Advertisements
Chapter 33 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   33 / 54

96K to 99K   out of 160.3K words

Ra'eez, Allah ya baka abinda kake nema duniya da lahira, ka bani account d'inka ina so nayi maka alheri.


Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in ka barshi, badan kud'i nayi maka ba, ko a iya abinda kamun ka biyani. Sameer yace nagode sosai, Jabeer nagode Allah ya huta gajiya.


Jabeer yace amin Allah ya k'ara tsare gaba, sai a daure a nemo mata kafin muma muzo mu wuce ka. Dariya suka sa gaba d'aya. Sameer yace insha Allahu zanyi kok'arin haka nima nasan na kusa tsufa damma bani da jikin kiba dan nayi arba'in idan ban wuce ba.


Ra'eez yace to Allah ya kawo ta gari. Murmushi Sameer yayi kwalla ta cika idonshi yana fad'in bazan ce maka komai ba domin kace Allah, amma bana tunanin zan samu mace tagari tunda ban kasance nagari ba.


Ra'eez yace kada kayi saurin yanke hukunci domin Allah baya duba da haka, abinda yake so ka tsarkake zuciyarka. Sameer yace insha Allahu nagode.


Suna shirin sallama wata mota ta tsaya a kusa dasu, kid'an da yake tashi ne a ciki yasa hankalin su ya koma kanta.


Wani gaye ne ya fito sanye da k'ananun kaya masu matuk'ar tsada a jikinsa fuskarsa sanye da wani bakin glass mai tsadar gaske. Rufe motar yayi yana taunar cingam.



Saurin cire glass d'in yayi yana fad'in Yaya Sameer, saurin k'arasowa yayi yana shafa kai. Murmushi Sameer yayi yana fad'in Fawwaz dama ka dawo k'asar nan? Risnawa yayi yana gaishe shi.


Hannu Sameer ya mik'a mashi suka gaisa, juyawa yayi yabama su Ra'eez hannu. Sameer yace lallai Fawwaz ka zama babban yaro da yawa ga abokin ka can hada yara biyu.



Fawwaz yace ai bansan meya shiga kan Adnan ba Yaya, ko kai bakayi aure ba sai shi, lokacin muna secondary kamar wayayye amma muna rabuwa shikenan yanemi zama ustaz, bansani ba ko jami'ar da yayi a Nija ne ya sashi komawa haka, shiyasa naji dad'i lokacin da Dad yace waje zai kaini karatu, koda na gama kawai nayi zama na acan sai wancan watan ne na dawo shima Mom ce ta matsa na dawo ta gaji.


Sameer yace ai gashi ya zama Baba ya bar ka, ina d'ayan abokin naku? Fawwaz yace Allah sarki Sufwan, har ka tuna mani dashi, ina can Adnan yake fad'a mani mutuwar sa domin kowa yasan mu three stars ne a Kings college amma mutuwa ta rabamu dashi daga zazzab'i na kwana biyu, gaskiya naji mutuwarsa sosai.


Sameer yace Allah yajik'ansa, lafiya kazo kotu? Fawwaz yace Dad ne ya aiko ni wajen Abba Barau. Kai Sameer ya jinjina yana fad'in ai kotun taku ce.


Murmushi Fawwaz yayi yace kai Yaya. Sameer yace emana, ai na d'auka kaima zaka biyo Dadyn ka ko lauya ka karanta ai yayi. Fawwaz yace Yaya wannan karatun ba irin namu bane.


Sameer yace to Allah ya taimaka, ka gaishe da mutanan gidan. Fawwaz yace zasuji agaishe da Adnan amma zanje naga Yaranshi. Sameer yace zasuji.



Sallama yayi masu ya wuce yana tafiyar 'yan gayu. Murmushi Sameer yayi yana girgiza kai. Jabeer yace dama wannan shine Fawwaz d'an tsohon Alkalin kotun nan? Sameer yace shine fa, kai duniya babu gaskiya, idan kana da iko da kud'i baka da matsala.


Ra'eez yace ai shiyasa mutane suke son kud'i. Sameer yace yaron nan fa alokacin suna makaranta har kisan kai ya tab'ayi amma da yake Mahaifinsa babba ne ko maganar ba'a tada ba, agaban su Adnan yayi kisan sai dai kasancewar su aminan juna ne yasa suka rufa masa asiri, kuma Mahaifinsa ya basu kud'i masu yawa shikenan sukayi shiru alokacin Adnan yana Niga, uhm shikenan maganar ta mutu, yaron ma da sukace ya gansu shima babu labarinsa sai gawarsa aka tsinta, silar haka aka tura Fawwaz waje karatu.


Shiru Ra'eez yayi yana tunani, da sauri ya kalli Sameer yana fad'in a wace shekara akayi abun? Sameer yace lokacin dai suna aji shidda dan har sun fara jarabawar fita, ina ganin kamar 2008 ne, E a lokacin Adnan ya kammala makarantarsa.


Jikin Ra'eez ne yayi sanyi, tabbas wannan labarin yana da had'aka da yaron da Kawu ya bashi labari, amma zaibi komai a hankali zai had'a kan zaren da sannu.


Sameer yace bara na wuce na tsaya ina cinye maku lokaci. Jabeer yace shikenan mungode sai munyi waya. Hannu ya basu yawuce.



Dafa Ra'eez Jabeer yayi yana fad'in lafiya kuwa Ra'eez? Ajiyar zuciya Ra'eez yayi yana fad'in me ka gani? Jabeer yace tun lokacin da naji an fad'i mutuwar wannan yaron ka tambayi shekarar da akayi abun naga kamar ka canza.


Murmushi Ra'eez yayi yace kawai abun ne ya bani tsoro, dalilin tambayar shekarar ina so nasan shekarunsu har suka iya aikata haka.


Jabeer yace to yaran masu kud'i meye basa aikatawa, kai dai kawai ayi sha'ani. Ra'eez yace Allah ya kyauta. Wayarsa ce tayi k'ara, yana dubawa yaga ansa Journalist, murmushi yayi dan ya gane Rafeek ne.


Bayan sun gaisa Rafeek yace ko anjima bayan isha'i kana da lokaci na kawo maka ziyara? Ra'eez yace ina nan kuwa, zan turo maka da kwatencen. Rafeek yace to nagode.


Kallonshi Jabeer yayi yana fad'in kai da wa? Ra'eez yace wani d'an jarida ne yake son mu had'u bayan isha'i. Jabeer yace sarakan tambaya, sai ka kula kada su saka fad'ar wani abun kasan su da wayon tsiya ga dabara.


Ra'eez yace ai tsakanin su da 'Yan sanda da kuma mu ana fafatawa, domin kowa yana da ilimin fasaha da 'yan dabaru, dan haka kada ka damu zan iya bi dashi. Jabeer yace ai nasanka.


****


Bayan sun tashi daga aiki sukayi sallama da Jabeer kowa ya shiga motarsa ya tafi. Har Ra'eez ya d'auki hanya wayarsa tayi k'ara, yana dubawa yaga Kawu Datti, saurin tsayawa yayi ya kashe wayar sannan ya kirashi.


Cike da farin ciki yace gani nan waje Kawu bara na matso. To shikenan bara na jiraka anan sai ka zo. Kashe wayar yayi cike da farin ciki.


Kwankwasa k'ofar da akayi yasa yayi saurin bud'ewa. Shigowa Kawu Datti yayi ya zauna ya rufe k'ofar. Kallon Ra'eez yayi kafin ya d'age rigarsa ya zaro kundu ya mik'a ma Ra'eez yana fad'in ban tsaya dubawa ba kawai na d'auko maka shi kaje ka duba amma ka maidoshi da wuri, Allah yasa kana da abun photo copy dan bana son kaje wani waje ayi maka idan baka dashi gara ka kwafeshi kawai.


Ra'eez yace nagode Kawu Datti, kuma babu wanda zai san dashi ina da komai a gidana zanyi na maido maka shi gobe. Kawu Datti yace ina maka fatan nasara.



Kud'i Ra'eez ya ciro ya mika masa yana fad'in amin. Girgiza kai Kawu Datti yayi yana fad'in idan na amsa tamkar cin hanci ka bani.


Ra'eez yace wallahi Kawu ba cin hanci bane, ai tsakanin mu babu wannan, ka d'auke ni tamkar d'anka dan Allah Kawu.


Murmushi yayi ya amsa yana fad'in nagode sosai. Ra'eez yace nima nagode. Sallama yayi masa ya fice daga motar ya koma ofis. Hamdala Ra'eez yayi yawuce gida cike da murna.


****


Sai da suga gama firar soyayya da Rumaisar sa kafin yayi masu sallama dan yasan Rafeek ya kusa zuwa. Har bakin mota ta rakashi sai shagwab'a take masa bata so ya tafi. Ra'eez yace kiyi hak'uri ai kullum muna tare, kicigaba damun addu'a domin nakusa fara bincike, dan haka dole ki aramun lokacinki.


Rumaisa tace bakomai in dai lokaci nane na baka domin naka ne, kuma ina maka fatan nasara, addu'a kuma kullum ina maka. Murmushi yayi yace nagode Pretty na. Sallama sukayi yawuce.


A hanya Raheena ta kirasa, kin d'auka yayi dan baya son damu yasan kuma daya d'auka zata tsaidashi da surutu. Ganin ta cigaba da kira yasa ya d'auka, ko magana batayi ba yace mata yana hanya ta bari wajen 11 zasuyi waya. Kashe wayar yayi yana tsaki ya k'ara gudun motar.


***


Lemu da ruwa ya aje masa yana fad'in sannu da zuwa Yaya. Murmushi Rafeek yayi yana fad'in yauwa sannu Ra'eez, yau dai bani da aikin dare nace zan zo mu gaisa sosai.


Ra'eez yace ai naji dad'i sosai, naso na fara kai maka ziyara gashi har ka rigani. Rafeek yace ai bakomai, na fad'a maka babu babba a abota.


Jinjina kai Ra'eez yayi ya mik'a masa ruwan daya zuba yana fad'in gidan gauro ne babu abinci. Dariya Rafeek yayi yace haba ai babu komai, wata rana idan kayi auren zan zo naci.


Kallon Ra'eez yayi yana fad'in gaskiya ka burge ni a shari'ar da kukayi jiya, kuma nayi mamaki da kayi masu haka, sai nake tambayar kaina dama kasan gaskiya ne yasa kace kaine zaka tsaya masu? Girgiza kai Ra'eez yayi yana fad'in Mahaifin yarinyar da ya fad'a mani abinda ya faru yasa nace zan taimaka masu, duk da alokacin na riga na amshi tayin su Sameer.


Rafeek yace ai ka kyauta sosai Allah ya biyaka, shima Mahaifin Halima ya burge ni, duk da yana talaka amma ya iya neman hakkinsa, wallahi ina son naga an zalunci mutum ya tsaya akan neman hakkinsa.


Ra'eez yace nima ina son irin mutane masu dakakkiyar zuciya haka, shiyasa nace zan taimaka masu sosai.


Rafeek yace shiyasa a shekarun baya da aka kashe K'ani na naso mushigar da k'ara amma Baffa yace baya so dole muka hakura, duk da alokacin ina makaranta amma naso ashigar da k'ara.


Ra'eez yace Allah sarki, ashe kaima an kashe maka wani, to Allah yaji k'ansa. Rafeek yace amin, har yanzu inajin d'acin mutuwar Naseer, yaro yana shirin kammala secondary d'insa amma aka samu wasu suka kashe shi, kamar marar gata haka aka wurgar da gawarsa.


Ra'eez yace wayyo Allah ya saka masa, yana gab da fara sabuwar rayuwa suka katse mashi ita, domin duk wanda ya gama secondary alokacin yake fara shirya burinsa.


Rafeek yace wallahi kuwa, a Kings college yake har sun fara jarabawa aka kashe shi, a shekarar su biyu aka kashe a makarantar kuma duk ajinsu d'aya.


Saurin kallonshi Ra'eez yayi yana fad'in a wace shekara ne Yaya? Kallonshi Rafeek yayi yace shekarar 2008 ne, ai bazan iya mantawa da wannan shekara ba, alokacin ina jami'a.


Shiru Ra'eez yayi jikinsa yana tsuma, runtse ido yayi yana tasbihi ga Allah, tabbas Allah ya fara haska masa akan shari'ar da zai gabatar, domin ayau ya fara had'uwa da abubuwan da sukayi had'aka da rayuwar Abbunsa, tabbas yana buk'atar natsuwa yayi dogon nazari, dole yaje kano yayi shawara da Abbah akan Rafeek, domin yaji ajikinsa shid'in zai taimaka masa da wani abu, yana jin zai iya bari yasan wayeshi da kudirinsa, amma idan Abbah be amince ba shikenan zaiyi yakin shi kad'ai.


Dafashi Rafeek yayi yana fad'in Ra'eez lafiya kuwa? Ajiyar zuciya ya saki yana fad'in Yaya abun ne akwai tausayi, wallahi bana so naji an kashe mutum, kawai ina hango yanda mutum zaiji alokacin da ake kashe shi, Allah yajikansu da rahma.


Rafeek yace amin. Amma Ra'eez ba anan garin kake ba ko? Ra'eez yace a Kano nake aiki ne ya maido ni nan. Jinjina kai yayi yana shirin jefo masa wata tambayar wayarsa tayi k'ara, yana dubawa yaga Baffansa ne.


Bayan ya gama wayar ya kalli Ra'eez yana fad'in Baffa ya katse mana fira, wai yana nemana yanzu. Ra'eez yace kai amma banji dad'i ba muna ta firar mu. Rafeek yace bakomai idan nasamu lokaci zan dawo dan bana so mu had'u a ofis d'in ku ko namu dan kowa yasan su waye mu, da an gammu tare kowa zai fara tunanin wani abu, dan haka idan ka samu lokaci idan zaka kawo mani ziyara a gidana zakaje.


Ra'eez yace insha Allahu nagode sosai. Tashi yayi yana fad'in nima nagode. Har bakin mota ya rakashi, sai da ya tafi sannan ya rufe gidan, kundin da Kawu Datti ya bashi ya d'auka ya nufi d'akin kayan aikinsa domin ya fara gamawa da su.


Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:40 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*



3⃣2⃣


A wannan dare Ra'eez kashe wayarshi yayi dan baya son damu, sai da ya gama copying komai kafin ya maida komai yanda yake yasa a leda dan kada ya manta, d'akinshi ya koma ya fara duba takardun.


A hankali ya gama karanta komai, ya mai-maita yafi so ukku, hawaye ne kawai suke zuba a idonshi, yana kallon abun kamar yana wajen yake faruwa, jiyake ina ma shine lauyen da yayi shari'ar a wancan lokacin, domin ga hujjoji nan da yawa daya kamata akare Kawu dasu amma ba'ayi amfani dasu ba, tabbas yasan lauyen daya kare Kawu sarewa yayi alokacin shiyasa be kula da hujjojin ba.


Jin kansa yana ciwo yasa ya tattara komai ya tura k'asan gado dan yasan anan ne kawai zasu b'oyu, duk da shi kad'ai ne agidan dole ya fara b'oye duk wata sheda tashi saboda ayanzu zai fara fuskantar kalubale saboda da manyan mutane zai gwabza, zesa rayuwarsa cikin had'ari, idan yana da tsawon rayuwa shikenan, idan kuma akan kwato ma Mahaifinsa hakkinsa zai rasa ransa a shirye yake daya bada ranshi.


Bayan ya adana komai ya kwanta yana tunanin ta yanda komai zai kasance da haka har bacci yayi gaba dashi.


**** ****


Washe gari tunda wuri ya isa ofis, sai da ya bama Kawu Datti kundin yayi ta masa godiya, sosai Kawu Datti yaji dad'i, hankali kwance yaje ya maida inda ya d'auko su.



Bayan ya rage aikin da yake gabanshi ya samu ya fita dan yaje ya d'auko Halima su gama komai da wuri. Babu b'ata lokaci suka kammala komai cikin lokaci.


Sai da ya maidata gida sannan ya koma ofis. Yana shiga yayi turus yana kallonta zaune a saman kujera Jabeer ya kawo mata lemu tana sha.


Saurin tashi tayi tana sakin murmushi, matsowa tayi tana fad'in D. sannu da dawowa wallahi na kasa hakurin rashinka shiyasa nazo, tun d'azu ma naso nazo Momy tace na bari sai anjima.


Murmushi Ra'eez yayi ya ratse ta yawuce ciki. Zama tayi tana fad'in na manta ina kwana? Ra'eez yace lafiya lau, daga shigowata ba gaisuwa kin rufeni da surutu.


Hannu tasa abaki tana fad'in wallahi mantawa nayi kewarka ce tamun yawa shiyasa duk na rud'e. Ra'eez yace ai na fad'a maki ina da aiyuka agabana.


Raheena tace duk da haka D ko waya ne sai ka kirani, bakasan yanda nake shiga damuwa ba idan banjika ba, dama kai ba kirana kake ba ni kuma na kira kace kana aiki.


Ra'eez yace daga yau kada ki sake zuwa wajen aiki na, duk macen da take iya bin namiji to bata da daraja a idon kowa, kuma ni bazan iya auren macen da take bina ba, domin zan rik'a ganin kowama haka kike masa.


Saurin tashi tayi tana fad'in Allah ban tab'a bin kowa gidanshi ba, kaima dan ina sonka shiyasa na biyoka amma kayi hakuri bazan sake ba. Kai ya d'aga ya jawo wasu takardu yana fad'in hakan zaifi maki.


Jabeer ne yashigo hannunsa d'auke da leda da alamu wani abu ne a ciki. Tsaye yayi yana kallon Ra'eez. Jaka Raheena ta d'auka tana fad'in Jabeer zan wuce.


Saurin kallonta yayi yana fad'in ban gane ba, keda kikace mun wuni kikazo mana taya zaki tafi kuma? Murmushi tayi tana kallon Ra'eez tace dama Momy ce tace nazo zata aike ni.


Kallon Ra'eez Jabeer yayi yana murmushi. Kauda kai yayi yacigaba da aikinsa. Jabeer yace shikenan ga wannan sai ki tafi dashi.


Amsa tayi tana godiya. Jabeer yace ki gaishe da Momy sai mun leko, Yallab'ai sai kaje ka rakata ai. Harara Ra'eez ya aika masa.


Raheena tace haba Jabeer ya kake son bama D wahala bayan yanzu ya dawo, ka barshi ya huta, kallon Ra'eez tayi tana fad'in D kayi aiki lafiya amma kada ka matsa ma kanka dan Allah.


Murmushi yayi yana kallonta, sai kuma ta bashi tausayi ganin yadda tayi kok'arin kareshi a wajen Jabeer, tabbas yasan zuwa yanzu Raheena ta canza sosai.


Tasowa yayi yana fad'in nagode Raheena da ziyara ki gaishe da Momy idan na samu lokaci zan zo nima. Murmushi ta saki tana jin wani dad'i.


Iyaka bakin k'ofa ya tsaya dan baya son kowa ya ganshi da ita. Sai da ta tafi kana yashigo ciki. Dariya Jabeer yasa yana fad'in Allah ya shiryeka abokina.


Tsaki Ra'eez yayi ya zauna yana fad'in zaka fara ko? Jabeer yace kai d'in ne sai a hankali wallahi kana wahalar da Raheena sosai.


Ra'eez yace ai sai ka rama mata. Jabeer yace ni na isa, kawai tausayinta nakeyi, saboda kai duk ta canza, kalli yanayin shigarta komai ya canza, wallahi tausayi take bani, irin su Raheena zasu iya yin komai akan abinda suke so, kuma ko aurensu kayi baka tab'a samun matsala dasu.


Tab'e baki Ra'eez yayi yana fad'in kaga malan ina da aiki gara kaje kayi hidimar gabanka. Rik'e baki Jabeer yayi yana fad'in lallai kam, ya Allah ka nuna mani ranar da Ra'eez ze fad'a son Raheena.


Tofar ta miyau Ra'eez yayi yana fad'in har abada wallahi, nan take idanuwansa suka canza kala yana b'ata fuska. Shiru Jabeer yayi cikin mutuwar jiki yake kallon Ra'eez.



Kasa rubuta komai yayi haka ya rufe takardun da k'arfi

33 / 54