, kawai ya had'u da sharrin su Alhaji ne.
Gyara zama Malan Hassan yayi yana fad'in nan wajen babu tsaro ko zamuje cikin motar ku? Da sauri suka tashi domin abinda suke nema kenan.
Bayan sun zauna Moses ya kunna wayarsa saboda kada Malan Hassan yazo ya k'aryatasu idan lokacin hakan ya taso. Malan Hassan yace Abubakar Alhaji Marusa da kake gani mugun mutum ne, Allah dai yasa a k'ark'ashinsa zanci abinci shiyasa nake zaune a gidansa har yanzu, duk abinda kukaji ance Alhaji Maiwada yayi wallahi k'arya ne, abu ne wanda aka shiryashi, hatta da kayan da sukace sun b'ace ina tunanin k'arya ne, domin akwai abinda nake gani.
Abubakar yace Malan Hassan kaima baka da tabbaci kenan? Malan Hassan yace tunda ban gani da idona ba bazan ce ba, amma akwai abubuwan da nake gani agidanshi.
Mr. Kallah da kuke gani abokin Alhaji ne sosai, domin yana yawan zuwa gidansa idan yazo Lagos, sannan akwai wasu mutane biyu suma irin aikin ku sukeyi ina yawan ganinsu, d'aya bahaushe ne, d'ayan ko hausa bayaji sosai, sai wasu manyan mutane da ganinsu kasan mugaye ne, tunda nake ganinsu hankalina bai kwanta ba, babu yanda za'ayi naje naji abinda suke fad'a saboda acan wajen hutawarsa suke zama, amma tabbas sune suka k'ullama Alhaji Maiwada wannan sharrin.
Abubakar yace muma abinda muke tunani kenan, akwai abinda mukeso asa mana a wajen hutawarsa, babu wanda zaiyi mana wanan aikin idan ba kai ba Malan Hassan, shine nace muzo ko zaka taimaka mana domin Allah.
Malan Hassan yace kome kuke so zanyi maku domin nima nayi aikin lada. Na'urar Moses ya fiddo yana masa bayanin inda suke so yasa. Malan Hassan yace dan wannan ai mai sauki ne, kawai ku koya mani yanda zan sata.
Nan Moses yashiga koya masa yanda zaisa ta, bayan sun gama Malan Hassan yace gobe nine zanyi aikin kwana, kuma agoben zanje na saka kada ku damu, Allah zai taimaka mana, idan na gama zan fad'a maka Abubakar.
Sosai sukaji dad'in abinda yayi masu, kud'i Abubakar ya ciro ya mik'a masa. Malan Hassan yace haba Abubakar, dan zanyi maka aiki sai ka bani kud'i? Abubakar yace ba biyanka nayi ba kawai kyautace. Amsa Malan Hassan yayi yana fad'in nagode sosai. Sallama sukayi masa suka tafi.
***
Washe gari suka samu Alhaji a ofis sukayi masa bayanin abinda ake ciki. Shiru Alhaji yayi yana tunanin sunan Mr. Kallah da aka fad'a, girgiza kai yayi yana fad'in gaskiya ban yarda akwai sa hannun Mr. Kallah aciki ba, nasan dai abokin Alhaji Marusa ne, kila wani abun yake kaishi gidan amma bana tunanin zai iya aikata mani haka.
Moses yace Sir, kada kayi saurin yanke hukunci, mujira ai gaskiya zata nuna kanta. Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in nagode sosai. Abubakar yace haba Alhaji wannan ba wani abu bane, insha Allahu gaskiya zata fito.
Alhaji yace wallahi ba saboda kud'ina su dawo nakeso a gano gaskiya ba, ina so na wanke kaina awajen mutane, sannan kowa yasan abinda Alhaji Marusa yake aikatawa. Moses yace zamu kamasu ne zasuci Ubansu. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in nagode.
A daren ranar Malan Hassan ya kira Abubakar ya fad'a masa ya gama komai. Abubakar yace nagode Malan Hassan Allah ya bamu sa'a. Yace amin.
**** ****
Haka rayuwa tacigaba da tafiya kowa yana aikinsa, duk hutu Ra'eez yana zuwa yayi sati d'aya ya koma saboda islamiya, alokacin da yazo sai da yayita tambayar dalilin da yasa suka canza gida. Ummunsa ce tayi masa dabara tace b'arayi suka matsa masu shiyasa suka tashi. Da wannan suka rufe bakinsa.
Tun bayan da Alhaji Marusa yayi ma Alhaji Maiwada wannan abun sai ya fara samun matsala a kasuwancinsa, cinikin da yakeyi sosai ya fara raguwa, ga yawan asara da yakeyi a wajen kawo masa kaya, amma da yake ya tara hakan yasa dukiyarsa bata girgiza ba, sai dai duk wacce ya fitar aka saro kaya da wuya ta dawo fiye da yanda take.
Haka su Umar da Adebayo komai ya fara lalace masu, mata da shaye-shaye ne suke cinye masu kud'i, duk yawan kud'in da suke samu basa masu afki.
Alhaji Maiwada kuwa tamkar anasa ma dukiyarsa taki, sosai yake samun bud'i, sai dai duk bud'in da yake samu sai yaji tsoron ya sayi kadara a Lagos, hakan yasa ya turama Alhaji Mansur kud'i ya saya masa gidaje a kano ya zuba masa haya, sannan ya bud'ema Ra'eez asusu a banki yana zuba masa kud'i a ciki dan baya son yarik'a tara kud'i a bankinsa dan ya tsorata da abinda ya faru.
**** ****
Dogon hutu su Ra'eez suka samu saboda sun zana jarabawa ta aji ukku zasu shiga babban aji idan sun koma, hakan yasa ya rok'i Abbunsa akan ya barshi yazo ko wata d'aya yayi tunda hutun dogo ne.
Alhaji yace Ra'eez wata d'aya yayi maka yawa, Labiba zata wuceka a islamiya da sauran 'yan ajinku, kuma kaga shirye-shiryen sauka kukeyi. Kuka Ra'eez yasa mashi yana rokonsa.
Ummu ce tasa baki tana fad'in tunda Ra'eez ya taso baka tab'a zaman sati biyu dashi ba, baka tsoron rashin mu ya tab'a karantunsa? kabarshi tunda har ya fito ya rok'a yakamata muyi masa wannan alfarmar, karatu ba wani abu bane tunda yana da kok'ari zai iske su, idan yazo nan bazai rik'a fita yawo ba sai yarik'a karatu.
Murmushi Alhaji yayi yana fad'in shikenan Uwargida na amince, nima inaso ya zauna akusa dani, rayuwar Lagos d'ince take bani tsoro shiyasa bana son yazo yayi rayuwa acikinta, nafiso sai ya kammala karatunsa yayi hankali kafin yazo muzauna.
Murmushi tayi tana fad'in nagode. Alhaji yace Ummun Ra'eez nifa ban yarda dake ba, naga kamar kin canza kwana biyu anya babu ajiyata kuwa? Dariya tasa ta rufe fuskarta. Alhaji yace wallahi bazan iya hakura ba tashi muje asibiti aduba idan ma babu komai duk zan gani.
Dariya tayi tace dan Allah ka barni bana son tashi. Mikewa yayi yana fad'in abu mai sauki bara na d'auke ki. Rik'eshi tayi tana fad'in zan fad'a maka. Zama yayi yana fad'in to inajinki. Duk'ar da kai tayi tana fad'in maganarka gaskiya ce, Ra'eez zai samu K'anwa ko K'ani.
Wani irin farin ciki ne ya lullub'e Alhaji, rungumeta yayi yana fad'in narasa bakin magana, Allah yayi maki albarka Bilkisu, tashi muje a duba aga ko wata nawa ne. Tashi tayi tana fad'in tunda kace sai anje muje.
Suna zuwa asibiti aka gano cikin watansa ukku, sosai yayi murna nan suka koma gida. Waya ya d'auka ya kira Alhaji Mansur yana masa albishir. Sosai sukayi farin ciki, anan Alhaji yake fad'ama Alhaji Mansur Ra'eez zeyi hutun wata d'aya anan idan yazo. Alhaji Mansur yace wannan yayi dai-dai, amma idan yazo yarik'a karatu bana son a wuceshi. Alhaji yace insha Allah.
**** ***
Tunda Ra'eez yazo baya zuwa ko ina, iyakar yawansa Malan Sani ya kaishi gidansa wajen Rumaisa wacce yanzu tayi wayau tana a aji ukku firamare, duk lokacin da yaje yana koya mata karatu, idan suka gama Malan Sani ya maidashi.
Sosai yake karatunsa, inda bai gane ba ya tambayi Ummunsa ko Abbunsa, zuwansa hutu suka k'ara shakuwa da Abbunsa, koda yaushe suna tare, yana dawowa ofis suke zama suyi ta fira, wasu abubuwan haka nan Alhaji yake fad'a masa duk da yasan wayonsa bazai d'aukesu ba, amma sanin natsuwar Ra'eez yasa Alhaji yake fad'a masa komai nasa.
Lokacin da hutu ya k'are haka suka had'a masa komai shida Labiba, alokacin Alhaji ya samu hutu sai suka tafi gaba d'aya kano. Sosai Maman Labiba taji dad'in zuwansu ita da Mijinta.
Satinsu biyu a Kano sannan suka koma Lagos cike da kewar juna. Haka Ummun Ra'eez ta aika ma Maman Rumaisa da tsaraba mai yawa, sannan ta aika Malan Sani yaje ya d'auko Ladi, itama ta samu tsaraba sai godiya takeyi.
**** ***
Dube-dube Malan
Hassan yakeyi a wajen daya aje na'urar da su Abubakar suka bashi amma be gani ba, mamaki ne ya kamashi ganin inda ya aje abun babu komai a wajen.
Motsin da yaji ne yasa shi saurin juyawa, Alhaji Marusa ya gani da wani mai aikinsa inyamuri. Jikin Malan Hassan ne ya fara rawa ya fara kok'arin barin wajen.
Alhaji Marusa yace Malan Hassan a iya sanina aikin ka agidan nan shine gadi, ko mai kula da tsaftar wajen