Advertisements
Chapter 108 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc Hausa Novels
Advertisements

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   108 / 138

321K to 324K   out of 412.8K words

Ga halin da miji ke ciki gana Wiya. Wani irin hawa da jininta yayi sai gata a ?asa zube...

? ? ? ? Huznah an samu nasarar tsayar da jininta ita, an mata allurar barci. Sai dai doctor baice komai game da cikin na nan ko baya nan ba. Yadai ce su kwantar da hankalinsu. A wannan halin Sageer da mahaifinsa suka iso, yanda kowa baiga Huznah Win ba suma basu ganta ba. Haka suka zauna cikin jimami biyu suma. Na al'amarin dake faruwa a ?asar da wanda ya shafe su na Huznah....

_______&

? ? ? ? Tunda Doctor ta tafi tabar Hajiya Basariyya a ?ofar gidanta taji ta kasa motsa ?afarta. Haka ta cigaba da tsaiwa ita ba gunki ba ba kuma mutum mai rai ba. Sai da taji hajijiyar dake jujjuyawa da ita na neman zubar da ita a ?asa sannan ta daddafa ta shiga mota, kanta ta kife a steering tai shiru tsahon lokaci. Kafin ta tada motar, da farko rasa ma inda zata dosa tayi, sai da ta samu waje ta tsaya tai kiran maman Yaseerah. Harta tsinke bata Waga ba, dan hakan ta Wauki hanyar Zarian.
? ? ? ?? Tunda ta shigo maman Yaseerah ta mi?e tana kallonta, dan suna zaune ne a falo ita da yara suna cin abinci hankali kwance duk da kuwa sunji halin da ?asar ke ciki akan zuri'ar Darma. Amma tunda ahalin kishiya ne sai abin bai wani taSata ba ita kam balle damunta. Duk da kuwa akwai Najma da ko ba komai ?a ce ga mijinta. Yaran kuwa duk da sun shanye a ransu suna cikin damuwa akan ?ar uwarsu. Ai jini ba ?arya bane ba, duk da uwarsu na rabasu da ?an uwan nasu shi tuwo dai tuwo ne ba'a sake masa suna. Najma dai jininsu ce dole suji rashin daWi idan wani mugun abu ya sameta.
? ? ?  Lafiya kuwa na ganki haka? Badai wannan abun dake ta yawo bane ya birkitaki? . Maman Yaseerah ce ta faWa tana kallon Hajiya Basariyya bayan sun shiga bedroom saboda yara.
?? Sai da Hajiya Basariyya ta kai zaune a bakin gado hannayenta duka biyu a saman fuskarta ta furzar da zazzafan iska a bakinta... Maman Yaseerah ta sake faWin,  Ke ko Basariyya ki rufama kanki a siri, har miye tsakaninki da wasu zuri'ar Darma da kikabi kika birkita kanki haka. Dama Huznah ta auri jininsun ne ma sai ace. Kada ki manta Yaseerah da ?ar uwar mijinta ke ciki wlhy banji komai ba tunda ba sonta suke ba balle ke......
? ? ??  Haba wai mi kike faWa haka ne? Ki ?yaleni da abinda ya dameni dan ALLAH. Kin dameni da wani maganar zuri'ar Darma zuri'ar Darma ni ban san miya faru da su ba, tawa ta isheni ma.....
? ? ?? Kallonta kawai Maman Yaseerah take yi a firgice, ganin hawaye share-share a fuskar Hajiya Basariyyan,  Basariyya kuka fa kikeyi? Wai mike faruwa ne? .
? ? ? ? ?  Miye ma bai faru ba, na kai Huznah anyi allurar nan amma ban san yaya akayi ba ta Soyo waya ta kira Daddynta ta sanar masa inda muke.....
? ??  Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ke ko ya akai kikayi wannan gangancin haka? Yanzu ina Huznar? .
? ??  Sun Wauke ta shi da Yazeed, na tabbatar asibiti suka tafi kaita .
? ??  Yazeed!? Shi Yazeed Win dama ya samu lafiya ne? .
? ? Kasa bata amsa Hajiya Basariyya tayi, dan hankalinta baya anan gaba Waya. Shiru itama maman Yaseerah tai tana tunani, zuwa can ta furzar da iska tare da faWin,  Ihmm nace ba, Hajiya Basariyya bai kamata ace nan kika tahoba ai gaskiya. Dan kinga shi Alhaji Usman zai iya tunanin dani aka haWa wannan al'amarin, alhalin kuma ban san komai ba gaskiya. Ya kamata ki tashi kije dan nikam ban shirya rasa aurena da ?ayana ba. Nima matsalolin gabana sun isheni. Dan yanzu haka su Yaseerah na hanyar tahowa Zaria .
? ?? Sosai Hajiya Basariyya kema maman Yaseerah kallon mamaki, amma sai ta daure ta ce,  Yanzu ni kike kora Hajiya Jummai? .
? ? ?  A'a nifa ba korarki nake ba Basariyya kada ki canja min magana. Amma dai kin san halin mazan nan namu ba sai na zauna miki bayani ba. Kidai je Win idan na samu lokaci zan shigo sai mu tattauna. Dan wlhy bana ma son Abban Yaseerah ya shigo ya sameki a gidan nan akwai babbar matsala. Sannan maganar kuWina dan ALLAH kiyi ?o?arin a cikin satin nan na samesu akwai uzirin daya taso min nima gashi duka abinda ke hannun nawa na tarkata na baki .
? ?? Ai kaWan ya hana zuciyar Basariyya fitowa waje. Maman Yaseerah ta mi?e ta fita a Wakin, dole Hajiya Basariyya ta mi?e kamar wadda ?wai ta fashewa ta bita a baya..........
'?



*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =??=?O?_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*


______________



.........Anyi hannun karSa hannun bayarwa tsakanin Mabera da jami'an tsaron akan Abah da Sille. Duk da dai bai yarda ya bada Abah ba sai da ya shiga mota shi da Wansa. Kafin ya shigan ya kalla jami'an tsaron da su Baba Sardauna fuska da murmushi ya ce,  Ku kwantar da hankalinku bazan taSa kashe Aliyu ba duk da shi a baya yayi i?irarin kashe ni akan laifin da ban aikata ba. Ba bu?atar haka dan shi kam babu abinda ya rage masa sai jiran mutuwar tasa in har ya tabbata matarsa Kamila ta bashi gubar data saya da kuWinta domin sa. Na yafe masa a yanzu, sai dai ku sani zan dawo Waukar fansar ?ayana akan Wansa Ajwaad.... ya hankaWa Abah ya wani irin ja motar da masifar gudu. Da gudu wasu a cikin jami'an sukayo kan Abah, wasu kuma suka shiga motoci akabi bayan su Mabera.....
? ?? Matu?ar tashin hankali su Baba Sardauna sunji akan batun wannan guba. Hakama su AA da suka zo da gudu suka kama Abah. Suna tada shi tsaye akan ?afafunsa Abbu ya da zancen guba yafi tsayama a rai ya matso ya buWe idanun Abah, ya kuma Waga ?asan harshensa ya duba. A rikice ya ce,  Mutumin nan fa da gaske yake akwai guba a jikin Aliyu harta fara nuna kanta. Oya ba Sata lokaci maza muje .
? ?? Lallai tashin hankali ba'a saka maka rana, ahalin Darma sun shaida wannan salla. Ana murna an rabu da bukar ashe an haifi habu. Kafin wani dogon lokaci an wuce da su Aba gaba Waya cikin jirgi mai saukar angulu. Sauran jama'an da aka bari a jejin kuma suna tattare komai da aka samu. Ga yan jarida har sun ?araso sunata Waukar komai. Dole kafin isowar jirgin aka tsaida motoci a kan titin asibitin KK domin samawa jirgin wajen sauka. Su Maanal da dukkan ahalin Darma sun fito suma wajen asibitin sunata kuka harma da mutane masu majiyyata. Dan labarin akwai guba a jikin tsohon ambassador Aliyu Darma harta fara yawo. Yanda al'amura suka gudana da batun gubar nan ya tsayama Abah a zuciya, dama ga waWanda ya jima yana tarama zuciyarsa akan Mamy tsahon lokaci. Zancen lalata mahaifar Oum da kashe masa yaro da Mabera yayi duk sai suka taru suka tsaya masa a ?ahon zuciya. Dan da nan jininsa yay wata irin hayewa ta tashin hankali. Lokacin da ake fiddoshi a jirgin ai komai ya rikice. Da gudu ma'aikatan asibitin suka fita da gadon Waukar mara lafiya, yanda ?irjin Abah ke wani irin Wagawa da sauka tamkar numfashin nasa zai bar gangar jikinsa dole ne hankalin duk wani mai imani ya tashi. ALLAH sarki Oum sai a lokacin ta yanke jiki ta faWi. Dama tunda aka baro jejin da su bata furta ko a ba na magana. A take hankalin kowa ya ?ara tashi, itama aka kwasheta zuwa ciki.
? ? ? ALLAH sarki AA tafiya kawai yake, ko gane abinda ke gabansa ma bayayi, Yaya Fawzan kam sarkin karaya jikin Baba kawai ya kife kansa ya fashe da kuka. Babban Yaya dashi aka shiga da Oum ciki.
? ? ?? Nibras da tun Wazun itama sun iso da Mamanta asibitin da Yayunta tunda ita ALLAH ya ?addara bata da rabon wahala, dan daga idi ta wuce gidansu duk hidimar da akai babu ita, sai dai itama tasha tashin hankali matu?a..

? ?? Su Abbu kam suna kan Abah, dan ana kaishi Wakin daya dace sai almakashi aka saka aka yanka rigar shaddar jikinsa ma. Dan danna aka saka masa oxygen. Kwararrun likitoci da suka san aikinsu da Abbu suka fara abinda ya dace. Dai-dai nan kuma sa?on rasa Anum ya isa ga ahalin Darma. Duk da kasancewarta yarinya ?arama mutuwar tata ta dakesu ?warai da gaske. To itama dai Nana sai abinda ALLAH yayi, ita da Mamy dai har yanzu su akwai doctors a tare da su......

_________&
KADUNA

? ? ? ?? Gab da kiran magriba ALLAH yay ma Nazeerah rasuwa. A dai-dai lokacin da Sabuwa ke farfaWowa daga sumar wahala. Tashin hankali ya sakata fasa gigitacciyar ?arar ihun kuka. To ya za'ayi, ta ALLAH ta riga ta tabbata sai kuma ha?uri. (Irin wannan wa'azin mutuwar ake jiye mana shiyyasa akowane motsi na rayuwarmu ake so mu dinga tunawa da hakan. Babu ruwan mutuwa da shekaru, ba ruwanta da gata, bata jinkirtawa kowa, bata rage maka ko sakanni domin tuba ga UBANGIJI ko ga mutanen daka tauyewa hakkokinsu ko zaluntarsu. Ga dai Nazeefa, iyayenta sun cuta mata matu?ar cutarwa, ALLAH yayi mata gata ya bata mijin aure, maimakon ta nutsu ta nema aljannar sai ta shagala, suma suka saka hannu a wajen shagaltar da ita, da taimaka mata cutar da mijinta da zaluntarsa. ?an dazai mata addu'a babu, tabar miji da Sacin rai da takaicin sakashi a masifar rayuwa. Uwa sai a hankali, uba nacan yana ta tashi rayuwar. ?an uwa mu daina tunanin dan munada ?arancin shekaru rayuwa zata cigaba da bamu damar yin abinda muke so har zuwa gaSar tuba ko tsufa, shi UBANGIJI ba abokin wasan kowa bane ba. Wlhy mu dawo hankalinmu, ki dinga sakawa a ranki idan gari ya waye da wuya kikai dare, idan dare yayi da wahala kikai safiya, mu yawaita istigafari, mu rage ma kammu Waukar nauyin mutane koda na kallon banza ne. ALLAH ya gafarta mana ya gafartama iyayenmu =?O? =?-?).
? ? ?? Ba sabuwa kawai ba hatta su Ammie da su Hajiya Yaya wannan mutuwa ta dakesu ?warai da gaske. ?ar samun nutsuwar dawowar su Maanal duk da ance Abah da matarsa Waya da ?anwar matar tasa na cikin wani hali ya Wan kawo nutsuwa a zukata kaWan. Ammie da Nene dake shirin wucewa Abuja jirgin bakwai sai suka fasa saboda wannan rasuwar. Haka shima Daddy da Yazeed dole suka ha?ura. Gida suka wuce aka bar gawar Nazeefa da Jaririnta mai tsannanin kama da ita anan asibitin sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu za'ai mata sutura a mi?ata gidanta na gaskiya. Huznah ma na asibitin aka barta da Salima tunda itace babba..

? ? ? ? Tun kafin magriba Hajiya Basariyya ta dawo gidan, sai dai tunda ta shige sashenta ta zauna a falo tai tagumi bata iya ta motsa ba har ?an asibitin suka shigo kusan takwas na dare. Motsin dawowar mutanen gidan ya saka zuciyarta dukan Wari-Wari, sai dai tun tana tsumayen shigowar wani a cikin ya?anta ko Daddy harta sallama. Dan ko autarta bata gani ba. Kasa ha?uri tayi ta tashi tana le?awa ta window. ALLAH sai da taji zuciyarta kamar zata zubo dan tashin tashin hankalin hango Sageer, Yazeed, Daddy, Baban Sageer, Yayanta, da Baban su Hajiya Yaya da tayi a tsakar gidan. Da sauri ta nufi bedroom Winta kamar zata faWi.
? ? ??  Na shiga uku ni Basariyya badai na rasa Huznah ba? .
? ? Babu mai bata amsa, ta kai zaune bakin gado, sai kuma ta sake mikewa zaram tayo waje. Sai tayi kamar zata buWe ?ofar falo ta fita sai kuma ta koma da baya tana girgiza kai. Hawaye kam da tarawa ake da yanzu an cika wani abu ai. Waya ta Wauka tai kiran Madeena ?arta ta biyu, amma bata Waga ba. Sai ta ?ara ruWewa tai kiran Maman Yaseerah. Itama dai bata Wauka ba. Tun tana le?a window tan hango su Daddy harta le?a taga su ?a?anta sun shiga mota, sai karaf taji makwafcinsa na faWin,  Alhaji Usman ALLAH ya ?ara ha?uri, ALLAH ya ji?anta ya gafarta mata. Bari muje sai da safen an haWu wajen jana'iza .
? ? ? Yaraf kake jin Hajiya Basariyya a ?asa. Ta daddage ta fashe da ihun kuka da faWin,  Na shiga uku ni Basariyya na bani, shike nan na kashe ?ata da kaina. Wayyo Huznah wayyo ALLAH na. Ba ?aramin tayar da hankalin kowa wannan kuka yayi ba. Kowane sashe suka shiga fitowa a guje. Amma duk sai Daddy yace su koma. Haka duk suka koma suna jiyo ihun Hajiya Basariyya da kururuwa tana ?wala kiran sunan Huznah. Tun tanayi da buWaWWiyar murya har muryar tata ta dishe. Daddy kuma ya hana kowa zuwa inda take har ?ayanta. Kuka taci na innalillahi. Daga ?arshe ta zube anan falon tana nishi ?arfinta ya ?are sai hawaye, tayi wujiga-wujiga da irin kukan mutuwar da ba'ason ma musulmi yayi ma mamaci koda ace mutuwar ce.

? ? ? ?? Washe gari ana idar da sallar asuba dangin su Hajiya Yaya suka fara isowa gidan, musamman mahaifiyarta da ?an uwanta. Dan da farko ance tunda babu aure tsakanin Nazeefar da Yazeed aje can gidan su Sabuwar ai jana'izar tata sai shi Baban su Hajiya Yaya ya ro?i alfarmar yi anan Win, tunda koba komai a wajen haihuwar jinin gidan ALLAH yay mata rasuwar. Ba kuma kowa ma yasan da batun sakin ba sai isu isu. Babu wanda ya nema Hajiya Basariyya balle tuna halin da take ciki har aka iso da gawar Nazeefa cikin gidan dana yaron misalin takwas da rabi. Kukan tashin hankalin da Sabuwa keyi ne ya farkar da Hajiya Basariyya daga barcin wahalar daya figeta da asuba. Ko salla batayi ba. Zane kawai ta yayuba ta Waura, ko Wankwali babu a kanta ta fito daga sashenta tana tangaWi. Hakan yayi dai-dai da fito da gawar Nazeefa a mota za'a kaita sashenta. Hajiya Basariyya taje da gudu tana kuka ta ri?e gawa ko lura da Sabuwa batayi ba da itama ta ri?e Win. Kuka take iya iyawa da kiran ta shiga uku Huznah ta yafe mata. Nan dai ta shiga tonama kanta da kanta asiri akan abinda babu wanda yasan ya akayi daga Daddy sai Yazeed, sai Sageer da Huznah ta turama massege..
? ? ? Mutane anyi cirko-cirko ana kallonta, sai Ammie ce tai ?arfin halin zuwa ta kamasu ita da sabuwar, amma babu wanda ya saurareta. Abin ya bama yayan Hajiya Basariyya haushi kawai yazo ya Wauketa da maruka har biyu. Anan ne fa dole ta saki gawar, taruwa akai ana bashi ha?uri, ita kuma aka kamata aka maidata sashenta. Sai lokacin ake sanar mata bafa Huznah bace ta rasu Nazeefa ce. Huznah na asibiti ita. Wannan shine ya kawo ma zuciyar Basariyya salama. Asiri dai kuma ta riga ta tonama kanta shi ai, dan yanzu dai kowa yasan mike faruwa sai ALLAH wadai ake da halinta........
'?



*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =??=?O?_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*


______________


........Anan Abuja har dare babu wani bayani akan Abah da Oum. Dole su Umma suka tattara kowa aka wuce gida musamman ma su Maanal dake bu?atar wanka da abinci tunda an dubasu babu wata matsala. Itace ma dai abinka da mai ciki sai da suka Wan saka mata drip. Anan aka bar su AA. Gawar Anum ma sai zuwa safiya zasu amsa. Haka suka kwana su da suke gidan, da su da suke a asibitin babu wani kwanciyar hankali..
? ? ? ?? Washe gari anayin sallar asuba suka koma asibitin. Isarsu babu jimawa kuma ta ALLAH ta kasance akan Nana itama ALLAH ya Wauke kayarsa. Gigicewa su Nuratu sukayi matu?ar gigita ma kuwa. Musamman Saheeba da sai lokacin ta farko daga nata barcin wahalar. Dan itama dai ta maku matu?ar makuwa. Ga ciki ya fita gaba Waya mahaifarta kuma ta samu babbar matsalar da har abada bazata sake haihuwa ba. ALLAH sarki Aunty kuka take tana ?ari ?an uwa duk suna neman kuSuce mata. Dan itama dai Mamy Win sai a hankali. Ga abin kunyar data tafka na ciyar da Abah guba, wai uban ?ayanka kai jama'a, wannan wane irin rashin imani ne da bushewar zuciya. A yanzu haka tana kwancen amma hannunta Waya da handcuffs. Dan ita ?ar?ashin ma jami'an tsaro take. Mahaifin su Nuratu ma da ?an uwansu duk sun iso Abujar. Haka suka Wauki gawar Nana suma aka nufi gidan Hajiya Turai da ita. Ita kuma Anum gidan Darma. Saheeba kam ma babu damar barin asibiti, haka ta dinga kuka sai da akai mata allurar barci mai ?arfi.
? ?? Umma ce tama Anum wanka, aka sallaci yarinyar aka binneta anan cikin gidan ta garden tunda yarinya ce sosai. Amma rasuwarta ta daki yan gidan, dam itace suka fara rasawa a gidan yarinya mai wayo. Sauran na baya da suka rasu

108 / 138

Chapters