Advertisements
Chapter 120 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   120 / 138

357K to 360K   out of 412.8K words

taimaketa ya fito da ita daga ?auyen ya kawota bakin titi inda yasan manyan motocin na wucewa kuma hausawa ne drivers Win. Da ?yar suka samu wani ya tsaya, a gurguje ya sanar masa komai, shima an dace mutumin kirki ne ya Wakkota shi kuma wancan ya koma. Wannan shine sanadin dawowar ta gida. Dan direban ya kaita kano daga can ya sakata a motar Kebbi..
Wannan labari na Ha?ila ya girgiza kowa, Sailu tace zata zubar da ciki maigari yace kull, idan kuma taje ta kashe ta wajen zubar da cikin fa. Ai dole haka zasu amshi ?addara ta haihu. Idan kuma wani abu ya samu ciki to sai sun kai ?ararta Suru wajen hakimi, a hakan ma maigari ya tabbatar da sai ya gayawa hakimi komai gudun abinda zai iya zuwa ya dawo koda nan gaba. Wannan fa takunkumi da akaima Sailu ne ya hana a zubar da cikin Ha?ilah. Dole ta cigaba da rainon sa zuciyarta babu daWi ta uwarta babu daWi. Ga halin da suke ciki akan hiv. Dan itama Ha?ilar na jin haka ta janye jikinta daga Gwaggo da Sailu. Tace bazasu goga mata jaraba ba.....

__________&

A yau su Maanal suka wuce ?asar Saudia. Ita da Ameerah, Najma, babban Yaya, sai Yaya Fawzan da AA. Dan har yanzu Nibras na gidansu suna neman mafita ita da uwarta. Sai zaryar asibiti sukeyi daga ?arshe suka samu Yaya Fawzan wai zasu kaita Egypt ganin likita kwararre. Bai hanasu ba yace ALLAH ya kiyaye hanya. Shi ko Babban Yaya babu ma wata kwana-kwana ko neman dalili ya gaya ma Saheeba ga inda zasuje, zata Waga masa hankali yaja mata gargaWi da tuna mata halin da take ciki na jiyya da shan magani. Dan har yanzu ko turaka bata koma ba, duk da taso yin hakan likita ne ya kafa mata sharaWin sai ta kammala shan maganinta. To a yanzu dai tana gab da kammalawar, sai kuma ga batun wannan tafiya da take ganin Babban Yayan ya samu na makalewa. Taso zuwa takai ?ara ma Aunty, Nuratu ta kwaSeta. Tace ta barsu suje mana kwana nawa sun dawo. Tace ita tana son zuwa taga Naufal ne. Nuratu tace,  Idan suka dawo basai muje ba .
 Da wane kuWin? Bayan kin san komai bamu da shi yanzu? .
 Shi Yayan zai biya mana ai. Muma sai muce zamuje duba Aban, shi ya?i ai Wan zamba ne ko . Da wannan karatun Nuratu ta kwantar mata da hankali. Sai dai ita Nuratu tana da nata shirin ne shiyyasa bata damu da tafiyar mutanen gidan ba. Hasalima daWi taji dan hakan zai bata damar yin komai yanda ya kamata. Haka kuwa suka wuce suka barsu gidan shiru. Aunty duk sai taji zaman babu daWi, gidan ya musu girma. Haka ma su Saheeban. Ashe mutane rahama ne.
Aunty na basu shawarar dawowa sashen Mamy caraf Nuratu tace to. Kallonta Saheeba ta tsaya yi, dan ita kam ta kasa fahimta da gane mi Nuratun ke nufi a kwanakin nan take son maida ala?arsu da sashen Mamy. Koda ta nema ba'asi sai Nuratun tace babu komai. Kawai dai ita tana jin tsoro ne gaskiya. Badan Saheeba ta gamsu ba ta amince. Haka suka tattara suka koma can. Mamy zatai magana Aunty ta hanata. Dole tai shiru amma dawowar su Saheeban sashenta ya sosa mata zuciya. Abinka da mugu shi yasan makwantar mugu sai ta kasa aminta da su. Dan haka ta saka sabuwar mai aikin da su AA Win suka kawo tana taimaka musu da abinci da gyare-gyaren sashen saboda kar abubuwan suma Aunty yawa ta saka musu ido. Sai dai kuma an samu matsala, dan kuwa a yanzu Mamy bata da ko sisin bama mai aiki tai mata aikin da take so koda na mugunta ne kamar su Haule, ita wannan Wauka ma take taimakon su Mamy Win akai aka kawosu gidan dan daga ?auye aka kawota bata san abinda ya faru ba. Sai dai irin ?war?wararrun matan nan ne da komai zasu iya aikatawa akan kuWi. Tsaff kuma Nuratu ta fahimci hakan dan haka ta fara janta a jiki, sannan ta dinga yima Mamy hidima har Aunty ta ji ta gamsu da Nuratu ta canja ne. Sai kawai tace bara ta Wan je kano taga yara ta dawo. Dan duk da sun girma suna karatunsu kuma babansu na kula da su da abokiyar zamanta, sun kuma zo har sau uku sunga Mamyn itama ya dace taje ta gansu. Mamy zata nuna mata isa wai bazataje ba Aunty tace  A dalilin mi. Ba gori ba Kamila idan bani Win ba wazai zauna dake? Ko kinga a cikin dangin nan namu wani ya kiraki ko a waya ya miki jajen abinda ya faru balle jin yaya kike? Wata kusan huWu ai kyamin adalci da kanki ma kice naje naga nawa iyalan, ko kin manta miji ne dani nima .
Shiru Mamy tayi dan kalaman sun mata zafi kuma. Itako Aunty ta watsar da ita tai shirinta ta wuce ta barta da su Nuratu......

________&

Oum da Abah da kansu sukaje taro zaratan mazajen ?a?ansu da matansu har jidda. Cike da farin ciki su AA suka rungume Oum, kafin su koma kan Abah, su Maanal suma suka rungume Oum, sunyi kewarta matu?a irin yanda baki ma bazai iya muslatawa ba. Haka itama tayi kewarsu, ga farin cikin ?aruwar da aka samu ?a?ayen nata duka uku da cikunnansu. Shi kansa Abah wani irin farin ciki yake ji, dan ya tabbatar da zuwa yanzu yaransa sun sami irin farin cikin auren daya jima yana musu addu'a da fatan samu. Sun sami irin matan da yake fatan ganin su a ?ar?ashin ikon su. Fatansa ALLAH ya saukesu lafiya daga alkairin da suka Wauka. A tare suka du?a suna gaishesa. Da sauri yace,  Haba yaran albarka ku tashi ku tashi abinku, muje mota kun gaji ayi gaisuwar a gida. Babu musu suka shiga haWaWWiyar motar da akazo Waukarsu suka Wauki hanyar Madina inda su Aban suke..........
'?
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*

*_Typing=???_*




AJIYAH A DUHU

189

......Sosai gidan da su Oum suke yayi ?yau, ba wani babba bane ba kuma mai hayaniya ba. Ga abinci kala-kala Oum ta shirya musu. Dama duk yunwar suke ji, dan haka babu Sata lokaci kowa ya baje sukaci suka ?oshi musamman Maanal da yanzu sam bata wasa da cikinta. Suko su Najma ma abincin sai da suka zaSa, musamman Ameerah cikinta nada tsurfa, ba komai take iya ci ba.
Su Maanal ne suka tattare komai zuwa kitchen, duk da akwai mai aiki suka taimaka mata aka wanke komai aka maidashi inda yake. Sai lokacin aka gaisa sosai aka Waura da hira. Abah babu ruwansa, shi kallon ?a?a yake musu ba surukai ba, dan haka jansu yake sosai a jikinsa da labari masu ma'ana. Sanin sun gaji Oum tace suzo suje masauki ayi hirar bayan sun huta. Basu musa ba dan tabbas sun gajin, musamman ma matan da kowa ke fama da kanta...

Masaukin da inda su Oum suke ba wani nisa sosai, dan a ?afa ma sukai musu rakkiya har Abah. Sun ji daWin hakan duk da shi Babban Yaya yasan wajen dan shine ma ya kama masauki, hakama gidan da su Oum Win ke zaune mallakinsa ne. Daga gate su Abah suka juya, su kuma suka ?arasa shiga ciki. Ai yanda kowa yay tiSis suna amsar keys Win Wakunan kowa yaja matarsa suka shige. Basu sake jin juna ba sai washe gari, dama Oum ta riga ta cika musu ciki miya rage kuma. Barci kawai. Aiko barcin suka sha sosai, sai washe gari zasu tafi gidan su Oum yin breakfast suka haWu da juna.
Rayuwar saudia tama su Maanal daWi, dan wata irin rayuwa ce mai saka farin ciki da sha?uwar zuminci. Sai suka ji kamar ace inama iya su kaWai ne kawai. Sun gabatar da umrah, sunyi yawo kuma sosai sunyi farin ciki. Dan ma Maanal bata jin daWi sosai dauriya ce kawai, har ma su Ameeran kowace laulayi ya sakata a gaba amma suna daurewa dan ji suke kamar kar a koma Nigeria anan kusa, dan tattali da soyayya kawai suke samu daga zaratan Oum. To ashe ma mazan nasu sun shirya musu ma shiri na musamman ne. Dan satinsu uku a Saudia suka Wauke Aban da Oum suka wuce wata ?asar. Abah harda musu faWan ai da sun san yawo suka fito da sun taho da Nibras da Saheeba suma. Su dai suka lallaSashi kawai aka tafi. Abin kamar wasa sai gashi sun zagaye ?asashe sosai. Dan kuwa watanninsu biyar ciff Maanal har ta shiga watan haihuwarta. Ameerah da Najma nasu cikin duk sun fito ana gani masha ALLAH. Da yake tuni su Oum sun sake komawa Saudia dan ?asa uku kawai sukaje sukace sun gaji sukam suka koma saudia suko sukai gaba. Suma saudia Win suka sake dawowa. Hankalin Oum ya tashi ganin yanda Maanal tai nauyi sosai. FaWa ta fara musu akan yanzu haka Maanal Win ta koma amma suka zauna. Yanzu ina zasu Wauketa haka zuwa Nigeria, ai dole su bari ta haihu anan kawai sannan su tafi.
Su duka sun gamsu da hakan, sai suka sake mi?e ?afafun hutawa a Saudia abinsu.....

_________&

A Nigeria kam tunda su Babban Yaya suka wuce Aunty ma ta tafi Kano Mamy da su Saheeba babu zaman lafiya. Basa taimaka mata da komai koda Worata a weelchiar ne dan yanzu dole a kanta take saboda ?afarta data samu matsala bata iya takata sam. Ba kuma harbin ne yaja matsalar ba ainahin karayar data taSa yi ce lokacin bikin su Maanal take neman zame mata damuwa a yanzu. Babu kunya idan ta zagi su Saheeba suke ramawa.
A randa Aunty ke cika kwana uku da tafiya sai Saheeba ta saka mai aiki ta dafa mata nama zata ci, ta fita zuwa sashenta Wakko abu sai ga Mamy ta fito a Waki dan yanzu itama a downstairs take saboda babu ?afafu. Ta gunguro kekenta ta ?walama mai aikin kira. Koda ta fito tana kallonta da idonta Waya duk da akwai gilashi dan dole take sakawa saboda rufe munin ido Wayan da Sille ya fasa mata duk da ya warke sun masa dabara an rufe shi amma babu ?yawun gani kuma bata gani da shi kwata-kwata sai ake sirrintashi da gilashin.
 Mi kikeyi a kitchen tun Wazun Ina kiranki kizo ki saukeni a gado? .
Mai aiki na Wan tuttura baki da yamutse fuska dan ko shakkar Mamy bataji, hasalima har rashin kunya take mata, tana zaune ne kawai dan kuWi gata dama ba yarinya ba ta ce,  Ayya Hajiya Saheeba ce ta sakani dafa mata nama, kema ya kamata kina Waga murya, kuma kina ?o?arin kanki bawai komai kice sai an miki ba kina zaune turus .
Sagale Mamy tayi tana kallonta, sai kuma cikin Sacin rai da gadarar data zame mata a jini ta ce,  Iye ni kike gayama haka kina ?as?antacciya ?ar aiki na da nake biya. Ko baki san nan gidan mijina da ?a?ana bane ba...
 Ake dai biya na, kuma kece ?as?antacciya wlhy, dan koba komai ni halak Wina nazo nema ba son kashe miji da kishiyar da tai min hallacin bani mijinta na aura danna handame dukiya ba. ?a?a kuma na mai su dai Hajiya Fateema matar ?warai ba naki ba, dan in za'ai ya?in duniya na uku zamu tsaya mata ?a?a nata ne kekam ga naki can barbaWaWWe Sille yake ko mi. Ke bari kiji nifa badan kuWin da ake biyana ba babu abinda zan zauna yi a nan, ke har kina tunanin kina da wani sauran capacity ne a yanzu, dibeki fa kamar wata almajira, yo banda ma kishiyar taki data matsa ki dawo gidan harta Waukeni matsayin mai aiki na miki hidima da yanzu kina bakin gada kina bara wlhy, dan wannan ?a?an da kike tunanin kin haifa ko ?aunar ganinki basa son yi yanzu banzar mata kawai. Ko ca kike ban san komai a kanki bane yanzu, to na sani wawuya .
Ta juya zata koma ciki, sai kawai ba?in ciki da zuciya suka kwashi Mamy ta fisgo matar mutane, keda kike zaune kina fama da ?afa Waya ga babu ido ina ke ina faWa da mace maiji da ?arfin jiki gata rainon ?auye jikinta ya ginu da ingantaccen tuwon dawa dana masara ga aiki. Ai ko tana juyowa ta falle fuskar Mamy da lafiyayyen mari, ta kuma shiga jibgarta. Ihun Mamy ya fargar da su Saheeba, suka shigo da gudu, tsabar mugunta Saheeba ta kulle ?ofa da windows tana faWin,  Wlhy ci ubanta uwangale karki raga mata. Ki mata lilis, kiyi komai ba komai abinki muna bayanki.
Wannan zuga ta Saheeba ta sake tunzura Uwangale, ta cigaba da jibgar Mamy da ?yau, Nuratu kam wata dama hakan ya bata, da sauri ta nufi Wakin da suke ta Wakko syringe, haka ta Wiba jinin jikinta tana matse baki ta fito da shi a Soye. Har lokacin Uwangale nakan Mamy tana suburbuWa, sai kawai tai kamar zata taimaki Mamy a hannun Uwangale ta samu ta danna mata allurar wannan jini a jiki. Ta Soye syringe a jikinta sannan ta kwaci Mamyn data gama yin lilis sai kuka take yi.
Nunata Uwangale dake hakki tayi, ta ce,  Shegiya munafuka karuwa maima maza fyaWe. Gobe dan ALLAH ki sake kawo min wargi ki gani. Ke bama ni ba ko wani a ma'aikatan gidan nan kika sake ma koda kallon banza sai na miki abinda yafi haka. Bakince ke muguwa bace mai ba?in hali, to kin sami mai horaki kuwa a gidan nan dan nice zan koya miki tarbiyyar da kika gagara samu tun daga ?uruciya. Kuma idan ?ai?ayin bakinki ya jaki kika gayama wani ko Hajiya Shuwa da Maimoon idan sun shigo ko Hajiya Asiya idan tazo zaki sha mamaki wlhy suna fita zan sake zaneki .
Sosai ALLAH ya tasirantar da tsoron Uwangale a zuciyar Mamy, su Saheeba kam suka dinga kwasar dariya. Sai gashi koda Hajiya Shuwa ta shigo Mamyn kasa gaya mata tayi, sai tace wai faWuwa tayi lokacin su Saheeba basa kusa Uwangale kuma na kitchen haWa mata abinci. Hajiya Shuwa harda yima su Saheeba faWa akan su daina nesa da Mamyn, su kuma kamar na ALLAH sukace in sha ALLAHU zasu kiyaye. Hakama da Ammie tazo suka tsarata. Dan Hajiya Shuwa da Ammie suna iya ?o?arin su na zuwa duba Mamy, Ammie idan tazo yau sai gobe ta huta jibi tazo, wani lokacin harda Hajiya Yaya da yara suke zuwa. Hajiya Shuwa kuwa safe da yamma ita da Maimoon suke shigowa. Damma ita Maimoon Win na fama da kanta ne dan laulayin ta mai wahala ne sosai. Shi kansa Ameer duk bayan kwana biyu yana zuwa yaji mi suke bu?ata duk da kuwa komai sai da su AA suka ajiye, ga RK kullum yana cikin musu hidima dan gidan yake kwana ma saboda Nuwaira na Kano. Oum tace kuma bai kamata abar su Mamyn su kaWai ba duk da akwai masu aiki da securitys da aka ?ara a anguwar dama ?ofar gidan nasu saboda guduwar Sille daga gidan mahaukata, ba'a san ko abin shiri bane watarana yace zai dawo ya cutar da su.
Sai dai duk wannan hidimar da su Ammie, Hajiya Shuwa, RK keyi akan Mamy ba birgeta suke ba, kullum cikin zaginsu take a zuciya da tsine musu, kawai dai ALLAH ya ragema aya za?inta ne bata da damar yin wata muguntar gata a tauye babu ?afa babu idanu bata kuma samu haWin kan mai aiki da zatai mata abinda take so ba sai ta ha?ura. To yanzu ma sai ga Uwangale tazo da sabon salon daya karantar da Mamyn cikin sau?i..........
'?

>?#?>?#?Yanzu ne fa Mamy ta shiga ainahin hannun ?an tuwo-tuwo. Uwangale maganin kukanmu=??=??=??=?? @&? @&? @&? @&?



*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*
AJIYAH A DUHU

190

.......A Wan tsakani nan wani irin tsoron Uwangale ALLAH ya dasama Mamy mai girma a zuciya, magana kaWan Mamy zatayi koda bamai zafi ba Uwangale ta mareta, bata isa sakata komai ba a gidan, sai yazam Mamyn ce ta koma yima kanta komai da kanta. Dan su Saheeba babu abinda ya shallesu sai dai su zauna ma suna dariya da kallon drama Win. Karo na farko da Mamy ke addu'ar Aunty ta dawo a gidan kosu AA. Amma shiru kake ji, ko kiran waya Aunty tayi sune suke Wauka su kanainaye su hanata magana, idan kuma sun bata Uwangale na tsaye a kanta da bulala idan ta faWi abinda bai musu ba tana ajiye wayar ta zaneta. Haka ma idan Oum ta kira suke mata..
Kai da abu yakai kukan kure tsakanin Mamy da

120 / 138

Chapters