Advertisements
Chapter 2 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 54

3K to 6K   out of 160.3K words

haka sai Hajiya Binta taji dad'i. K'awarta ce ta kawo shawarar kada ta bari Zainab ta haihu agidan, hakan yasa mukaje wajen wani k'asurgumin Boka ya bada maganin hana d'aukar ciki.


Bayan da muka dawo na rik'a zubama Zainab magani a abinci tana ci, kuma Allah ya taimaka bata d'auki cikin ba. Bayan shekara biyu da aurenta Alhaji ya sake aure inda ya auri Amina, itama mace ce mai hakuri da kwantar da kai, hakan yasa Hajiya Binta taji dad'in zuwanta, anan itama mukayi kokarin bata magani a cikin abinci.


Jin shiru bata d'auki ciki ba yasa hankalin mu ya kwanta, sai dai abinda bamu sani ba ashe ciki ya shiga jikin Amina, nice na fara sanin tana da ciki, a hankali da wayau da dabara irin tamu ta manya na tambayeta rabon data ga al'adarta, a yanda tayi mani bayani yasa na gano cikin watanshi d'aya da kwanaki, anan nayi mata dabara nace kada ta fad'ama Alhaji zaiga rashin kunyarta, ta bari na fad'ama Hajiya Binta ita zata masa albishir hakan zaisa yafi ganin darajarta.


A ranar muka koma wajen Boka, anan ya bamu maganin da za'a rufe mata baki bazata fad'ama kowa tana da ciki ba, zata manta da wani ciki ma ajikinta, sannan Boka ya bamu maganin zubar da cikin, sai Hajiya tace tana tsoron yaki fita, gara dai a kwantar dashi zata san abinyi. Anan Boka yayi mana aiki muka dawo gida.



Tun daga ranar maganar cikin Amina tasha ruwa, bata sake maganar ba, har gwada ta nayi amma ta nuna ita bata san da maganar ba bata da wani ciki. Muna cikin haka Hajiya Binta ta samo maganin da zai kwantar da Alhaji ta bani na zuba mashi a abinci, tunda yaci bai sake lafiya ba.


Wata rana na dawo daga cikin gari kai tsaye na wuce d'akin Hajiya Binta, abinda naji ya firgitani, magana suke da k'awarta akan ta kashe ni, domin ita bata yarda da kowa ba, tunda ina da son kud'i wata rana zan iya juya mata baya idan na samu wasu kud'in. Nan take ta amince akan washe gari zata kashe ni, sannan Alhaji yana mutuwa zata koma wajen Boka ya tashi cikin domin ta jama Amina sharri kuma aki amincewa da cikin jikinta, ita kuma Zainab zata nuna mata soyayya domin ta bata dama su kwarema Amina baya, idan komai ya kammala itama tasa akasheta sai taci dukiyar ita kad'ai.


Cike da firgici Hajiya Binta ta mike tana fad'in wallahi k'arya take, Zainab kada ki yarda da abinda tace makirar tsohuwa ce. Bubbuga tebur Alkali ya buga hakan yasa ta natsu. Kallon tuhum kawai Zainab take binta dashi.



Brr. Ra'eez... Iya cigaba da bayaninki muna sauraron ki.


Iya... Aranar hankalina ya tashi, cikin sand'a na shige d'akina na had'a kayana na bar gidan, ko mai gadi be ganni ba dan yashiga sallah, kafin na bar garin sai da na samu wani yaro da nake mutunci dashi na sashi ya rubuta mani wasik'a, anan na sheda ma Alhaji Amina tana da ciki, alokacin zai kai wata biyu, ban iya fad'ama Yaron komai ba dan bana son ya gano ni, kawai nace masa ina jin kunyar Alhaji nafiso ya karanta a rubuce.



Bayan ya gama nace ya taimaka muje ya bama maigadi kuma ya tabbatar mashi Alhaji zai bamawa. Ina tsaye har Yaron ya bama Mai gadi takardar, bayan ya dawo ya fad'a mani Mai gadin yace zai bama Alhaji duk da baya fitowa amma zaiyi kok'arin kai mashi.



Godiya nayi mashi na bashi kud'i na bar garin, a ranar cikin dare na isa Funtua, a tasha na kwana sai washe gari na isa kauyen mu, ban sake sanin abinda yake faruwa ba sai lokacin da kaje gidana, nayi mamakin ganinka da bayanin da kazo mani dashi, nayi kukan mutuwar Alhaji domin hada ni aka kashe shi, naso na nemi yafiyarsa babu dama saboda banyi ilimin boko ba dana rubuta mashi a wannan wasikar, zuwanka yasa naji kwarin guiwa kuma na amince zanzo na bada sheda akan abinda na sani domin duniyar ta juya mani baya.



Brr. Ra'eez... Zaki iya tafiya mungode. Ya mai shari'a iya kar mutanan da zanyi ma tambaya kenan, wannan takarda ce dana samu a d'akin marigayi alokacin da mukaje gidan bincike nida 'Dan sandan da yayi mani jagora.


Takarda ce mai d'auke da rubutun Marigayi tare da sa hannunshi, tun daga ranar daya samu labarin cikin Amina ya rubuta kwanan watan, ya nuna farin cikinsa, har yayi fatan Allah ya tashi kafad'arsa domin yaga jininshi, atare da takardar da Iya ta aika masa ya had'esu ya b'oye a cikin dirowarsa, Allah ne ya bani ikon ganinta, domin gaba d'aya takardun dirowar an kwashe su, itama daga k'asan dirowar akwai wajen da yake b'oye abubuwan sirrinsa anan ya aje ta.



Mik'ama Magatakarda yayi yana fad'in ya mai shari'a, iya abinda zan fad'a kenan, ina rokon wannan kotu mai alfarma data yanke hukunci ga mutanan da suka zalunci Amina da Marigayi, sannan ta hukunta Likita daya goyi bayan k'arya. Nagode ya Mai shari'a.


Gaba d'aya kotun ta d'auki hayaniya, mutane da yawa Brr. Ra'eez ya burge su, acikin sati d'aya ya gano gaskiya, abinda akayi wata anayi sai gashi acikin sati guda ya gama komai.


Bayan da kowa ya natsu Alkali ya d'ago yana fad'in kotu tana son ganin Hajiya Binta, Iya da Likita agabanta. Haka suka fito jiki a sanyaye, Hajiya Binta sai kuka take dan tasan ta k'are mata.


Kallon Hajiya Binta Alkali yayi yana fad'in kinji shedun da aka kabartar ma kotu, ko kina da ja akan abinda aka fad'a? Girgiza kai tayi tana goge hawaye tace na amince da abinda aka fad'a, amma wallahi sharrin shed'an ne, son zuciya da neman duniya yasa na aikata abinda ban tab'a yi ba, ina rokon wannan kotu da ta mani sassauci.


Alkali yace Likita kana da ja akan abinda aka fad'a? Girgiza kai yayi yana goge zufa yana fad'in na amince, amma wallahi Hajiya Binta ce ta bani mak'udan kud'i akan nayi rubutu akan k'arya kuma nazo na bada sheda, dan Allah arufa mani asiri.


Alkali yace kotu wajen adalci ne, duk wanda kaga yazo kotu to yazo ne domin abi masa hakkinsa, babu batun wani rufin asiri a kotu domin wajen tonon asiri ne, dan haka kowa ya tsaya yaji hukuncinsa.



Hajiya Binta.... Kinfi kowa laifi anan, dan haka kotu ta yanke maki hukuncin d'aurin rai da rai agidan yari, sannan zaki biya Amina tarar dubu d'ari biyar abisa kok'arin ki na b'ata mata suna da kikayi.


Iya.... Kema kotu ta yanke maki d'aurin rai da rai agidan yari, amma kin samu sassaucin aikin wahala abisa kokarin da kikayi na warware gaskiya da kikayi.


Likita..... Kaci amanar aikin ka, an had'a baki da kai anyi rashin gaskiya, dan haka kotu ta yanke maka d'aurin wata biyar agidan yari, kuma zaka biya Amina tarar dubu d'ari biyu abisa b'ata mata suna da kayi.


Wannan kotu tana yima Brr. Ra'eez jinjina akan namijin kok'arin da yayi wajen gano gaskiya, da fatan kowa zai d'auki darasi akan wad'annan mutanan, sannan kotu ta wanke Amina daga zargin da ake mata, ciki na mijinta ne, kuma dole yaci gadon mahaifinsa.... Kotttttt!!!!


Gaba d'aya mutanan mik'ewa sukayi suna ma Alkali tafi, sosai mutane suke son Alkalin su, domin suna ganin shi d'in adali ne, yana kokarin zartar da hukunci akan duk wanda aka kama da laifi.


Hannu Brr. Bajinta ya mik'a ma Brr. Ra'eez yana fad'in ina taya ka murna akan wannan nasara da kayi, ba'a tab'a samun wanda ya kada ni a shari'a ba, sai gashi sabon zuwa yayi mani warwas, duk da ba yaune ka fara aiki ba, anyi maka canjin wajen aiki ne amma duk da haka kayi kok'ari, sai mun had'e wani lokacin.
Murmushi Brr. Ra'eez yayi yana fad'in nagode.



Har kusa da Brr. Ra'eez dangin Amina suka zo suna masa godiya. Brr. Ra'eez yace haba ai bakomai ku godema Allah. Sallama yayi masu suka fita shida Jabeer.



Bayan sunyi sallama da Jabeer ya zo shiga mota yaji ana masa magana, yana juyowa yaga *ALKALI NE,* murmushi yayi yana masa sannu. Alkali yace kaine da sannu, gobe idan kashigo ina son ganinka a ofis. Jinjina kai yayi yana fad'in to yallab'ai. Sallama yayi mashi ya tafi.


Da kallo Alkali ya bishi yana sakin murmushi, a zuciyarsa yana nanata sunanshi (Brr. Ra'eez Hamza MWD), kamar ya san mai shigen sunansa sheru da yawa, sai dai kuma wancan ba haka sunansa yake ba, to me MWD take nufi kuma? Kafad'a ya d'aga yayi gaba.


**** ****

Kai tsaye babbar gidan yari ya nufa, bayan sun gama gaisawa da masu gadin yashiga ciki ya zauna yana jiran akira masa wanda yazo wajensa.


Wani babban mutum ne ya fito yana sanye da kayan gidan yari ajikinsa, da ganinsa daga aiki yake. Yana zuwa Brr. Ra'eez ya mik'e ya bashi wajen zama.


Bayan sun gaisa Brr. Ra'eez yace *KAWU* nayi nasara, yanzu aka gama yanke hukunci anjima za'a kawo masu laifin nan. Murmushi wanda aka kira da Kawu yayi yana fad'in nasan zakayi nasara Ra'eez, an haifeka ne domin Nasara, yanzu kam hankalina ya kwanta, nasan k'arfin ka ya kawo, zaka iya gogawa da kowa, nayi farin ciki da aka maidoka wannan kotu da aiki, nasan aikin *Alhaji Mansur* ne, yana matuk'ar kok'ari akan ka, yarik'e amana, shima Allah bazai barshi ahaka ba.


Brr. Ra'eez yace ai Kawu ban tab'a kukan rashin Mahaifina ba, Abba Mansur ya gama mani komai arayuwa, fatana Allah ya bani ikon saka masa. Kawu yace Allah yasa, kai dai kacigaba da hak'uri arayuwa zaka cigaba da samun nasara, kaje wajen Umman ka kuwa? Brr. Ra'eez yace yanzu dai zan biya.


Kawu yace ka dubata da jiki, sannan ka kiyaye da wannan Alk'alin, zuwa gaba zaka gane nufina, nasan Alhaji Mansur ya fad'a maka wasu abubuwa amma dole kasan komai domin ka shirya yakin kwato 'yanci tare da d'aukar fansar Mahaifinka, kada ka sake ka fad'ama kowa abinda MWD yake nufi har sai burinka ya cika, shiyasa naji dad'i da akafi sanin mahaifinka da sunansa na biyu. Ra'eez yace insha Allahu zan kiyaye. Tashi yayi ya mik'a masa kud'i yana fad'in sai na sake dawowa. Kawu yace Allah yayi maka albarka.


***

*PSYCHIATRIC HOSPITAL* (ASIBITIN MAHAUKATA)


Zaune Brr. Ra'eez yake akusa da wata babbar mace, duk wanda ya ganta yasan tana cikin yanayi na hauka, zaune take tana kallon 'Danta wanda ya bud'e ledar da yazo da ita wadda take d'auke da kayan motsa baki.


Lemu ya d'auko yana kok'arin bud'e mata, da sauri ta warce tana kok'arin fasa kwalin. Murmushi yayi ya mik'a hannu yana fad'in Ummu na bani na bud'e maki kinji. Kallonshi tayi kafin ta mik'a masa kwalin.


Bud'e mata yayi ya zuba mata akofi ya bata. Amsa tayi ta shanye tana mik'a hannu. Aiba ya b'are mata ya bata. Rabi taci kafin ta mik'a masa rabin abaki, amsa yayi ya gutsura hawaye suna zubo mashi.


Hannu tasa ta goge masa hawayen tana fad'in Likita yace adena kuka, yace Alhaji zai dawo, ba dai sun kashe shi ba? Idan na fito zamuje mu kashe su dukan su, ai dai zaka siyo mani wuk'ar Makka ko? Kasan ita kad'ai ce zata iya kashe su.


Murmushi yayi yana fad'in Ummu bazan kyale jinin Abbu ya tafi abanza ba, zanyi kwakkwaran bincike, akwai rud'u acikin wannan lamarin, dole sai nasa natsuwa kafin na gano su, bazaki dawwama ahaka ba, Allah zai baki lafiya.



Dariya tasa ta kamo hannunshi tana fad'in nima binshi zanyi, kai kad'ai zamu bari ai, sai kaje makka kasiyo wuk'a ka kashe su. Wani likita ne ya k'ara so. Bayan sun gaisa Brr. Ra'eez yace nagode likita, kana kok'ari akan Ummu na. Likita yace haba bakomai, tana samun kulawa sosai, yanzu ma lokacin shan maganinta ne, kasan tana sha take bacci. Jinjina kai Brr. Ra'eez yayi yana fad'in nima tafiya zanyi, nagode sosai likita. Hannu ya bashi yana fad'in Allah ya baka lada Brr. Ra'eez, hakika da wuya asamu irin ka da yawa aduniya, kana kok'ari akan Mahaifiyarka. Hawaye Brr. Ra'eez ya goge yana fad'in dole nayi Likita, duk wanda yasan darajar *UWA* zaiyi fiye da abinda nakeyi, Uwa ba abun wasa bace.



Likita yace haka ne gaskiya, Allah yayi mana jagora. Brr. Ra'eez yace amin. Sallama sukayi ya wuce yana kallon Ummunsa.



Kai tsaye gidanshi yawuce da yake unguwar ( *APAPA*). Kwance yayi a falo hawayen da suka zamar masa jiki suna kwaranyo masa, gaba d'aya baya jin dad'in ranshi, duk lokacin da ya kai ziyara wajen Ummunsa haka yake kasancewa, kuma duk da haka baya iya faashi wajen zuwa ganinta, can ne kad'ai yake zuwa yaji dad'i aranshi. Runtse ido yayi yana fad'in Allah gani gare ka, Allah kayi mani jagora akan wannan al'amari, bani da gata sai kai ya Allah, kashige mani gaba wajen gano gaskiyar wannan al'amari, Allah ka tona asirin wad'an da suka aikata ma Mahaifina wannan abun, Allah ka tona asirinsu ta yanda bazasu iya k'aryatawa ba. Juyi yayi yana sakin kuka marar sauti.


*GA DUK WANDA YAKE SON CIGABAN WANNAN LABARI ZAI TURO NAIRA 200 KACAL, MTN CARD TA WANNAN LAMBAR.. 08147669770, SAI KAYI SCREEN SHOT KA TURA TA WHATSAPP A LAMBAR K'ASA, IDAN KUMA BANK TRANSFER NE, KA TUNTUBE NI TA WHATSAPP NO 08028525263 ZA'A SAKA GROUP DIN DA ZA'A RIKA POSTING. NAGODE. SAI KUYI HAKURI DA YANDA LITTAFIN YAZO.*


Ur's.
NABILA RABI'U ZANGO
(Nabeelert Lady)
08028525263
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kud'i ne. naira 200 kacal, MTN card ta wannan lambar.. 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer zakayi sai ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar. 08028525263*


0⃣2⃣



Da kyar ya tashi yayi wanka, bayan yayi sallah ya fita zuwa gidan Kawu dan can ne waje na biyu da yake d'ebe masa kewa, duk da Kawu ya so ya koma can da zama amma yaki komawa, acewarsa yafi son kad'aici.


Da sallama yashiga cikin gidan, a tsakar gida ya iske matar gidan tana kok'arin kauda kayan da suke a tsakar gidan. Amsa sallamarsa tayi tana fad'in Ra'eez sannu da zuwa.


Zama yayi yana fad'in yauwa sannu da aiki Mama, ina *RUMAISA* kike aiki ke kad'ai? Murmushi Mama tayi tana fad'in na aiketa siyen kayan miya ne shiyasa nake rage aikin kafin ta dawo.


Jinjina kai yayi yana fad'in Kawu yana gaishe ku. Mama tace ka je kenan? Ra'eez yace naje na sanar dashi yanda shari'ar tamu ta kasance ne. Mama tace ikon Allah, ashe fa yau ka fara shiga babbar kotu ko? Ina fatan dai komai yayi dai-dai? Ra'eez yace Alhamdulillahi Allah ya amsa addu'ata, komai ya tafi yanda ya kamata, domin nine nayi nasara.



Mama tace kai amma naji dad'i, Ubangiji Allah ya baka ikon yin nasara akan shari'ar da zaka fara nan gaba domin kwato hakkin mu da aka danne.


Ra'eez yace amin Mama. Hannu tasa ta goge kwallar data zubo mata tana fad'in ina Kawun naka babu dai abinda yake damunsa ko? Ra'eez yace lafiyarsa lau yace agaishe ku ma.


Mama tace amma yana cikin wahala ko? Murmushi Ra'eez yayi yana fad'in Mama ki daina damuwa, sam basa sashi aikin wahala domin akwai mutane na acikinsu, muna mutunci sosai hakan yasa suke sauk'ak'a masa, addu'a itace abinda zamuyi masa.


Mama tace haka ne, shiyasa fa bana son zuwa wajensa, duk lokacin da naje ina dad'ewa kafin na warware, ya jikin Ummun ka? Duk'ar da kai Ra'eez yayi yana fad'in kamar kullum Mama.


Girgiza kai tayi tana fad'in Allah ya bi mana hakkin mu, an zalince mu an tauye mana hakkin mu, Allah ne kad'ai zai iya saka mana, Allah ya baka ikon jure wannan jarabawa Ra'eez, hakika an zalince ka, an rabaka da Mahaifinka, ga halin da Mahaifiyarka take ciki, Allah ya baka ikon gano gaskiya kuma ya baka sa'a akan kosu waye suka aikata hakan, babu abinda zamuce da kai sai godiya, Allah ya saka maka da alkhairin abinda kake mana, karike mu amana tamkar jininka.


Ra'eez yace amin Mama, amma bana so kina mani wata godiya, kun wuce duk yanda kuke tunani a waje na, bani da kowa a garin Lagos sai ku, duk da bamu had'a komai da ku ba amma Allah ya had'a mu, ku da Abba Mansur kun zame mani 'Yan uwa na jini, ku kad'ai nake kallo naji dad'i arayuwata, ta silar Mahaifina Kawu yashiga halin da yake ciki, tunda babu Abbu dole na maye gurbinsa awajen ku, domin nasan da yana raye shi mai rik'e ragamar gidan ku ne, dan haka kada ki sake mani godiya, ke Uwace agare ni.


Jinjina kai Mama tayi tana goge hawayen idonta tace haka ne Ra'eez, hakika kai 'Dah nagari ne, ko wace Uwa zatayi alfahari da samun ka, kada ka sake cewa ta silar Mahaifinka Malan yashiga wannan halin, dama can Allah ya rubuto masa K'addararsa a haka, fatan mu Allah ya bashi ikon cinye wannan jarabawar. Ra'eez yace amin.



Sallamar Rumaisa ce

2 / 54