Advertisements
Chapter 135 Reading Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc Hausa Novels
Advertisements

Ajiya A Duhu Book 2 Complete Hausa Novel.doc

Author :  Billyn Abdul Category :  Complete Novels

Chapter   135 / 138

402K to 405K   out of 412.8K words

dare. Shima Baba Sardauna ne yay kiransu a waya yay musu nasiha sosai data ratsasu....

Washe gari mutanen Kano suka wuce suma da safe saboda jikin Maanal Alhamdullah da sau?i babu wani damuwa sai fatan ?arasa murmurewa. Nibras ce dai ?an uwanta ma sun yanke hukuncin fita da ita waje saboda illar da ?ugunta ya samu.. Sai Oum da itama dai bata jin daWi saboda damuwar tafiyar Mamy data sakama kanta. Dole aka kwantar da ita asibiti itama.....

__________&

Anan Sangaren Hajiya Basariyya rayuwa ta mata zafi sosai. Komai babu daWi. Tun tana tunanin kuSuta a rayuwar Alhaji Balala harta fahimci al'amarin fa bamai sau?i bane ba. Ta rame ta lalace tai ba?i kamar ba ita ba. Tun tana hawayen aikin yin tuwon gidan Alhaji Balala a ranar girkinta harta saba. Jini ko tunda Alhaji Balala ya fahimci na asiri ne ya tattara matansa ya musu tas, da yake shima sun san hatsabibin kansa ne babu arzi?i sukaje suka karya asirin ya cigaba da ragargazar amarcinsa. Sai ga Hajiya Basariyya da ciki. Wannan abu ya sake Waga mata hankali matu?a. Tana tsaka da wannan laulayin jaraba suka samu ba?uncin Maman Yaseerah tazo bibiyar bashin kuWinta. Itama dai Baban su Najma tuni ya tasheta a gidansa ganin iskancinta na ?ara gaba, yanzu haka yaran suna wajen uwargidasa ita kuma ta shiga buga barikinta da hatsabiban yan iskan bariki. Sun kuwa buWe mata ido dan yanzu haka ma sune suka rakota har nan garin da Hajiya Basariyya ke aure. Babu mutunci suka dinga shekama Hajiya Basariyya dariya wai haka kuma duniya ta maida ita? Ita dai bata tanka musu ba, dan tsoro ma suka bata. Maman Yaseerah tace kuWinta take bu?ata. Hajiya Basariyya bata da su, babu mutunci tai waya da wani akan yazo ya sai kayan Wakin Hajiya Basariyyar. Haka kuwa mutum yazo da ?atuwar motar Wibar kaya daga kankia. Akai cinikin kujerunta dake a waje rufe har yanzu babu wajen sakasu, da yake sayen mugunta ne kuWin bai kai ba. Suka kuwa haWa dana Wakinta, haka suka sauke mata katifa a ?asa suka zazzage mata kayanta daga wadrob a katifar suka kwashe komai sukai gaba suka barta da kuka da dana sanin sanin Hajiya Jumai a rayuwarta. Kishiyoyi kuma suka samu nayi da dariya da habaici har suna gayyato matan ?auyen. Aka saka Hajiya Basariyya gaba harda wa?a idan ana luguden daka. Ko'a jikin Alhaji Balala duk da yaji haushin an rage masa jin daWin hawa katon gado, amma tunda katifar na nan ai ba damuwa a Wan shana ai rigijib-jib inji (Hadiza Kabara=??).
Hajiya Basariyya bata gane ALLAH Waya bane sai da aka fara aikin gona. Ashe Alhaji Balala tattara matansa yake kaf da ?a?a da jikoki aje gona aiki. Tana kuka tana komai ga laulayi babu tausayi haka ya sakata a gaba kuwa itama aka tafi. Tun bata iya ba harta zage tana aiki. A wannan halin yayanta da su Madeena daya kwasa suje dubata suka sameta. Kuka su Madeena suka dingayi dan da farko wlhy basu gane Ummy Winsu bace ba ganin yanda ta ?omaje ta tsofe ta fita a hayyacinta. Shi kansa Yayanta ya girgiza. Ga ciki, wlhy da babu ciki sai ya raba auren nan, amma yaya za'ayi da ikon ALLAH. Asibiti kawai suka kaita tai kwana uku, Alhaji Balala nata fushi amma yaya zaiyi. Ta Wan murmure, ?a?anta ya sake siya mata kayan Waki dai-dai zaman ?auyen ba irin wanda ta rasa ba, ya bata jarin yin sana'a. Data kalla yaranta sai hawaye. Ko ma?iyi ya kallesu yasan suna jin daWi suna kuma cikin kwanciyar hankali. Da zasu tafi ta basu kayan kuka kuSewa daddawa sunkaima su Ammie. Haka suka tafi tana kuka sunayi. Bayan tafiyarsu da kusan wata guda Sageer ya tilasta Huznah suka zo suma. Suma hankalinsu ya tashi da ganin makomar Hajiya Basariyyar amma yaya zasuyi. Huznah na kuka Hajiya Basariyya nayi da neman gafararsu ita da Sageer. Da zasu tafi ya kawo alkairin mai yawa yayi mata. Ranta fal mamakin yaushe Sageer ya ji?e haka, ga mota mai ?yau ga kuWi, kallo Waya tai musu shi da Huznah ga Wan yaronsu kamar ta cinye dan kyau tasan hankalinsu kwance suke. Ga Huznah Win ma kamar da ciki a tare da ita. Suma haka suka wuce suka barta cike da jimami dan basu kwana ba.
Labarin da su Madeena sukaje suka bama su Ammie akan halin da Umminsu ke ciki ya Wagama su Ammien hankali sosai. Haka Yazeed ya shiryo shima yazo ya mata alkairi sosai, a ransa kuma ya kudira sai ta Wauketa a garin nan ko bajika koba daWe. Koda ya koma shima ya labartama Daddy komai ko tari baiyi ba balle ya nuna ya jishi, dole ya tsuke bakinsa dan wargi ma waje yake samu......

& Bisa tirsasawar Daddy su Basira duk sun fidda mijin aure suma. A yanzu haka an tsaida rana harda Yaya Yazeed da Khadijah da suka daidaita kansu. ?an uwa nata farin ciki da wannan al'amari. A tsakanin ne kuma Amaal ta haihu. Kasancewar Maanal na asibiti bataje ba, hakama Oum na fama da kanta. Sai Ameerah da Najma. Su Umma ma sun zo daga Kano. Ta haifi namiji abinta.

_________&

Su Mamy an isa Kano lafiya, gidan babu laifi da Wan ?yansa gwargwado amma dai ?arami ne dai-dai zaman mutum Waya. Su Saheeba da sunce bazasu zauna ba. Dan haka suka wuce gidan Babansu wai can zasu zauna. Haka suka wuce can kayansu ma can aka sauke.
Kamar gaske matar babbansu ta tarbesu da farin ciki da murna. Suko suna sha mata ?amshi saboda ganinta ?arama. Basu san kwantar musu da kai tayi ba kawai. Tun suna nuna isa har suka fara sakkowa ganin ita babu ruwanta, shima Babban yana sake ji da su saboda tausayin halin da suke ciki, duk da ya yarda su masu laifi ne dan har kiran Abah yayi ya sake bashi hakuri da su AA. Amma yayi imanin duk laifin uwarsu da yar uwarsa Turai ne da Mamy da suka Worasu a kan hanyar banza.
Da wayo da wayo sai da sabbin ?awayensu suka sakasu salwantar da komai da suka zo da shi, na kayan Waki da sutura da duk wani kayan adonsu. Sai da komai ya ?are aka fahimci harkar shaye-shaye suka shiga, aiki matar babansu tace bazata zauna da su ba dan sun fara mata ?an sace-sace. Rikicin yau da ban na gobe daban babu arzi?i suka bar gidan dan baban nasu ma ya daina raga musu. Komai matarsa ta gaya masa sunyi yarda yake dan ta fisu gaskiya, duk kuma rantsuwar da zasuyi baya saurarensu sai yace dama haka suke da ba?in hali kamar uwarsu. Ganin fa abin bana wasa bane babansu na neman tsine musu suka tattara suka koma wajen Mamy da tuni Uwangale ta gudu ta barta. Sai wata mai aikin da su Babban Yaya suka Wauka mata dan sun zo har sau biyu sun dubata. Sai dai ranar suke suwa su koma dan har yanzu Maanal da Oum na asibiti. Amma suna saka ran a satin nan za'a sallamesu. Idan kuma an sallamesun ?asar zasu bari dan samu su huta zuwa nan gaba sa dawo ko hakan zai sa su sami sau?in zuciya dana al'amura.

Da farko Mamy ta?i amsar su Saheeba. Sai da Aunty Babba ta saka baki tare da mata nasiha sannan. Dan Mamyn kam yanzu ba tada bace. Tayi laushi sosai kawai dai har yanzu ALLAH bai bata ikon kwantar da kanta ta nema gafarar kowa bane. Amma har kiran Oum take taji yaya jikinta. Ta kuma kira AA a haWasu da Maanal itama tai mata yaya jiki. Hakan na Wan saka musu jin farin ciki a ransu. Suna kuma mata addu'ar shiriya da ?ara gane gaskiya koda anan gaba ne kafin dai lokaci ya ?ure mata..
Dawowar su Saheeba gidan kuma sai rashin jituwa ya shiga tsakaninsu, kullum faWa ita da su. Wani lokacin tana zaginsu suna zaginta. Basa raga mata sam. Bata isa sakasu aiki ba. Dan kai tsaye zasuce bazasuyi ba. Ga yawon darensu na tsiya. Ga kudi data ajiye su sace. Tun tana iya daurewa harta fito fili ta sanarma su babban Yaya saboda wani duka da Saheeba da Nuratu suka haWu suka la?aWa mata saboda Saheeba tayi shaye-shaye tazo ta musu amai a falo Mamyn tayi magana.
Babu ma wanda ya sani babban Yaya ya zo Kano. Shi kansa yanda yaga su Saheeban sun koma sai da mamaki ya kamashi. Kallo Waya zaka fahimci shaye-shaye suke yi. Basu da wata maraba da karuwai wlhy. Ga uban ?arin gashi, ga ?arin farce dana girar ido. Idanu duk sun juye saboda shaye-shayen ma na hauka sukeyi komai aka samu Worawa ake yi. Aiko ya lakaWa musu shegen duka ya korasu, ya kuma saka yan bijilanti duk randa suka gansu a jikin gidan ma su musu dukan tsiya. Sai ya samu mijin Aunty Babba ya ro?esa akan ta dawo nan ta zauna tunda dama can gidan ya musu kaWan ita da kishiyarta, yaranta kuma sun kaisu karatu waje shi da su yaya Fawzan ita kaWai take zaune. Sai kawai ya amince Aunty ta dawo nan kusa da Mamy Win. Aka samo musu mai tayasu aiki. Duk wata zasu dinga aiko mata da maganinta na HIV, ?afa da ido dai an riga da an rasa su sai ha?uri. Koda ya koma Abuja bai bama kowa labarin nan ba. Dan yanzu har kunyar kawo zancen Mamy suke gaban Abah da Oum dama matansu. Abin farin ciki kuma ya samu ma an sallami Oum da Maanal daga asibiti, bayan jiyyar kusan sati uku. Dan Maanal gaskiya ta wajigu matu?ar wajiguwa. ALLAH dai ya ?addara tana da sauran kwana ne a gaba da yanzu wata maganar akeyi.........
'?
*_Typing=???_*








*_=???AJIYA A DUHU....=???_*




*_Bilyn Abdull ce >??

*_(P3REP 'DDQNGP 'D1QN-RENpFP 'D1QN-PJE_*
_Da sinan Allah, Mai rahama, Mai jin ?ai._

*_My TikTok account =?G?_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram=?G?
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R


_Duk wanda bai fallowing Wina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama=??=??
*_BOOK 2_*
AJIYAH A DUHU

214

.......A washe garin da aka sallami Oum da Maanal suka bar Nigeria gaba Wayan su. Kuma da alama wannan tafiyar mai daWewa ce. Dan ?asar Chaina suka dira. A block Waya suka kama wajen zama. Sai dai kowa da apartment Winsa, amma floor Waya suke kuma a jere guda huWu reras. Kowanne a nashi akwai bedroom Waya, kitchen, falo, sai wajen karatu. Komai dai tsaff, babu takura babu gajiyawa. Tsarin kuma duk iri Waya ne. Duk a gajiye suke, dan haka kowa yaja matarsa suka shige nasu. Oum ta amshi ?an biyu ita da Abah, idan akai musu wanka a maido su. Hakan ya bama AA damar jan hannun Maanal suka shige nasu suma. Dan shekaran jiya ?iri-?iri da aka sallamosu asibiti ta?i zuwa sashensu ta wuce wajen Oum. Haka ta barshi ya kwana shi kaWai, sai a jirgi ne suka zauna waje Waya. Suna shiga ya maida ?ofar ya rufe ya mannata a jiki. Kallonsa take fuskarta babu walwala sam, ga idannunta sun Wan ?ara fitowa saboda ramar da tayi ta jiyya. Shima kallon nata yake cikin wani yanayi mai wahalar fassara, kafin a hankali ya motsa lips Winsa cike da raWa ya furta,  Besty bazaki yafe ma Ajwaad ki daina fushin nan ba? .
Kanta ta Wan kawar gefe kaWan, idannunta na tara ?walla, ALLAH har yanzu ta?i daina ganin yanda yake dukan Nibras a idanunta da yanda take tsirara sai kimono a jiki, da yanda ta dinga ro?onsa akan yaransu amma taurin kai irin na mutumin nan ko. Hummm. Hannu yasa ya dawo da fuskar tata inda yake, sai kuma a hankali ya matsar da tashi gab yana busa mata numfashi. Cikin sake sauke murya ya ce,  Yanzu minene laifina anan? Ko sai yanzu kike jin kishi? .
Hannayenta biyu ta saka ta turashi, dan wlhy da gaske fa sai yanzu take jin kishin abinda Nibras Win tayi, dan tun bayan lafawar komai zuciyarta ta kasa nutsuwa, tana matu?ar son tasan minene ya faru har yay ma Nibras dukan nan, musamman data ganta tsirara sai kimono a jiki. Amma babu wanda ya gaya mata komai har shi. Bata zarginsa, kuma ai tasan Nibras Win ce ta kawo masa kanta, amma idan ta tuna ko wani abu ya faru zafi zuciyarta take mata. Yanda take turashi shi kuma ko gezau baiyi ba ya sake fusatata tasa hannaye biyu tana dukan ?irjinsa. Tsayawa kawai yayi yana kallonta yana danne dariya da ?yar, sai da tayi iya iyawarta har ta gaji dan kanta ga hawaye sannan yay murmushi da kamota ya rungume tsam a jikinsa. Sai ta sake sakar masa kukan kawai. Baice mata komai bai har tayi shiru dan kanta sai a jiyar zuciya kawai take saukewa, sannan ya Wagata cak ya nufi bedroom, saman haWaWWen gadon Wakin ya kwantar da ita ya fita ya jawo akwatinsu Waya jal sai dai babba ne sosai, sai bag Winta da bag Win laptop Winsu ita da shi dan aiki kam dole a cigaba da yinsa daga nan. Har lokacin tana a kwance inda ya barta. Baiyi magana ba ya shiga bayin ya dudduba sannan ya dawo bedroom Win ma ya dudduba, ya fita falo da ko'ina na gidan ya sake dawowa ya shiga bayin ya haWa ruwa a jacuzzi mai Wumu da ?amshi sannan ya zo ya Wagata ya cire mata kaya ya cire nashi ya wuce da ita. Cikin ruwan ya saka su, a tare suka sauke ajiyar zuciya. Sai kuma yanda ya Wan ?an?ameta ta Wago tana kallonsa. Murmushi yay mata ?asa-?asa fuskarsa a shagwaSe ya ce,  Please Besty ki huce mana .
KafaWa ta ma?e masa tana tura baki da kauda kai. Ya ri?o haSarta cike da lallashi yace,  Mizan miki ki huce to? .
 Ka faWa min abinda ya faru a ranar .
Ajiyar zuciya ya sauke, sai kawai ya shiga bata labarin komai bai Soye ba. Kai tsaye ta ce,  ALLAH ya isa ban yafe mata hawa min jikinka da tayi ba wlhy .
Dariya ce ta kusa kufcema AA ya danne da ?yar, sai kuma ta kalleshi itama kamar wata yayarsa ta ce,  Kai ma ka kalleta ko? .
Kansa ya girgiza mata yana sake rungumota.  Ai har abada babu wata surar jikin mace da zata sake birge Ajwaad balle ta zame masa abin kallo in sha ALLAHU Besty. Kiyi ha?uri Besty mubar maganar nan wlhy ko tunawa bana son yi dan ?ona ni take matu?a, ina jin nauyi da kunyar Yaya Fawzan da ke kanki da yarana, shiyasa har yanzu ji nake ban gamsu da abinda nai mata ba ma .
Karon farko Maanal tayi murmushi tana shafa ?irjinsa cike da kulawa. Sai kuma ta tausasa murya ta koma lallashinsa. Sun jima a bayin kafin su fito, haka ya taimaka mata tai shirin barci shima yayi, basa jin yunwa dan sun ci abinci a jirgi gab da zasu sauka. Dai-dai nan bell tai ?ara, yasan su twins aka kawo dan haka yaje ya amso su hannun Abah, sai coffee da Abah yay musu order shima suma su Babban Yaya sun amshi nasu. Sukaima juna sai da safe ya koma nasu shima ya shigo. Bayan sunsha coffee Win Maanal tayi feeding su twins kwanciya kawai sukayi duk da AA na cikin yanayin bu?ata haka ya daure....

__________&

Satinsu Waya kenan a Chaina, Alhamdullah jikin Maanal kuma yayi sau?i sosai, dan anan ma ta sake ganin likita sun tabbatar musu komai kuma normal. Shi AA ma ranar baya nan sunyi tafiya da abokinsa prof.. wani program. Oum da dama tafe take da kayan gyaranta sai tayi amfani da wannan damar ta shiga gyara Maanal ta jiki data ciki. Dan danan ta ?ara murjewa da gogewa dama ramar nan da tayi duk ta ciko abinta, sai wani glowing take kuwa Masha ALLAH. Ameerah da Najma suka sakata gaba, wai da alama Yaya AA na dawowa ba sau?i za'a sake samo twins. Tun tana ?yalesu harta fara ramawa itama. Kai daka gansu kasan suna cikin farin ciki da ?aunar juna ta ha?i?a. Su twins sam basu da taka maiman wajen zama. Barci kawai ke kaisu wajen Maanal.
Kwanan su AA takwas suka suka dawo. Kallo Waya da Maanal tai masa ta fahimci babu sau?i, dan bai Soye mata ba ya fito fili ya nuna mata yana cikin wani hali. Murmushi kawai tayi batace komai ba, sai da ta taimaka masa yaci ya ?oshi ta jashi bayi yin wanka. Anan ne fa ya kasa jurewa aka fara sakin layi, ?arshe dai babu arzi?i aka kammala wankan aka fito. Daga nan ne fa labarin ya canja. Haba ai yayi ha?uri, kusan wata biyu.
Yako tabbatar mata yayi ha?urin, dan taji a jikinta har sai da ta koma masa kuka da magiya. Amma ina sai da ya tabbatar ya samu yanda yake so sannan ya koma lallashi da ban ha?uri, itako tana zuba masa shagwaSa. Tun daga ranar aka buWe sabon shafin amarci. Kullum suna sake mannema juna, kowa ?o?arin ?yautatama Wan uwansa yake. Kamfani kuwa suna tafi da komai yanda ya dace daga nan tamkar suna a gida Nigeria. Ga yaransu sunyi ?yau sosai kamanin iyayensu na sake fitowa a tare da su.
Haka suma su Babban Yaya komai Alhamdullah, daga Sangaren aiki har samun soyayya wajen matayensu, dan daga Ameerah har Najmah suna iya

135 / 138

Chapters