Advertisements
Chapter 79 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc Hausa Novels
Advertisements

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   79 / 138

234K to 237K   out of 412.8K words

tada mu salla ba.
? ? Nusaiba dake kusa da ita ta ce,  Yanzu nake son yin magana Amrah, amma jeki le?ata ko itama makarar tayi jiki da jini. Balle Kinga kwana biyun nan ba wani isasshen barci take ba .
? ? Kai Amrah ta jinina tana mi?ewa, mintuna kaWan sai gata da gudu har maganarta bata fita sai nuna hanyar waje take. A zabure duk sauran ?an uwan nata suka mi?e suka bita. Wani irin shock da tashin hankali suma suka shiga da ganin Hajiya Yaya a Waure. Ga Wakin yay kaca-kaca alamar ansha bincike a cikinsa. Atare kuwa sukai kanta suna kiranta kowa na fashewa da kuka. Sai dai koda suka cire abinda ya Waure bakinta ma bata numfashi, kuka suke na tashin hankali. Siyama dake babba a cikinsu ce tai hankalin kiran layin Daddy. Yana Wagawa ta sanya masa kuka da faWin,  Daddy wlhy Sarayi sun shigo mana gida jiya da dare. Sun Waure Mamma gashi nan ma bata numfashi .
? ?? Matu?ar bugawa ?irjin Daddy yayi, dama yau yake shirin su koma gida Ammie dai sai gobe idan ALLAH ya kaimu dama sukai da ita. Cikin ruWewa Daddy yace,  Ina Yazeed, ku kirashi, nima in sha ALLAHU gani nan tahowa .
? ? ?  Daddy kasan ko mun kira Yaya ba zuwa zai yi ba. Daddy mun shiga uku idan Mamma ta rasu ya zamuyi . Kuka ya sar?eta. Tausayin yaransa ne sosai ya ratsa shi. Cikin kwantar da murya ya ce,  Siyama bazata rasu ba in sha ALLAHU. Ku kwantar da hankalinku bara na turo muku Doctor. In sha ALLAHU nan da awa biyu nima zan iso, idan kuma mun samu train shike nan ma, kumata addu'a kudai, kinga kace babba sai kin nutsu suma sauran zasu nutsu okay .
? ?? Kai ta jinjina kamar tana a gaban Daddyn ta share hawaye. Gaba Waya Daddy ma shi ya rasa ina zai kama. Sai kawai yay kiran layin Ammie. Amma ba'a Waga ba. Doctor Winsu ya kira ya sanar masa yaje gidansa Please da gaggawa ana bu?atarsa. Yana yankewa ya kira dpo Win dake station Win kusa da anguwarsu. Da ga haka ya sake gwada kiran Ammie amma ba'a daga ba. Dole ya ajiye wayar ya tada su Waleed da suka koma barci yace su shirya. A gurguje duk sukai shiri, cikin sa'a ya kira train station ya samu ticket. Gidan su AA suka nufo yana cigaba da gwada kiran Ammie. Amma har suka iso bata Waga ba...
? ?? Ammie wayarta na'a silent ne, anata kuma wannan kai-kawo na Maanal sai ga na Mamy, shiyyasa sam bama tasan Daddy na kiranta ba. Sai yanzu da kowa ke fita ta Wauka wayar dan kiran su Shahidah taci karo da miss calls din Daddy da yawa. Sai da gabanta ya faWi, tai ?o?arin kiransa back. Aiko kasancewar ita Win shima yake son kira dama ko ringing batayi ba ya Waga. Cikin tashin hankali Ammie ta ce,  Daddyn Hameed lafiya dai kuwa. Tarin miss call Winka sun tada min hankali .
? ?? Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya sanar mata ai gashi ma a gidan Darma Win. Yana tare da Babban Yaya yanzu haka. Dan cikin sa'a motar Daddy na shigowa Babban Yaya na fitowa daga sashensa shar da shi. Sashen Oum yake shirin wucewa ya hango Waleed na fitowa a mota shine ya nufosu. Koda Ammie ta fito ta samu har su Abah ma sun fito dan Daddy yace bazai shiga ba. Train Winsu na gab da wucewa.
? ?? Koda Daddy ya gaya mata ta shiryo su wuce hankalinta sake tashi yayi. Abah ne yace ta kwantar da hankalinta ga abinda ke faruwa ne. Aifa Ammie da saurinta ta juya ciki tana sanar masa Hajiya Basariyya na nan tare da su ai. Daddy yace ya korata. Shi kuma ya fara ?o?arin saya mata ticket Win da farko ya manta ne ma gaba Waya tana nan itama. Babu abinda Ammie ta Wauka sai wayarta da handbag, acewarta Amaal ta taho mata da sauran kayan. Kowa nata jajanta al'amarin. AA nason tashi babu dama, haka ya ha?ura yabi Ammie da addu'a, amma yasa a ransa in sha ALLAHU ko yau bai bi bayansu Kaduna ba zuwa gobe zaije.
? ?? Sai da su Ammie suka wuce sassan su Oum suka dawo ciki ana ?ara jajantawa. Sai lokacin kuma Babban Yaya kejin Lilly da Mamy babu lafiya. Sai ga Yaya Fawzan shima kamar an saita. Farin ciki matu?a suka nuna da jin labarin cikin jikin Lilly, suka jajanta na Mamy dake kwance tana jin kowa amma tai lambo. Shi dai RK yasan ba barci take ba, amma yay shiru kawai....
Cike da tsokana Yaya Fawzan dake kallon AA bayan ya gama duba result Win gwajin Maanal da RK ya bashi dan neman magana. Kasancewar yana zaune ne a bed side drawer kusa da AA ?asa-?asa ya ce,  Uhm-uhm wato yaron nan kai bala'i ne, afa ranar daka tafka tsiyarka a ranar komai ya kankama...
? ? ?? Baki buWe AA ya kalla Yaya Fawzan, sai kuma ya kalli inda Babban Yaya ke tsaye jikin mirror yana danna waya. Ganin hankalinsa ba'a kansu yake ba ya dawo da kallonsa kan Yaya Fawzan dake dariya shi da RK. Caraf RK yace,  Kai ko babban sauro ne fa, kaima kasan sau Waya yake shan jini a kwanta. Bugun ?an ball ake gaya maka Son .
? ? Ai dariya suka sake kwashewa da shi, har Babban Yaya na Wagowa ya kallesu. Ya ce,  Kuna lafiya kuwa? .
? ? ? AA daya watsa musu harara ya ce,  Inafa sukaga lafiya Yaya. Ai sai kun haWa da addu'a .
? ? ? ??  Tare dakai za'a haWa ai mana addu'ar ai. Ka gama tafka tsiya a Waki ka fito kana mana wani sanyi-sanyi kai na ALLAH .
? ? ? RK ne mai maganar yana hararar AA. Kai AA ya girgiza kawai. Babban Yaya yayi murmushi da faWin,  Ku biyun nan dai kun saka min Auta a gaba. Bayan kuma da naku tambarin a goshi.
? ?? Yaya Fawzan ya ce,  To ai mu Yaya bamuyi musu ba. Shi ko fa, yayta wani ciccin magani yana dakewa. Kai yau ba gashi fuskarka murmushi ya?i barinta ba alamar godiyar UBANGIJI  .
? ? ? Da gudu Babban Yaya ya waro idanunsa akan Yaya Fawzan.  Oh iya shegen naku ya bar kan Auta ya dawo kaina kuma kenan? . Yay maganar yana wurgoma Fawzan gwangwanin turare. Mi RK da Fawzan zasuyi in ba dariya ba. Shi kansa AA ?asa yay da kai yana murmushi, dariyar kuwa ya danneta da ?yar. Dan harga ALLAH shima fa tunda Babban Yaya ya shigo gulmarsa yake a zuciya. Fuskarsa a sake, ga wani ?yallin angwanci da cikar kamala a tare da shi. ?amshinsa kam gaba Waya ya gauraye da wanda ba nashi ba...........
'?



Ehem-ehem >?#?>?#?=??



*_AJIYA A DUHU na kuWi ne, 500 ne kacal, ?ar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai =??=?O?_*

*+234 805 568 7449*



*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*

*_=???AJIYA A DUHU....=???_*

*_Bilyn Abdull ce >??
*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*

*_BOOK 2_*

______________

......... Oh jama'a, yaran nan jiyya kukeyi ko shargallenku? .
Oum data le?o ta faWa tana kallonsu. Mu?uy AA ya haWiye murmushinsa yana nuna RK da Fawzan.  Oum kin san in dai waWan nan biyun na a waje to sai addu'a. Sun addabemu ki korasu waje dan ALLAH .
Oum dake satar kallon Babban Yaya ganin yanda fuskarsa ke ta annuri ga murmushi ya?i barinta ta ce,  Ai za'a kai ga hakan Auta. Kunsa marasa lafiya gaba dan iya shege sai dariya kuke? .
RK yace,  Aunty ai barci suke. Kuma dariyarmu nutsuwa ma zata basu su duka kedai jeki cigaba da hidimar bikinki Maman anguna .
Kai Oum ta girgiza kawai da faWin,  ALLAH to ya shiryeku ta juya ta fita. Kusa da Babban Yaya RK ya koma ya tsaya. Da sauri Babban Yaya yace,  Kana cewa tak zan ajiye kawun gefe nima nayi ta auta yau. Tunda na fahimci kai da Fawzan kun zama ?an iska yanzu .
Ai yanzu kam AA sai da ya dara. ALLAH sarki babban Yaya yana tsoron yan iskan biyu su tasashi gaba. RK da Fawzan kam dariya ba'a magana. RK ya ce,  Haba Son yada tsarguwa haka? Nifa tambaya kawai zanyi amma kana neman fassarani da wani abu kuma .
Babban Yaya ya hararesa da faWin,  Bar tambayarka na yafe. Shiyyasa auta ya raina ku wlhy, manyan banza ne anan kawai. Kudai tuna ga Lilly nan kwance zata iya farkawa ta jiku. Ga kuma Mamy .
Cike da mugunta RK yace,  Ai Mamy barci take bil ha??i, Lilly kam tashinta ba yanzu ba.
A hankali hawaye suka silalo ta gefen fuskar Mamy, kasancewar tacan take kwance ta juya musu baya ba gani suke ba. Tsinuwa take jerama RK a zuciyarta tari-tari. Dan yau tsanar da take ji tana masa tafi ta kullum shi da kowa ma dake a Darma Family. Wani irin sukar zuciyarta da ?onata dukkan hirar da sukeyi take mata. Zuwa yanzu ji take tazo gaSar da bazata iya ha?uri ba, dan in har tai hakan lallai Fateema na shirin cinta wasa ne. Kuma wannan cikin tayi alwashin ko zata tafi tsirara sai ta zubar dashi wlhy. Manaal bazata taSa haihuwarsa ba...

Ehem-ehem. Ashe watan samun matsalar AA da Mamy ya tsaya kuwa>?-?, dan wannan cikin duk wanda yay gigin taSashi to bara dai nai shiru, Wan soyayya ne fa, komu ai sai inda ?arfinmu ya ?are ko ya kukace mutane na?=??=??

_______&

Anan Mamy na a birkice da batun ciki can ma Sangaren Nibras da Saheeba da su Nuratu da uwarsu cike zukatansu suke da ba?in ciki bayyananne kai kace sun haWa miji ne da Maanal Win su duka, dan kishinta suke ji na gaske a zukatansu bayan kishiyoyin nasu. Karan farko Nibras taji wani abu mai kama da tashin hankali a ?asan zuciyarta game da haihuwa. A sati huWu kacal cikin na biyar Maanal nada cikin masoyinta AA, itama Najma fa nanda wata sati biyar Win za'a iya cewa tana da cikin mijinta kuma. Hakama Ameerah zata iya samu. Ga Saheeba ance ciki ne da ita itama. To itafa?. Zuciyarta tai wani kalar motsawa. Ai babu shiri ta Wauka waya ta kira mamanta ta labarta mata komai. Itama dai Maman tata hankalinta ne ya tashi, dan sak irin tunanin Nibras Win ne yazo mata. A sanyaye Mom dinta ta ce,  Nibras kodai kinsha wani abun hana Waukar ciki ne a farkon aurenku? Shekara biyar ana shirin kulle ta shida ba wasa ba. Kin fa samu Saheeba da tsohon ciki a gidan nan, ta haihu kina nan, ta raina ta yaye ta sake samun wani ta haifa ta raina ta yaye, badan ma jinkiri data samu ba da yanzu maybe tayi wani wannan cikin da akace ta samu zai zama na huWu ne. Ga kuma wadda aka auro jiya-jiya itama harta samu. Suma wannan da suka shigo karki raba Wayan biyu nan da sabon wata su fara nasu amaye-amayen tunda Waukar cikin yanzu ba wuyane da shi ba. Shi ke nan kin zama ?ar kallo mu da dukiyar Darma sai hasashe daga nesa muna ji muna gani wasu naci. Lallai muna cikin babbar jarabawa, dan ba haukan kishi ya kamata na tayaki ba Nibras rashin samun cikin ki ya kamata ya dameni ma a wannan gaSar. Nibras kinsha wani abu ne? Ki gaya min dan ALLAH nasan ina zan kama ina zan samo mafita .
Shiru Nibras tayi kalaman mahaifiyarta na mata luguden daka a zuciya da ?wa?walwa. Mahaifiyar tata ta daka mata tsawa daga can.  Nibras! Magana nake dake fa kika min shiru! Ki faWa min kinsha wani abun hana Waukar ciki ne dan ubanki?!!! .
Tsabar yanda tsawar ta ratsata sai da ta zabura jikinta na Wan rawa. Sai kuma hawaye sharrr suka shiga ziraro mata kamar an buWe fanfo. Tasan halin mahaifiyarsu sarai, da abinda zata iya, ta musu raino na gata musamman ma ita da take mace, amma idan tana son abu bakai mata ba ka banu, sarai zata iya Waukarta takai asibiti a bincikata. Dan haka gara ta faWa mata gaskiya kawai. Murya na rawa ta ce,  Wlhy Mom allura ce kawai nayi kuma lokacin ma da sukace zata daina aiki tuni yayi, kuma wlhy daga nan ban sake zuwa nayi ba, ban kuma sake shan komai ba shekara kusan huWu kenan .
 Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un! Amma ban taSa sanin ke wawuya ce ba mai dusa a cikin kai irin yau. Ashe ni wahalar banza ma nake. Nibras dama ke muguwar yarinya ce ban sani ba. Wlhy dana san abinda zakiyi kenan da ni na auri Aliyu Darma Win ma kawai bayan mutuwar ubanku, kuma wlhy babu abinda zai hana na haihu masa a shekarun nan nawa. Ai shike nan sai ki fara shirin dawowa gida mu cigaba da goga jigida dan amarya dai kam ta gama samun gida. Dama gata ?ar uwarsa, ke da kanki yanzu kike faWin irin murnar da sukeyi akan cikin facalarku, shiyyasa dama gaki nan ko kwarjini baki da shi a gidan, to kin kasa sama musu abinda suke so mara hankali wawuya kawai......
?itt ta yanke kiran. Wani irin fashewa da kuka Nibras tayi dan kamar uwarta ta mata wata allura ne mai ?arfin gaske a yanzu.....

&&

A Sangaren su Saheeba kam, ko le?owa duba Mamy basuyi ba kuma sunji sarai ance ta faWi, balle Maanal ta samu itama, suna can suna ?ulla hanyar salwantar da cikin Maanal Win kamar yanda Mamy tai alwashi. Maman Saheeba ta rantse ta ?ara rantsewa Saheeba ce kawai zata haihu a gidan sai Nuratu idan ta shigo itama. Amma har Najma da Ameerah da Nibras basu isa ba, dukiyar Aliyu Darma ta ?ayanta ce kawai a gidan. Har Mamy data haifi ?a?an zero zata tashi. Balle Oum datai wahalar banza.
Saheeba dai da akema ?arin ruwa hawaye kawai take yi, hakama Nuratu kuka take rurus jikin Hajiya Turai data zo da likitar data duba Saheeba. Dan da wani mugun zazzaSi ta tashi tanata sambatu dole Nuratu ta kira Nana ta sanar mata. Shine Babban Yaya na fita suka shigo bayan hanyar bedroom Win Ameerah tasha harara. Hajiya Shuwa kanta yau tasha zagi gwargwadon iko bama Oum kaWai da Babban Yayan kansa ba.
Suna gama ?ulle-?ullensu Hajiya Turai data fito tai kiran Sille ta labarta masa komai. Dariyar mugunta yayi da faWin,  Ai na daWe da gane shegiyar matar ?anin nan naki mayyar kuWi ce. Shashasha kafin ?a?an nata su gama haihuwa mazan nasu su mutu ni na gama tatikesu tas. Dan sai na ?arar da abinda kamila ta tara kaf ta koma amso na ?a?an nata tana tura min, ?arshe ta fara satar na mijinta shima dan ubana ma nada ha??i a ciki ai.... sai kuma ya wani kwashe da dariya cike da mugunta. Hajiya Turai na tayashi. Dama Haule ta kira shi ta gaya masa komai na zancen ciki da faWuwar Mamy yanzu babu jimawa....

_______&

Barci Babban Yaya ya bar Ameerah nayi, dan haka bata san wainar da ake toyawa ba sai kusan sha Waya ta farka. Wani irin zazzaSi take ji a jikinta, ga ciwo da ko'ina ke mata. Tunda taga babu Babban Yaya a Wakin tasan ya fita ne. Sai dai akwai wayarsa Waya ajiye bed side drawer. Cikin dauriya ta Wan kintsa Wakin ta shiga bayi tai wanka ta sake gasa jikinta yanda taga yayi mata Wazun. Sai kuma cikin ikon ALLAH taga maganin da Mommy ta dinga dafama Maanal tana sit bath. Tunanin itama tayi amfani da shi ne yazo mata. Dan haka koda ta fito a wankan sai ta zura dogon hijjab ta Wauka Wauri Waya ta fito cike da dauriya domin dafawa a kitchen. Gida cike da mutane ai bataso a shigo a ganta tana wannan tafiyar gwale-gwalen ba. Sannan ai ya kamata ta fita ta gaida su Oum amma take a haka ai da kunya. Dan duk wanda ya ganta ALLAH sai ya gane abinda ya faru. Ga idanu a kumbure tasha kuka. A bisa tsautsayi ta fito Win ne tana shiga kitchen taji wayar da Hajiya Turai keyi, kuma tas taji abinda ta maimaita ma wanda suke wayar da Nana ta faWa. Mamakin duniya ya zagaye zuciyar Ameerah. Gabanta ko sai faWuwa yake. Da sauri ta baro kitchen Win ta koma Wakinta zuciyarta na kai-kawo da fasa maganganun dalla-dalla. Tofa babbar magana, shin Maman kishiyar tata ba uwa Waya uba Waya suke da Mamy bane? Kamar dai haka ta sani tun tuni. To kenan akwai wata a tsakaninsu kokuma AJIYA A DUHU Maman Saheeban keyi batare da sanin Mamy ba. Wato su bazasu haihu ba sai ?a?anta kawai. Tur?ashi. Eh lallai tasan yau ta shigo family house aure kam. To lallai akwai tsallen baWake kenan. ALLAH sarki Maanal ashe ciki gareta, ta tayata murna sosai ita da Yaya AA, kuma sai inda ?arfinta ya ?are wajen kare cikin nan. Za kuma ta sanya ido akan su Saheeba ?warai d gaske..........
'?


Tofa, sabon wasa kenan tsakanin su Saheeba da Ameerah >?q?=??

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu =?-?=?O?_*
*_Typing=???_*

*_=???AJIYA A DUHU....=???_*

*_Bilyn Abdull ce >??
*_(P3REP

79 / 138

Chapters