Advertisements
Chapter 44 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   44 / 54

129K to 132K   out of 160.3K words

bana so mutane suga gazawarka musamman da shari'ar take tsohuwa, gara ace kayi nasara zaifi.


Kai Ra'eez ya jinjina yana fad'in insha Allah. Tashi yayi yana fad'in nagode zan tafi. Alhaji Barau yace ka kula da kanka.


**** ****

Kada ka damu Rafeek, wannan abu ne mai sauki, ina tabbatar maka ayau zan kama Fawwaz, nasan Iyayen shi sun killace shi agida suna jira lokacin tafiyarsa yayi sannan su fiddoshi ya tafi, nasan dan wasa yanzu bazamu ganshi ba, amma nasan wanda zansa ya fiddo manishi cikin sauki.


Rafeek yace nagode Hamza, sai maganar su Adnan, tabbas nasan sune sukasa aka kamasu, amma na tura su Brr. Jabeer suje abi mana diddikin layinsu.


Hamza yace bara nakira amintattun ma'aikata na dole wannan aikin yana buk'atar sirri saboda kasan yanzu duniyar babu gaskiya zasu iya siye masu matattar zuciya acikin mu, shiyasa sai amintattuna kad'ai zan d'auka domin na saba fita dasu irin wannan aikin sirrin.


Rafeek yace yanzu waye kake tunanin zai iya fito da Fawwaz? Murmushi Hamza yayi yana fad'in akwai babban abokinsa d'an uwan su Maid'akina ne, nasan yanda zanyi ya fito mana dashi.


Hamdala Rafeek yayi yana fad'in nagode abokina. Hamza yace haba bakomai, insha Allahu komai zai tafi lafiya lau, kuma zan tsaya har sai an tabbatar da gaskiya.


Wayar Rafeek ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Jabeer, saurin d'auka yayi. Jabeer yace Yaya gaba d'aya layinsu a waje d'aya ya dena aiki, sai dai kuma alamu sun nuna wajen da yabar aikin waje ne da yayi nuni da b'oyayyan waje dan ba cikin gari bane.


Rafeek yace shikenan ku taho zamu san yanda za'ayi. Hamza yace ya dai? Fad'a masa abinda ya faru yayi. Murmushi Hamza yayi yana fad'in sace su akayi, idan kuma har abinda aka duba gaskiya ne to zamu duba daga inda layin ya tsaya dole suna ata wajen. Rafeek yace nagode. Sallama yayi mashi ya tafi.


**** ****

Dan Allah Sweetheart ki nutsu, idan akabi komai a sannu babu abinda zai faru. Zama Momin su Marwan tayi tana goge idonta, kallon Yaronta tayi tana fad'in wallahi kashe shi zasuyi, kasan kuwa dokar k'asar saudiya? Ni na rasa wannan abu na Marwan, shida yake india bansan ya akayi yaje saudiya ba, duk da nasan yana fad'a mun yana kasuwanci a Madina amma be fad'a mun zeje can ba.


Gyara zama saurayin yayi yana fad'in to dama baki san Marwan yana dillacin kwayoyi ba? Momy tace wallahi ban tab'a sani ba, idan nasani taya zan barshi, dan Allah *Nuress* idan kana da mafita ka fad'a mani.


Murmushi Nuress yayi yana fad'in gashi kuma gobe zan koma, kuma gaskiya ni bani da wanda na sani a Madina, tunda Alhaji zai dawo gobe ki barshi yazo nasan abun zaizo da sauki tunda sune masu k'asar.


Ajiyar zuciya tayi tana jawo wayarta tace bari na turama Khalil kud'i yace mun kud'inshi sunyi k'asa, nima ba kud'in gareni ba tunda duk na kwashe su nayi wannan siyayyar gashi kuma asara ta sameni, jira nake Alhaji ya dawo ya k'ara mani jari dan duka kud'in account d'ina bazasu wuce million goma ba.


Matsowa Nuress yayi yana shafa mata baya yace kada ki damu Baby komai zaizo da sauki, tunda Alhaji ya warke daya dawo kud'inshi zasu dawo.


Murmushi tayi tana kok'arin tura kud'i, tsaf Nuress ya haddace code d'inta. Bayan ta gama ta mik'e tana cire sark'ar zinarinta dan tunda suka dawo daga unguwa bata samu cire kaya ba ta samu wayar an akama Marwan hakan yasa hankalinta ya tashi.


Durowa ta bud'e ta d'auko wani akwati, bud'eshi tayi saiga wasu sarkokin da abun hannu hada zobuna duk na gwal, maida wadda ta cire tayi ta rufe akwatin da mukullinshi ta maida mukullin inda yake.


Koda ta juyo sai taga Nuress ya juya mata baya da alamu baisan abinda takeyi ba dan hankalinshi yana kan waya. Abinda bata sani ba ta cikin wayar yake kallonta.


Sunanshi ta kira hakan yasa ya juyo. Nuress yace Baby kije kiyi wanka naga jikin ki duk yayi sanyi. Murmushi tayi tana fad'in zanyi amma kad'an zo ka sakani nishad'ani sai nayi wankan da hujja. Murmushi yayi yana fad'in yanzu kuwa, ai gara nayi na bankwana tunda anjima zan bar gidanki zuwa gobe na wuce.


**** ****


Wai abokina dan zaka koma waje shine ake kullen ka? Fawwaz yace wallahi ba haka bane, kasan na fad'a maka abinda ya faru lokacin muna sacondary, to ashe munafuki Adnan yaje ya fad'ama Iyayen yaron da nake fad'a maka na yanka da wuka, shine fa aka maido shari'ar babbar kotu, yanzu haka nemana akeyi shi ne fa Dady yace komawa zanyi bazan sake zuwa Nija ba.


Milo yace yana da gaskiya, domin idan ka tsaya nan dole a kama ka, amma haka zaka zauna har lokacin tafiyar ka yayi bazaka d'an shana da budurwarka ba? Fawwaz yace gobe ne fa tafiyar kuma inaji jirgin safe zanbi.


Milo yace gaskiya zanyi kewa, amma ya kamata kazo muje kayi na bankwana. Fawwaz yace gaskiya Dady yace kada naje ko ina, kuma idan na fita dole zai gane.


Milo yace motata bakin glass ne, ka fara fita kashige zan biyoka daga baya kaga babu wanda zai san tare muka fita. Fawwaz yace shikenan, amma dole zaka k'ara mani wannan kayan. Milo yace baka da matsala. Dariya sukayi ya tashi, wayarsa ya aje yana fad'in nan zan barta kada Dady ya kira.


**** ****


Wallaji Oga munyi iya binciken mu bamu samu komai ba, har mun wuce inda wayarsu ta dena aiki amma babu abinda muka samu, kuma bamuga kowa wanda zamu iya zargin wani abu ba, shiyasa muka dawo ko zuwa gobe sai mu canza waje.


Gyara zama Hamza yayi yana fad'in ba sai kun canza waje ba, dole suna nan inda kukaje, ba k'ananan b'arayi bane shiyasa basu bar wata alama da za'a iya ganesu ba, dole sai munsa basira a aikin kafin mu kamosu, dan haka ku barshi sai gobe sannan mu koma.


Sara mashi yayi kafin yayi waje. Wayarsa ya d'auka yana fad'in ina jinka Milo, toshikenan kayi yanda nace dan bana so ya zargeka, gamu nan zuwa kawai ka nuna baka san komai ba. Nagode.


**** ***

Ra'eez tashi muci abinci kaji. Tashi Ra'eez yayi yana dafe kai. Jabeer yace jarumta zakasa aranka insha Allahu komai zaizo da sauki, idan suna tunanin wannan abun da sukayi sunyi nasara to hakan zai jawo masu fitina, domin Allah baya barin azzalumai, idan ka bari damuwa ta kaika k'asa shikenan zasuyi galaba akan mu.


Kallonshi Ra'eez yayi yana fad'in wallahi aikin shari'a ya fitar mun akai, dama can saboda d'aukar fansa na tsaya na karanceshi, amma ina kammala wannan shari'a to zan kammala ta tare da aikina, wallahi Jabeer bazan iya ba, aikin lauya aikine na halaka.


Kada ka sare Ra'eez. Saurin juyowa sukayi jin magana daga bakin k'ofa. Alhaji Mansur ne tsaye yana kallonsu. Duk'ar da kai Ra'eez yayi.



Shigowa yayi yana fad'in wannan fa somin tab'i ne, duk da ma shine mai wahalar domin kafin akai k'arshen shari'ar kowa zaisan matsayinsa, dan haka kadena damuwa yanzu haka Fawwaz yana hannun Inspector Hamza.


Cike da farin ciki Ra'eez ya d'ago kai yana kallonshi. Kai ya jinjina yana fad'in Rafeek ya kirani ya tabbatar mani da haka, kaga komai zaizo da sauki. Jabeer yace amma naji dad'i, sai ka matso muci abincin yanzu.


Murmushi Ra'eez yayi ya matso yana fad'in ko yanzu ma akoma kotu. Dariya Alhaji Mansur yayi yana fad'in banda cika baki fa. Ra'eez yace Allah Abbah naji sauki yanzu, sai dai hankalina yana wajen su Adnan da Abban Nabeel, bana so ta silata su rasa rayukansu.


Alhaji Mansur yace Hamza ya tura amintattun yaranshi, duk da sunje basu samu komai ba amma gobe zasu koma, bazasu tab'a kashe su yanzu ba, nasan zasu jira zuwa jibi kafin nan kuma insha Allahu an kwatosu. Ra'eez yace Allah yasa.


Wayar Alhaji Mansur ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Bala bakanike, murmushi yayi yana fad'in ko har an kammal gyaran motar? 'Daga wayar yayi. Bayan sun gaisa Alhaji Mansur yace Bala an kammala ne? Daga can Bala yace wallahi yanzu haka aikin nakeyi, kasan motar ta dad'e a aje dole sai da na fiddo komai dan tayi kura sosai, amma kuma injinta lafiya lau yake, to bayan da na fito da kujerun motar sai na samu wani tsohon flash, shine nace bara na kiraka na fad'a maka.


Alhaji Mansur yace flash kuma? Saurin gyara zama yayi yana fad'in Bala kana ji na ko, ina so ka samu abinda zaka saka mani shi, ka jira ni nan da mintuna zan kira ka, ina so yazo lagos daga nan zuwa gobe. Kashe waya yayi yana fad'in Allah amin.



Ra'eez yace Abbah lafiya? Murmushi yayi yana fad'in Ra'eez gaskiya tana ta kok'arin bayyana kanta, kasan Bala ya tafi da motar Alhaji zai dubata, shine yace mun a k'asan kujera ya tsinci wani tsohon flash, duk yanda akayi ajiyar Marigayi ce, Alhamdulillahi Allah mungode maka, dole nayi waya a samu wanda zai taho lagos ya kawo manashi, badan ma bana so wani abu ya faru ba da ko amotar haya sai a d'oroshi, amma bari nayi waya da abokina shine shugana 'yan Union.


*** ****

Ka kwantar da hankalin ka Mr. Kallah babu abinda zai faru, ina fatan baka fad'ama Alhaji Marusa komai ba dan kaga daga ciwo ya tashi? Mr. Kallah yace ban fad'a masa ba amma dole na damu Alhaji Barau, tsohon sirrin mu da yayi shekara da shekaru fa akeson bankwad'owa taya hankalina zai kwanta.


Alhaji Barau yace kada kamanta fa mune kotu, Alhaji M. Sanda bazai tab'a bari asirinmu ya tonu ba, kai tun daga can sama muna da k'afa taya kake tunanin asirin mu zai tonu, kai dai kawai sai kun dawo goben, ka gaishe mani da 'Yallab'ai Marusa. Dariya sukasa ya kashe wayar.


**** ****


A zabure ta tashi daga kwancen da take ganin sakon daya shigo wayarta, hannu tasa ta murtsike idonta ta d'auka ko bacci takeyi amma tabbas zahiri ne.



Gaba d'aya ta rikice, taya aka amsar mata makudan kud'i har haka, gashi kuma acikin bankin aka amshe su, dole tasan a volk room ne kad'ai za'a iya amsar wad'annan kud'in domin tasan acan take amsar kud'i masu yawa. Suman zaune tayi, wasu hawayen tashin hankali ne suka zubo mata lokacin data kalli balance d'inta, ita da take da kusan million takwas dan d'azu ta turama Khalil kud'i amma yanzu itace take da dubu d'ari biyar.


K'arar sakon daya shigo mata ne yasa tayi saurin dubawa. Ido ta tsura ma sakon tana karantawa a hankali.


*Nasan da ciwo aci amanarka, amma ciwon mai sauki ne idan akayi duba da abinda mutum ya aikata, nasan baki san koni waye ba shiyasa kika fara tarayya dani, ni kuma sanin da nayi maki ne yasa nashigo rayuwar ki, ina fatan hakan zai zama darasi agareki idan kina da sauran Imanin da zaki iya koyon darasin. Nuradden Hambali, 'Dah ga Shehu Hambali Rigacukum zariya, ko ahaka na barki nasan ya isheki ki tuna komai, kinci amanar mahaifina wanda hakan ya jawo ajalinsa, kin wulak'antani akan nazo neman taimakon kud'in da zan kai Mahaifina asibiti, duk da kece silar jefashi halin da yake amma kika tozartani, tun daga ranar na d'auki alk'awarin tozartaki, na tausaya maki shiyasa na rage maki na cefane, kada kiyi tunanin nemana domin zakisha wahala kuma hakan zai kaiki ga mutuwa ma, ki gode Allah daya baki basirar zab'en akwati mai kyau na ajiyar gwalagwalai, na barki lafiya. Ur's Nuress.*



Wurgi tayi da wayar cikin tashin hankali ta bud'e durowa, ihu ta saki ta zube tana wani irin kuka, tabbas Nuress ya gama da ita, bayan da ya mayar da ita tamkar matsarsa, ta siya masa gida da mota, duk hakan be ishe shi ba sai da ya aikata mata cin amana.



Runtse ido tayi a hankali ta furta *Shehu Hambali*

****

Shine saurayinta na farko arayuwarta, tana kaduna yana zariya amma haka yake zuwa wajenta, sunyi soyayya sosai, kasancewarta mai idon cin naira yasa ta tasoshi gaba, shi kuma yana sonta shiyasa baya iya mata gardama, a hankali ta rik'a tatseshi, kafin asa masu rana duk wani abu nashi sai da ta cinye, bayan ansa masu rana akazo had'a lefe tace ga irin wanda takeso, beda kud'i sai gidanshi na gado, dole ta sashi ya raba gidan biyu ya siyar da rabi tace zatayi maleji tasan bayan aure zasuyi kud'i.


Ana saura sati d'aya bikinsu ta had'u da Alhaji Marusa, cikin k'ank'anin lokaci labari ya canza, aranar d'aurin aure Shehu da abokansa suna zaune sukaji an d'aura da wani bashi ba.


A asibiti ya kwana, kwananshi ukku aka sallamoshi, yana zuwa gida ya iske amaryarsa, domin tun acan Kawunsa yasa aka d'aura da diyarshi, ana dawowa kuma aka siya mata komai ta tare.



Yayi kuka har ya gaji, tun daga ranar ya kamu da ciwon zuciya, sau d'aya ya tara da matarsa rabon Nura yashiga, ga talauci, ana haka ya samu labarin inda Karimatu take a Lagos, haka ya wanke kafa yaje, sai dai wulakancin da tayi masa ko kare bazai d'auka ba, tunda ya dawo ya samu littafi ya rubuta tarihinsu, haka yacigaba da rayuwa cikin kunci, duk da matarsa tana kula dashi.



Bayan shekaru Nura ya tasa, tunda ya taso haka ya iske Mahaifinsa babu lafiya, zuwa lokacin basu da komai, ga ciwo, ganin zai mutu suka kaishi asibiti, makudan kud'in aikin da za'a mashi ya tada hankalinsu, haka yazo d'akin Mahaifinsa yana duba takardun gidan ya siyar ayi masa magani.



Littafin daya iske yaja hankalinsa ya karanta. Yayi kuka har ya gaji, a washe gari yaci bashin kud'i ya nufi Lagos, duk da bayanin da yayi mata besa ta tausaya mashi ba, haka ta wulakantashi tasa masu gadi suka masa duka suka wurgoshi waje.



Kafin ya dawo sai zaman makoki ya iske, ta silar haka Mahaifiyarsa ma ziwon zuciya ya kasheta, yasha wahala hakan yasa ya taso da niyar d'aukar fansa. Dole tasa ya siyar da gidan gadonshi yaje ya sayi kaya masu kyau ya koma Lagos da zama.



A hankali ya fara bibiyar Karimatu, wata rana ta fito daga wani Mall suka had'e, shine ya amsar mata kayan ya kai mata mota, tunda ta ganshi ta mace akanshi. Wannan ne silar had'uwarsu, yana sane ya maidata kamar matarsa duk da ba hakan yaso ba, zafin dake ranshi yasa ya biye mata, tayi masa hidima a ciki hada gida da mota, a yau daya kammala aikinsa sai yaji duk wani kunci ya bar zuciyarsa, haka yabar Lagos.



Ajiyar zuciya ta saki mai k'arfin gaske bayan data gama dogon tunani, wato shiyasa Nuress yashigo jikinta har haka kenan, ta aminta dashi hatta da aiken banki shi take turawa ko nawa ne zai karb'o mata kuma be tab'a mata sata ba, ma'aikatan bankin duk sun sanshi dan tace masu k'aninta ne shiyasa da ta aikeshi da check matuk'ar akwai sa hannunta suke bashi kud'i, to ya akayi ma tasa hannu a check d'in? Dole sai idan satar fasaha yayi mata.


Wani sako ne ya sake shigowa wayarta, saurin dubawa tayi... *Nasan zakayi mamakin yanda akayi aka bani kud'i ba tare da sa hannun ki ba, to idan baki sani ba yanda na iya sa hannun ki ko ke bazaki nuna mun iyawa ba, wannan dalilin ne yasa na iya saka hannunki, ada nayi tunanin na cira ta Atm, sai naga bazan ciresu alokaci guda ba, shiyasa na shirya tafiya da rana saboda na samu naje banki, sai kuma naci sa'a aka gama komai na bar bankin kafin kisan anyi, na barki lafiya.*


Wani irin ihu ta saki data tuna abinda yayi mata, da sauri Mai aikinta tashigo, ganin halin da take ciki yasa tayi saurin kiran masu aiki maza, kafin suzo ta sume, dole suka d'auketa zuwa asibitin su.


*** ***


Wai ina Fawwaz yaje ne? Ammi tace tun bayan da abokinsa yazo har ya tafi yana d'aki kwance dan naga lokacin da abokin ya tafi sai dai ban shiga d'akin ba dan nasan baya son takura.


Amma ai nakira wayarsa tana k'ara kuma be d'auka ba, jeki duba mani d'akin, ko kuma muje ma. Turuss sukayi ganin baya d'akin, saurin tura k'ofar band'aki yayi amma baya ciki, hankali tashe ya d'auki wayar Fawwaz yana duba sunan Milo, sai dai babu lambarshi babu alamunta.


Zama yayi zufa tana keto mashi. Ammi tace wai lafiya Alhaji? Kallonta yayi yana fad'in burinki ya cika kin barshi ya fita saboda akamashi dan bakiso yabar k'asar.



Ammi tace mekake fad'a haka, nice zan barshi ya fita? Tomeyayi ma da za'a kamashi? Tsaki yayi yafice daga d'akin.


Wayar Lucky ya kira, yana d'agawa yace Lucky Fawwaz ya fito, inaso ka kokarta ka dawo dashi gida tun kafin aganshi, ka duba gidan hutawarsa kuma ka bincika inda yake zuwa bana so asamu matsala.


Kashe wayar yayi yana huci.


Ur's.
Nabeelert Lady🖋[3/10, 8:41 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta

44 / 54