Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
yayi yana fad'in ko d'aya, kawai nayi masu.... Gyaran murya yayi yana fad'in haka ne, kasan mu likitoci akwai mu da taimako, idan kuma mutum yasan alkhairi to baya mantawa damu, wannan shine abinda ya had'ani dasu har muke abota.
Rafeek yace gaskiya kai d'in na daban ne, gashi dai kaine mai taimakon amma duk da haka kana ganin sune suka taimaka maka, Allah ne zai iya biyanka.
Murmushi Dr. Aliyu ya saki yana fad'in maganar ka gaskiya ce Rafeek, ya kamata ace har yanzu suna bani girma, sai dai kuma nine nake nemansu ba sune suke nemana ba, akwai Alhaji Marusa da Mr. Kallah duk mutane na ne.
Rafeek yace saboda ka gama masu amfani shiyasa suka kyale ka, kasan suna hud'd'a da mutane da yawa dole surik'a samun masu yi masu alfarma da yawa shiyasa bazasu rik'a neman wad'an da suka taimakesu ba.
Murmushi Dr. Aliyu yayi yana fad'in aiko be kamata ace sun manta dani ba musamman shi Brr. Barau, domin na bada gudummuwa wajen hayewarsa wannan kujera, gaskiya ka sosa mani inda yake mani kaikayi ma, maganar ka gaskiya ce, bekamata ace nine nake binsu ba domin nine nayi masu rana.
Murmushi Rafeek yayi ya mik'e yana fad'in 'Yallab'ai zan koma, dama nace zanzo mugaisa ne. Hannu Dr. Aliyu ya bashi yana fad'in nagode Rafeek, ga katina sai murik'a gaisawa ko.
Rafeek yace nike da godiya. Sallama yayi mashi ya fice ya barshi yana juyi a kujera cike da tunani. Murmushi ya saki yana fad'in Allah yayi maka albarka Rafeek, ka sosa mani inda yake mani kaikayi, ga babban Lab can zan fara ginawa dama ina tunanin gininshi bara nayi amfani da wannan damar, Allah ma yaso banyi sub'utar baki ba dana fad'a masa tsohon sirrin mu.
Waya ya ciro ya fara neman Alhaji Barau. Bugu biyu ya d'auka, bayan sun gaisa Alhaji Barau yace babban likita kwana da yawa, ka ganni nan nazo asibiti an kawo Alhaji Marusa.
Dr. Aliyu yace kunki dai dawowa asibitina duk da kunsan nima ina da kayan aiki. Alhaji Barau yace ba haka bane, kasan asibitin mu hada turawa kai kuma naka babu wasu kwararrun likitoci, kasan ni kuma bana son wasa da rayuwa shiyasa na rik'e asibitin Dr. James.
Jinjina kai Dr. yayi yana fad'in idan da amana ai ruwa bazaici gwani ba. Alhaji Barau yace me kake nufi? Gyara zama Dr. yayi yana fad'in manta kawai, dama wasu 'yan kud'i nake so zan fara gina parmanent side na Lab d'ina kuma babu kud'i masu yawa a hannuna shine nace bara na maka magana.
Shiru Alhaji Barau yayi kafin yace haba likita, taya zaka zo mani da maganar kud'i da rana tsaka haka. Murmushi Dr yayi yana fad'in ko bashi ne ai zan samu ko? Alhaji Barau yace amma kaji nace ankawo Alhaji Marusa asibiti ko? Kuma ni yanzu banida kud'in da zan iya baka aro dan bikin d'iyata za'ayi, wai Likita meyasa kake son tambayata kud'i ne.
Dr yace yanzu dan nace ka bani bashi shikenan ya zama laifi, haba Alhaji kada ka mance da alkhairin da nayi maka fa, ko shekaru dubu za'ayi bekamata kamance da abinda nayi maku ba, domin nayi maku babbar rana kaima kasani, kuma har yanzu da bazata kake rawa.
Tsaki Alhaji Barau yayi yana fad'in ni bangane abinda kake magana akai ba danni bani da lokacin tunawa da rayuwar baya, koma menene bani da kud'i sai dai kajira Alhaji Marusa ya warke, ka gaishe da iyalin ka sai anjima.
Kallon wayar yayi jin an katse. Murmushi yayi yana fad'in maganar ka gaskiya ce Rafeek, dama nayi haka ne dan na gwadasu, lallai Brr. Barau ya cika butulu, amma bakomai indai nine bazan sake nemanshi ba, nagode Allah nima ina da kud'i, ko ba komai naci daga jikinsu da kud'in su ma nayi wannan ginin.
*** ***
Wai *Marwan* meya faru ne? Wanda aka kira da Marwan ya yamutsa fuska yana fad'in nima bansani ba, nazo zan amshi wasu kud'i ina shiga falon kawai na ganshi ya mik'e daga zaunan da yake, kafin na shiga kawai naga ya zube k'asa, gashi can dai ana dubashi.
Alhaji Barau yace shima Alhaji Marusa sai da nace mashi ya zauna nazo amma ya tashi, ba'a son idan tashin hankali ya same ka ka tashi. Marwan yace kamar ya ban gane ba? Labarin abinda ya faru ya fad'a masa.
Yamutse fuska yayi yana fad'in amma ai babu abinda zai tab'a dukiyarshi dan ya rasa d'an wannan abun dan nasan Dad yana da mak'udan kud'i, meye nashi nashiga damuwa gashinan zai jama kanshi, da kyar idan bai samu mutuwar b'arin jiki ba, yanzu ko kula dashi ai aiki ne, sai dai ya biya kud'i a fiddashi waje yayi jinyarsa acan danni cikin satin nan zan koma India.
Ido Alhaji Barau ya tsura ma Marwan har ya gama maganarshi. Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in yanzu ina K'anin naka? Marwan yace kasan baya son zaman k'asar nan, dama kuma Dad baya son muna zuwa gida, Mom kuma taje Dubai sai jibi zata dawo.
Alhaji Barau yace to Allah ya kyauta, sai ka tsaida tafiyarka ka kula dashi kafin asan abunyi. Waro ido yayi yana mik'ewa, kallon agogo yayi yana fad'in yanzu ni ina da wajen zuwa, dama kai na tsaya jira da naji kace kana hanya, zanje kafin anjima na dawo.
Bai jira amsar Alhaji Barau ba yayi gaba. Baki Alhaji Barau ya saki yana kallon Marwan, a hankali yake fad'in Allah nagode maka da baka bani namiji ba, tabbas yanzu Alhaji Marusa zaiyi nadamar rashin kula da yaranshi da yayi, koba komai ita tarbiya wani abu ce, saboda baka son takura ka tura yara waje sai dai ka aika masu kud'i, lallai Alhaji Marusa taka tazo k'arshe, nima ba zama zanyi ba ina da aikinyi.
Fitowar likita yasa yayi saurin binshi zuwa ofis. Bayan sun gaisa yake fad'a masa sanadiyar fad'uwar da yayi ya samu mutuwar b'arin jiki, dole abashi gado saboda za'a fara masa gashi, anci sa'a ma akwai sauran kud'inshi da yawa a asusun asibitin da ya zuba ana juyawa saboda rashin lafiyarshi data iyalinshi, dan haka yanzu kulawa kawai zasu bashi, sannan jininsa ya hau dole ya samu hutu.
Alhaji Barau yace lallai tashi ta sameshi, tunda akwai kud'i ai damuwar da sauki, yanzu acigaba da bashi kulawa zamu rik'a waya. Likita yace ba komai zamu kula dashi. Sallama yayi mashi ya fita.
**** ***
Wai Rafeek lafiya kwana biyu ka canza ba kamar yanda kake ba? Murmushi yayi yana fad'in lafiya lau Baffa kawai wani aiki ne ya tasoni gaba shine yasa bana zama.
Gyara zama Baffa yayi yana fad'in bana so kana matsama kanka, nasha fad'a maka aikin ku yana da had'ari, shiyasa kaji ina yawan tambayarka dan bana so kajefa kanka cikin damuwa kazo kaja mana, dan Allah Rafeek kada kajawo mana abinda zamu rasaka kamar yanda muka rasa d'an uwanka, kome zakayi arayuwa yana da kyau karika sanar mana domin addu'ar mu agareka kariya ce.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in Baffa banyi niyar sanar da ku komai ba har sai na kammala abinda nakeyi, amma wannan maganar da kayi tasa jikina yayi sanyi, tabbas akwai abinda nake shirinyi, kuma ina da niyar sanar daku nan gaba kad'an, amma dole yanzu na fad'a maku.
Dama shari'ar marigayi Naseer ce nakeso zan dawo da ita domin abi masa hakkin sa sabo.... Dakata Rafeek! Ummansu ta fad'a cikin karaji, da sauri ya d'ago kai yana kallonta.
Hawaye ne suka gangaro a fuskarta tacigaba da fad'in ban amince maka ka tado wannan maganar ba, abinda yawuce shekara da shekaru meye amfanin tadoshi, wato acan baya k'arfin ka be kawo ba shiyasa da mukace abarshi ka hak'ura, yanzu kuma kana ganin kayi kwari ka isa tsayawa da k'afafuwanka shine zaka tado mana da tashin hankalin da muka manta dashi, wallahi Rafeek ka fita a idona, zan sab'a maka akan wannan maganar, babu wanda ya isa ya maido da wannan maganar baya, domin nasan ruhin Naseer yana can cikin salama.
Matsowa Rafeek yayi yana had'a hannu, magiya zai fara mata ta daka masa tsawa dole tasa yayi shiru. Girgiza kai Baffa yayi yana fad'in shiyasa jikina be bani ba kaji nayi maka wannan tambayar, yanzu Rafeek so kake kaima mu rasaka kamar yanda muka rasa Naseer? Allah ya fimu sanin wad'an da suka aikata masa haka ka barsu dashi zeyi maganinsu, idan ma ka shigar da k'ara inaso kaje ka soketa, domin babu wanda zai sani shiga kotu, ko kai babu inda zakaje.
Hawaye ne suka zuboma Rafeek, kai yashiga girgizawa yana fad'in dan Allah Baffa ku saurare ni, wallahi ba saboda Naseer zanyi wannan abun ba, inaso a tabbatar da gaskiya shiyasa na fara sako maganarshi amma.... Tashi kabar gidan nan Rafeek, kuma kada ka sake shigowa matuk'ar da wannan maganar zaka zo. Umma ta fad'a cikin dakiya.
Kallon Baffa yayi yana hawaye. Kai ya jinjina masa hakan yasa ya fice yana share hawayen idonshi, yanzu ya zeyi dasu Ra'eez, duk wani sa ransu akanshi ne, sai da komai yazo k'arshe za'a hanashi.
Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga Ra'eez, saurin seta kanshi yayi kafin ya d'auka. Bayan sun gaisa Ra'eez yace Yaya mun gama rubuta k'arar da za'a shigar, zan kawo maka kagani zuwa gobe juma'a sai ashigar da ita zuwa litinin ashiga kotu.
Runtse ido yayi cikin k'arfin hali yace Ra'eez kai da Jabeer ina so anjima kuzo inaso muje wajen su Baffa ne. Ra'eez yace Yaya kamar akwai matsala ko? Murmushi yayi yana fad'in bakomai kawai kuzo. Jiki a sanyaye Ra'eez yace Allah ya kaimu.
Kashe wayar yayi yana goge hawayen idonshi, dole ya sako su Ra'eez a wannan maganar idan ba haka ba Umma bazata tab'a amincewa ayi shari'ar ba, shi kuma yana so kowa yasan cewar ba Abbun Ra'eez kad'ai suka kashe ba, yafiso kowa yasan yanda suka aikata mugayen abubuwa. Motarshi ya nufa ya bar gidan.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
3⃣9⃣
Guiwa biyu Ra'eez yasa a k'asa ya had'e hannuwansa biyu yayin da hawaye suke ambaliya a idonshi, matsawa kusa da Baffa yayi bayan daya gama basu labarinshi, cikin kuka mai tab'a zuciya da raunanniyar murya yake fad'in Baffa na roke ku da girman Allah ku bar Yaya ya tayani wannan yakin, zuciyata tana da rauni, Allah shine yasan hakan shiyasa ya had'ani da Yaya tare da Jabeer, tabbas Yaya jigo ne agareni, shid'in tsani ne wanda zai taimaka mani zuwa ga kai matakin da nake fatan kaiwa da dad'ewa, matuk'ar kuka janyeshi acikin wannan shari'ar nasan zuciyata zata raunana, duk wani sa rai da nake dashi zan rasa shi, na amince a janye shari'ar Naseer amma dan Allah ku bar Yaya ya tayani kwatoma Ummu na hakkinta ko hakan zai zamo silar samun lafiyarta.
Shiru yayi yana wani irin kuka mai ban tausayi. Gaba d'aya falon shiru yayi babu wanda baya kuka, duk dauriya irin ta Baffa sai da ya zubar da kwalla.
Umma ce tayi saurin kamo hannun Ra'eez tana share masa hawaye yayin da nata suke zubowa. Girgiza kai tayi tana fad'in ban tab'a jin labarin daya tab'a zuciyata irin naka ba, ya isa kadena kuka, daga yau ka zama 'Dah na, haka zalika ga Baffansu nan ya zam mahaifinka. Kallon Rafeek tayi tana fad'in na amince maka ka tayashi tabbatar da gaskiya, shari'ar Naseer kuma baza'a fasata ba, kushigar da k'aran aranar litinin za'ayita.
Tabbas ayanzu bazan yafema kaina ba idan naki amincewa ayi wannan shari'ar, dan haka na amince maka. Runtse ido Rafeek yayi hawayen farin ciki suna zubo masa.
Murmushi Jabeer ya saki yana rungume Rafeek. Hannu Baffa yasa yana goge idonshi yace tabbas duniya babu gaskiya, ashe dama wad'an nan azzaluman sune sukayi silar mutuwar Mahaifinka? Tabbas nasan mahaifinka mutum ne mai gaskiya, duk da bani da alak'a dashi amma zuwanshi ya samar mana kwanciyar hankali, duk wasu masu shigo da haramtattun kaya sai da yayi maganin su, lallai barin irin su Alhaji Barau a duniya babbar illa ne, dan haka nima na amince a tabbar da wannan shari'a.
Gaba d'ayansu farin ciki ya rufeso haka suka shiga yi masu godiya. Umma tace babu komai Allah yayi maku albarka, kuma yayi maku jagora akan wannan aiki da zaku fara, insha Allahu sai naga yanda k'arshen azzalumai zai kasance.
Bayan sun fito Rafeek ya kallesu yana fad'in yanzu kam hankalina ya kawanta, shiyasa dama nace kuzo nasan zuwan ku ne kad'ai zaisa su Baffa su amince dani, dan haka Ra'eez akai wannan takardar kotu, nasan kana da basira ina so kasan yanda zakayi magana.
Ra'eez yace insha Allahu. Sallama sukayi mashi suka wuce cike da farin ciki. Kai tsaye gidan su Jabeer suka wuce, acan suka ci abinci, sai da suka zauna suka huta kafin suka wuce gidan su Rumaisa.
*** ****
*Liberty Radio*
'Yallab'ai barka da zuwa. Kwamishna yace yauwa sannu Rafeek, amun afuwa aiki yamun yawa shiyasa ban samu zuwa da wuri ba hakan yasa na kira ka nace sai da dare zan samu shigowa.
Murmushi Rafeek yayi yana fad'in har na cire ran zaka zo, dama aikin dare nakeyi yau shiyasa tunda nashigo da safe naga baka zo ba kawai na fita sai kuma ga kiranka.
Gyara zama yayi yana fad'in ai bana son karya alk'awari, shiyasa nace maka sai zuwa dare nasan lokacin na samu saukin aikin. Rafeek yace barka da zuwa, ruwa ya aje masa tare da zubawa.
Amsa yayi yana fad'in nagode. Bayan ya shanye ya kalli Rafeek yana fad'in sai mu fara kada na samu wani kiran. Murmushi Rafeek yayi ya tashi yana fad'in bismilla dama kafin kazo mun shirya komai.
'Yallab'ai gidan redion mu yana maka barka da zuwa.
Murmushi Kwamishna yayi yana fad'in yauwa barka dai.
Rafeek.. Jama masu sauraron mu barkan mu da sake had'uwa a wannan gidan redion namu mai albarka, ayau muna da babban bako wanda ya kawo mana ziyara kuma zamuyi fira dashi, mai sauraro idan kana biye damu zakuji sunan bakon namu da kuma yanda firar tamu zata kasance, kubiyomu a cikin shirin namu.
To 'Yallab'ai mutane zasu so suji cikekken sunan ka da kuma irin matakin da kake ayanzu saboda kowa ya sheda ka.
E to, ni dai sunana Bello Kabir, kuma nine kwamishnan 'yan sanda a garin lagos.
'Yallab'ai nasan kafin ka kawo wannan matsayin kasha gwagwarmaya har zuwa lokacin da Allah ya kawo ka wannan matsayin, ko zaka fad'ama masu sauraron mu irin gwagwarmayar daka sha?
Kwarai kuwa nasha gwagwarmaya kafin nazo wannan matsayi, kuma dama kowa yasani kafin aji dad'i dole sai ansha wuya, kamar yanda kowa ya sani aikin 'Dansanda aiki ne na jihadi, aiki ne wanda dole sai ka bada k'arfin ka, dukiyar ka da kuma lokacin ka, duk wani d'an sanda yana fuskantar kalubale arayuwarsa, wasu ma suna rasa rayukansu akan wannan aikin, kamar yanda na bada misali da dukiya, tabbas akwai wani abun idan yazo maka dole sai kayi amfani da dukiyar ka kafin kaci nasara akanshi, haka ma lokaci, duk wani d'an sanda beda lokacin kanshi matuk'ar yasa aranshi k'asarshi yakema aiki, wani lokacin koda kana hutu zaka iya samun kira daga sama kuma dole kaje, shiyasa nace maka aikin d'an sanda aiki ne na sadaukarwa, d'an sanda beda lokacin kanshi sai lokacin al'umma domin su yake ma aiki, hakki ne ya rataya akanshi dole ne ya bama kowa tsaro, to da haka dai mukayi ta fafatawa da dad'i ba dad'i har Allah ya kawo ni wannan matsayi.
Jinjina kai Rafeek yayi yana fad'in gaskiya dole na sara maka, tabbas aikin d'an sanda babban aiki ne, yakamata mutane su k'ara jinjina ma 'yan sanda kuma su k'ara basu muhimmanci domin suna da muhimmanci arayuwar mu baki d'aya.
Kwamishna yace nagode, amma ina ganin mutane kad'an ne suke fahimtar muhimmancin mu, domin kuwa masu zagin mu sunfi yawa.
Murmushi Rafeek yayi yana fad'in tabbas nasan akwai masu zagin 'yan sanda da yawa, sai dai kuma wasu suke b'ata wasu, da yawa mutane suna ma 'yan sanda kallon masu cin hanci da rashawa, wannan bakin fentin har yanzu yaki goguwa a wajensu, kuma wasu ne suka jawo wannan abun, duk yanda kuke aiki matuk'ar ana samun masu k'arb'ar cin hanci to al'umma bazata tab'a ganin muhimmancin ku ba, shiyasa ake son arik'a kamanta gaskiya.
Kwamishna yace wannan shine babban abinda muke yaki dashi, amma har yanzu an kasa dainawa, saboda mutane suna d'aukar cin hanci shine abinda zai rik'esu.
Murmushi Rafeek yayi yana fad'in 'Yallab'ai a matsayin ka na wanda yayi shekaru yana aikin d'an sanda, nasan dole akwai wani babban kalubalen daka fuskanta wanda bazaka iya mantawa dashi ba, ko zaka fad'ama masu sauraron mu irin kalubalen daka fuskanta?
Kwarai kuwa akwai kalubale da yawa dana fuskanta, kowa yasan idan kana irin aikin mu akwai kalubale sosai akan mu, kuma nasha wahala sosai, amma juriya da jajircewa irin