Author : Marubuciyar Zamani Category : Complete Novels
yasan dai yashiga d'akinsa amma gashi a wajen 'yan sanda. Runtse ido yayi yana salati tunawa da abinda ya faru, kada dai sun kashe Ummun Ra'eez? Saurin sa hannu yayi a wuyansa, zafi yaji a wajen dan har yayi fushi saboda yakushin da sukasa Ummun Ra'eez tayi masa, a hannunsa yana jin shatin faratan ta.
Girgiza kai yashigayi hawaye suna zubo masa, tabbas yasan yashiga tsaka mai wuya Allah ne kad'ai zai iya fitar dashi, domin wannan abun daya faru yasan duk shirin su Alhaji Marusa ne. Dafe kai yayi yana kuka, ko a wane hali Halima take ciki yanzu? Jin motsi yasashi saurin d'agowa.
Wani d'an sanda ne yazo wajenshi dan yaga beyi sallah ba kuma shi zai tafi shine ya matso yaji ko yana da buk'atar yayi sallah, dan tunda aka kawoshi jiya yana zaune a ofis kawai yaji ya tausaya mashi, yanayin da aka kawoshi yasan akwai abinda ya sha ko kuma akasa mashi.
Saurin tashi Malan Sani yayi yana fad'in dan Allah inaso nayi sallah kaga har gari yayi haske sosai. Murmushi d'an sandan yayi yana fad'in ai tun d'azu naga kana bacci shiyasa ban tasheka ba, fito ga wajen sallah can.
***
Mota ce ta sauke Alhaji Mansur da Matarsa a k'ofar gidan Alhaji Maiwada saboda ta jirgi suka zo. Idanuwan Maman Labiba har sun kumbura saboda kuka, shikanshi Alhaji Mansur idanuwansa sunyi ja saboda ba k'aramin tashin hnkali yashiga ajiya ba.
Isowar Alhaji Musa ne yasa suka k'arasa cikin gidan saboda da suka zo basu shiga ba. Da sauri Madu ya taso yana masu sannu da zuwa, shima duk jikinsa a sanyaye yasha kuka.
Bayan sun gama gaisawa suka jajanta abinda ya faru, anan Alhaji Mansur yayima Alhaji Musa godiya sannan yace su wuce asibitin domin a gama komai a basu gawar Alhaji ayi masa sutura.
Alhaji Musa yace shikenan bara na d'auko mota ta sai mutafi, zansa a kawo tabarmi saboda zaman gaisuwa, Madu sai ka gyara cikin rumfar can idan suka kawo sai a shimfid'a. Kai Madu ya d'aga yana share kwallah.
***
Sosai Abubakar da Moses suka tsorata da abinda sukaji, gashi su Peter basu kyalesu haka ba sai da suka basu wahala sosai, domin a wajensu suka kwana, sun jigata sosai, haka kuma sunyi kukan mutuwar Alhaji Maiwada da Malan Hassan, Abubakar yanaji kamar laifinsa ne, da be sako Malan Hassan a cikin wannan abun ba da haka bata faru dashi ba, gashi babu halin yaje ya sanar da Iyalinsa yanzu za'a tsareshi ya nuna gawarsa kuma besan inda take ba, hakan kuma zai sashi cikin matsala,, dole ya bar abun sai dai Allah ya basu hak'uri.
Shigowar Lucky da Peter ne yasa sukayi saurin kallon su. Matsowa Lucky yayi fuska babu annuri yana fad'in kunci sa'a ba'a bamu umarnin kashe ku ba, kashedi kawai akace muyi maku, nasan zuwa yanzu jikin ku ya fad'a maku abinda muke nufi, dan haka zaku samu takardar canjin wajen aikin ku da zaran litinin tayi, matuk'ar kuka sake nuna kan ku ko kuma wani yaje neman wata sheda akan ku zamu kashe kowa naku.
Cike da tsoro Moses yace wallayi aboki bazaka sake gani na a lagos ba, tsautsayi ne yasa nayi haka, amma na goge komai bani da wata sheda kada ku kashe ni.
Abubakar yace insha Allahu bazaku sake ganina a lagos ba koda da yawo, kuma babu abinda zan fad'a, bazan barima asan nasan wani abuba, dama bani da iyali anan suna can dan haka ayau zan bar garin.
Murmushi Lucky da Peter sukayi kafin suka kwance su, hannu suka rik'e saboda tsamin da yayi masu, ga kansu da yake ciwo saboda abinda suka shak'a masu. Haka suka d'aure masu fuska suka fita da su.
***
Kuka kawai Maman Labiba takeyi alokacin da taga gawar Alhaji Maiwada, Alhaji Mansur kanshi kasa daurewa yayi, juya baya yayi ya saki wani irin kuka, Alhaji Musa ne yayi ta bashi baki.
Gaba d'aya gawar Alhaji ta canza kama, fuskarsa duk da kumbura, wuyansa yayi wani irin ja gwanin tausayi. Brr. Barau ne tare da d'an sandan da yake kula da case d'in Alhaji suka shigo.
Hannu suka bama su Alhaji suka gaisa, kallon Alhaji Mansur yayi yana fad'in sunana Brr. Barau, kuma nine lauyen da zan kula da wannan shari'ar ta Alhaji Maiwada, domin nine lauyensu na wajen aiki, bazamu tab'a bari jininsa ya zuba abanza ba, duk wanda yake dasa hannu akisanshi sai mun kamashi, to abun yazo da sauki domin an kama direbansa da ake zargin shine ya kashe shi, saboda an kamashi da laifin yima matar Alhaji fyad'e har yayi sanadiyar zubewar cikinta, yanzu haka yana kulle.
Tunda ya fara magana Alhaji Mansur ya zuba masa ido har sai da Brr. Barau ya tsargu da kallon da yake masa. Gyaran murya yayi yana fad'in kada ka damu Alhaji zanyi aiki sosai akan mutuwar Alhaji Maiwada.
Kauda kai Alhaji Mansur yayi yana jin wani irin tukukin bakin ciki, yasan komai akan Brr. Barau, domin babu abinda Alhaji Maiwada ya b'oye masa, amma kaji saboda rainin hankali wai shine zai tsayama Alhaji, gashi sun kullama Malan Sani sharrin da babu mai fitar dashi sai Allah, tabbas yasan sune suka aikata hakan, amma iya abinda ya sani a baki ya tsaya beda sheda ko kad'an a hannu, ita kuma kotu da sheda take amfani, dole yasa ido yaga yanda komai zai kasance, idan aka cutar da Malan Sani sai dai Allah ya saka masa.
Muryar Alhaji Musa yaji yana fad'in bakomai Brr, mungode sosai, gaskiya ka kyauta da zaka tsaya domin a kwatoma Iyalan Alhaji Maiwada hakkinsu, domin har yanzu ita Hajiyar bata farfad'o ba, shi kuma wannan direba ayi masa hukunci dai-dai dashi domin hakan ya zama darasi a wajen 'yan baya.
Brr. Barau yace insha Allahu babu abinda zai gagara. Alhaji Mansur yace yanzu dai muna so a bamu gawar Alhaji muje mu suturta ta. Brr. Barau yace nima abinda yasa nazo kenan saboda nasan Alhaji Maiwada beda kowa a garinnan shiyasa nazo domin an fad'ama wajen aikinsu suna jira suji lokacin jana'izar domin suzo a suturtashi.
Dan sandan yace ai duk wani bincike mungamashi, duk wani abun daya kamata anyi dan haka zakuje wajen likita ku gama dashi sai abaku gawar, sannan motarsa nasa yarana su kaita gidanshi yanzu. Jinjina kai sukayi kafin suka nufi ofis d'in likita.
Haka aka gama komai aka basu gawar Alhaji Maiwada, acikin motar asibiti aka d'aukeshi saboda babban mutum ne, a motar Alhaji Musa suka tafi.
***
Kafin wani lokaci mutuwar Alhaji Maiwada ta yad'u, manyan mutane duk sun halarci k'ofar gidansa domin ayi masa sallah, 'yan wajen aikinsu gaba d'aya sun halarci wajen, Malan Bala sai kuka yakeyi yana tuna rabuwarsu da Alhaji jiya, ko kud'in daya bashi bai gama kashe su ba amma wai ya rasu.
Kafin wani lokaci an gama shirya Alhaji, haka mak'udan mutane suka taru aka sallaceshi, kafin Alhaji Marusa ya iso har an sallame, yana zuwa sai dai ya juya domin rakiyar kai gawa. Mr. Kallah kuwa yana gida sai sun dawo zai zo masu gaisuwa, gaba d'aya hankalinsa tashe yake, tunda Alhaji Marusa ya kirashi ya fad'a masa an kashe Alhaji yake jin babu dad'i aransa, amma babu yanda ya iya dole ya bar komai aransa tunda mai faruwa ta faru.
Hatta da Abubakar sai da yazo jana'izar Alhaji, duk da baya jin dad'in jikinsa amma haka yazo saboda yana tsoron rashin zuwanshi yasa a zargeshi musamman da mutane suka san suna shiri da Alhaji.
Bayan an dawo daga binneshi aka shiga yima juna gaisuwa, sauran abokan aikinshi wad'an da ba musulmai ba haka suka fara zuwa suna gaisuwa, Mr. Kallah ma yazo gaisuwa kuma ya zauna a kusa da Alhaji Marusa anan aka cigaba da zaman gaisuwa dasu.
Cikin gida kuwa Maman Labiba itace Uwar amsar gaisuwa, matan unguwa duk sunzo suna tayata zaman makoki, abinci kuwa azahar tanayi aka fara shigo dashi kuloli, abunka da birni sai dai akawo abinci daga waje, *sab'anin wani wajen da zaka iske masu mutuwa sune suke ciyar da 'yan zaman makoki, d'an abincin da suka samu sadaka kafin a share makoki mutane sun cinye wasu hada guzirin na gida*.
***
Sai da Ummu tayi kwana d'aya da yini kafin ta farka, Hajiya Amina matar Alhaji Musa tana zaune a gefenta tayi saurin tashi ganin tana motsi, hannu Ummu tasa ta dafe kanta, da k'arfi ta saki ihu tana kiran Abbu. Saurin matsawa Hajiya Amina tayi tana rik'eta.
Shigowar wata ma'aikaciya ne yasa Hajiya Amina ta matsa domin ta bata waje, ganin yanayin da Ummu take ciki yasa ma'aikaciyar tayi saurin danna wata alama, kafin wani lokaci sai ga likitoci sun shigo.
Fita Hajiya Amina tayi cike damuwa. Haka suka shiga duba Ummu, ganin ta kasa natsuwa yasa dole sukayi mata allurar bacci kafin suka gungurata zuwa wani d'akin gwaji.
***
Alhaji Mansur ne da Alhaji Musa suka iso da sassarfa dan Hajiya Amina ta kirashi shine suka taho, Alhaji Mansur yaso ya taho da matarsa amma baya so abar gidan abud'e saboda basu san halin wasu ba.
**
Zaune suke a ofis d'in babban likita. Bayan ya gama 'yan rubuce-rubuce ya d'ago kai yana fad'in agaskiya Hajiya ta had'u da lalurar tab'in hankali sakamakon dukan da akayi mata akai da kuma abinda yashiga zuciyarta na tsorata, sannan cikin jikinta ya zube, yanzu haka munyi mata allurar bacci saboda jikinta babu kwari muna buk'atar ta samu hutu shiyasa mukayi mata allura, idan ta samu saukin ciwon jikinta dole zamu maidata asibitin mahaukata wanda nine zan mayar da ita can saboda takasance matar Alhaji Maiwada, tunda na fahimci tana d'auke da wannan lalurar nayi alk'awarin zan kula da ita.
Salati Alhaji Mansur yayi yana fad'in Allah mungode maka da wannan jarabawa taka, ya Allah ga baiwarka nan Allah kada ka mayar da Ra'eez Maraya gaba da baya, ya Allah ka bata lafiya. Gaba d'ayansu sukace amin.
Alhaji Mansur yace amma likita ina da magana, inaso idan ta samu sauki zamu maidata Kano domin zatafi samun kulawa akusa damu, kuma haka ne kawai zanyi na kyautata ma Alhaji Maiwada, domin yanzu bani da burin daya wuce na rike iyalinsa, kuma na cika masa burinsa na barin garin nan da yayi niya.
Gyara zama likita yayi yana fad'in ban tari numfashin ka ba Alhaji, dama tunda naji Alhaji Maiwada beda 'yan uwa agarin nan nake jiran wani nashi yazo domin na nemi wannan alfarmar, naroke ka da girman Allah ka barni na samu wannan ladar, Alhaji Maiwada yana da muhimmanci agaremu, ta silarsa Yayana Alhaji Usman ya samu kayansa da aka sace suka fito tun yana farkon zuwa garin nan, Yayana tunda yaji wannan labari yace shine zai d'auki nauyin kud'in jinyar Matar Alhaji, ayau da muka gano matsalar da take ciki nayi alk'awarin zan kaita wajen abokina da yake kula da masu irin wannan lalurar, kuma acan asibitin zata zauna har Allah ya bata lafiya, sannan idan tana garin nan zatafi saurin dawowa hankalinta tunda anan abun ya sameta.
Shiru Alhaji Mansur yayi dan likita ya d'aureshi, ajiyar zuciya ya saki yana fad'in shikenan likita bazan hanaka aikata aikin alkhairi ba, nasan abubuwan alkhairin da Alhaji Maiwada yayi sune suka jawo masa haka, dama ance idan kana aikin alkhairi ko bayan mutuwarka aikinka yana nan, bakomai Allah ya baka lada, kuma zamucigaba da magana ta waya ina jin halin da take ciki.
Godiya likita yayi masu, anan sukayi musayar waya Alhaji Mansur yace da anyi sadakar ukku zasu tafi, kafin lokacin yana so su gana da wancan likitan. Murmushi likita yayi yana fad'in babu damuwa.
Alhaji Musa yace 'yan sanda sunzo nan kuwa likita? Likita yace sunzo tun a washe garin ranar, sun d'auki hoton shatin hannun Hajiya na dama wanda naga jini acikin k'umbarta, sai sukasa mukayi awon jinin da yake cikin farcanta muka basu sakamakon, sai dai sunce fyad'e akayi mata amma gaskiya babu alamun haka, kila dai garin yin fyad'en ne cikin ya zube, ganin jini yasa sukace fyad'e ne, amma gaskiya babu wani fyad'e.
Girgiza kai Alhaji Mansur yayi wani takaici ya turnuk'eshi, gashi dai yasan gaskiyar wasu al'amuran amma beda halin magana. Tashi yayi yana fad'in likita mungode sai mun had'u a kotu ranar litinin dan nasan bazasu ja shari'ar ba, idan angama da wuri zamu wuce saboda ranar ne sadakar ukku. Godiya yayi masu suka fita.
Alhaji Mansur yaso Hajiya Amina tazo su koma gida itama ta huta amma Alhaji Musa yace ai babu komai baza'a bar mai jinya ita kad'ai ba. Haka suka tafi bayan sun aje masu abincin da suka zo dashi.
Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne, Naira 200 kacal, ka tura Mtn card ta wannan lambar.. 08147669770, sai kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a wannan lambar ta k'asa, idan kuma transfer zakayi sai ka tuntub'e ni ta whatsapp a wannan lambar. 08028525263.*
1⃣7⃣
Zaune Alhaji Mansur da Maman Labiba suke a tsakar gidan Malan Sani yayin da Halima take jingine da filo Rumaisa tana gefenta gwanin tausayi.
Tunda aka tafi da Malan Sani washe gari ta tashi da rashin lafiya, makwabciyarta ce ma tashigo saboda ma'aikaciyar asibiti ce tazo su gaisa dan ta saba kullum sai tashigo sun gaisa kafin ta wuce, bayan ta shigo ta isketa cikin wannan yanayin hakan yasa ta tsaya sai da ta taimaka mata tayi wanka ta had'a mata shayi sannan ta koma gida ta kira mai aikinta suka kama Halima suka nufi asibiti.
Bayan anyi mata gwaji aka gano tana da ciki har ya kusa b'arewa sakamakon tashin hankalin data shiga, hakan yasa aka bata magunguna har yamma tana can, sai da matar ta tashi daga aiki kana suka dawo tare kuma ta hanata aikin komai har sai ta warke, taso ta barta a asibiti Halima tace bata so, shiyasa suka dawo, Mai aikinta tasa ta kawo masu abinci dan tace Halima kada tayi aiki.
Cike da tausayi Alhaji Mansur yake mata ya jiki tare da kwantar mata da hankali. Hannu tasa ta goge hawayen da suka zubo mata tana fad'in wallahi Alhaji sharri akayima Malan, tunda yashigo na gane ba'a hayyacinsa yake ba, taya za'ace Malan ne zai... Hannu Maman Labiba tasa ta rufe mata baki tana fad'in ya isa haka.
Alhaji Mansur yace yanzu kam bamu da wata sheda, duk da nayi magana da Brr. Kamal kuma shima yace sunyi waya da Alhaji akan yana so yaje suyi wata magana mai muhimmanci saboda zai shigar da k'ara, amma yace Alhaji bai riga ya bashi wata sheda da zai iya tsayawa da ita ba, kawai zaije ya tsaya ma Malan Sani idan Allah yasa basu da shedar da zata kada Malan Sani komai zaizo cikin sauki, idan kuma suna da ita sai dai Allah ya bimasa hakkinsa domin kotu da sheda take amfani.
Halima tace bakomai nayi imani da k'addara, kuma ina rokon Allah yasa mani juriya akan wannan abun tashin hankalin daya samemu, insha Allahu Allah bazai bar kosu waye suka aikata haka ba.
Alhaji Mansur yace haka ake son mutum mai yarda da k'addara, inaso kuma idan komai ya lafa mutafi gaba d'aya Kano tunda Malan Sani yace shima can zai koma.
Murmushi Halima tayi tana fad'in matuk'ar aka yanke hukunci mukayi nasara to tare zamu tafi, amma idan sune sukayi nasara zan zauna anan har sai ranar da Malan ya rasu, idan ina raye zan koma Kano da zama, idan kuma nima na tafi to ga Rumaisa nan ku kular mani da ita.
Tausayin Halima ne ya kamasu, hannu yasa ya goge idonshi kafin ya mik'e yana fad'in ina so naje naga Malan Sani. Saurin kallonsa tayi tana fad'in dan Allah ka tafi damu. Alhaji Mansur yace shikenan muje.
***
Kuka kawai sukeyi Alhaji Mansur ne yake lallashin su. Bayan sunyi shiru Malan Sani yace shikenan yanzu an rufe Alhaji ba tare da nayi rakiyarsa ba? Wallahi an cutar dani, Allah ne kad'ai zai saka mani, yanzu ina Ummun Ra'eez take?.... Labarin halin da take ciki Alhaji Mansur ya bashi.
Sosai yake kuka yana fad'in Allah ya isa, Allah ka saka mani. Alhaji Mansur yace bani labarin abinda ya faru.....Komai Malan Sani ya fad'a masa har zuwansa gida ya kwanta. Hannu Alhaji Mansur yasa ya goge kwallar data zubo masa, kallon Malan Sani yayi yana fad'in wad'an nan mutanan shed'anu ne, dalilin barinka araye saboda su d'ora laifin awajenka.
Malan Sani yace bakomai Alhaji, zan d'auki kaddarata da hannu biyu, fatana Allah ya albarkaci abinda na bari. Alhaji Mansur yace insha Allahu zaka kara samun wasu zuri'ar ma.
Saurin kallon Halima yayi ita ko ta duk'ar da kanta. Tambayarta yayi wata nawa? Da hannu tayi masa nuni wata biyu. Murmushi ne ya sauka akan fuskarshi, itama Halima murmushin takeyi.
Malan Sani yace narokeki Halima da ki cire damuwa aranki saboda ki kular mana da zuri'ar mu, kinga dai halin da nake ciki, ke kad'ai zaki cigaba da kula da tarbiyar yaran mu, ki daure kisa juriya aranki dan Allah.
Jinjina kai tayi tana hawaye. Alhaji Mansur yace zanga Brr. Kamal insha Allahu zamu san abunyi. Murmushi kawai Malan Sani yayi, dan yasan Alhaji Mansur ya fad'a ne kawai dan ya kwantar masa da hankali, amma yasan dole ayanke