Advertisements
Chapter 6 Reading ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ALKALI NE Hukuncin Boye by Marubuciyar Zamani

Author :  Marubuciyar Zamani Category :  Complete Novels

Chapter   6 / 54

15K to 18K   out of 160.3K words

mukullin mota mu tafi tare. Sakin baki Malan Sani yayi yana kallonshi jin irin karamcin da yayi masa.


Yana tsaye har ya fito suka nufi waje. Hannu Malan Sani ya mik'a yana fad'in Alhaji kawo na tuk'a mu. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in haba yanzu ai baka cikin natsuwar ka, ka bari na tuk'a mu. Madu ne ya k'araso yana tambayarsu lafiya? Alhaji ne yayi masa bayani. Murmushi yayi yana masu fatan alkhairi. Haka suka fice Malan Sani sai addu'a yake Allah ya sauketa lafiya shima yaga kwanshi a duniya.


Ur's.
Nabeelert Lady🖋
[3/10, 8:38 AM] +234 703 008 7807: *Wannan littafin na kudi ne, naira 200 kacal, MTN Card a wannan lambar... 08147669770, kayi screen shoot ka tura ta whatsapp a lambar k'asa, idan kuma bank transfer ne ka tuntube ni a whatsapp ta wannan lambar 08028525263.*


0⃣5⃣


Tsaye suke a cikin asibitin, Malan Sani ya kasa zama duk yashiga damuwa, tsoronshi d'aya kada ya rasa Matarsa, gashi tun kafin suzo aka kawota tana nakuda har sunzo da kusan mintuna ashirin amma shiru.


Alhaji Mai Wada ne ya dafashi yana fad'in addu'a zakayi mata Malan Sani, wannan damuwar bazata amfanar da komai ba, kai namiji ne ya kamata kasa dauriya aranka.


Jinjina kai Malan Sani yayi yana fad'in nagode Alhaji. Fitowar wata ma'akaciyar asibitin ne yasa sukayi saurin matsawa wajenta. Bakinta a washe take tambayarsu sune suka kawo Halima? Da sauri Malan Sani ya amsa mata.


Murmushi tayi tana fad'in Halima ta sauka lafiya Allah ya azurta ta da 'Diya mace, tasha wahala sakamakon dad'ewar da tayi bata haihu ba kuma gashi haihuwar faari, wannan shine ya jawo mata doguwar nakuda amma yanzu suna lafiya.


Hamdala Malan Sani yayi yana mata godiya. Murmushi tayi tace ai bakomai, yanzu ana gyara ta idan aka kaita d'akin hutu zaku iya ganin ta. Hannu Alhaji Mai Wada yasa a aljihu ya ciro kud'i masu yawa ya bata yana fad'in ga tukuicin ki. Amsa tayi tana masa godiya ta wuce tana fad'in idan kun gama kuje wajen likita akwai maganar da zakuyi.


Bayan da aka maida Halima d'akin hutu Malan Sani yaja Alhaji Mai Wada suka nufi d'akin. Sai murmushi yake yana kallon matarsa. Alhaji kuwa yarinyar ya d'auka ya tsura mata ido domin Allah yayi mata kyau tun tana jaririyarta, yana matuk'ar son mace amma Allah be bashi ba.



Mika ma Malan Sani ita yayi yana fad'i kayi mata hud'u ba. Murmushi yayi yana fad'in Alhaji wannan yarinyar da namiji ne sunanka zan saka, domin had'uwata da kai akwai alkhairi acikinta.


Murmushi Alhaji yayi yana fad'in bakomai a hakan ma nagode. Amsarta yayi nan take yayi mata hud'uba da *RUMAISA*, suna ne da Halima take matuk'ar so, tasha fad'in duk ranar data haifi mace wannan sunan za'asa.


Ajeta yayi akusa da Halima yana fad'in Allah ya amsa addu'arki ya baki mace kuma ansa mata sunan da kike so wato *RUMAISA.* Murmushi tayi tana duk'ar da kai dan kunyar Alhaji take ji.



Tare da Alhaji suka fita yace ya mik'ashi wajen aiki sai ya dawo da motar saboda d'aukar matarsa da Rumaisa. Sosai wannan abun yayi ma Malan Sani dad'i, haka yayi ta jera masa godiya kamar zaiyi kuka.


Bayan ya kaishi Alhaji ya miko masa dubu goma yana fad'in ga wannan kasa a aljihun ka nasan zaka buk'ace su. Har k'asa Malan Sank yazo duk'awa da sauri Alhaji ya rik'osa yana fad'in daga yau kada ka sake yunkurin aikata hakan, ni ba kowa bane dan haka ka d'aukeni tamkar d'an uwanka.


Jinjina kai Malan Sani yayi yana goge hawayen farin ciki yayi masa godiya yana fad'in anjima zan dawo na d'auke ka. Alhaji yace kada ka damu zan hau motar haya ka aje motar a wajenka saboda zirga-zirga, idan ka gama zuwa dare sai ka kawo mani.


Rasa bakin magana Malan Sani yayi sai kawai ya fashe da kuka. Murmushi Alhaji yayi ya dafashi yana girgiza masa kai kafin ya shige ofis d'insa.


Wannan abu da Alhaji yayi ma Malan Sani ba k'aramun dad'i yayi masa ba, yanaji aransa duk duniya baya da kamar Alhaji ayanzu, yasa aranshi zai iya bada ranshi akan Alhaji. Haka ya nufi kasuwa domin sayen abubuwan buk'ata kafin a sallame su.



A ranar Malan Sani ya kira gidan su ya fad'a masu haihuwar, sosai sukaji dad'i domin abinda kowa yake fata ne. Nan aka turo wata Gwoggonta da 'Diyar Kawunta suka taho.



Sai k'arfe d'aya kafin Malan Sani yaje amsar sallama. Anan likita yayi masa bayanin kada ya bari Halima ta sake d'aukar ciki yanzu saboda mahaifarta ta wahala akan wannan haihuwar, idan samu ne su bari kamar nan da shekara biyar kafin ta sake d'aukar ciki.


Malan Sani yace to mungode likita, sai ku aunata domin abata abinda zaiyi dai-dai da jininta wanda zai hanata d'aukar cikin. Murmushi likita yayi yana fad'in ina son mutane irin ku masu saurin fahimta, bara na had'aka da wata ma'aikaciyar mu itace take kula da wannan b'angaren, Allah ya bada lafiya. Sallama Malan Sani yayi masa yana masa godiya.


Haka suka tafi gida cike da farin ciki. Lokacin da suka isa har Jamila makwabciyarsu ta sauke ruwan wanka ta kammala girki. Sosai Halima taji dad'i, dama irin abinda take gudu kenan ace ta haihu babu kowa nata, sai gashi Allah ya bata makwabciya tagari.


Sai dare Malan Sani ya maida ma Alhaji motarsa yana sake masa godiya. Alhaji Mai Wada yace haba bakomai, zuwa gobe kazo akwai abinda zaka amsa. Malan Sani yace nagode Allah ya kaimu.



Sai tsakiyar dare Gwoggon Halima suka iso saboda basu taso da wuri ba, Malan Sani ne yaje ya d'auko su. Halima baki yaki rufuwa yau 'yan uwanta sunzo.


Washe gari haka 'yan barka sukayi ta shigowa wad'an da suke mutunci dasu kasancewar unguwar ba laifi akwai hausawa, yaren ma akwai wad'an da suke mutunci.


Sai da akayi azahar Malan Sani yaje gidan Alhaji dan baya so yaje ya tashesa. Malan Sani ya cika da mamakin kayan abinci da Alhaji ya bashi, sannan ya kawo kud'in rago ya bashi hada na cefanan suna wanda zasu ishe sa ya saya ma Halima kayan fitar suna.


Yana hawayen farin ciki yashiga yimasa godiya. Tare da Madu suka d'auki kayan a mota shima yaje ganin jaririya. Bayan ya ganta sukayi sallama Malan Sani ya nufi kasuwa domin ya siyo ma Halima kaya ya k'aro ma Rumaisa kaya duk da sun sayi wasu sai da lokacin basu san abinda zasu haifa ba hakan yasa suka sayi na jinsi d'aya wanda mace da namiji duk zasu iya sawa.


****


Ranar litinin tunda wuri Malan Sani ya isa gidan Alhaji bayan daya gama aje masu komai na buk'ata. Zama yayi wajen Madu suka shiga fira kafin Alhaji ya fito.



Alhaji yana fitowa ya cika da mamakin ganin Malan Sani ganin har yazo shida yake da hidima. Tasowa sukayi gaba d'aya suna gaishe shi. Alhaji yace lafiya lau, Malan Sani ina masu jego? Malan Sani yace suna lafiya. Alhaji yace ai da ka bari sai gobe ka fara zuwa.


Malan Sani yace haba Alhaji nida ba mace ba, na gama masu komai shiyasa na fito, nima bazanji dad'in zama agidan ba, nagode Allah da yasa na samu wannan aikin da yanzu haka zanyi ta gararan ba. Murmushi Alhaji yayi ya mik'a masa mukullin yana fad'in haka ne, gashi muje.


Sallama suka yima Madu suka tafi. Malan Sani yayi mamaki ganin Alhaji ya zauna agaba, kasa daurewa yayi ya kalleshi yana fad'in Alhaji ai daka zauna a baya. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in hakan ma yayi nafi buk'atar na zauna agaba. Murmushi Malan Sani yayi yana fad'in Alhaji kai na daban ne. Beyi magana ba yacigaba da duba wasu takardu.


Lokacin da suka isa ofis mutane sunyi mamaki ganin Alhaji Mai Wada tare da wani, sai dai basuyi tunanin direba bane saboda sun ganshi agaban mota.


Sai bayan da suka tsaya Malan Sani ya fito ya d'auko masa takardunsa yabi bayansa sukayi tunanin direba ne. Haka yayi ta gaisawa da mutanan wajen anan ya gabatar masu da Malan Sani amatsayin direbansa. Sunyi mamaki da jin haka domin sunyi tunanin acikin masu aikin wajen zai d'auki direba.


Kai tsaye suka wuce ofis d'inshi, bayan ya aje masa takardu Alhaji yace Malan sani zaka iya tafiya idan ina da buk'atar wani abu zanyi maka waya tunda kana da hidima.


Risnawa Malan Sani yayi yana fad'in nagode, mukullin motar ya d'ora masa saman teburi yana niyar barin ofis d'in. Sunanshi Alhaji yakira yana fad'in idan ka bar motar anan ai babu abinda zanyi da ita, kawai ka tafi da ita kayi abinda ya dace.


Dawowa yayi ya d'auki mukullin yana sake masa godiya. Murmushi Alhaji yayi yana fad'in agaishe da Maijego. Fiya yayi yana murmushi yace zataji.


Kwankwasa k'ofar akayi hakan yasa Alhaji ya bada izinin shigowa. Masinjansa ne yashigo yana gaishe sa. Alhaji yace *Malan Bala* katashi lafiya? Nashigo ban ganka ba nazo da sabon direbana naso in had'aku amma ya tafi.


Risnawa Malan Bala yayi yana gaishe shi kafin yace na zagaya baya ina d'auraye tsumman dana goge ofis d'in ne, amma ai zai dawo ko? Alhaji yace zai dawo yaje gida ne matarsa ce ta haihu.



Malan Bala yace masha Allah, Allah ya raya, gaskiya naji dad'i daka samu direba, domin wasu suna tunanin baka son ka d'auki direba saboda karik'a cinye kud'in da ake fidda masu.



Murmushi Alhaji yayi yana fad'in hada kai acikin masu fad'in haka kenan? Zaro ido Malan Bala yayi yana fad'in haba dai Alhaji, kaima zaka mani shedar kirki ai, wallahi ko d'aya bana maka mugun zato, domin tun bayan zuwanka nan rayuwata ta canza, mezaisa na shiga cikin masu zagin ka? Jinjina kai Alhaji yayi yana fad'in wasa nake ma Malan Bala, kada ka damu da duk abinda mutane zasu fad'a akaina, domin idan kana biye ta mutane bazaka tab'a yin gaba ba, kai dai kasa Allah aranka.


Malan Bala yace insha Allahu. A had'o maka shayin ne? Alhaji yace sai zuwa anjima nasha agida. Risnawa yayi yana fad'in ahuta lafiya. Yana kok'arin fita sai ga mataimakin Alhaji yashigo ofis d'in, gaishe sa Malan Bala yayi kafin ya fita.


Hannu Adebayo ya mik'a ma Alhaji yana fad'in barka da safiya Sir, murmushi Alhaji yayi yana fad'in yauwa Mr. Adebayo ka tashi lafiya? Cikin harshen turanci ya maida mashi da lafiya lau, saboda Adebayo yafi son magana da turanci duk da yana jin hausa sosai, amma saboda bata zauna abakinsa ba yasa yafison yayi magana da turanci koda kuwa abokin maganarsa da hausa yake masa magana saboda yana jin hausa maidawarce take masa wahala.


Zama yayi yana mik'a ma Alhaji wata takarda yana fad'in *Alhaji Marusa* babban mutumin nan mai shigo da kayan na'urori da sauran kayan masarufi na k'asar waje shine ya aiko da wannan takardar akan yana son sa hannunka saboda yana samun matsala da ma'aikatan mu akan kayansa, duk da kowa yasanshi yasan matsayinsa amma ana samun wasu daga cikin ma'aikatan mu suna rik'e masa kaya, wani lokacin kuma suna bincikar masa kaya suna b'ata masa lokaci har hakan ya kan jawo masa asara, kafin zuwanka Oga ne ya tsaya masa, domin kowa yasan irin matsayin daya taka ak'asar nan, to bayan tafiyar Oga sai ya fara samun matsala da mutane, duk da akwai wad'an da suke kular masa da kayanshi amma wannan karon sai da ya kira Oga yayi masa magana, shine ma Oga yakirani akan nazo kasa hannu domin ya zama sheda akan duk wasu kaya da za'a shigo dasu nashi ba sai an bincike su ba tunda ansan abinda yake shigowa dasu.


Tunda ya fara magana Alhaji ya had'e hannu ya jingina da kujera yana kallonshi murmushi kwance a fuskarsa. Jin Alhaji yayi shiru bece komai ba yasa Adebayo yacigaba da fad'in Alhaji akwai babbar sallamar da muke samu daga Alhaji Marusa, sam beda rowa, yasan yanda muke masa mutunci shiyasa yake sakar mana kud'i, kuma munyi bincike babu abinda yake shigowa dashi wanda ya sab'a doka hakan yasa muka aminta dashi.



Wannan karon k'aramar dariya Alhaji yayi ya gyara zamanshi yana fad'in Mr. Adebayo taya kasan cewar baya shigo da kayan da suka karya doka? Saurin kallon Alhaji Adebayo yayi yana motsa baki. Takardar Alhaji ya amsa yana fad'in idan har zamu iya sa hannu akan wasu surik'a shigo da kaya ba tare da an bincike su ba ina ganin babu amfanin gwamnati ta ajemu tana biyan mu anan, idan muka kyale wasu wad'an da muke kamawa kuma su basu da hakki akan mu? Mr. Adebayo ina so ka fahimci wani abu guda, duk abubuwan da suke faruwa ak'asar nan mune muke haifar dasu, idan muka rik'e aikin mu babu yanda za'ayi arik'a shigo mana da haramtattun kaya a k'asar mu, kana ganin k'asashen da suka cigaba sai dai ashigo da kaya marasa kyau ta b'arauniyar hanya, domin ma'aikatansu sun rike gaskiya, mu kuma sai muka banzatar da aikin mu muka rik'a barin ana shigo mana da kaya ta hanyar daya kamata ace mun tsare ta, sam masu aikata hakan basu da damuwar bin b'arauniyar hanya domin sun san mud'in kwad'ayayyu ne, da sun watsa mana tsaba sai mu saki hanya mu koma muna tsintar abinda suka watsa, su kuma sai su koma suna abinda suka ga dama, duk abubuwan da suke faruwa anan babu wanda ban sani ba, wasu tun kafin nazo wajen nan nake da masaniya akan su, wasu kuma bayan zuwa na na karance su, wannan dalilin ne yasa tunda nazo bance komai akan aiki ba, na zuba ido domin na gama karantar kowa, kuma daga yau ne aikina zai fara, wannan dalilin ne yasa na cireka daga bakin boarder domin ba aikin daya kamata kayi ba kakeyi.


Wata takarda ya d'auko yana fad'in wannan sune sabon tsarin dana kawo, kuma yanzu nake jiran kashigo na fad'a maka k'arfe goma akwai taro domin kowa yaji sabon tsari, sai kuma gashi kazo mani da wannan maganar, dan haka ka fad'ama sauran ma'aikata sakona, ina fatan ka fahimce ni? Kai Adebayo ya jinjina zuciyarsa tana masa zafi, dama shi tunda Alhaji Mai Wada yazo haka kawai yaji baya sonshi, shiyasa yafi son akawo masu yaran su sunfi jin dad'in aiki dasu, amma idan aka kawo bahaushe musulmi da wuya ya basu goyon baya musamman idan mutumin bashida had'ama.


Tashi yayi ya d'auki takardar da ya bama Alhaji yana fad'in shikenan zan koma ofis sai zuwa anjiman. Murmushi Alhaji yayi yana d'aga masa kai. Haka ya fita cike da jin haushi. Murmushi kawai Alhaji yayi yacigaba da aikin da yake gabansa.


***

Cike d'akin taron yake da ma'aikatan wajen tun daga masu gadi, masinjoji har zuwa manyan ma'aikata. Bayan an bud'e taro da addu'a Alhaji Mai Wada ya bama Adebayo izinin yayi ma sauran 'yan uwansa jagoranci suyi tasu addu'ar. Bayan sun gama Alhaji ya bama Adebayo takardar yace yarik'a karantowa sai shi yayi bayani.



Zuciyar Adebayo a cunkushe ya mik'e, sai dai da yake d'an duniya ne babu wanda zai iya fassara abinda yake a fuskarsa. Haka ya fara karanto sabon tsarin Alhaji yana bayani d'aya bayan d'aya.


Gaba d'aya wajen kowa yayi shiru, masu jin dad'i sunayi masu jin haushi sunayi. Bayanin da Alhaji yayi na k'arshe yafi d'aga ma wasu hankali, musamman masu aikata irin laifin.


Kallon mutanan wajen Alhaji Mai Wada yayi yana fad'in wannan dokar itace doka ta k'arshe acikin jerin dokokin dana rubuta, shiyasa na barta a k'arshe domin ba abu bane na wasa.


Kamar yanda na fad'a zan sake maimaitawa, duk wanda aka kama da laifin karb'ar cin hanci daga wajen masu kaya za'a dakatar dashi har na wata ukku ba tare da albashi ba, idan aka maidoshi ya sake aikata hakan to kora ce, ba haka dokar take ba, nine na sassautata domin bana fatan na zamo wanda zaiyi silar korar wani daga wajen nan, domin bazanji dad'i ace nine silar katse mashi hanyar abincinsa ba, amma abinda nakeso daku shine ku daure ku bani had'in kai domin mu gyara tare, kowa yasan yanda yankin mu na nan garin Lagos yayi suna, domin mune manya, inaso na kawo cigaba, ba dole sai mun amshi cin hanci zamu samu kud'i ba, akwai mutanan da suke bada kyauta saboda kawai an tsare masu kaya sun sauka lafiya, dan haka kowa yayi kok'arin kiyayewa, insha Allahu zaku sameni mai adalci agare ku.


Sai magana ta biyu, kowa ya tsaya a inda aka ajeshi, duk wanda kayansa suka iso zamu tsaya muyi binciken daya kamata kafin mu badasu, babu wani dalili da zaisa ace baza'a binciki kayan wani ba, komin matsayinsa, komin ikonsa matuk'ar kayansa suka iso dole a tabbatar da ingancinsu kafin a sake su, duk wanda muka kama da wannan laifin zai fuskanci hukunci, ku daure ku tsaya a binciki kaya, gara su dad'e ba'a sake su ba da muyi sauri mu saki kaya bayan akwai haramtattu aciki.


Wannan shine iya sabon tsarin dana kawo, ina fatan kowa zai fahimceni, nasan wasu zasuji haushi, dama haka abun yake, dole sai anyi b'arna kafin ayi gyara, kuma sai an daure kafin a tsaida gaskiya, dan haka wanda beji dad'in wannan sabon tsarin ba ina mai bashi hak'uri haka aikin kwastam yake.


Gaba d'aya wajen ya d'auki tafi, masu jin haushi ma haka suka daure suka tafa masa, Adebayo bazaka tab'a gane yanayin da yake ciki ba. Haka taro ya tashi kowa ya koma wajen aikinsa.



Tsaye Adebayo da Umar

6 / 54