Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
ganin a kwato masa hakkinsa, amma koda mukaje gaisuwa Mahaifin Yaron yace abar maganar.
Amma Abbah.... Kaga Nabeel bana son yawan tambaya, kana son jin abinda ya faru kuma na fad'a maka, bansan ta yanda aka kashe shi ba tunda ba'a makaranta ya mutu ba, dan haka bana so ka tado mani da abinda yawuce shekaru da yawa, ka maida hankali wajen aikin ka zaifi maka. Tashi kaje, kuma bana so naji ka sake tada maganar dan nasanka da son kwato ma mutane hakkinsu, shiyasa ma ka zab'i kayi aiki a hukumar kwato ma d'an Adam hakkinsa.
Jiki a sanyaye Nabeel ya fice, kai tsaye wajen masu gyaran d'akin ya nufa, yana zuwa ya iske har sun gama sun rufe d'akin an kwashe dattin. Zama yayi yana murmushi, dama yasan za'a iya samun tsohuwar jarida a wannan d'akin, shiyasa tunda Adnan ya fad'a masa an buga labarin ajarida a daren jiya yayi tunanin yazo ya bincika dan yasan Abbanshi akwai aje tsofaffin kaya, hakan yasa yau tunda safe yashiga d'akin, cikin ikon Allah yaga jaridar, shiyasa yasa masu aiki su gyara d'akin gudun kada ya kaima Abbah jaridar yace da niya ya bincikota.
Ajiyar zuciya yayi yana tuna yanayin da yaga Abbansa aciki, tabbas akwai wani b'oyayyan lamari, akwai abinda Abbansa ya sani yake b'oyewa, haka ma Adnan ba gaskiyar labarin ya bashi ba. Dole yasan gaskiyar labarin kodan ya taimaki Abbansa kada mutuwa ta riskeshi da hakkin wasu.
Waya ya ciro ya kira Adnan, bayan sun gaisa yace mashi yana so su had'u anjima. Adnan yace shikenan. Kashe wayar yayi ya koma cikin gida.
**** ***
Hello Alhaji Marusa lafiya kuwa naji kamar kana cikin damuwa? Alhaji Barau ya fad'a cikin tashin hankali. Alhaji Marusa yace nima tambayar da zan maka kenan najika cikin tashin hankali, yanzu nake shirin kiranka sai gashi ka kirani.
Narke murya Alhaji Barau yayi yana fad'in store d'in kayana akazo cikin dare aka yashe ni, komai basu bar mani ba, da asuba Mr. Kallah yamun waya babban shagonshi na garinsu cikin dare ya kama da wuta ko tsinke ba'a fitar ba, shine nace bara na kiraka na fad'a maka halin da muke ciki.
Hawaye ne suka zubo ma Alhaji Marusa yana fad'in naku me sauki ne, tun jiya na kira ku amma wayar ku bata shiga, wallahi jiya banyi bacci ba, gaba d'aya tashin hankali yamun yawa ko abinci na kasaci, shikenan talauci ya fara mani sallama Alhaji Barau.
Mekake fad'a ne haka Alhaji Marusa? Sun takaita ni Alhaji Barau, kayan da nayi oda jiya an d'auko mani su cikin dare aka tare masu motar aka kwace sannan aka kashe su, kaya ne masu tsadar gaske, na saka dukiyata mai yawa wajen d'aukosu, sannan babbar ma'ajiyata itama yau da asuba akamun waya ta kone kurmus, shikenan nashiga ukku.
Murmushin gefen baki Alhaji Barau yayi kafin ya canza fuska yana fad'in yaushe ka bada odar kaya Alhaji Marusa? Ai na d'auka mun yanke shawarar had'a guiwa mu d'auko wasu kaya gaba d'aya, tun daga lokacin kuma babu wanda ya sake shigo da kaya amma gashi kace an kawo maka kaya jiya? Daburcewa Alhaji Marusa yayi yana fad'in ba su bane, wad'annan wasu ne daban abokin harkallarmu yamun tayinsu shine na tura masa kud'i, dan Allah kazo inaji dole muje asibiti dan numfashina baya tafiya dai-dai.
Alhaji Barau yace shikenan kazauna kada ka tashi gani nan. Godiya yayi masa ya kashe wayar. Wata irin dariya Alhaji Barau yasa yana fad'in damu kake magana, Allah yasa ma kasheka mu huta. Jakarsa ya d'auka ya saukko.
A falo ya iske su Momy, kallonta yayi yana fad'in direba zaizo ya amsar mani kayan kari sauri nake Alhaji Marusa beda lafiya. Momy tace ikon Allah, meya sameshi kuma? Alhaji Barau yace idan na dawo zakiji amma dai bala'i ne ya afka masa.
Momy tace to Allah ya kyauta, ince dai babu komai naka a cikin bala'in? Murmushi yayi yana fad'in babu. Kai ta jinjina tana fad'in to mun gode Allah, sai ka dawo.
Yana fita direbanshi yazo ya amshi jakar hannunsa ya bud'e masa mota yashiga suka bar gidan. A hanya aka kirashi da wata lamba, yana d'auka aka fad'a masa babban 'Dan Alhaji Marusa ne. Alhaji Barau yace naji dai, lafiya ko? Daga can aka fad'a masa Alhaji Marusa ne ya fad'i an wuce dashi asibiti. Cike da jimami yace gashinan zuwa.Murmushi yayi ya kalli direba yana fad'a masa su wuce asibitin su. Mr. Kallah ya kira ya fad'a masa yace gashinan zuwa.
**** ***
Fawwaz meya had'a ka da wannan maganin mai k'arfi haka? Kauda kai yayi yana fad'in Dady mura nakeyi shine nasha. Ammi tace murar ce tasa ka shanye kwalba d'aya? Saurin kallonta yayi yana fad'in Ammi wace irin kwalba d'aya kuma, ya dad'e fa iya yanda akace asha nake sha kawai jiya ne ya k'are.
To meya saka dogon bacci haka? Dady yace isa haka Ammi tunda yace ba duka yasha ba abar maganar. Tab'e baki tayi tana fad'in kaje kaci abincin ka. Dady yace sa akawo masa nan.
Tashi tayi tana fad'in wallahi Alhaji kana shagwab'ar da yaron nan, ya girma amma ka hanashi ya fahimci haka. Dady yace e naji bakomai. Murmushi Fawwaz yayi yana fad'in Dady da Ammi nah.
**** ****
Abbah ina kwana ya gidan? Lafiya lau jiki yayi sauki ai. Alhaji Mansur yace to madalla, sai ka k'ara kula, bana so kana saka damuwa aranka, sai jiya Maman ku take fad'a mani baka da lafiya.
Ra'eez yace ai na warke Abbah. Alhaji Mansur yace ta fad'a mani kokarin da kukeyi kai da abokan ka, kayi masu godiya, insha Allahu komai ya kusa zuwa k'arshe.
Ra'eez ya fad'a masa yanda sukayi da Kawun Jabeer. Alhaji Mansur yace Allah sarki Brr. Kamal, kaga kuwa na rasa lambarshi ka turo mani sai muyi magana dashi, Abubakar ma zan kirashi na fad'a masa shari'ar ta kusa zuwa dan ya shirya.
Ra'eez yace yanzu zan turo maka. Alhaji Mansur yace maganar motarka ban manta ba, wannan satin zai dawo zai zo ya dubata. Ra'eez yace to Abbah nagode, agaishe dasu Umma.
**** ***
Yes, shigo. *Malan Dauda* lafiya dai,,? Risnawa yayi yana fad'in 'Yallab'ai kana da bako. Bako kuma, waye ne? E to ya nuna mani katinshi ma'aikacin gidan babban redion ne.
Shikenan kace yashigo. Da sallama Rafeek yashigo ofis d'in Kwamishna, amsawa yayi yana nuna mashi wajen zama. Hannu Kwamishna ya mik'a masa suka gaisa. Murmushi yayi yana fad'in lallai yau muna da manyan baki.
Murmushi Rafeek yayi yana fad'in 'Yallab'ai barka da aiki. Kwamishna yace yauwa kaima sannun ka da aiki, ai kune masu aiki domin kuna nishad'antar damu da labaruka masu gamsarwa, musamman kai, dan ina kallon labaranka.
Ruwan da masinjan ya aje ya d'auka yasha yana fad'in ai abun ba sauki 'Yallab'ai. Kwamishna yace to Allah yasa mudace. Rafeek yace amin.
Wato dama nazo ne ina so naroki alfarmar fira da kai agidan redion mu idan babu damuwa. Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in haba babu damuwar komai, ai gidan redion ku babba ne, kunsan abinda kukeyi shiyasa nake matuk'ar son sauraren abinda ya fito daga can, babu komai yaushe ne lokacin firar? Rafeek yace 'Yallab'ai kaine zaka sa mana lokaci ai.
Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in ko gobe ma yayi. Rafeek yace to mungode Allah ya k'ara girma. Kwamishna yace amin. Kati Rafeek ya mik'a masa shima ya bashi nashi. Godiya yayi masa ya baro ofis d'in cike da farin ciki, kai tsaye asibitin da akayi masa kwatance mallakin Dr. Aliyu Sani ya nufa.
Kwamishna kuwa farin ciki ne ya rufeshi jin za'ayi fira dashi a babban gidan redio, yasan tunda suka gayyaceshi sun yaba da aikinsa shiyasa suke son fira dashi, yasan kilama ya samu lambar yabo idan aka ga karramawar da 'yan gidan redion zasuyi mashi.
**** ****
Adnan maganar daka fad'a mani gaskiya ce kuwa? Kallon Nabeel Adnan yayi yana fad'in baka yarda dani bane? Girgiza kai yayi yana fad'in na yarda da kai, sai dai acikin labarin daka bani baka fad'a mani gaskiyar yanda abun ya faru ba, da alama kasan komai tunda makarantar kuce, kuma Yaron ajinku d'aya, kawai dai kana b'oye mani ne saboda kana jin kunyar ka tona asirin mahaifina.
Adnan yace ya kake fad'in haka, waye ya fad'a maka Abbanka yana da hannu acikin abinda ya faru? Idan beda hannu ka fad'a mani waye yake bayanshi to? Ajiyar zuciya Adnan ya saki yana fad'in wai Nabeel lafiya kake kuwa, yanda ka d'auki wannan abun kamar wani naka ne haka ta faru dashi.
Murmushi Nabeel yayi yana fad'in kada kamanta aikina ne, Allah ya bani ilimin sanin yanayin da mutum yake ciki, gashi kuma ina aiki a k'arkashin masu kare hakkin d'an Adam (Human right), tun daka fad'a mani wannan labarin nasan dole Abbah yana da alak'a dashi, kaima kana neman wani abu ne shiyasa kazo mani da maganar, domin bani da had'i da labarinka amma gashi kazo mani dashi, shekarar mu nawa tare baka tab'a bani wannan labarin ba sai jiya. Uhmm Adnan ko baka fad'a mani ba dole Abbah yana da masaniya akan wannan abun, kuma ka sani idan baka fad'a mani ba zanje nayi bincike da kaina, domin tunda ka bani labarin nan ya tab'a zuciyata, kuma naji ina da sha'awar taimakawa.
Jinjina kai Adnan yayi yana fad'in kayi hak'uri zan baka labari, abun ne babu dad'in ji dan bansan yanda zaka kalleshi ba tunda ya shafi ahalin ka, amma tunda kace na fad'a maka zan fad'a maka, sai dai ina rokon ka koda kaji labarin idan har bazaka taimaka ba saboda Mahaifinka dan Allah kada ka fad'ama kowa.
Nabeel yace wallahi koda Abbah ne ya kashe Farouk sai na tabbatar da gaskiya, dan haka ina jinka....
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣8️⃣
Hannu Nabeel yasa yana share hawayen da suka jik'a masa fuska na tausayin labarin da Adnan ya gama bashi, Adnan ma kukan yakeyi, jiyake kamar ayanzu abun ya faru.
Girgiza kai Nabeel yayi yana fad'in na sani dama Abbana yana da masaniya akan wannan abun, tun d'azu da mukayi magana naga halin da yashiga hankalina bai kwanta ba, hakan yasa nace ka fad'a mani gaskiya.
Adnan yace wallahi Nabeel tunda Yaya Sameer yazo mani da maganar hankali na yake tashe, duk da abaya ina d'an tuna abun amma ba kamar da Yaya yazo mani da maganar ba, tun daga ranar komai ya canza mani, wallahi jiya har mafarkin Naseer da Farouk nayi, shiyasa na kudirta araina ko zan rasa raina sai na bayar da sheda akan shari'ar da za'a gabatar, gaba d'aya laifin mu ne, da ace mun fad'i gaskiya duk haka bazata faru ba.
Nabeel yace dole a tabbatar da wannan gaskiyar, koda ace dasa hannun Abbah akayi kisan wallahi sai an tona komai, sai kuma Allah yasa babushi aciki, laifinsa d'aya daya taimaka ma masu laifi wajen b'oye gaskiya, nasan shima dole ayi masa hukunci.
Jinjina kai Adnan yayi yana fad'in nagode Nabeel, hakika kai d'in abokine nagari, na d'auka zansha wahala kafin ka bani had'in kai sai gashi kaima zaka bada taka gudummuwar, tabbas ka dace da yanayin aikin ka, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi.
Nabeel yace amin, sai dai kuma banso kayima Fawwaz wannan maganar ba, domin nasan duk inda yake maganar tana masa yawo akai, duk lokacin da yaji an shigar da k'ara kaine zaka fad'o masa arai, zai iya yin duk abinda zeyi wajen ganin bakaje kotu ba.
Adnan yace ka barshi Allah ya fishi, gara da nayi masa maganar na tabbata bazai sake kwanciyar hankali ba. Nabeel yace haka ne, Allah ya bamu ikon tabbatar da gaskiya. Adnan yace amin. Sallama yayi mashi yawuce cike da farin ciki.
**** ****
Tsaye Rafeek yake a bakin k'ofar asibitin Dr. Aliyu Sani sai kallon agogo yakeyi, wani ma'aikacin wajen ne yazo wucewa, da sauri Rafeek ya k'arasa yayi masa sallama.
Murmushi mutumin yayi yana amsawa dan ya gane Rafeek saboda ba b'oyayye bane kasancewarsa ma'aikacin gidan babbar redio.
Hannu Rafeek ya bashi suka gaisa. Mutumin yace yau muna da babban bako, shine kuma kake tsaye a waje Malan Rafeek. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in ai ban dad'e da zuwa ba dama ina jiran naga wani ne.
Mutumin yace barka da zuwa ni sunana *Dr. Sageer Isah*, kai kam nasan naka domin sananne ne a wajen kowa. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in nagode sosai Dr. Sageer.
Shiru yayi kafin yace dan Allah Dr. Aliyu fa? Dr. Sageer yace aikuwa yau zaishigo dan yau ranar zuwansa ne, kasan Dr. Ba kasafai yake shigowa ba akwai wasu aiyukan da suke gabansa, amma yau munyi waya yace zaishigo, sai dai ban sani ba ko da wuri zai shigo.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in ina jin labarinsa gaskiya babban likita ne, gashi har ya bud'e asibitinshi, ga na gwamnati da yake aiki, ga sauran wajaje da yaje gudanar da aiyukansa, hakan yasa nakeso mu d'an gana dashi.
Murmushi Dr. Sageer yayi yana fad'in ai Dr. Ba sauki, mutum ne mai matuk'ar son kud'i, shiyasa gaba d'aya rayuwarsa beda lokacin kanshi, duk wani abu indai zai kawo kud'i to Dr. yana gaba wajen nemoshi, shiyasa asibitin nan muke da abubuwa da yawa, ba dai muje waje muyi wani abu ba sai dai ma azo wajen mu ayi.
Rafeek yace Allah sarki, gaskiya yasan kanshi, ai duniyar sai da neman kud'i. Dr. Sageer yace muje daga ciki ka jirashi ai bazamu bar babban bako a waje ba. Rafeek yace shikenan muje, amma idan naga bezo ba zan tafi saboda na baro aiki.
****
Ra'eez Yaya fa yace mu fara shirya yanda za'a shigar da k'arar su Naseer, dan sunyi waya da Adnan ya fad'a masa an samu Nabeel zai taimaka, tunda ba'a gano Iyayen Farouk ba gara ashigar da shari'ar Naseer hakan ne zai tono ta Farouk.
Ajiyar zuciya Ra'eez yayi yana fad'in nima so nake zuwa litinin afara shari'ar dan bana so murasa damar da muke da ita. Jabeer yace sai dai Yaya yace beyi magana da Baffansa ba, yafiso sai anshigar da k'arar kafin yayi masu magana.
Ra'eez yace ina tsoron kada suce basu amince ba. Jabeer yace zasu amince, domin babu wanda zaiji labarinka be tausaya maka ba, kuma ta shari'ar su ce za'a tado taka.
Ra'eez yace Allah yasa. Jabeer yace amin, wai ina mutuniyar? Tsaki Ra'eez yayi yana fad'in ko jiya tamun waya muka gaisa. Jabeer yace baiwar Allah. Tashi Ra'eez yayi yana fad'in muje ni kada ka fara kawo mani maganar wata Raheena. Dariya Jabeer yayi yana fad'in daga fad'in gaskiya.
**** ***
Dr. Sageer ya aiki ina fatan komai yana tafiya dai-dai? Jinjina kai Dr. Sageer yayi yana fad'in aiki lafiya lau babu matsalar komai, sai dai kana da babban bako.
Glass ya cire yana fad'in bako kuma? Ai babu wada yace mun zai zo. Dr. Sageer yace wannan ma'aikacin babban gidan redion ne *Rafeek Sambo Jarmai*.
Jinjina kai yayi yana fad'in meya kawo d'an jarida waje na kuma? Dr. Sageer yace yanda kake cigaba 'Yallab'ai ai dole 'yan jarida surika son ganinka, shima d'azu ya gama yabonka.
Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad'in ka shigo dashi to. Dr. Sageer yace yanzu kuwa.
Bayan Rafeek yashigo suka gaisa sai Dr. Sageer ya basu waje. Dr. Aliyu yace yau kaine da kan ka? Rafeek yace wallahi kuwa, jiya nashiga babban asibiti wajen wani abokina shine ake maganar irin kwazonka shine nace ni kuma zanzo naga asibitinka kuma mugaisa.
Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad'in amma nagode, ai mutum baya zama gwarzo dole saiya jajirce, kafin na kawo wannan matsayin nasha gwagwarmaya sosai, da haka dai ina hak'uri har Allah ya d'aga ni.
Rafeek yace wannan haka yake, ai kamar babban Alkali ne Alhaji Barau, duk wanda yasanshi yasan yanda yake da jajircewa awajen aiki, saboda kok'arinsa sai da sunanshi yayi fice a gidan redion mu, sannan ga tsohon Alkali, su duka biyun mutane suna alfahari dasu.
Gyara zama Dr. Aliyu yayi yana fad'in Allah sarki Brr. Barau, ai mutumina ne sosai, yanzu ma aiki ne yamun yawa shiyasa muka rage gaisawa, ai ta silarsu na samu alkhairi sosai, zan iya cewa ta silarsu na kai wannan matsayin da nake ayanzu, domin sun taka rawar gani arayuwata.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in da alama kayi masu abinda sukaji dad'i hakan yasa suka tsaya maka. Dr. Aliyu yace sosai kuwa, domin nine na fara taimaka mashi ya kai wannan matsayin da yake kai kafin shima yasa tsohon Alkali da wasu manya suka dafa mani, tabbas nine na fara taimaka masu.
Rafeek yace idan haka ne kaine ka tsaya masu ba sune suka tsaya maka ba, domin duk wanda zai maka wani taimako har kaci nasara arayuwa to baka da kamarsa, duk da bansan abinda kayi masu ba amma nasan amatsayinka na babban likita nasan ka cece rayuwar wani daga cikinsu.
Girgiza kai Dr. Aliyu